Showing 39001 words to 42000 words out of 107296 words

Chapter 14 - UMMI A'ISHA(THE MAGNIFICIENT) COMPLETE

22 Aug 2024

7717

atsakar gidan ta wanke jikinta ,matar tayi tayi takai mata ruwa bayan gida ta wanke jikinta taki,haka ta damalmala kayanta koma ta xauna se kumbura take Kamn funkaso,

Fitsari ne ya matsi magajiya ba shiri ta mi'ke tana xare ido"akwai bandaki mekyau fitsari nakeji"

"Ehh bari akai maki ruwa yanxu aka deboshi na dam ne"

Magajiya ta rataye mayafinta a kofar dakin Sannan tashiga cikin bandakin dake tsakr gidan,ware Ido tayi ganin shaddar a bude ga kashi nan yana mata Sannu da zuwa dake shaddar a bude take,amai yataho mata cikinta ya kulle taje xata tsugunna agefen shaddar dataga yadanfi kyau kawai seganin wani wandon yara tayi cike da kashi fal aciki,dukkoda warin daya cika hancinta haka ta takarkare ta daki Kara,bashiri baby Kay,UMMI AISHA da matar suka kwaso aguje sukai hanyar bandakin,ca'ba ca'ba suka sameta cikin kashi tana kuka,matar taso tayi daria seta daure de kawai,

Ta tayata ta tashi taje ta dakko mata zani da ruwa abokiti ta ajiye mata da sabulu irin yankan na wanki dashi suke wanka,magajiya tana kyankyami tana komi haka ta wanke jikinta tafito,matar ta bata kayanta sabo fil atamfa,bayan ta gama tafito UMMI AISHA tadaure tace"Sannu umm..."bata karasaba magajiya ta wurga mata harara"se intashi namaki dukan kawo wu'ka Wallahy,duk ba lefin Ki bane yar kan uba dangin mahaukata"

UMMI AISHA tai shiru inda Sabo ai ta saba,matar tai shiru tana naxarin wannan BAKON LAMARI,dakyar ta iya fadin"diyar mijin kice itama?!"

"Ehh itace 'yar kishiyata mahaukaciyar nan hafsatu ba,dangin mahaukata ba"

Itade matar bata Kara maganaba,ba acika minti 30 ba dakin ya cika da matan kawunansu,sunfi mintina talatin ana gaisawa bayan an malala taburma cikeda Kayan abincin kauye ,dukkoda bawanda ya ishisu magajiya,"ke 'yar balarabiya baxakiciba"acewar wata mata dake tambayar UMMI AISHA"wallahi a'koshe nake,amma barinsa albarka"bayan tadan gutsiri biskin gero tasa a bakinta....baby Kay kuwa ko hannunta bata yarda tasa kan abincin nan ba,

Ana cikin haka captain ya shigo cikin gidan,gaggaisawa sukai da matan Sannan ya masu sallama yabasu wrapper dubu hamsin yace matan su raba,bayan can waje Kuma yaba kawunnannata dubu Dari yace su raba,haka magajiya sukai sallama da yan uwanta ko kwabonta bai shiga hannunsu ba saima murnar barin garin daxasuyi takeyi....

Akan hanyar su ta komawa captain adam ke kallon magajiya ganin ba kayanta bane jikinta"ya akayi na ganki da wasu Kayan davan?!"

Takwashe labarin komi tabashi harda 'kari,captain Adam ya girgixa Kansa"amma abu beyi dadi ba Ina Kayan naki to?!"

"Ga sucan cikin boot ko cikin gidah baxasu shiga ba se laundry"

"Amma magajiya kinban mamaki kinaso kice min wa'encan da bawani hali ne dasu ba su fiki wadatar zuci kenan tunda har suka barki kika taho da kaynsu amma kika kasa bar masu naki tir da halinki Wallahy"

"Akan wannan yamutsattsiyar atamfar kake gayamin magana?!lace Dina Kasan nawa ne kuwa xan bar masu?!"

"Nasani mana tinda dukta je tadawo nina siyo shi Kuma ko nawane lace dinki ai dattako ko Ma Abu ne mai Kyau,Sannan ko nawa suka siya atamfar idan Ma naira Dari ne Wallahy sunfiki sau dari tinda sun barki kin taho masu dashi,Kuma ko bakyaso sena gaya maki gaskiya abinda kikai har ga Allah baki kyauta ba,gashi nan abinda suka bamu cikin boot Kuma dukke xakiji dadin amfani dasu,kije Kiyi tayi"

Magajiya tacika tai fam,har suka Isa kaduna Batai magana ba,maigadi yatayasu shiga da Kayan kauyen da aka basu cikin gidan,,,bayan dawowarsu daga Zaria da sati daya UMMI AISHA ta shirya kamar yadda baffanta Yayi niyya taje tayi sati daya akano kafin moc exams dinsu,har Kano driver yakaita gidansu mama kakarta wannan karan Aunty mjay tananan da ya'yanta guda biyu 'yusra da haneef'se shrye shryemu bikin su habbab da hanbal ake Wanda a satin ne akayi bikin,kwananta bakwai cif tadawo kaduna cikeda kewar yan'uwanta,,,bayan tadawo washegari taje islamia a hanyar dawowa wani matashi a Benz yake binta ta mota yana tuki da hannu daya ya xuro da kansa ta window"malama dan Allah minti daya"

UMMI AISHA tai biris dashi taci gabada tafiyarta,shikuma yana binta ta baya har sukaje kofar gidan se magiya yake mata"Dan Allah fa nace gaki Kuma daga Islamiyya kika dawo daga ganinki anga ustaxiya"hakan daya fada bakaramin Daria yabata ba bayadda ta iya haka taja ta tsaya ganin ya hadata da Allah"Yawwa ko kefa"yace da ita yana futowa daga cikin motar..hakan daya faru karaf a idon baby Kay bayan ta fito daga wani shopping complex dake kallon gidan nasu,fuu tashige cikin gidan kamar iska taxubarda ledar data siyo Kayan kwalliyan a kasa tana bubbuga kafa,magajiya ta mi'ke daga xaunen datake tana nifar inda baby Kay din take"lapia babyn ummah?!"

"Ummah,Kinga zungureriyar jeep na Benz new model dataxo wajen UMMI AISHA?!ummah bakiganshi ba Wallahy"tafadi hakan tane lekensu UMMI AISHA dake balcony din gate din gidan dayake ana gani ta cikin window,

"Kan bala'i"magajiyan tace taname sake bude curtains din tana kallon zankadeden yaron da yazo wajen UMMI AISHA"Sannan tajuya tafara sauka daga stairs tana huci kamar tsohuwar zakanya.....!





Gaisuwa mai tarin yawa gareku masoya littafin UMMI AISHA,Nagode kwarai da gaske naganin sa'konninku a Wordpress dina da Kuma whatsapp chart,harda masu kirana awaya danjin ko lapia shiru haka Kwana biyu banyi posting ba?!
Na koma makaranta shysa abubuwan se ahnkali,ina me Baku hakuri Ina Kuma fatan xa'agane uzirina...
Nagode kwarai da gaske Allah yabarmu tare#Ameen...!


WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;NANA HAFSAT.....
[4/18, 11:57 PM] Asy Khaleel: •✨UMMI_A'ISHA✨•

(THE MAGNIFICENT)
42

©®MISS XOXO
👄

DEDICATED TO;
UMMI_A'ISHA👌🏼

nanahafsat.wordpress.com

•✨•✨•✨•✨•✨•


Azuciye tafara sauka daga stairs tana huci kaman zakanya,da sauri baby kay tabiyota tana magana"ummah bade wajen su zakiba ko?!"

Magajiya na huci take fadin"can zanje mana"tafadi hakan tana karasa sauka daga stairs din...da sauri baby kay tariko hannun magajiyan tana girgiza kanta"ki kyalesu ummah yanxu inkinjema yaya yahya(abokin baffansu) yana facing wajen da suke"

"To yaya kikeson nayi, kinasan nabar UMMI AISHA dawancen na wajen dayaxo a Benz?"tafadi hakan tana nuni da Inda suke da hannunta

"Ummah fault dinki za'agani its better kibari baffa yadawo seki san mexaki ce masa"

"Shikenan muje aiya kusa dawowa"

Haka suka koma saman suna shirya yadda xa'ai idan baffan yaxo

Bangaren UMMI AISHA kuwa tsayawa tai kaman statue of liberty mutumin se zuba yake shi kadai kamar famfo"Toh dafarkode kamn yadda nace maki sunana abdulshakur Mahmoud,asalina dan garin maiduguri ne dake jihar borno aiki ne yakawoni nan garin Kaduna inada mata ta daya da 'ya guda daya kuma tunda naganki baiwar Allah najikin kwantamin,ko xan iya sanin naki sunan?!"

UMMI AISHA tai shiru kamar me tunani da kamar baxatai magana ba sekuma tace"tohh malam abdlshakur ni sunana UMMI AISHA ina xaune anan tareda iyayena da yan uwana,sannan aji na biyu a secondary"

"Masha Allahu"yafadi hakan yana shafa cyboc dinsa "tohh malama UMMI AISHA naji da'di kwarai dagaske dakika bani hadin kai mukai magana dake ta fahimta,kuma tunda na'dora idona akanki bawai yaudara ba naji inasonki har cikin zuciyata inakuma fatan kizama matata uwar ya'yana"

UMMI AISHA tai murmushi hade da kallon lokaci ta fuskar agogon dake hannunta na hagu"well naji duk abinda kace kuma zancen gaskiya badan ka hadani da Allah ba walllahy baxan saurare ka ba,kuma mu ka'idar gidan muce se mun karashe karatun secondary muke sauraron mutane zancen aure ma kuma wannan bai taso ba domin mahaifinmu yanaso muyi karatu,kuma insha Allahu zamu cika mashi burinshi,ni xan wuce gidah"

Gaba daya se yaji UMMI AISHA takara kwanta mashi azuciya domin tanada kaifin hankali da basira daga ganinta,murmushi yai wanda yake kara fito da ainihin kyansa domin ba laipi kyakkyawane kuma baxe wuce shekara talatin da biyar ba a duniya"tohh shikenan gimbiyata yadda kikace hakan za'ai,barin kyaleki karmuyi laifi wajensu mama ko?!kar nazo nan gaba neman aure a hanani"

Itade UMMI AISHA daria kawai tai sannan ta masa sallama ta wuce cikin gidah bayan yayi yayi ta karba hasafin dayai mata na kudi taki,hakan ba karamin sake burgeshi tai ba domin ya lura da ita ba irin yammatan zamanin nan bace wanda suka zamto kaji seda 'tsaba,kaida kudinka suke ko kari kamar su dan neka su kwace,haka yajuya kan mota yai reverse cikeda kaunar yarinyar daya fara tozali da ita yaga kuma ta kwanta masa arai wato UMMI AISHA...


•✨•
43

____Tana shiga cikin gidah gabanta yafara dukan uku uku nasanin abinda xataje ta tarar ganin Baby Kay taganta dashi,da sallamarta tashiga cikin parlour din tayi mamakin rashin halin ko'in kula da magajiya da baby kay din sukayi mata,haka tashiga cikin daki tana mamaki dukkoda tasan akwai wata a 'kasa .....

Bayan sallar isha'i kamar kullum captain Adam yadawo se magajiya ita kadai a parlour tarairayar arxiki tayi masa dan yayarda da abinda zatace

Seda yagama cin abinci yahuta hankalinsa kwance sannan magajiya ta goce tafada mashi karya da gaskiya harda fadin wannan bashine karo na farko ba tanayin hakan tun captain adam najinta kawai harya yayarda tunda tafadi in karya take yatambaya abokinsa yahya yaji agabansa akai komai

Haka yakira UMMI AISHA yaimata fadan fitar hankali,Ranar magajiya dadi kasheta kamarta zuba ruwa akasa tasha don farin ciki.......

Har su UMMI AISHA sukai moc exams dinsu babu wanda takara saurara dukkoda samari ke turereniya a kofar gidan kamar tururuwai wataran baby kay ke fita wai koxasu kyasa amma duk a banza ....

Ranar wata litinin dasafe lokacin su UMMI AISHA na makarnta sunshiga ss3,muna-b abokiyar magajiya ta tsibbu da makirci ita taxo gidan,bayan sungaysa sunyi komai muna-b kefadin"kawata haryanxu bawani labari a kasa?!"

"Hmmm kawata kenan ai babu komi ingaya maki shiru fanai nakasa fada maki dr nmadi yaciremin mahaifa baxan sake haihuwa ba,sannan wannan zubar gashinde haryanxu ina yinta,daxu ma da safe Allah gashin daya xuba akaina sekin tsorata,danasa hannu yake fita yanxu kuwa abin was far beyond worst danacire dankwali zakiga yaciro da tulin sumar kaina"


"Kai amma dr nmadi yacika dan iska yanxu seya cire maki mahaifa for what reason?!,saunawa nake samin irin matsalanki kuma magani da shots kawai yake bani amma may be nakin yafi nawa, maganar xubar gashin nan naki yafara bani tsoro,karde ace ?!!!! Kai insha Allah ma bahakan bane"muna-b tafadi hakan tana girgixa kanta alamar tausayi

"Ameen de, nifa takaici goma da shatara suke damuna kinga adam tun ba'tan hafsatu ya kauracemin bama hada shimfida dashi kwata kwata, gashi kullum cikin maganarta yake,kullum hafsatu,hafsatu,Hafsatu yake. Rannan secayaimin wai wallahi magajiya inaji ajikina my hafsat takusa dawowa garemu inaji ajikina my hafsat tana raye kuma duk inda take insha allahu xata dawo gidah kullum maganarsa kenan kamar zaucacce fa,ga abinda yafi tsayamun awuya ma shine yarinyar nan mekamada diyar aljanu kullum kyau take, bakiga samari ba yanda suke layi kamar ranar za'be nayi nayi amma duk a banxa gashi tawa'yar se mutanen banza ke zuwa wajenta harda Wanda bekai matsayin ace yana sallama da itaba shi zakici muryarsa na dukan dodon kunnenki wai khadija tazo .....kai nagaji wallahi menene mafita yanxu kawata bani shawara?!"magajiya tafadi hakan tareda kara zabga uban tagumi!!!

Nannauyar ajiyar zuciya muna-b tasaki sannan ta nisa kafin tace"yanxu mafita'daya ce kawai kawata,inkikayi amfani da ita ita kadai ta wadatar"

"Ina jinki kawata"

Tashi muna-b tai tadawo kusada magajiyanta zauna"kawata abu xa'a maki da zaki maida adam din tafin hannun ki tunda kingama haihuwa kisamu ki banbari rabonki wajenshi,ki tatse shi tass, sannan ita kuma UMMI AISHA xamusan yadda xamuyi da ita Wannan aikin duk kibarshi a tafin hannuna"

"Nagode kawata Allah de yamaki albrka,yaya zancen alhaji lirwan din kuwa?!"

"Kyale wannan banxan shi aure yakeso muyi nikuma nagaya masa ba aure a policy dina"

Magajiya ta tuntsire da daria"shegia kawata,kunci xamaninku kunacin nawasu"

"Kede bari kawata abin se hamdala kawai"

Haka sukaita hirarsu ta yadda xasu magance wannan gobarar dake neman kunnowakanta cikin gidan...



•✨•
44

____Kwanci tashi ba wuya awajen Allah su UMMI AISHA anfara waec kyau da kokari se abinda yai gaba,ba lefi kam magajiya ta fara samin captain adam a hannunta,....

Zaune suke a babban parlourn gidan,baffa sameer ne da captain adam ke magana irinta yan uwan juna wanda suke sada xumunci kuma suke bawa yan'uwantaka hakkinta,Baffa sameer dake kishingide a babbar couch din dake parlourn ya ajiye wayar dayake YI kenan tareda sakin siririn tsaki"wai kaji kuma meeting dinnan na yarannan farkon watan gobe ne"

"Ohh haba,ARFAAN KO MUS'AB?!"

"A'a wane ARFAAN kuma?!MUS'AB dake katsina nake nufi fa"

"Ohh allah yakaymu yaya,nixan wakilceka insha Allahu,Allah deyakymu"

"To shikenan Allah yakaymu adam"

A ranar dasu UMMI AISHA suka gama last paper dinsu na ssce school dinsu ta hada masu babban party Wanda yakunshi tundaga kan daliban makarntar har izuwa iyaye da yan gayyata,cike dogon table din dake gaban principal din makarntar yake da awards kala kala na daliban da suka gama makarantar,

Su magajiya anzo tareda matan baffa sameer harda su mama da ikhlas duk sun hallara dayake akwai walima da captain sameer din ya shiryawa ya'yan nasa kwara biyu a duniya UMMI AISHA DA KHADIJA!!!

Sosai da bude taro da addua aka fara,then se Dan speech daga bakin school teachers din dakuma wasu students din dake fadin alma mata dinsu na makarantar,seda aka gama Bawa kowa lokacin har anbawa KHADIJA nata award din amma Akan best fashionista and breath taking student of the year saboda tsabar kwalliya data iya da Kuma fashion a school din,bangaren academic performance ba'aya betaba ko kadan sefa bangaren fashion da Kuma wacce tafi kowa iya shiga,,,

Se lastly but not the least,abinda principal din yafadi kenan,I will like to call on stage the best student of the year base on academic performance ,award din nata me ta ken"masterly brilliant and spectacular impressive"Wayyo xokuga yadda audience suka dau murna dan kowa yasan ta cancanta Kuma abin a yabeta ne akuma girmamata,"Masha Allah"abinda captain Adam yafadi kenan ,

Taro Yayi taro anci ansha Ankuma kashe selfies ba iyaka,UMMI AISHA Tasha Congrts ba adadi,bayan sunkuma gida kuma aka fara walimar da captain adam yahada masu,walima tayi Kyau anyi buffet kala kala masu takeaway sunyi masu doubling suce ba'a basu Ma duk sunyi ,savouniers ne kala kala arubuce boldly congrts on your ssce grad,UMMI SHATU and KHADIJA,

Bayan sati daya da kammala SSCE dinsu UMMI AISHA taje Kano wajensu mama kamar yadda baffansu yace tayi sati biyu tadawo,akuma karshen satin ne captain Adam ke shirye shiryen xuwa katsina halattar taron da aka saba shekara shekara na daliban da suke karshen zangonsu na karatun degree a jami'ar Umar musa yar'adua dake katsina,

•KATSINA

___"ASHRAF badakai nakeba?! Nace kafadamin meyasa baka zuwa makaranta har malamin ku ke kirana batin ko kasamu spill over ne baxa'ai graduation din dakai ba?!,badakai nakeba baxaka bude baki Kai magana ba?!kasan halina sarai wallahi bakai girman dabaxan laka'da maka danbanxan duka ba agidannan"fa'dan da Hajia barira keyi kenan mahaifiyar su ASHRAF ,uwar 'dakin Hafsat matar captain adam dake garin katsina ayanxu!!!!

ASHRAF dake gefe a hakimce yana danna waya yamike tsaye yana fadin"mama nifa bani count me out a wani graduation da xa'ai a umyuk saboda project dina Ma na yagashi into pieces malaman basuda manners wai su abu kadan sesuce they give result in learning and character,to kawai saboda mun samu sabani da wani abokinmu aiharda khaleel ma yasani shine malamin yake gayamin magana akan wai banida characters project dinama sede yatema kamin yabani D nikuma na yayyaga project din na xuba masa akansa,that's it kawai mama"

Hajia barira tabude baki tana salati tana tafa hannuwa"ASHRAF dama abinda kai kenan a makarantar to nemi waje kaxauna Bari babanku yadawo nagaji wallahi shekararka nawa?!tun a secondary kake wannan shirmen naxata yarintace ashe tsantsar rashin mutuncine da rashin sanin halin yakamata,ubanka ba tafiya yake kudi na xuba ba ballanta kace xakai abinda kaga dama,koshi daka ganshi a haka seda yai karatun Sannan yasamu aiki,Dan anbaka D baxaka karba kace Allah yasawa abin albarka ba?!seka karba ka yaga,ammade anji kunya sa'oin ka dakuka shiga tare Gashinan xasuyi graduation din ai su barka Wanda bakowane yajanyo maka ba kada ka zargi kowa Se kanka,koda yake ni yadda malamin Ma Yayi yamin daidai don KO Bakada character din sam Bakada Ita,kaga khaleel dakuka taso tare shi xe gama kaikuma sede ka fara da karamar kanwarka Ayush data gama secondary wannan shekarar,kaga kuwa kaji kunya"Neman waje tai tanata mita Ita kadai shima ASHRAF din samin gefen kujera yai yaxauna Se taunar chewing gum yake abinsa,da alama ASHRAF irin arrogant mutanen nanne da basusan yakamata ba,

Hajia barira bata karasa xancen zucin datake a zuciyarta ba muryar mijinta Kuma mahaifin ASHRAF ta doki dodon kunnenta"assalamu alykm"alhaji kabeer yafada yana Neman sunce igiyar sau cikin takalminsa na company din hems(h)

"Wa alykm salam"Hajia barira Tafada tana mikewa tsaye takarba brief case dinsa..,,


•✨•

"Gashi captain adam xashi katsina,inda Hafsat dinsa take,KO Hafsat xataga hayatee din nata kuwa shin xata ganeshi KO kuwa?!"

___gaisuwa mai yawa tareda 'dimbin fatan alkhairi ga masoya littafin UMMI AISHA,Ina sonku Kuma Kuna Raina akoda yaushe,mamma Jameesh acigaba da hakuri dani,Ina miko gaisuwa ta ta musanman,makaranta KE dawainiya dani,

"Congrt darl sis(UMMI AISHA)for the successful completion of your astonishing woven fiction RUWAN KASHE GOBARA,Allah yakara basira ,littafi Yayi bawani dogon turanci,Allah yamaki albarka(THE MAGNIFICENT)da DUK Ma Wanda suka kammala novels dinsu Allah yakara basira da kaifin Ido,dama wa'enda suke kanyi ayanxu Allah yabamu kwarin gwiwar karasa fadakarwar da mukeyi.
Barka da juma'atu babbar rana Allah yabamu alkhairin dake cikinta amiin.....!"




WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;NANA HAFSAT......
[4/18, 11:57 PM] Asy Khaleel: •✨UMMI_A'ISHA✨•

(THE MAGNIFICENT)

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login