Showing 36001 words to 39000 words out of 107296 words

Chapter 13 - UMMI A'ISHA(THE MAGNIFICIENT) COMPLETE

22 Aug 2024

7697

takashe gas din takwashe taxuba a foodflask taware nasu na yan aiki sannan tadebi nata tatafi daki,bayan taci takoshi lokacin hajia hajja ta leko sukai sallama har gate hafsan tarakata sannan tadawo daki takwanta dayake dare yayi, karfe daya da rabi tafarka tafara nafilfilinta kamar yadda tasaba ......!


•KADUNA


•✨•
37

Da sassafe UMMI_A'ISHA tatashi tashiga bandaki tai wanka tayo alwala tafito tai sallar asubah raka'a biyu,gefen gadon Khadija taje dake shararar bacci tadan daddaki gefen pillow dinta"khadija kitashi karmuyi late a school''

Meyakwan Khadija tatashi sema gyara kwanciya datai tacigaba da baccinta haka UMMI AISHA tacigabada da tashinta amma duk a banxa hakura tayi tasa uniform dinta da socks dinta sannan ta rataya school bag dinta tafita parlor taxauna,dede lokacin da magajiya tafito daga daki tana hamma ware ido tai tana kallon UMMI AISHA datai kyau cikin uniform dinta ga kitson shuku biyu yayi dass kamar zanashi akai dukse bakin ciki yatararwa magajiyan tahade rai tana jefa mata harara kotakan gaisuwar datake mata bata biba musanman data duba parlor din babu Khadija babu alamarta"ke ina Khadija?!"

"inata tashinta taki tashi"abinda UMMI AISHA tafada kenan muryarta se rawa take. .

"karya kike,muguwa wato ke kin shrya ita kuma bata shrya ba in baffanku yafito yayi mata fada kenan ko?!to zoki koma cikin dakin seta gama shryawa tukun 'karamar yarinyarki dake se mugun hali"'kwas takai mata rankwashi akai"shige muje"tana nuna mata daki"kuma kika kuskura hawaye yazubo wallahy senamaki lilis agidannan"

Dakin suka shiga tare,itade UMMI AISHA neman waje tai taxauna akan stool, magajiya tasha fama kafin tatashi Khadija dake faman bacci har abandaki sekace wadda xa'a sake mata dare....dakyar tashiryata kayan uniform dinma kowanne dakyar aka hadashi hijab akan gado,skirt akan mudubi rigar da tie kuwa cikin drawer suke hade da kayan wanki masu datti dama safa ba'a maganarta kullum sabuwa ake siya,

Parlor suka fito lokacin har captain adam yafito daga daki yana parlor din yanashan Coffee,gaysheshi sukayi ya amsa cikin fara'a"ya akai kukaso kuyi latti yau?"

Caraf Khadija ta Cafe"baffa ba UMMI AISHA bace tundaxu nake jiranta tashrya se bacci takeyi dakyar ummah tatasheta"

UMMI AISHA tai shiru tana tunanin karyar da Khadija tayi mata kamar ba itace ke jiranta tun daxun ba,muryar bafface tasa tadena mamakin datake"shikenan yawuce kuxo Kuci abinci nai dropping dinku school"

Abincin sukaci sannan suka tafi school,koda suka dawo da aka basu assgnnt Khadija bata iya ba UMMI AISHA tace taxo takoya mata taki,tagwan mace aunty Helen tai purnishing kota kwafi na frnds dinta ....

Kwanci taci bawuya awurin Allah,su UMMI AISHA sungama primary school dinsu inda duk wani awards seda taci kuma ita taci best student of the year akabata scholarship a one of the best school a kaduna wato 'danbo'

Khadija bataci komiba dan da ana bada award akan wadda tafi kowa dakikanci to xa'abawa khadijan magajiya,haka magajiya ta kafa kahon zuka da naci da magiya da sihiri dakomi magajiya tashawo kan Capt adam yayarda yabiyawa Khadijan danbo din itama,

Alokacin UMMI AISHA nada shekaru goma ita kuma Khadija nada tara,kyau,ilimi,tarbiyya,biyayya,ibada awajen UMMI AISHA ba'a magana,aranar baffansu yakarbo masu uniform wanda ita UMMI AISHA kyautane har books da komi duk under scholarship ne ita kuma Khadija duk seda aka siya mata .....

Shekara uku kenan da komawar UMMI AISHA kaduna amma bata tab'a fadawa capt adam tsangwamar da muguntar da magajiya keyi mata ba,ranar monday suka fara xuwa school din aranr UMMI AISHA tai kawa wata me hankali kuwa sunanta WALIYYA,bayan antashi daga school suka koma gida da wata mota a fake jeep jikin Khadija se rawa yake dama gata da son maxa me aikinsu delu itace ke wanke wanke a gefen babban kitchen din dake waje Khadija tamatsa kusa da ita tana Bin motar da kallo"delu suwaye sukazo?! "

"ya'yan baffa sameer ne"

"ARFAAN KO MUS'AB?!"

"ARFA..."delu bata karasa fada ba Khadija tashige cikin gidan da gudu don ba karamin sonsa takeba kankanuwar ta da ita,shi abinma daria yake bashi dukkoda shidinma yaro ne baxe wuce shekara goma sha bakwai aduniya ba..

UMMI AISHA dake gefe sanda Khadija tafadi haka tai murmushi kawai itama tashiga cikin gidan,tasa hannu kenan xata bude kofar taji muryar ARFAAN 'din yana fadin "to ina kuma UMMI AISHA?!!!!"




WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:NANA HAFSAT!!
[4/18, 11:57 PM] Asy Khaleel: •✨UMMI_A'ISHA✨•

(THE MAGNIFICENT)
38

©®MISS XOXO
👄

DEDICATED TO;
UMMI_A'ISHA👌🏼

nanahafsat.wordpress.com

•✨•✨•✨•✨•✨•

'Karasa tura kofar tai tashiga ciki, ARFAAN yajuyar da kansa dan ganin waye,magajiya harda murmushinta kamar gaske"ai gata ma wadda ake nema,ARFAAN ke tambayanki maza zokici abinci kicire uniform kije ki wanka sekuma islamiyya,baki bude UMMI AISHA ke kallon magajiyan da tsananin mamaki atattare da ita.

Basarwa kawai itama tayi sannan ta karasa kusada ARFAAN din dake aika mata da sakon murmushi har kasa ta tsugunna tana gaisheshi "yaya ARFAAN ina yini?!"

"Lapia qalau UMMI AISHA ya studies!!"

"Lapia qalau"

"Masha Allah,kuje kuci abincin ya fada yana kallon khadija data maida hankali kan game din datake a wayarsa"sannan yasa hannu yakarba wayar tasa......

Magajiya dake gefe tace"nikwa ARFAAN next yr xakaje university ko?!".

ARFAAN yai daria"aunty nashiga level one hundred fa anan umyuk"

"Habade?!lalle girman dan mutum ba wuya to mus'ab ne xeshiga nxtyr kenan?!"

"Ehh shise nextyr da nima se next yr din Greece suka bani admission,to kumade se baffa yace kawai naje umyuk din tunda dama nayi jamb kuma naci point dina yakai,shine se naje can umyuk din ina studying mechanical engineering"

"Ai gwara hakan dakai ta zama,toh Allah yatemaka ameen"

"Ameen"

ARFAAN yadan da'de anan din harse bayan isha'i sannan ya masu sallama yatafi yaso ganin UMMI AISHA kafin yatafi amma babu dama saboda tana gama homework dinta tai bacci...

•KATSINA

Hafsat tareda sauran masu aiki suketa aiki a kitchen din da alama ba'ki zasuyi....Hajia barira matar gidan ita tashigo cikin kitchen din tana 'dan duba abin da xa'a kara da Wanda xa'arage sannan ta karasa kusada hafsat dake faman soya snacks da hada coleslow...

"Firdausi sannu kinji kitashi kije ki huta se innar wasila tacan jeki"bayan tasa hannu takarba robar da coleslaw din ke cike aciki....

Hafsat ta mike tana karkade zaninta"to aunty barinje,amma aiba wani aiki bne Wannan yanxu xan karasa"

"Kide je kihuta firdausi inde su ASHRAF ne sekin gaji da tsurfarsu"

Hafsat batai musu ba ta mike tatafi dakinsu da aka tanadar masu..

Bayan sun kammala komi suka koma daki suna hutawa dama su uku ne dattijawan masu aiki hafsat da jummai me wanke wanke se inna me 'ya wasila haka 'yar karama baxata wuce shekara uku a duniya ba shine akece da ita innar wasila...

Kamar kullum suna xaune a farfajiyar dakinsu,wasila diyar inna dake kwance akan gado tafara kuka tatashi daga bacci
Da axama hafsat tasa hannu tadauketa don tana matukar son yarinyar har magudanar jininta take sonta innar wasilan dake gefe tai murmushi"firdausi kidena daukar katuwar yarinyar nan kina dorata akan cinyarki"

Hafsat tai murmushi kawai tana shafa kan wasilan tana mata wasa"xakici abinci?!"

"Andima danci"tafada ahausarsu ta yarinta....

•✨•
39

Ita de hafsat tana son yrinyar sosai inkuma tadauketa setaji kamar diyarta,kwakwalwarta tafara charge tafara tunanin da kanta yafara ciwo"menene firdausi?!"abinda innar wasila tace da ita kenan....

"Babu komai inna kawaide narasa meyake damuna ne kwanakin nan sena dingajin wani iri,kuma kullum sena dinga mafarkai wasu iri"

"Kamar yaya kenan banganeba?!"

"Kamar muna zaune tareda wasu da bansan suba kuma muna hira,inaji ajikina kamar jini nanesu,amma bansaniba ko sharrin mafarkine tunda nide nasan banida kowa se Allah seku"

Innar wasila tai shiru sekuma tai ajiyar zuciya tanemewa Allah godia acikin zuciarta tunda tasan abinda yasamu da abokiyar aikin tata wadda ko satin daya wuce malamin dake was hafsat din rokon Allah seda yace da yardar Allah tunaninta xedawo ahankali......

"Ba sharrin mafarki bane firdausi kede kici gabada addua kawai"

"Banganeba innar wasila"

____muryar jummai abokiyar aikinsu ita takatse musu maganar dasukeyi"Hajia tace kuzo su ASHRAF sun karaso"

"Toh gamunan" suka fada atare ,maganar da basu'kara saba kenan suka tashi suka tafi parlor inda Hajia bariran take da wasu kyawawan yara guda biyu mace da namiji.....

"Yawwa"abinda hajia bariran tace kenan tana kallon yaran nata oya kutsugunna ku gaishesu dama kunsan inna da hajia jummai Wannan kuma tasa hannu tana nuna Hafsat"sunanta aunty firdausi"

Hafsat tai murmushi tana kallon yaran data kejin sonsu,da gudu yarinyar tatafi ta rungume hafsat din tana ta'ba jelar gashin hafsat din data fito ta bayan dankwali tana tabawa tana kallon maman nata"mama kinga gashinta kamar na barbie doll"

Hafsat tai daria"yaya sunanki?!"

"Sunana ayush,ga yaya nacan sunanshi ASHRAF"tafada tana nuna ASHRAF din dake zaune yanata durawa cikinsa chocolate....

"Ohh ni barira"Hajia bariran tafada tana dafe ha'ba"Ayush yaushe zaki dena shirmene?! Bari abbanku yazo ummah ta shagwaba ku dayawa"

Hafsat tabi yadda suka 'bata parlor din da kayan ledar chocolates da sauran tarkace duk sun zubar,...
Sun danyi hira sannan Hajia bariran tasallamesu suka koma dakinsu bayan sunyi sallah ne su jummai da inna suna maganar marassa ji sunzo aiki xeyi doubling hafsat tai shiru tana mamakin to ya'yan waye?!

"Nikwa inna su ASHRAF dinnan ya'yan waye?!,ni nakasa ganewa"

"Ya'yan hajian ne to abokiyar zamanta bata haihuwa shine farko seta fara bata ASHRAF lokacin yana shekara biyar to bayannan seta kara haihuwar ayush itama bayan ta yayeta seta barwa kishiyar,tunda kinga ita bata taba haihuwa ba ita kuma hajian ya'yanta takwas mata uku sunyi aure harda ya'yansu aikin sansuma se maza uku biyu sunyi aure dayan kuma bana xa'ai nasa shima se laila dake karo karatu a turai,se su ASHRAF din"

"Amma ta kyauta kam,kuma anan katsinan take itama?!"

"A'a ita tana kano,a can suke ita dinma tana zuwa nandin tai Hutu lokaci lokaci itama hajian tana zuwa,suna zaman lapia da mutunta juna yaranne de basaji ko miskala zarratan ansha canxa mashi aji a makaranta"

"Tabbas naga yadda sukai kaca kaca da parlor ma dazu"

"Haka suke wallaby,barin ASHRAF din miskili ne sosai shi magana fa inba wani sabawa kukaiba ko cikin yan uwansa bayi yakeba,gashi duk yafisu kyau kamarsa daban"

"Sosai kuwa tubarkALLAH,Allah yarayasu amiin"
Haka sukaita hirarsu har dare yaja sannan sukai addua suka kwanta......


#teamARFAAN
#teamASHRAF
#teamMUHANNAD....



WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;NANA HAFSAT........
[4/18, 11:57 PM] Asy Khaleel: •✨UMMI_A'ISHA✨•

(THE MAGNIFICENT)
40

©®MISS XOXO
👄

DEDICATED TO;
UMMI_A'ISHA👌🏼

•✨•✨•✨•✨•✨•

___WANENE ALHAJI KABEERU KAMILU KANKIYA?!

Alhaji kabeeru kamilu kankiya babban dan kasuwane agarin nakatsina sanannene sosai yana da company din motoci nasiyarwa dakuma oil and gas shares ba'anan yatsaya kadai ba babban 'kusa ne a gwamnati inda shine director general na depence, shine babba agidansu basuda yan uba mahaifiyarsu ita kadaice wajen mahaifinsu shine namiji babba se kannensa mata su uku kawai.......

Alhaji kabeeru yanada mata biyu,matarsa ta farko Hajia barira wadda Allah ya albarkacesu da ya'ya har takwas,inda biyu daga ciki mace daya namiji daya tabarwa kishiyar tata hajia aishatu wadda sunanta ne akasawa ayush autar hajia bariran,ita hajia ayshatun bata haihuwa...ita a kano takeda zama daga daya daga cikin gidajen alhaji kabeerun dake unguwar Lamido crescent,tana zaune tareda ya'yan kishiyar data rikesu kmn nata wato ayush dakuma ASHRAF.......zamane sukeyinsa cikin karamci da mutunta juna,suna ziyartar mahaifiyar tasu duk sanda suka damu dogon Hutu!!!!!!

Haka rayuwa taja lokuta suka shu'de,bangaren hafsat tana samin sauki sosai ba laifi,tunda hartana tuno tanada diya mace UMMI_A'ISHA dakuma mijinta captain abinda ta'iya tunanowa kenan sefa kanwarta datake yawon anbata wato mjay dakuma mahaifinsu Wanda bata iya fadin sunanshi,tabbas cikin kashi 'Dari na sihirin da ake mata kaso saba'in babushi ciki abin se godiar Allah Kuma Hajia barira da Ma maigidanta sunji dadi kwarai dagaske Kuma sunyi alkawarin inde takara samin lapia xasu nemi duk inda danginta suke adoron duniya sukaita...,

Bangaren UMMI A'ISHA Ma abin ba sauki,samari tun tana jss classes suke binta ballantana yanxu datake ss2,Masha Allahu ta Kara Kyau,fara ce farinta mekyau ne me daukar ido,Sannan tanada tsahonta Dede misali,jikinta ma moderate ne tanada yalwataccen gashin gira da Kuma sumar gashi harta zubo tagefen fuskarta taxama kamar saje,ga ido dara dara,Masha Allahu UMMI A'ISHA batada wata makusa wai ance dan adam Tara yake becika goma ba to itade UMMI A'ISHA tacika taranta cif,

Tun farkon shigarsu ss2 da suka samu wani dogon Hutu bayan sunje gidan gwaggo wadda yanxu ta manyanta sunyi mata hutu sunje gidan Yaya sameer shima sunyi masa hutu,sekuma sukaje hadejia danginsu captain sameer nanma sukayi hutu,bayan sundawo ne captain adam yake cemata yakamata suje zaria danginsu magajiyan na uba suwunar masu suma tunda basu taba xuwa ba,

Shiri sukayi nazuwa kaduna,KHADIJA wadda yanzu sunanta yakoma BABY KAY,babu Wanda besantaba a school dinsu inde harkar ya'yan masu kudi ce to tana ciki,duk wata latest waya data fito to se magajiya tasaya mata,tana daya daga cikin Wanda aka sani a kaduna Wanda sukai forming Union wato 'richest babes of kaduna'babu Wanda be san baby kay ba,'yar karya ce ta ajin karshe...sun shirya cikin manyan Kaya ko wannen su,magajiya tayi shiga cikin tsadadden lace din French lace Ita Kuma baby kay tasaka atamfar super holland dinkin ya amshi jikinta dukkoda bawani kyan jikine da ita ba seta yafa yalolan mayafi kalar kayan shidinma tasa Kane saboda baffansu karyai mata fada,saka mayafi babu shi acikin agenda dinta,UMMI A'ISHA tasa atamfarta mekyau itama super holland purple da torches black setasaka wadataccen mayafinta baki tai rolling dashi...

Zungureriyar mota kirar sienna Ita tajasu zuwa garin na Zaria,tunda asalin magajiyan dama ba zazzagiya ce,se daure fuska take tamau Ita adole kar a renata,dakyar sukai parking a layin daya sha jar kasa kaikace karkarace kodayake a zarian ma a outskirt dinta suke,dede wani gida ginin kasa suka tsaya Wanda seda sukai tambaya dakyar suka samu gidan dayake magajiyan ba zumunci ne da su ba,Iri dayane gidajen amma kowa da kofarsa,

Kawunsu ta hango wato kawu tanimu se faman asuwakhi yake da hakoransa da suka rine suka koma ja saboda cin goro,baby Kay se buya take a bayan uwar kamar wadda xa'a saceta,captain adam ya bude kofa yafito yasamu waje akan tabarmar dayaga kawun yake dashida wasu matasa da alama yaran sane,ya samu waje yaxauna ya mika masu hannu suka gaisa daya daga cikin yaran Kawu tanimu yace"kamar magajiyan kawun birni ce ko da mijinta ?!"yaname nuna magajiya da hannu data dora fuska tamau kmar bata taba daria ba!!!

Captain Adam yai murmushi"ehh mune"

Yakalli magajiyan dake yatsina fuska ga baby Kay a gefe datake masu kallon banxa se UMMI AISHA dake rakube ajikin dakalin kofar gidan"tohh saiku shiga daga ciki gurin matan ko"

Ran magajiya be so ba haka suka shiga cikin gidan ta tsaya a tsakar gidan tai jim tarasa wacce kofar zasu shiga domin ita babu wadda xata iya ganewa ciki duk kuwa da cewa sunje bikinta ammafa sunga wulaknci wajen yan uwanta da muna_b don duk wani aiki sede kaji ana akira mutan zaria gashi kuma babu wani kyakkyawan magana tsakaninsu ko gurin kwana ma dakin me aiki suke kwana duk kuwa dacewa dangin ubanta ne amma sundau kesu a wulakance,sunmanta cewa ko cikin rashi anasamin damar samu Wanda Allah keda ikon hakan....

Suna nan tsaye UMMI AISHA tanemi gefen wani bokiti daya tsage tazauna don baxata iya tsaiwarba,Banda baby Kay data makale kunnuwanta dana'uwar nan wato ear piece se kida ketashi,magajiya tai shiru tana naxarin tawanne kofa xasu shiga ciki tunda duk kawunnannata ciki suke Kuma gashi babu Wanda xata iya ganewa acikin gidan koda sukaje bikinta Ma basu samu ganinta ba saidai su hango ta daga nesa,




•✨•
41


"Ummah nifa I'm damn sick of this place,haba mana ummah ga wani gutter atsakar gidan Kuma kinsan ni I'm allergic to all sort of this"baby kay ce tafadi hakan tana mewa magajiyan nuni da kwatar dake tsakiyar gidan cike da kayan gwa'bi gwa'bi

Magajiya tabude baki xatai magana taji motsin yara sun shigo da gudu cikin gidan ganinsu yasa yaran suka tsaya suna kallonsu wani yaro me dan tsaho daga cikinsu yasa hannu yana nuna UMMI AISHA"Laaa ga India taxo gidanmu"

Sauran yaran dabasu gantaba hancinsu fal cikeda tasono da majina suka zuro kai suna zungurin yaran dayaga UMMI AISHA"habu tana ina indian,!"suka fadi hakan suname kokawar ganin UMMI AISHA dake aika masu da sa'kon murmushinta me dauke hankalin duk Wanda yai tozali da ita,baby kay ta juyar da fuskarta tana me toshe hancinta tana kallon magajiyan"ewwwww ummah I can't stand th...."bata karasaba ji kake tumbul kwata a watse waje sai fuskar baby Kay,kwatar Ita ta raba hanyar shiga gidan lokacin data zo tsallakewa kenan wai tana kyaman kwatar har tana mamakin ta Yaya mutum xaici abinci agidan nan ai itakam amai xatayi segashi shegun yaran nan ya'yan talakawa sun watsa mata kwatar a fuskarta batasan lokacin data xube a wajen tafara kuka ba takaici goma da ashirin dama Ita ba san xuwannan takeba,gashi nan ai abinda ummanta tajanyo mata,yaran kuwa mai zasuyi inbanda ihu,

"Ta Kamo kifi,soyayye,ni da su'din kwano soyayye,ni da siyo manja"da karfi sukeyi har saida Maman daya daga ciki ta jiyo hayaniyar tayi yawa ta fito ta leka me yake faruwa?!sai taga magajiya da diyarta dakuma wata balarabiyar yarinya,da alama diyar kishiyartace..sekuma diyar magajiyan jikinta duk kwata yara suna mata ihu da saurinta matar ta iso gurinsu ta kori yaran sannan ta kama hannun baby Kay dake tuttujewa tana zunduma ihu kamar wadda akaiwa rasuwa,matar wadda da alama tana daya daga cikin matan kawunnen magajiyan tashiga dasu bangarenta tana"lale da xuwanku sekuma kannenki suka watsa maki kwata Kiyi hakuri kinsan yaranmu na kauye yanzu haka garin kallonkune kunsan basu saba ganin yan gayu ba shyasa"

Itade baby Kay aranta catake wadannan kalaman yaran Wallhy ba kannenta bane,hanci fal majina kayansu ayage kaman almajirai itakam gaskiya ba kannenta bane...dakyar baby Kay tayadda ta tsaya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login