Showing 33001 words to 36000 words out of 107296 words

Chapter 12 - UMMI A'ISHA(THE MAGNIFICIENT) COMPLETE

22 Aug 2024

7720

©•MISS XOXO
👄

DEDICATED TO;
UMMI_A'ISHA👌🏼

nanahafsat.wordpress.com

•✨•✨•✨•✨•✨•

Tashi UMMI A'ISHA tai akan gadon ta 'karasa inda hafsat 'din take takwanta akan cinyarta ,hafsat tasa hannu ta rungumeta,,,daren ranar ahaka sukai bacci kowa da abinda yake sa'kawa azuciarsa....

Washegari da safe magajiya ta kira captain adam a waya kan tanaso taje kaduna takai xiyara be mata musu ba yace Allah yadawo lapia tagaishesu,

Da wuri magajiya ta gama shirinta jirgi driver yajata se kaduna hanyar unguwarsu yadosa magajiya dake hakimce a owners corner tai saurin dakatar dashi"bagida xamuyi ba tukun xan karba sa'ko a unguwar locust"

"to hajia"abinda jirgi yace kenan sannan yai reverse ya juya kan mota se locust area unguwarsu muna_b...

Yana zuwa yai parking akofar gidan ita kuma tashiga ciki,gidane flat ya amsa sunansa dan ko unguwarma masu farcen susa ne ke zama cikinta, ita ka'daice aciki dan iyayenta na garin maiduguri karatu ne yakawota kadunan daga nan kuma ta hadu da kawayen bnza suka gurbata mata tarbiyya harde idonta ya bude daga karshede ta ba'dawa idonta kasa taki komawa garin nasu,tabiyewa miyagun kawaye tafara halin banxa kwata kwata ba aure agabanta taguji iyayenta shekara da shekaru sunyi neman harsun godewa Allah. ..

Tana shiga tai sallama muna_b na kwance tana danna waya"wa alykm salam"tadago kanta ganin magajiya ce yasa tasaki ihun dadi taje ta rungumeta "kawas ashe zakizo? walhy naxata wasa kike"

"habade zanzo mana akwai labari de ko?!"

"mezafi kuwa"

Neman guri magajiya tai taxauna tareda kwantar da KHADIJA agefe dake shararar bacci"inajinki kawas bani nasha"

"da frko de yaya wajen hafsatun akwai wani latest a kasa?!"

"rannan 'dahare ke bugun cikin haule ai tace wai hafsat din ciki aka cire mata"

Muna-b ta kece da daria "lalle aikinsa yna kyau Kenan"

Magajiya ta ware ido tana kallon muna_b"kawata kina nufin shirinki ne Wannan?"sekuma ta kyalkyale da daria...

"Kwarai kuwa kawas,ai naki jinin kishiyar ki kaman mutuwata"

"kibari kawai aibanki intashi inji ance ba ita a duniyar ba natsani nabude ido naganta a doron duniya shiyasa banasan zaman kanon gaba daya ma"

"to albishirinki boka yabada choice ki xabu daya nafarko ko abaki abu kisamata a abinci taci baxata shura ba awajen xata mutu nabiyu kuma ko a haukatar da ita tashiga duniya gaba daya a mata kurciya adenajin ta a duniya gaba daya,wanne kika dauka?baxa'a cika sati ba aiki zeci"

Magajiya tai shiru tana tunani can ta nisa"ina ganin a haukatar da ita tashiga dunia shiyafi don kinga a Iya samin wani yamurje mata kai akan titi ta mutu kinga hakan yafi ai..Amma ta mutu ina wani wahala anan kilama tacika da imani kingakwa bama fatan hakan ta samu koya kikace?"

Muna_b ta kece da daria"wannan zabi naki haka yake barin tashi nadakko maki sakon"

Tashi tai ta tashiga daki tadakko wata leda tadorawa magajiyan akan cinya"gashinan kisan yadda zaki kisa mata ko a abinci,abinsha ko acikin Man kitso dinta ko turaren shafawarta"

"wai Allah yakawo yadda xa'ai amma babu matsala"

"kada ki wasa dashi ki tabbatr kinyi,Allah yabarki dagake se adam dinki"

"Ameen kede bari kawai,to wani hanzari ba gudu ba ita kuma UMMI A'ISHA fa yaxa muyi da ita?!"

"wannan kuma senan gaba semuyi shawarar yadda xa'ayi"

Magajiya Sun da'de suna hira da muna_b kafin tai mata sallama tatafi gidansu,kwananta biyu kullum tana zuwa wajen gwaggo su gaysa a ranr daxata tafi ma da safe tatafi gidansu gwaggo tamata sallama kamar kullum gwaggon na parlour tanajan tasbaha, magajiya tai sallama tashiga bayan sungaysa Sun dan taba hira magajiyan tace"gwaggo zantafi kada nayi dare a hanya"

"to shikenan magajiya Allah yakaiku gida lpia gashinan nono da fura kidau jarka daya kiba hafsatun daya kifinma haka gashinan kusada daddawa anan gefe"gwaggon tafa'da taname nuna mata kayan da hannu

"to shikenan gwaggo Allah yasaka da alkhairi"

Tana fitowa dga gidan gwaggo Suka biya gidan muna-b inda tace mata xata Iya zubawa acikin nonon koda captain din yashama babu abinda xefaru tunda da sunan hafsat din akai komi atake awurin tajuye kullin maganin duka acikin nonon tagirgixa sallama taiwa muna_b sannan jirgi yaja se kano ta dabo tunbin giwa....

Akwana atashi bawuya wurin Allah kwanan magajiya biyar da komawa kano hafsat taji tana marmarin nono lokacin fitar captain adam kenan daga gidan tatsiyayoshi a cup UMMI AISHA tataho da gudu ta fa'da jikin uwar "ammi dan ta momo"

Hafsat tai murmushi tasa hannu tana shafa kan UMMI AISHA "ba lemo bane UMMI AISHA,kuma da sanyi dana baki jeki wajen haule tana kitchen tabaki"

Haka hafsat ta kafa kai ta shanye nonon tass ta ajiye kofin,sihiri ba karya ba tuni hafsat taxube akan kujera tana dafe kai can ta mike idonta yakada yayi ja tasa hannu xata cire hijabin jikinta takasa wata razananniyar kara tasaki tafice agidan da gudu lokacin su hannafi suna sallah a kofar gidan...

Fitowar haule da UMMI AISHA kenan daga kitchen ba alamar hafsat, haule tashiga dubata amma bata ko'ina gakuma wayarta akan kujera tabarta,bangaren magajiya haulen tanufa bayan tayi sallama tadan tsugunna magajiyan nakwance tana kallo"hajia,aunty muke nema bamu gantaba naxata ko taxo nan"

"bade nanba gaskiya bataxoba kila ba nisa tyi ba"

Jiki sanyaye haule tamike tafita ita kuma magajiya tashiga cikin daki tadinga daria tana kyakyatawa"ohh hafsatu anxama mahaukaciya kenan"waya tajanyo takira muna b tafada mata yadda ake ciki,

Shiru har dare ba alamar hafsat haka UMMI AISHA tagama kukan rashin ganinta tai bacci,koda captain adam yadawo yasamu labarin da ake ciki fitayai nemanta amma shiru kakeji,har radio channels da stations na police duk an fada.....

Washegari ma haka abu har tsahon sati biyu captain adam ya rame yayi baki hakama UMMI AISHA kullum cikin kiran "amminta"take.

Lokuta Sun shude rayuwa taja batan hafsat wata daya kenan captain adam yatattara yakoma kaduna da xama kamar yadda magajiya tabashi shawara kuma yana yawon mafarkin hafsat din da gizo datake yawon yi masa kullum se an sauke mata qur'ani....
Hakika ba'tan hafsat yagirgixa yan uwa hr izuwa kan yan unguwa,mjay kullum setayi kukn hakan har Kano taxo na sati biyu amma shiru haka ta hakura takoma akarshen shekaranne Allah yayiwa abbansu Hafsat din rasuwa dangi ysake rudewa musanman inka waiga kaga duk an hadu ba hafsat din ..

Mama itace ke ri'kon UMMI AISHA yanzu,bayan shekara biyar lokacin UMMI AISHA nada shekaru bakwai aduniya gwaggo tce lalle captain yadawo da ita nan kaduna wajen yan uwanta,hakan kuwa akai aranar yaje yadakkota da kansa tagirma sosai farace ga tsaho ga gashi,har suka iso kaduna tana bacci yadauketa a kafada yashigar da ita cikin gida magajiya na hakimce akujera se KHADIJA dake kwance kan cinyarta yana shigowa magajiya tabude baki"wacece Wannan din?!"

Be bata amsaba kansa tsaye yashiga wani 'daki da alama don yaran akatanadeshi gadajene guda biyu aciki pink da purple yakwantar da ita akan purple din ya lulluba mata bargo yafuce daga dakin...komawayai parlor din yadauki remote yana canxa channels yakalli KHADIJA dake faman danna wayar magajiyan"ke tashi kishiga daki ki kwanta gobe monday akwai school ga yar uwarki can gobe xa'ai admitting dinta itama"

Tashi tai tana zumburar baki tatafi daki,tunda ya ambaci yar uwarta magajiya tagane UMMI AISHA yake nufi, itama din mikewa tai tatafi daki batabi takansaba,tabe bakinsa yai yacigaba da kallon dayake....

Washegari da safe bayan sungama breakfast sunayi magajiya najefa mata harara hakama KHADIJA,captain adam da kansa yakaisu makarantar Wanda dama Khadija anan din take. Uncle bado shine sunan makarantar ,straight Khadija tatafi ajinsu sukuma suka tafi office din principal,successfully tai passing exams dinta akasata a pri 3 ajinsu Khadija dukkoda ita tsallake akai mata hr kofar ajin captain adam yarakata yana in antashi xexo yadaukesu,principal din mesuna uncle David shiya shigar da ita har cikin ajin lokacin English teacher ce a cikin ajin ,ganin UMMI AISHA da Khadija tai duk se ranta ya baci dayake tadakko halin uwarta,sosai principal yai introducing UMMI AISHA yan ajin se sonta sukeyi,sit dinta two sit intevals ne tsakaninsu da Khadija,aunty Helen ta tambayi quetion ajin yai tsit basusan amsa ba dukkoda kunya UMMI AISHA keji hakan be Hanata daga hannunta ba,
Sosai Aunty Helen taji dadi "silence class, okay UMMI AISHA I'm all ears go ahead"abinda aunty Helen tace da ita kenan........!

Gaba daya ran KHADIJA ya'baci musanman dayake Ita bata taba answering questions a class ba batada ko'kari,sosai UMMI AISHA tabada amsa ajin akahau tafi,aunty helen taita yabonta,har aka tashi kowane teacher yashigo class din se UMMI AISHA ta amsa questions,gaba daya ran KHADIJA ya ba'ci musanman dataga malaman suna yabon UMMI AISHA agaban captain adam din,suna xuwa gidah ya ajiyesu shikuma ya juya kan mota yafita ,a 'darare UMMI AISHA tashiga cikin gidan,ganin tundaga bakin kofa KHADIJA tafara kuka tasan makirci xata kulla mata awajen magajiyan...

Ko Yaya labarin hafsat?!!!!

•✨•



WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;NANA HAFSAT.......
[4/18, 11:57 PM] Asy Khaleel: •✨UMMI_A'ISHA✨•

(THE MAGNIFICENT)
34

©•MISS XOXO
👄

DEDICATED TO;
UMMI_A'ISHA👌🏼

nanahafsat.wordpress.com

•✨•✨•✨•✨•✨•

KHADIJA nashiga ta fara wurgi da school bag 'dinta tana buga kafarta a kasa tana kuka,magijyan ta taho da sauri"menene Khadija wani abin aka maki a school?!"

"ummah ba UMMI AISHA bace take ta ko'Kari a class yau Wannan aunty helen 'din bakiga yadda take sontaba itada sauran teachers har baffa suka fadawa wai ita tanada kokari"

"kan bala'i ina UMMI AISHA din take yanzu?!"

"Tana waje......"bata karasa fadaba magajiya ta mike tana huci tai hanyar waje nan tagano UMMI AISHA arakube ajikin kofar shiga parlour din ta hada gumi da alama atsorace take....

"zonan dan ubanki"abunda magajiya tace kenan tareda sa hannu tajanyota.."shegia dangin mayu dama ainasan angama jikawa anbaki kinsha xakici na jaki kuwa yau agidannan me rabani dake se Allah"

"Dan Allah ummah kiyi hakuri"

"umman uwarki,kar in sake jin kin kirani da ummah niba mahaifiyar ki bace kinajina?!"

"ehhh naji"UMMI AISHA tafa'da a tsorace,

Rankwashi takai mata har sau hudu akanta"shanye kukan nan dan ubanki kika bari hawaye yaxubo sena laka'da maki na jaki"

Bayadda UMMI AISHA ta iya haka tashanye hawayen dake ko'karin zubowa daga idonta,"mtsceew"magajiya taja tsaki tareda jan hannunta bata direta ko'ina ba se dakinta tashiga bude wardrobe dinta tana ciro inner wears dinta da manyan towels"gashinan ki wanke su tass kishiga cikin bandaki kada ki xubar da ruwa akasa wanki uku dauraya uku zakiyi"

"tohmm"abinda UMMI AISHA tace kenan sannan ta debi kayan takai bandaki tadade tana kallon inner wears din wanda suka kunshi tulin braziers,panties,under Wears da towels na wanka Wanda itade Iya saninta aunty ikhram tagani tana sasu sannan ita take wanke abinta da kanta towels din kuma a washing machine taga ake sawa,hasalima bata taba wanki da kanta ba su farila ke mata ..

Tana hawaye sha'be sha'be haka tadinga wankesu sedatai sa'bi uku dauraya uku ta shanya a hanger data gani a bandakin,sannan takoma parlor xaune magajiyan take da Khadija a gefe dakeshan corn flakes..
"nagama wankin"

Se asannan magajiya ta'dago takalleta a wulakance"kin tabbatar sun wanku kuwa?! dan idan naduba naga basu fitaba sena ci miki mutunci agidannan"

Muryar UMMI AISHA narawa take fadin"Allah sun wanku"
"shikenan tashi kije"magajiyan tace da ita,jiki asanyaye UMMI AISHA ta mike tatafi daki tana hawaye ga kukan yunwa da cikinta keyi rabonta da abinci tun nasafe don ko a school bataciba ta tsaya tana revising class work din da aka basu,bandaki tashiga tayo alwala kamar yadda akeyi sannan tai sallah baxaka taba cewa yar shekara bakwai ce tanutsu take sallah hakan ba....

Bayan ta idar da sallah kenan captain adam baffansu yadawo,duk suna parlor yaga babu ita kuma shiru bata fito ba"magajiya ina UMMI AISHA?! "


•✨•
35


"nan muke da ita suna bani labarin school tace yau tayi kokari sosai inaga bandaki tashiga"

"barin kirita baffa"abinda Khadija tace kenan sannan tashiga dakin nasu"ke kizo inji baffa,saura kuma kice ummah tadakeki"
Itade UMMI AISHA batace komiba illa bin bayanta datai suka fita parlour din...
Capt Adam naganinta yafara washe baki"xo yammatan baffa,yar albarka"

Da sauri UMMI AISHA tanufi inda yake tana murmushi"kinci abinci?! "kafin tabada amsa magajiya tarigata"catai se xuwa anjima"capt adam yawatsa magajiya mugun kallo sannan yasake duban UMMI AISHA akaro na biyu"xakici yanxu?!"

"zanci Baffa"

Haka Capt adam yaxuba masu shida ita spoon by spoon tadinga ci seda takusan tashi da rabin abincin sannan tadawo ci ahankali seda yaga takoshi sannan yabata ruwa tasha yadauraye mata bakinta, wasu hawayene ke neman zubomai yai saurin maidasu musanman dayaga tafara juyewa kama da Hafsat dinsa, dakyar yadaure yajawo leda agefansa yaciro school uniform set biyu da school bag da Socks guda biyu da takalmi guda biyu da textbooks dakuma notebooks da sauran abubuwa su pen da mathset yamikawa UMMI AISHA"gashi jeki ajiye adaki seki fara amfani dasu gobe in Allah yakymu"
"to baffa nagode"sannan ta mike tatafi daki ta ajiye..
Magajiya tacika tai fam kamar ta fashe"baffa nimatextbook dina na ugo c ugo ya bata"

"bade wanda nasiyo maki shi shekaran jia ba?!"

"Allah Baffa sacewa akai a ajinmu"

Capt adam yagigrixa kansa yana Kallon magajiya"wannan duk lefin kine,saboda allah yarinyar nan kullum batada adani littafinnan nasiya mata yafi akirga,kwata kwata batada adani,yau littafinta ya bata gobe mathset dinta ya bata kullum kuma yan ajinsu ke sacewa saboda ita kadai suka tsana kenan?!safa kuwa kullum semun tsaya a shago ansiya sannan tasaka tashiga cikin makaranta,haka zata tashi ba adani kenan?!tun yanxu awannen shekarun idan baki koya mata tattali ba wallahy haka zata tashi"

"to yaya kakeson ayi kenan?!yarinyar nan tace ansace aibaxatai karya ba ko?!ansace 'dinne"

"okay hka zakice?!to shikenan wallahi baxan siya ba"mikewa yai yatashi yashiga cikin dakinsa be tsaya jin mexata ce ba,

Sa hannu tai ta rungumo yar tata meyakwan tamata Fada batayinba sema hakuri datake bata"yi hakuri yar gatan ummanta,kyale baffa nixan siya maki kinji?!"
Shiyasa khadijan tatashi asangarce ga rashin kunya da tsiwa....

•KATSINA

___dattijawan matane su biyu zaune suke akujerun da suka amsa sunan royal chairs,kayan alatu ne cike agabansu acikn wani tray hira suke abinsu hankali kwance dayar daga ciki wadda da alama itace taxiyarci dayar tace "hajia barira nikwa ina yar aikin nan naki take me kirki?!"

"ohh firdausi kike nufi tana kitchen sarkin aiki"

"nace ki aramin ita na sati biyu takoya wasu amal girki kinki"

"bahaka bane inajin dadin xamanta agidannanne amma xataxo maki insha Allah"

"to ko xa'asa momin wata kamar ita dn Allah"

"naga yamaki itama labrinta yanada tsaho,kinsan gidan yaya Yakumbo tai aiki harna tsahon shekaru biyu daxata koma jos shine tabarmin ita"

"okay haka itace wadda kikace kamar an gusar mata da hankali ko?!"

"kwarai kuwa ko sunan da ake kiranta dashi firdausi yaya Yakumbo ce tasaka mata"

"tamanta komai nata kenan?!"

"kwarai kuwa,bari ma inkirata ku gaysa"sannan tadan daga murya tana fadin"firdausi"


•✨•

WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:NANA HAFSAT ......
[4/18, 11:57 PM] Asy Khaleel: •✨UMMI_A'ISHA✨•

(THE MAGNIFICENT)
36

©®MISS XOXO
👄

DEDICATED TO;
UMMI_A'ISHA👌🏼

nanahafsat.wordpress.com

•✨•✨•✨•✨•✨•

Da sauri ta'karaso wajen ta tsugunna tagaisheda da aminiyar aunty bariran wato hajia hajja,murmushi fa'da'de a fuskar hajia hajja ta amsa mata gaisuwar tareda doriyar"inata cigiyarki ai"

"ina kitchen ne hajia"

"ohh ayyah,to shikenan ki koma aiba yanxu xan tafi ba"

"to hajia"sannan ta mike ta koma bakin aikinta a kitchen...

Hajia hajja ta cire tagumin data zabga"mutum yaji tsoron duniya,dan Allah me Wannan baiwar Allahn tayi xa'ai mata Wannan mummunar sakayyar?!"

"kibar mutum kawai,ai wasu mutanen Sun dauka babu hisabi,wallahy hajia hajja nikaina seda nazubar wa da baiwar Allahn nan hawaye"

"shekaru kusan uku ko?!"

"hudu de,kinga labarin nata me tsawo ne fa,farko ai kawu haruna ne yakadeta a mota can hanyar katsina yace kawai tafiya take bata kallon gabanta yanata mata horn duk abanza gashi yakasa tsayar da motar,nande yakadeta though bataji wani rauniba yakaita asibiti aka bata magani,bata magana bata komi shine seyatafi da ita gidansa dake funtua akaita yi mata magani da sauka inda wani malami yace ai kurciya akai mata tashiga dunia tareda sihirin gusar da hankalinta"

"wayyo Wannan mata tashiga halin tsaka me wuya"hajia hajja tafadi hakan tareda girgiza kanta alamar tausayi ..

"wallahi ina gaya maki akaita mata magani wallahi,yadikko gaji matar Kawu harunan tace bayan kamar wata daya da hakan da safe setaji tanace mata ina kwana?!,tace setace mata yasunanki?!wallahi yadikko tace setace min wallahy bansaniba atakaice duk tambayar dasukai mata bata saniba tamance komai nata"

"Allah sarki baiwar Allah"

"wallahi shine suka gayawa wanda yake mata rokon Allahn yace ai agodewa Allah ma da abu yazo da sauki,don mugun sihiri akai mata tashiga dunia takuma zamto Me gusar hankali abin kyama cikin mutane,saboda haka se ahnkali tunaninta ze dawo jikinta komin daren da dewa,shekararta daya agidan kawun bayan rasuwar kawun se rikonta yadawo hannun yaya Yakumbo dake funtua inda take kiranta da firdausi shekararsu biyu tare ita kuma kinsan mijinta aikin Bank yakeyi kullum cikin chanza garuruwa Sukeyi ashekara biyun ne akai posting mijinta jos shine fa tabarmin ita haryau de muna adduar tunanin ta yadawo don mumai da ita gida shekaru biyar kenan nasan yan uwanta sunacan suna nemanta baiwar Allah, Allah de yakawo karshen koma menene amiin"

Hajia hajja tagoge hawayen dayake tsiyaya daga idonta"Allah yasakawa baiwar Allahn nan,kowaye yai mata Wannan abu bekyau taba, ubangiji Allah yaimana katangar karfe da makiyanmu amiin"

"Ameen ya rabbi,makiyinka babu
Abinda baxeyiba dan ganin yayaye maka farin cikin rayuwarka,rayuwar yanzu se du'ai kullum nai sujjada sena mata addua Allah ya karya sihirinnan yahada baiwar Allahn nan da yan uwanta nasan sunacan sunyi neman sungaji wasuma sun fitar da rai"

"insha Allah nima zan tayata"

_______koda hafsat(firdausi kamar yadda ake kiranta yanzu)takoma kitchen neman waje tai tazauna akan kujera hade da tabe habarta tana hawayen dabata san na menene ba,

'kaurin kamawar tuwon data keyi shiyadawo da ita daga tunanin datake wanda batasan na menene ba,sauri tai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login