Showing 9001 words to 12000 words out of 107296 words

Chapter 4 - UMMI A'ISHA(THE MAGNIFICIENT) COMPLETE

22 Aug 2024

7693

yakai hannunsa kan kafadarta,,my hafsat gwaggo tayanke min decision din da haryanxu nakejin xuciata tayi nauyi,my hafsat wai Ma....magajiyan inno fanta fa gwaggo tace naje na aura,saboda Allah wannan matar fa,,beside bataganin girmana bataganin mutuncinki,infact bata ganin kan kowa da gashi,she's very disrespectful wai kuma ita yarannan suka sa gwaggo tahada dani I wonder nawa tasiya bakinsu daxasumin wannan mummunar sakayyar arayuwa ...

"Dukda sunan dayafada ya girgixa hafsat kwarai matuka ,Dan sosai tasan halin magajiyan ,sarai hartafi su surayya mugunta da munafunci,hassada da kuma annamimanci,tunkafin mijin magajiyan yarabu da ita take takalar hafsat din da fada sosai take Gaya mata bakaken maganganu masu zafi masu cin rai,bata tashi ci mata mutunci se a taro(biki,suna ,mutuwa),datemakon addu'a hafsat tasamu tadanne xuciarta dukkoda wani bakon al'amari daya xiyarci xuciarta Wanda tasan fargabace hade da kishi,amma Yata iya adole takakaro murmushi Sannan tace"Haba hayatee Dan wannan kakejin zuciar ka wani Iri?!to Dan Allah Ina rokanka hayatee ka kwantar da hankalinka kasawa zuciarka salama(peace),Sannan tai yar' daria da dan haka kake fadin mucanxa gari?! To wannan ai bawani abun daga hankali bane hayatee,abin kasa goshinka akasane kaiwa Allah godia bisa wannan babbar kyauta da yai maka,samin aure a wannan lokacin ai sa'a ne kuma gashi kasamu kana neman gujemata,

"Kuma de ina adduar Allah yasa tashigo a sa'a,muxauna lapia harmukoma ga ubangijinmu nawa rayuwar take ma ?!,Dan Allah karmu jefa kanmu cikin MATSALAR RAYUWA(littafin Nafee Anka tare dani miss xoxo)wannan ni inaganin WANI HASKE (littafin Ummi_Aisha)ne daga Allah ,karkai wasa dashi,tunda ba'a gujewa maganar iyaye musamman Uwa ,Wanda sau uku ana fadarta,insha Allah babu Wata matsala daxata faru komai xa'ayi cikin lapia agama lapia da yardar Allah,

"Capt Adam yai ajiyar zuciya sosai maganar hafsat taratsa jinin jikinsa,hannunsa yasa yakamo hannunta yasa cikin nasa,"my hafsat Allah yamaki albarka hakikanin gaskia NI DA KE(littafin pherty) HADI DAGA ALLAH(littafin Al'eeman)ne Ina kuma alfahari dake akoyaushe,my hafsat bansan dawanne baki xangode maki ba,tunba yauba kike gayamin kuskurena kuma kike dorani ahanyar gaskia Allah yasaka maki da alkhairi yacika mana burinmu damuke rokansa a kullum amin.

"Hafsat tai murmushi Wanda yake Kara bayyanar da kyakkyawar fuskarta take dimples dinta suka lotsa,"tai fari da idonta,nice da godia hayatee,thanks for everything,"Sannan tai kasa da murya , inasan inje gidah ance murjanatu taxo amma seka yarda fa,"Capt Adam yasa hannu Yana taba dimples dinta Dan suna matukar birgeshi sosai ,Sannan yace Allah yakaymu my hafsat yaushe xakije?!"hafsat tai murmushi nextweek nakesan xuwa,"Capt Adam yace bakomai my hafsat nabaki dama,kina matukar birgeni yadda kike fadan haka,wallahy Ina alfahari dake,kinsan karar da IMRAN yakawomin kenan wai sajeedah matarsa namatukar bashi matsala,

"Wai bata tanbayrsa unguwa se ranar daxata,shine ingaya maki Wata yar' Kasan layin nasu kawar tace tana bata shawara kan hakan datake ,haryashigo kwanaki yaji sunayi,you knw wht?!"Hajia hafsat takada kanta a'a seka fada hayatee,"Capt Adam yace hmm yarinyar xe aura upper week daurin auren,

"Hafsat tabude baki,kan bala'i amma sajeedah bata kyauta ba,Kasan dama ni bama wani shiri da ita ,kullum taita mita wai Bana xuwa itake yawon xuwa gidannan,"Capt Adam yace gwara haka ae dabakya biye mata ,yanxu gashi ai yawon fitanta yaja mata Karin kishiya,

"Hafsat tai daria Allah de yayi ne ,Toh Allah yahada kansu,"Capt Adam yace Amiin ya rabbi

"Haka sukaita hiransu Sannan suka nufi daki donyin bacci dayake dare yayi sosai,,,,

"Kwana biyu da dawowar Capt Adam daga kaduna suna zaune a center carpet dake parlor din ga kamshin abinci Se tashi yake,foodflask ne kala kala ,abinde ke kan plate din dasuke cin abincin yabani damar sanin,vegetable spaghetti ce dataji hanta,gefe daya kuma sauce ce na minced meat da kuma hadadden salad Se soup din mushroom....se gefe daya kuma lemonade ne dayashe madara karara dashi yasha kankara,,

"Wayar captain Adam ce tafara ringing,kamar baxe daukaba sekuma yasa hannu yadauka ,ganin me Kiran nasa da sauri yadanna okay yasakala a kunnensa,



•✨•
9


"Salam alykm Yaya Yaya barka da rana,Ina yini Ina gajiya?!

"Alhaji sameer yace wa alaykm Salam Adam,lapia qalau Wlhy Yaya jikin hafsat din dafatan tasamu sauki?!

"Capt Adam yace taji sauki Yaya,Alhamdlh ,Yaya su Aunty zainab dasu little Mus'ab??

"Alhaji sameer yace lapia qlau Wlhy ,dama gwaggo ce tabani sako nafada maka nayi nayi da ita kanta fadama da kanta ma taki,saboda gaskia nibansan abinda hafsat xataga kaman da hannuna ciki,

"Capt Adam yai saurin kada Kansa yadda kukasan Alhaji sameer din naganinsa saboda tsabar girmamashi dayake,,aa bakomai Yaya,hafsat tasan ba hannunka ciki duk namata bayani kuma tunkafin nafada mata Ma tafahimta tasan sarai wannan shirin su surayya ne gwaggon Ma ba hannunta ciki,

"Alhaji sameer yace Toh Masha Allahu,kanaji Adam bayan tafiyarka washegari kenan gwaggo tasa gidado driver yabugo invitation cards (katin daurin auren)na bikinka ,jiya takirani tace naraba,na nuna mata nibansan abinda xanshiga ciki saboda kada hafsat taxata hadda hadin kaina,caraf surayya da sadeeya suka karbi xance kansu xasu raba dakansu sunji sunyadda dukkoda nadaurin aurene kawai,

"Nikam bance kala ba nabari suka dauka suka tafi,shine gwaggon tasake mikomin wasu katin wai narabawa mutanena da kuma abokananka na kaduna,harna juya xantafi tace ga wasu katin inbawa danbaxau driver dinta yakawo maka,Toh shaf na sha'afa wallahy danni a mota ma nabarsu seyanxu kaga nashiga gida nafito xanje company ,seganin katina nai a bayan mota a xube yanxu Yaya naturo danbaxau yakawo koxaka xo kakarba tunda naga wannan asabar dinne daurin auren,

"Capt Adam yai Shru Sannan yai ajiyar xucia'babu komai Yaya kabar katinan nan kawai kace ka aikodin,danni gaskia babu Wanda ma xangayyata ni,

"Alhaji sameer yai Daria calm down Adam nasanka da BIYAYYAR IYAYE(littafin ummi_Aisha)saboda haka kada wannan bakon al'amari yasa kai watsi da abinda kadade kana aikatashi ake kuma sa maka albarka kan hakan,bance kabi abokananka duka ka kai masu katina ba kawai de kadauki wasu tsirari daga ciki kabasu ,yaxakai tunda Allah yarubuta hakan?!!komai mukaddarine daga gareshi,kuma de wannan mata da aka hadaku aure yar'uwarkace da mahaifiyarka da tata uwarsu daya ubansu daya,first cousin dinkace kuma JINI DAYA(littafin anee lurv)kadubi girman xumunci katsaida tunanin ka guri daya katsya ai abinnan lapia agama lapia kanaji Adam?!

"Capt Adam yace inajinka Yaya yaxanyi?!tunda haka Allah ya kaddara rayuwata,

"Alhaji sameer yace Yawwa Sannan abu nabiyu kashigo kaduna gobe in Allah yakymu ,semusan yadda xa'ai na kada ahadasu waje daya da hafsat,dan abu baxe Kyau ba,mu roki gwaggo tayadda karaba masu gidah ko ita kabarta Ma nan kaduna gidanka na kawo ko yakace?! "

"Capt Adam yace naji Yaya hakan xa'ai Allah yakaymu goben lapia ,nagode Allah yasaka da alkhairi ameen,

"Alhaji sameer yace Amiin ya rabbi nine da godia,Se Allah yakaymu goben,agaidamin da uwargida Sarauta mata,

"Capt Adam yai Daria xataji insha Allah ,agaidamin dasu Mus'ab kila goben Ma nabiya,,,
Sannan sukai sallama ,,Capt Adam yacire wayar daga kunnensa ya aje a gefe,

"Sannan yai ajiyar zuciya ahankali yake fadin Allah kashiga tsakanina dasu surayya wannan bala'i dasuka sani ciki Allah kaimin sakayya,

"Hafsat tai shiru ,Sannan tai magana kasa kasa,hayatee kayi hakuri please komai yafaru da Bawa mukaddarine daga Allah saboda haka ka fawwala masa al'amuranka,yan'uwanka ne Ina rokanka da Allah da kada ka rikesu cikin zuciyarka,addua xakai ta masu Allah ya shirye su ,

"Capt Adam yadago idonsa Yana cije lebansa nakasa 'baxaki ganeba my hafsat wai katin daurin aurene gwaggo hartasa anbugo anfara rabawa kuma nima tabayar abani shine Yaya sameer yace lalle naxo kadunan gobe kanmu shawo kan gwaggo tabari na aje ita magajiyan a gidana na unguwar kawo kaduna,daurin auren ranar asabar ne,ranar daxan koma Abuja kenan ranar dakuma xaki gidah..

"Hafsat tai shiru Sannan tadan dafe Haba,bakomai hayatee aiko guri daya xamu iya xama,"Capt Adam yamike Yana gyara rigarsa 'aa my hafsat baxeyiwuba Wlhy,hakurin ki yayi yawa,Nina fita wurin dr NAUFAAL senadawo,

"Hafsat tamike Tana Daria tuba nake hayatee na kaina bisa wuya,mexakaci da daddare Toh?!

"Capt Adam yabata peck a kumatu,I have no choice my hafsat ,duk abinda uwargida ran gida tadafa shi xanci,ni aibanda xabi,naxama rakumi da akala seyadda kikai dani,,,Sannan yafice Yana Daria...

"Hafsat tai murmushi tareda daga hannayenta sama ya Allah kabarmun mijina,Adam dina bahadeje daya tamkar da dubu,sanann tashafa a fuskarta ,,,,,


nanahafsat.wordpress.com




WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO👄
[4/18, 11:56 PM] Asy Khaleel: •✨UMMI_A'ISHA✨•

(THE MAGNIFICENT)
10

©•MISS XOXO
👄

DEDICATED TO
UMMI_A'ISHA👌🏼

•✨•✨•✨•✨•✨•

SAFIYA TAGARI;
"Washegari da safe Capt Adam yagama shirinsa tsaf cikin manyan kaya kirar bauchi style kalar sararin samaniya(sky blue)kenan,sosai ya mirza Karin hularsa,Sannan yahau fesa turaren Hugo boss Dana shafawa ajiki na company din ulul alharamein ,tuni kamshin yafara gauraye ko'ina nadakin,

"Hafsat ce tashiga dakin dauke da Vaseline a hannunta,cikin shigar doguwar rigar material pink me ratsin blue dinkin Senegalese sosai dinkin yamata Kyau kamar Wata yar' budurwa,ahankali takarasa kusa dashi fuskarta dauke da fara'a "hayatee ga Vaseline din kokaga chapette din naka?!

"Capt Adam yajanyota jikinsa bayan yasa hannu acikin Vaseline yalakato kadan yadan Sa a lebensa saboda bushewa,sakala hannunsa yai tacikin waist dinta suna masu kallon kansu ta mudubi,"ahankali yace magana kasa_kasa 'banganshiba my Hafsat ,amma tunda nasa Vaseline dinma it's okay,Kinga yadda kikai Kyau kuwa my Hafsat ?!"Hafsat tai murmushi tana kallon dinkin Sannan ta kalleshi 'hayatee opposite site kake nufi aikaine kaikyau har nake tsoron kada 'yammatan kaduna su rikemun kai,

"Capt adam yai daria,haba haba,me 'yammatan kadunan suke dashi Wanda baki dashi?ai kece Ma kika fisu tunda har idona yarufe bana ganinsu dakyau seda nai tattaki har Kano sannan naga LIFE PARTNER dina,my Hafsat ke kadaice acikin zuciata karkisa waswasi azuciar ki wallhy xuciata mallakin kice kuma kinsa padlock kinrufe babu Wadda takai matsayin tashiga,(please the 'YAMMATAN kaduna remark was a joke ,,kaduna ladies wasa nake fa..lol)

"Hafsat tai murmushi sannan tasa hannu tana Shafa cyboc dinsa hayatee I just dunno what to say you take care of me like a little child and appreciate me despite my flaws....."Capt Adam yasa hannunsa kan lebenta alamar tai shiru ahankali yake girgixa Kansa Sannan yasa hannu yarungumota murya kasa kasa yake radakamata'you have accepted me the way I am and love me every seconds of everyday ,Sannan ya tsugunna har kasa Yana fadin I am one lucky man,I married the best woman on earth."Hafsat tasa hannu tadagoshi Sannan Tarungumoshi tsam tana hawaye 'inagodia hayatee kaisauri kutafi kada rana tayi Allah yakaiku lapia yadawo mindaku lapia,"Capt Adam yace ameen Sannan yaisauri yasa hannunsa Yana goge mata hawayen,
"Dakyar sukai sallama da junansu Sannan Capt Adam yafita jirgi driver yadaga suka tafi,(Allah kabar soyayya,Allah kabarmu damasu sonmu..Ameen ya rabbi!

"Bayan tafiyarsu Capt Adam ko minti 20 ba'aiba kanwar Hajia Hafsat taxo wato murjanatu amma anace mata mjay' itace karamar kanwarsu adakinsu Batai aure ba kwanannan tadawo daga capetown(South Africa)inda tahado bsc dinta akan karantar dan adam dakuma yadda suke rayuwa acikin doron kasa(Sociology,study of man and the society in general for eg British industrial revolution)kamarsu daya sede ita bakace,

"Da sallamarta mjay tashigo gidan tana murmushi 'ina Yaya Hafsat din ga mutan capetown sun Iso tunda baki xoba ,ninaci girman naxo,

"Hajia Hafsat tana daki taji kamar magana,fitowatai tana kallon parlor,hango mjay tai,dagudu tanufeta Tana daria Sannan tarungumeta tana murna,mjay Kinga yadda kika Kara Kyau harwani Fresh kika sake wallahy,"mjay tai daria Kai Yaya Hafsat wallahy inanan da bakina,sannan nifa badanke nazo ba Dan Yaya Adam nazo ,Jia ma munyi magana dashi ta whatsapp amma bance mashi xanxoba suprise namashi ,yananan ko yafita cux naji gidan shiru?!

"Hafsat tai murmushi Wlhy kinyi Kyau,sannan yayan naki yaje kaduna yanxunnan kukai 'sabani,"mjay tace kassh bakomi nasake xuwa ,sannan tasa hannu tarufe baki tareda sunkuyawa kasa bamu gaysa ba ashe "Ina kwana Yaya Hafsat naga sha biyu saura?!ya gida Yakomi ?!

"Hafsat tai murmushi lapia qalau Alhamdulillah mutan capetown ,I heard kinfito da first class ko?!to Allah yasanya alhairi yasa a amfana da abin da'aka karanta ,Allah yasa albarka aciki amin,

"Mjay takoma kan kujera da xauna Sannan tace "amin ya rabbi nagode Yaya Hafsat ,Ina haule ne?!"Hafsat takalli kofar kitchen dayake kofar tana kallon parlor din ,sannan tadan daga murya'"haule,haule,'

"A million haule ta iso parlor din da serving spoon a hannunta,"mjay takyalkyala daria a'a haulatu kenan kice naxo a Dede kenan tunda naganki nasan da akwai aroma medadi balle danaga serving spoon dinnan hakan yatabbatarmin dayau akwai dibar beta kenan,Ina kwana haule yagida ya aiki?!

"Haule tawashe baki tana murmushi lapia qalau murjanatu yakaratu ya gidah Yasu Hajia?!tabbas yau xaki kwashi girki,yanxu kika iso ne banji shigowar kiba ?!

"Mjay tai murmushi ehh gaskia bandade daxuwa ba,lapia qalau Alhmdlh su Hajia sunanan qalau ..."Sannan tadakko Wata leda agefen jakarta da alama kayane kunce sekuma riga doguwa aleda sabuwa dal,tamika mata ungo haule gashi bayawa arika sawa nikwa Ina wannan bazawarin naki iliyasu?!

"Haule taduka takarba a'a murjanatu kullum da wahala Toh Allah yasaka da alhairi nagode sosai Allah yakara budi, iliyasu yanxu.....

"Hafsat takarbe xancen tana Daria mjay angode sosai,iliyasu yanxu basa tare da haule ai,yanxu yar'gida xamuyi fa,

"Mjay tace kai amma kwa ilyasu akwai kirki Wlhy banso kuka 'bataba yanxu waye nagidan a 'kauye ne?!

"Hafsat tace wane kauye Ina haule ta yanxu a birni xata xauna itama'hadin gida xamuyi da modu kinsan shima bara matarsa tarasu dama kuma bata haihu ba,

"Mjay tamike harda 'yar rawarta dole mukwaso shoki ranar kenan toh Allah yasanya alhairi yasa ayi damu,wallahi kundace dama gashi bafulatani kekuma babarbariya(kanuri)abu yayi kenan,

"Haule tai murmushi Sannan tace Amiin,barin je kitchen kada girkina yakama,Sannan takoma bakin aiki ...

"Mjay tace Yaya Hafsat yanaga mood dinki yacanxa tunda naxo nakesan intambayeki?!!!

"Hafsat tai murmushi Bakomi mjay kawai de banjin dadine,

"Mjay ta girgixa kanta Haba Yaya hafsat nasanki fiye da yadda kike xato bahaka kike ba Wlhy,Dan Allah Yaya Hafsat menene nifa kanwarkice atleast idan wani abun ne yake daminki senabaki shawara,

"Hafsat tai murmushi Kai mjay akwai ki dasan jin kwakwaf,bawani abun bane fa,sanann Hafsat takwashe xancen auren tagaya mata tareda doriyar ranar asabar ne daurin auren ma,

"Mjay tabude baki,tohh toh Allah yashiga tsakanin nagari da mugu nifa shysa Bana shiga harkan sisters din Yaya adam,kawai inbanda jealousy ba abinda suka sa agaba,amma babu komai akwai Allah ,gaskia Yaya Hafsat hakurinki yayi yawa upon all this years kice baxaki fada ba,toh Allah ya kyauta ,Allah yasa yadda kikai hakurin nan yabaki abinda kike bukata dunia da lahira...Sannan tadakko Dayan ledan dake Jakarta tamikawa Hafsat din,perfume din ciki na Yaya Adam ne,

"Hafsat tabude ledan taxaro wani kwali jakace maroon aciki da takalminta designer ne kirar company din guess,sosai Hafsat tabude baki tana murna"awww mjay thank you so much,wannan designer nane fa meshegen tsada gashi keda kika je karatu,Nagode sosai mjay Allah yabaki miji nagari,"mjay tai murmushi Amiin ya rabbi,I'm very glad you liked it,"Hafsat tadaga jakan tana kallo I really loved it sunyi Kyau beyond Wlhy...Sannan tadaga kwalin turaren arubuce boldly Elizabeth Aden ,nanma Hafsat taita godia danshima designer na ne,

"Haka sukaita hiransu suna bawa junansu sisterly advice,


KADUNA

"koda su Capt Adam suka Isa kaduna gidan Yaya sameer suka fara xuwa,sosai matansa suka karbeshi hannu biyu,dayake Yaya sameer din matansa biyu tabiyun Ma 'yar Kano ce,

"Site din alhaji sameer din yanufa inda amaryar Hajia nafeesa ce a duty ,sosai takawo masa lafiyayyen abinci da drinks ,tare sukaci da Yaya sameer dinma ,seda sukai sallah Sannan suka tafi can gidan nasu inda gwaggon take,

"Bayan sunje sosai Capt Adam yagaida mahaifiyar tasa seda yai ruwa yai tsaki Sannan gwaggo tasakko daga fushin datake,harde tace masu tama hada Kayan lefe da kudinta tasa dangi sunkai gidansu magajiyan,Sannan sukai hira daga baya kuma,

"Gyaran murya Yaya sameer yai Yana kallon Capt Adam ,Sannan yace gwaggo wurinki mukaxo munasan mudanyi Wata magana dake,

"Gwaggo tace toh,Allah yasa wadda xan iya ji kuma Inyadda da itace,

"Capt Adam yace insha Allah xaki Ma yadda da ita gwaggo ,

"Alhaji sameer yakaikace murya yace 'gwaggo dama xancen aurennannne,akan inda magajiya xata xauna ne,munyi magana inda ni nashawarci Adam gashi,kan cewar ya ajiye ita magajiya anan gidansa dake kawo,shine muke Neman yardarki gwaggo,

"Gwaggo tadauke kanta kamar baxatai magana ba sekuma tace......




nanahafsat.wordpress.com




WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO
[4/18, 11:56 PM] Asy Khaleel: •✨UMMI_A'ISHA✨•

(THE MAGNIFICENT)
11

©•MISS XOXO
👄


DEDICATED TO
UMMI_A'ISHA👌🏼

•✨•✨•✨•✨•✨•

"Gwaggo tadauke kanta kamar baxatai magana ba sekuma tace,'yaxa'ai kabarta anan gidanka dake kawo bayan kaida aiki yamaka yawa baka cika xuwa ba,kuma naga gidan naka dake Kano da girmnsa xeci mata hudu,ballantana biyu..'ita hafsatun ce takitsa maka haka kenan,

"Da sauri Yaya sameer yatari numfashinta'uhm uhm gwaggo Wlhy bahaka bane,Hafsatu ma batasan da wannan zance namu ba,wallhy nine nabawa Adam shawarar hakan saboda zaman lapia,gwaggo tashin tashina batada dadi,abinda za'axo ana dana sani,gwara tun wuri ai maganin lamarinnan,kuma gwaggo kinga gidannan dake kawo kato ne shima harda bangaren baki kusanma ince xedanfi na kanon girma,amma idan har kunfison magajiyan taxauna akano ita hafsatun se'ai mata magana tadawo nan kaduna,

"Capt adam ya sadda Kansa kasa ahankali yace gwaggo kixabar wa magajiyan inda kikaga yadace ta xauna,ita hafsat batada matsala ma gwaggo,

"Gwaggo ta daure fuska wannan hafsatu tagama dakai,ashe de abinda su surayya ke fadi Se yau nagasgata haka,dama tashirya makircin ta dole tanuna ba matsala mana,Sannan tai ajiyar zuciya 'nayadda ka aje magajiyan anan garin,Allah yasa hakane yafi alkhairi,ita kuma waccan Allah ya 'kwatoka daga hannunta ameen,

"Bayadda captain adam ya'iya adole murya adakile yace ameen,Shide yasan Hafsat bataxuwa gurin boka ko Malam,takanyi sallolin darenta ta roki Allah bukatunta,Uwa uba biyayyar datake masa ita tasa ra'ayinsu yaxo daya kuma suke xaune cikin lumana,karamci dakuma dattako..kuma gwaggon tasan da haka ,annamimancin dasu surayya suka haka suka Shuka akanta duk shi ya haifar da abinda take fada yanxu,amma kowa yasan duk cikin surukanta(matan ya'yanta)tafison Hafsat din ...

"Alhaji sameer yai murmushi ,ayi hakuri gwaggo insha Allah irin haka baxata sake faruwaba,Sannan Muna godia da yardar dakikayi na xaman magajiyan a nan garin,Allah yahada kansu itada abokiyar xamanta Amiin,

"Shide Capt Adam Kansa akasa yake,gaba daya jikinsa yayi sanyi naganin yadda kirikiri gwaggo tadau karan tsana tadorawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login