Showing 27001 words to 30000 words out of 107296 words
ina tsoron abinda xeje yadawo"
"Toh seki zauna ana takaki ae 'bawon albasa ma yafiki daraja agidannnan,nina tafi"bata jira cewar magajiyan ba tanufi parking arena din gidan,magajiya tabiyota abaya tana fadin"kawata kya baride mu....."
'Karar horn din mota shi yahana ta karasawa,zungureriyar motar captain adam ce tashigo ciki kirar Lincoln lx new model,fitowa yai bayan jirgi yagama parking yanatafe yana waya muna_b tatsaya su gaysa,katse wayar yai suna gaisawa da muna_b,sewani sunkuyar da Kai take kasa kamar mutuniyar arziki tana magana sekace ustaxiya "sannu da dawowa yaya,Nima yanxu nace barin karaso mugaysa naje yiwa kanwata visiting acan shekara boarding school dinsu"hakade suka gaysa Sannan sukai sallama taja mota tatafi,shikuma yanufi site din hafsat dinsa bayan yacewa "magajiya inta gama abinda take taxo takarba sa'ko"
Da wannan zancen dayai magajiya tai murmushi ganin aikinsu yakusa cinma buri ,tana gama abinda take tanufi site din hafsat din kamar yarda yace amma sungama kitsa yadda xasuyi itada 'daharen dayake Itama 'daharen duk kanwar ja ce mugayene dukkansu babu Wanda yafi wani mugunta,kar tasan kar ce!
..tana zuwa bayan sun sake gaysawa ya bata akwatin tsarabar ta tanuna farin ciki kmar gaske amma kasan zuciyarta bakin cikine karara musanman ganin akwatunan biyar datai atsakiyar parlor din cike da kaya,"haule,haule"haka hafsat tadinga kiran haulen amma shiru,
Magajiya tai murmushi "ko inkira maki Ita?!"
"A'a Wallahy barinje ainan bakin kitchen ne zani banisa zanyiba naji da'din 'kafata ma"
Mikewa hafsat din tai tatafi alokacin Kuma captain adam yabar parlor din yana waya dan dayana nanma baze bari hafst din taje takantava sede shi'din yaje,magajiya tai murmushin mugunta azuciarta kwa fadi take"wannan shine karshen tafiyarki adoron dunia"(Allah ka'dora mu Akan ma'kiyan mu ameen)
Wata razananniyar 'Kara hafsat din tasaki bayan fitarta bawani jimawa,alokacin magajiya tatafi da gudu ha'de dasa moper tai mopping wajen gaba daya yadda kasan wani abu betaba xubewa ba Sannan ta duka santar hafsat din tana dafe kai ha'de da kwalla Kara"Wayyo Allah nashiga uku"Ita Kuma hafsat din idonta arufe yake se hawayen azaba take,
Dagudu captain adam yafito yana ganinta yajefar da wayar dayake beyi wata wata ba yaciccibeta yasa acikin mota,yan aikin gidan duk suka fito harda haule da 'dahare ashe magajiya 'dahare tasa tadauke hankalin haulen tahanyar rokonta datai datayimata kitso ko 'kwara hudu ne,bude mota itama magajiyan tai tashiga se asibiti suna zuwa dr NAUFAAL ya nufi inda suke yana magana "lapia Yaya haka captain?!"
Captain adam dukya fita haiyacinsa"I know nothing Wallahy ,Dan Allah Doctor kace to rayuwar my hafsat"
"Calm down captain Insha Allah I will try my possible best yanxu kanutsu addua xakai mata"
Labor room suka shigar da ita kusan awa biyu ana abu daya but no avail ,kuka shabe'shabe'captain adam yadingayi,magajiya Kuma nagefe kaman tahadiyi zuciya tamutu dan bakin ciki da bakin hali,dr NAUFAAL yafito yanacire handgloves dinsa yawullar agefe yadoshi inda captain adam yake hade da dafashi"captain ya akai matarka tai wannan mummunar faduwar haka?!how on earth ko wani abin yafarune gashi she's unconcious ma gaba daya sede mu mata operation mu ciro babyn kawai if not akwai matsala Wallahy"
Captain adam yashare kukan dayake da tissue "dr bansaniba nima kawai kuyi mata abinda yadace pls dan Allah save my hafsat"
Takarda dr NAUFAAL yabashi yacike Sannan suka dunguma se labor room din,addua,kuka,magana shi kadai haka captain adam yadingayi,Allah me yadda yaso me bayarwa me hanawa me kashewa me rayawa,Allah ya albarkaci hafsat din adam da sunkuto santaleliyar 'yarta 'katuwa kyakkyawa Masha Allah exact copy din babanta ce sak wato captain adam sekuma sumar gashin mahaifiyarta data dakko wato hafsat,atake awajen captain adam yai sujjada ya godewa Allah ,amma hafsat haryanxu de she's unconcious haihuwarma Allah yayine kawai se numfashi take da kyar'ga bleeding datake internally!
Dakyar dr NAUFAAL yashawo kan captain adam yarage kukan dayake,"captain pls kayiwa yarinyarnan duk abinda muslulunci yace ayi,matarka Kuma Insha Allah xamuyi yadda yadace danganin ceto rayuwarta ,Sannan Ina Kayan babyn?!"kamar Statue of Liberty haka captain adam yaxama da aka miko masa yarinyarsa ahankali Kyau de abin har ba'a magana!ko takan abinda dr NAUFAAL ya kecewa bebiba,dr NAUFAAL yaceda wata nurse dake gefensa"nurse dan Allah jeki waje akwai dayar wife dinsa awaje waiting area kice Ina Kayan baby?!"
Da axama nurse din tafita tsaye taga magajiya se zagaye take kafin tayi magana magajiyan tarigata"Yaya tamutu ko?!"
Nurse din taxaro ido"pardon?!mutuwa kuma?!ni Kayan babyn akace natambayeki"
Magajiya tai shiru "kina nufin bata...to babyn fa wai kina nufin...??"
Nurse dintai tsaki tai tafiyarta tana magana Ita kadai"ko mahaukaciya ce ne,Ana xancen baby meye kawo mutuwa Kuma mtscw"
gaba daya magajiya seta nemi tsayuwa tarasa kamar xata fadi,sekace tababbiya taje takawo haka tadinga YI"Kai bade hafsat ba Ita ai yanxu tadade da mutuwa"
Nurse nakomawa labor room din dr NAUFAAL yataho da sauri yana"Ina Kayan?!"
"Dr Wallahy nibanga wadda kake nufi ba,sewata acan din Ita Kuma kamar psycho I don't think she's normal"dr NAUFAAL yai tsaki sannan yakira wata nurse awaya kan "lalle takawo Kayan baby na mata yanxu"Sannan yakoma wajen hafsat din suka cigaba da Neman tsayar da internal bleeding din datake,
Captain adam yarike 'yarsa wadda aka nannade ta a towel pink neatly se tsotsan thumb dinta take da pink lips dinta da alama yunwa takeji,rungumeta yai yana jin sonta akowane sassa najikinta tareda fadin"Allah yai maki albarka'UMMI_A'ISHA"
•
Welcome to the world baby UMMI_A'ISHA
(THE MAGNIFICENT)
The woven fiction just started,don't be left out!!!!
nanahafsat.wordpress.com
WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;NANA HAFSAT....
[4/18, 11:57 PM] Asy Khaleel: •✨UMMI_A'ISHA✨•
(THE MAGNIFICENT)
29
©•MISS XOXO
👄
DEDICATED TO
UMMI_A'ISHA👌🏼
nanahafsat.wordpress.com
•✨•✨•✨•✨•✨•
Rungumeta yai tsam ajikinsa yana fadin"Allah yamaki albarka UMMI_A'ISHA...muryar dr NAUFAAL ce ta katse masa albarkar dayake sawa tilon 'diyar tasa,
"Captain mi'ko yarinyar xa'a samata kaya"
Mi'ka masa yarinyar yai yaneme sonta har cikin zuciarsa,,,,nurse hidaya itace tashirya baby UMMI_A'ISHA cikin over roll riga pink me kwalliyan lulu catty black,da hula tayi Kyau 'das da ita se murmushi take tana 'bangala 'dan wawulan bakinta sosai tanada fara'a Kai kace babbace ake mata wasa take hakan,
Da temakon nurse hidaya Hafsat tai feeding baby UMMI_A'ISHA tanasha tai bacci dama yunwa takeji, a'dan karamin gadon babies dake gefe kusada hafst din aka ajiye UMMI_A'ISHA,hafsat tajuyar da kanta da kyar tana kallon 'yar tata...
Dr NAUFAAL yakalli captain adam da ke gefen hafsat din azaune yana addua yana tofa mata ba bakin magana tunda hafst 'din bata magana se hawaye kawai datake na azabar ciwo sunyi sunyi su tsaida bleeding din amma ya'ki tsayawa ta galabaita ba ka'dan ba shisa sukai mata allurar bacci don tasamu bedrest din da akeso mai haihuwa tayi"
"Captain kakira su gwaggo kuwa da side din Hafsat din?!"
"Wallahi bankiraba amma bari nakira su yanxu"mike wayai bayan yadanna kira yakira gwaggo mintina kalilan yasanar mata da halin da ake ciki,Sannan yakira mama ma yashaida mata,
"Yawwa captain sekuma Kayan sawan Ita Hafsat din seka tura adakko ko daganan Kuma Ina office Dina akwai takardar da danakeso kacike"
Fita captain adam yai zuwa waiting area inda yaga magajiya Ita kadai se safa da marwa take tanaganinsa tanufe shi hankalinta atashe kamar tsohuwar mahaukaciya,"yaya jaririyar?!"don duk axatonta hafsat din ta mutu
"Daga Ita har hafsat din sun samu bacci"murya narawa yake fadin"magajiya kokinsan meyasa hafsat tai wannan muguwar faduwar Xaki'iya recalling?!don tana cikin wani hali"
Hankalin magajiya seya Kara tashi najin tabbacin ai Hafsat din bata mutu ba,gaba daya meyakwan tabashi amsa ma neman guri tai tai maxauni a kujerun waiting area din tafara kuka,
Captain adam duk axatonsa yaxata don yace hafsat din nawani hali yasa take wannan kukan"addua xaki tayata da'ita magajiya kiyi hakuri dan Allah"sannan yamike yafuta daga sashen yana hawaye shima.. Yana fita parking lodge din yahango jirgi driver 'daga masa hannu yai sanann jirgin yataso yaxo inda yake"oga gani"
"Gidah xakaje gurin haule kace taxo tadakko Kuma akwatin kayan dasuka shirya na haihuwa itada auntyn ta"
"To oga yanxu kuwa,tasauka lapia kenan Toh Allah ya albarkaci abinda aka samu"sanann yashiga mota ya tayar shikuma captain yakoma cikin asibitin.....!yana komawa mama taxo ita da tawagarta da food flask na abinci dakuma katon flask na shayi cikeda kunu,
Gaisawa sukai dasu maman se sunkuyar da Kai yake mama tace "nayi mamaki aini naxata se on 30th tacemin shine expected delivery date din(edd)to Allah me yarda yaso sekuma naji kace tahaihu bacci tasamu kenan"tana kallon hafsat din
"Ehh on 30th 'din shine ainihin date din tokuma se santsi yakwashe ta,ta zume ta fa'di "
"Garin Yaya kenan?!wannan ai hatsarine inyazo da 'karar kwana"
"Wallahy nafita ina waya kenan dawowar daxanyi hakan tafaru shima mukai gaggawar kawota asibitin "
"Toh Allah yarufa asiri amma ba cs aka mata ba ko?!"
Captain adam yasosa keyarsa yana sunkuyar da kai "bashi bane dashi din xasuyi mata dansuce tabu gu sosai toh sekuma Allah Yayi ta haihu daknta ma"
"Toh Allah ya albarkaci rayuwar abinda aka samu"Sannan takalli 'yar tata yar autar su hafsat din (wadda 'yar mamance da suke uba daya kenan)data dawo daga makarnata da take a amsterdam wato ikhram"ikram ajiye yarinyar nan tasamu tayi bacci tundaxu kike jagwalgwalata kinsan babies skin yadda yake very sensitive Dan Allah ajiyeta ta huta"
Ikhram ta ajiye baby UMMI_A'ISHA badan taso ba,sosai yarinyar tashiga ranta dukkoda bacci take ba idonta biyu ba"mama na ajiye ta babyn ce she's so cute Kinga pink lips dinta,gata Kuma first niece dina inama Yaya mjay tana nan"
"TubarkAllah"cewar maman tana gyara wa babyn kwanciya,"ai gatanan setaita shan dauka 'yar mummuna da ita"tana mata wasan kaka da jika,
"Uhm uhm mama wannan ai tafiki Kyau kishi de kike kar baba(mahaifinsu)yafi sonta akanki"
"Kintuno min dakika ce baba"Sannan takalli captain adam dake gefe a xaune"babansu yace yana dawowa daga tafiya shima xexo Kasan yaje General checkup a berlin"
"Ehh munyi waya dashi 'daxu Allah yabashi lapia ameen"
Sundan jima suna hira da Maman har yan kaduna sukaxo dayake jirgi sukahau Kuma yan mintinan ka'danne,sosai aka shiga hira a nakuma jajantawa hafsat din abinda yafaru hade da murnar sunkuto yar kyakkyawa yarinyar ta datayi kowa yakalleta seya sake kallonta sosai baby UMMI_A'ISHA keda kyau ga farin jini se daukarta ake tunma baga yan Uwa ba har nurses na asibitin bangaren maternity,Banda magajiya dake gefe daka kalleta Kasan bakin ciki take dukkoda tadanne xuciarta ahankanma...!
Bayan captain adam yagaisa dasu gwaggo mikewayai yatafi office din dr NAUFAAL kamar yarda ya umarceshi dayaje din,knocking yai Sannan yashiga ciki hade da sallamarsa,dr NAUFAAL ya'ajiye files din dayake cikewa agefe tareda dago Kansa yakalli captain din waba lokaci daya yafita haiyacinsa kamar bashiba"have a sit mana captain"yanayi yana nuna masa kujeran gefe,xama captain adam din yai"gani Doctor Wallahy su mamane sukazo shiyasa seda na'dan tsaya muka gaysa"
"Ohh okay,captain pls kabani hankalinka nan wannan damuwar dakajefa kanka ciki bashi bane kalli kanka this is so not like you,har ka fada kamar Wanda ya wuni yana ciwo,worry not mana matarka Insha Allah xata samu lapia,abinda yasa nace dama kazo nafarko munaso mu'dan mata aiki ma'ana mu wanke mahaifarta kagade wannan faduwan datayi badan darabo ba Wallahy xata iya rasa ranta sosai tabugu ba kadan ba Kuma takasan mararta abin yake gashi Kasan kusan shekara ashirin ne so gurin yaxama very weak jini yana fita taciki Kuma duk internal abu yanada hatsari so xamuyi wankin after then semu dinke gurin dayahuje hakan yafaru ta sanadiyar akan abinda tafadi,seka dan sarara mata for some months.. aikanada wata matar dan dabaka da wata xance kaje Kai aure ma se gurin Yayi healing irin shine inbe warkeba haka ta faru ana samin matsala shine abinda xanfada"
"Tohh shikenan dr,Allah yabata lapia Ita Kuma Allah yarayata amma Ina mamakin yadda hakan tafaru coincidentally hakan tafaru naje waya kenan nadawo natadda da haka"
"Tohh Allah de yabata lapia shine kawai,ayau xamuyi mata komi first thing tomorrow morning kuxan fara sallama se weekly shot(allura)daxa'a dinga mata kawai Banda drugs saboda karyai affecting baby din"
"Shikenan dr,nagode Allah yasaka da alkhairi ameen"
"Ameen,haba captain Dan Allah kadena fadar haka ainine yakamata nadinga maka godia kullum,Banda abin arzikin dakake mana hadda wahalar biyan kudin Umara nida madam na harta dubai kuma gaskia mungode wanann shine best suprise ever,madam dina Ma anjima xataxo Insha Allah nabarta tadanyi abu me ruwa ruwa takawo wa me jego,yanxu anjima xan rubuta maku abinda yakamata tadinga ci saboda health dinta,Allah yabata lapia "
"To mungode fa"
"Shikenan captain xaka iya komawa nasan a nacan ana nemanka "
"Kamar Kasan sace jikinai na fito,barinje"Sannan yabashi hannu SUKA tafa yafita,
Masha Allah aranar akaiwa Hafsat aiki successfully bawani matsala aka gama,washegari da safe aka sallamesu,akullum tana samun sauki sosai captain Adam yake bata kulawa ta musanman,bayan kwana bakwai aka cika layin da motoci na tents a ko'ina a layin ana raba abincin suna super ganishing dishes aka yi Wanda akai ordering musanman daga wurin meenah center,gidah yacika yai makil da mutane harda yan gayyar sodi ga yan unguwa saboda hafsat din mutuniyar kirki ce kome aka gayyaceta tana zuwa gashi batada wulakanci mutuniyar kirkice,hafsat tayi Kyau ba karya cikin shigar ta dabaxata kirguba tasa tacire tasa Kaya yafi a kirga ga kunshi da yalayalan kitson maiduguri style....
Suna Yayi suna Yayi armashi,Wanda mjay ce kawai bataxo sefata Skype suketa magana da ita tayi kiba tayi Kyau itama hafsat nata tsokanrta kode "itama tanada unborn baby ne a makale a mararta?!"mjay tai daria tana fadin wai bakomai kawai de ni'mace irinta kasar waje dakuma kulawar mu'ayyad,amma tananan xuwa bada da'dewaba"
Anci ansha masu doubling sunyi,komai awadace tunda asubah da liman yasanar da sunan yarinya UMMI_A'ISHA aka fara sadaqa,se wurin 10 dare sunan ya tsaya Wanda akai a farfajiyar gidan dayake katoto ne xa'a faka mota sama da talatin dayake duk yasai filin kusa da gidan seya shigo dashi ciki, shanu biyu raguna uku aka yanka duk na sunan UMMI_A'ISHA,savouniers kala kala haka adinga bin mutane dashi da rubutu boldly a rabuce'welcome to the world baby 'UMMI_A'ISHA'......!
WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;NANA HAFSAT.......
[4/18, 11:57 PM] Asy Khaleel: •✨UMMI_A'ISHA✨•
(THE MAGNIFICENT)
30
©•MISS XOXO
👄
DEDICATED TO;
UMMI_A'ISHA👌🏼
nanahafsat.wordpress.com
•✨•✨•✨•✨•✨•✨•
__Sosai baby UMMI_A'ISHA ke 'kara girma 'bul'bul da ita kamar wadda ake bata wani abun lokacin datakai kwana arba'in kuwa kamar wadda tai wata uku saboda girman jikinta kowa sonta yake yana daukarta 'yar gwanin sha'awa da ita ,inka cire iyayensa Capt Adam yanxu babu Wanda yafi so duk duniya irin baby UMMI_A'ISHA yanakiranta da(honey boo boo)'daki sosai aka gyara mata komi nacikin 'dakin pink and purple kamar dakin 'yar budurwa babu abinda babu aciki an tanadeshi inta girma dayake tanada garin jiki xatai saurin girma...!
Tana cika kwana arba'in sukaje kaduna sosai sun zaga dangi har hadejia sukaje suka gayda yan'uwansa na uwa dana uba tunda'yancan 'dinne dukkansu iyayen nasa,bayan nan suka biyata yola suka yada xango a family house dinsu hafsat din dayake mahaifinsu asalinsa dan yola ne jimeta,aikine yakawo mahaifin nasu alhaji kasheem bn muhammad Kano inda yahadu da mahaifiyar tasu a Kano din marigayiya Hajia ameena,Wanda su yan kano ne yan cikin gari unguwar tudun wuzirci can kusada unguwar gwangwazo,ta rasu lokacin data zo haihuwar mjay inda daga baya aka bashi kanwarta hajia fareedah ya aura..daga yola suka dawo kano nan suka zazzagaya danginta sosai duk inda sukaje se captain adam yamasu abin arziki itama danata kyautar turamen atamfofi da sun'kin sabulai...!
Lokacin da UMMI_A'ISHA tacika wata biyu aka fara kaita gidansu hafsat din ana matso mama a feeder atafinmata dashi,ikhram ce ke yawon xuwa daukarta har hutunta yakare ta tafi,mjay ma taxo da nata 'dan karamin cikin satinta biyu mu'ayyad yaita kiran awaya adole mama ta matsa mata tatafi.....!
Ranar wata alhamis da safe lokacin captain adam yatafi abuja kai resignation letter dan yanxu yayanke decision din yai retire awurin aikinsa yabude wajen saida motoci da company sosai kuma yakeda share holders asauran oil and gas holders,zaune take adoguwar couch din dake gefen parlor din nata gefe daya Kuma haule ce zaune da UMMI_A'ISHA ahannunta tanata bu'de wawulan bakinta,
Knocking akai akofar parlor din,haule harta mike xata bude kofar hafsat tadakatar da ita"barshi haule xanbude ke aida yarinya a hannunki"bu'de kofar tai saikuma tai saurin komawa baya tana dafe ha'ba"kode gixo nai,kai banan bane batan kai kikayi"Sannan tasa hannu tana janye kofar kushigo ciki,
Matar da akacewa haka tai murmushi tana "babu wani batan kai ainafiki mutunci ma waye yazo gidannan last?!ni ce"
Hafsat tai daria "kede shigo kawai kinci albarkacin handsome boy 'dinnan"tafada tana shafa kan 'dan kyakkyawan yaron dabaxefi shekara 5 zuwa 6 ba,
Drinks da snacks aka kawo masu sannan haule tamike tatafi kitchen don kawo masu abinci,hajia fatee 'kawar hafsat din tataso tadawo inda hafsat din take tasa hannu takarba UMMI_A'ISHA dake faman wangale mata baki"Masha Allahu tubarkAllah kyakkyawa da ita wallahi Allah yarayata yanzu tayi wata biyar ko?!"
"A'a fah watanta biyu da sati 'daya"
"TubarkAllah kinsan dakika turomin pic 'dinta a whatsapp duk axatona xatai 5months wallahy,Allah yarayamana ita"
"Ameen,ashe dagaske kike daki kacemin xakixo naxata iya shegen dakika sabane badan handsome boy dinnan ba aibaxan barki kishigo ba"
"To tuba nakeyi kaina bisa wuya,Wallahy balefina bane tunda mukabar zaman america muka dawo abuja wallahy babansu baya bari inzo garinnan gashide anan ya aureni ya gwanmace idan yara suka samu dogon hutu muxo Kuma bama wuce sati xuwa sati biyu,amma Kuma ninaxo karshe"
Hafsat tai daria"fatee kenan Banda abinki shekara nawa rabonki da nan 'din?!dan inaga tunkan asan da cikin wannan handsome boy 'din"
"Gaskia anyi shekaru aide gani nazo,gashinan dan auta"tanayi tana kallon 'dan nata"zo MUHANNAD kaga kyakkyawar baby,yanasan baby yace mama yaushe xaki bamu baby muma?!"
"Gaskiane gwara ki haifo masa kanwa shima,sunan wa'aka samai ne?!wanann dukyafisu kyauma kode mucanje akai a asibiti?!"ta kyalkyale da daria,
"Haka ake cewa waiyafini Kyau dagani har uban,dama bakisan MUHANNAD ba?!gaskia mundade bamu haduba,sunan baban mahaifinsu akasa mai IBRAHEEM KHALEELULLAH amma se ake cemasa 'MUHANNAD' gashinan shekararsa shida fa yana primary one"
Tasowa MUHANNAD 'din yai yaje inda maman tasa take yasa hannu yana Shafa kan baby UMMI_A'ISHA,"mama yasunanta?!"
"Sunanta UMMI_A'ISHA"
"Mutafi da ita mama"
"Rufamin asiri MUHANNAD,kafin kasa akawo bataliyar 'yan sanda suka mamu,kana sonta ne mekyau da ita ko?!"
MUHAMNAD yai nodding kansa,
Hafsat tai daria "xataxo maku Insha Allah kafin kutafi batada rigima,kusan kullum agidanmu