Showing 57001 words to 60000 words out of 107296 words
yana reverse da motar,dede lokacin da hafsat da UMMI AISHA suka fito daga gidan bayansu Kuma MUHANNAD ne da Hajia sakeena da alama rakosu sukayi sunfito wajen,se haule agefe dake rike da leda a hannunta,
"What the fu.."ASHRAF yafadi hakan yanasake runtse idanuwansa,
"What??"jay ya tambayeshi yana gyara xaman sunglasses dinsa ta mirror,
"UMMI AISHA ce gatacan"
"Where?!"
"Gatacan tareda wani suna magana"
"Mysterious gurl dinka xakace"Sannan jay ya leka yana kallonsu da'di kasheshi naganin yanzu dole ASHRAF yadauka plan dinsa,
"Wow perfect match"jay yakara fadin hakan in a romantic sound'
"What the ...,abeg yanzu yaxanyi jay?!kalli yanda suke magana da guy dincan"
"Kuma sundace ba"
"Jokes apart,pls yaxanyi?!"
"Wannan plan 'din shine best solution de"
"Ohhh f*ck it!yanzu dole senayi hakan,Shikenan"
Shide jay shiru yai abinsa yana sake 'karo volume din 'kira'ar shureim dakeyi bil tartil'sannan yaja motar sukai gaba,ASHRAF se lekensu UMMI AISHA yake da MUHANNAD musanman yadda take sakarwa MUHANNAD dinwannan tsadadden murmushin nata Wanda bakowa takeyiwa ba sewanda ya 'can'canta,
Bayan Dawowar ASHRAF gidah yarasa yadda xeyi kan plan dinsu da jay,se mirgine mirgine yake akan gadonsa,dakyar ya iya tashi yadakko wayarsa yakira baby Kay kamar yadda jay yace masa,ringing biyu tadauka tasa akunne,
"Hello baby boo"
Yadan jima yana naxarin sunan daxe kirata dashi taji da'di can yanisa yace
"Soulmate"
"Na'am baby boo yagidah?!"
"Lapia qlau soulmate,couldn't sleep inata tunaninki"
Baby Kay taware ido kaman yana kusa da ita"awwwn how sweet!?"
Dauriya kawai ASHRAF yakeyi gefe daya Kuma yanawa jay Allah ya isa na halin daya sashi ciki,sundanyi hira babu lefi Sannan yasako plan din jay ciki,
"Soulmate"yafada ahankali cikin muryar daxata ratsa magudanar jininta,
"Baby boo"tabashi amsa a shagwabance,
"Nace kinada note din logic and method of law?!"sarai yasan ba note takeba,shiyasa plan dinma xeyi working,
"Baby boo"sekuma tai shiru can tace"nabarshi wajen Frnd dita xata kwafa"
"To yaxanyi kenan yanxu?!dan Akwai abinda xan duba ciki"he's getting more interested kan xancen da suke saboda yaga plan dinsu yafara working,
"Sede natambaya UMMI AISHA"
kamar ya daka tsalle saboda murna,jinta ambaci hakan,amma ya basar shi adole bedamuba"soulmate dole se wurinta?!"
"Gaskia dole sede ita kace Akwai abinda xakai ba?!"
"Of course"yafadi hakan da sauri kafin tacanxa abinda tai niyya
"To barin karbo senai snapping na turo maka ta whatsapp,xankiraka bayan na karba"
"No karki kashe,bakisan yadda nakejin sweet voice dinki ba,amma inbakiso shikenannnnnn...."yaja Shikenan din cikin sigar da xata tarwatsa mata lissafi,
"No it's okay,"Sannan tatafi da wayan a hannunta suna waya ahaka har part dinsu UMMI AISHA dake xaune sunata hira itada haule,Ita kanta UMMI AISHA tayi mamakin ganin baby datai awannan daren tunda bayan isha'i ne lis
Koda ASHRAF yaji alamar baby Kay tashiga bangarensu UMMI A'ISHA dasauri yasa a handsfree yasake gyara kwanciyarsa,yanajin sanda baby Kay ketambayan UMMI AISHA,
"Ina note dinki na logic and methods of law?!"
"Mexaki dashi"
Dasauri ASHRAF yace "soulmate"
Jin ya kirata yasa baby Kay tamaida wayan kunnenta"yes baby boo"
"Kisa a handsfree banajin muryanki sosai pls love"
Aifa baby kay tafara blushing,gaba daya se murmushi take kaman Wanda akaiwa bushara,
"Okay baby boo"
Sannan tadanna tasa a handsfree,ta juya takalla UMMI AISHA Sannan tabata amsa"baby boo nane xe duba abu ninawa note din baya wajena"
"To fa"UMMI AISHA tafadi hakan Sannan tadakko littafin ajakarta ta mika mata,
"I love you hun"ASHRAF yafadi hakan gashi a handsfree ne Kuma yana sane,
"Love you most baby boo"baby Kay tafadi hakan a takaice tana kallon UMMI AISHA da hankalinta ma baya wajensu,ita danna wayarta ma take,
"Barin snapping xankira back kaji?!"
"Take ur time precious,muryanki meant alot pls"
ASHRAF fa yafara hargitsawa 'Yar mutan hadejia lissafi dakyar baby kay take iya daukar pages din a Dayan wayan nata,sedata kammala tsaf Sannan ta mikawa UMMI AISHA,
"Thank you"
Nodding kanta UMMI AISHA tai Sannan ta karba littafin ta maidashi cikin jakarta,a hankali baby kay tamike tsaye tafuce ASHRAF se kwararo love words yake Wai dukdan UMMI AISHA taji haushi,koda baby Kay tafita haule tagyara xama tana kallon UMMI AISHA,
"Nikwa uwata dawa take waya hakan?!"dayake khadijan sunan mahaifiyar tane,
"Waya sanine kila wanine,Yawwa Aunty haule cigaba da bani labarin yarintar tawa ko saida safe?!"
"Allah de yabaku maxaje nagari ameen,Allah yatashemu lapia"
•BAYERO UNIVERSITY KANO,
(POLITICAL SCIENCE DEPT)
"Kai Waliyya kawai dan yau kinzo dept dinmu shine xakice xaki tafi yanxu bayan kince bakida lec?!"UMMI AISHA ce ke maganada childhood Frnd dinta Waliyya!
"Tawan ke dince se meyakwan muyi hira kinxauna se danna waya kike kina murmushi"
"Ni da ya MUHANNAD ne"
"To masu yaya,kece ya ARFAAN,ya MUS'AB,gakuma wani ya MUHANNAD din"
"Are you jealous?!"
"Allah yarufamin asiri"
Daria suka kyalkyale dashi sannan suka tafa,dede lokacin kiran MUHANNAD yashigo wayan UMMI AISHA da sauri tadaga ta Kara a kunnenta,
"Hello ya MUHANNAD!,ehh,Ina school,kashigone?!nagama lectures tundaxu,na'am nida 'kawatane Walisco,to barin tambayeta tukun.."Sannan ta cire wayan tamaida dubanta gun Waliyya,
"Ya MUHANNAD ne wai Dan Allah muje can flavors yasai abu seya maidamu gidah pls muje ko?!"
"Kinsan inde akwai special yummy treats mexe hanani xuwa?!"
Daria UMMI AISHA tai Sannan tamaida wayan kunnenta
"Shi kenan sekaxo"
Ba'awani 'dau Lokaci ba MUHANNAD yaxo cikin motarsa Lincoln lx,,yadebi su UMMI AISHA,duk wannan abin dasuke akan idon jay da ASHRAF dake xaune cikin motarsu,
"To yaxamuyi yanzu?!"
"Just call her sis"
Kiran baby Kay ASHRAF yai ba'awani dau Lokaci ba baby Kay ta iso tana rangwada,
"Baby boo"
"Soulmate,you lk beyond beautiful"
"Thank you baby boo and so you"
Fitowa jay yai daga motan yana shafa cyboc dinsa bawanda yasashi yafadi wani abin bakinsa tsulum yake fadin
"nice catch dude,kanatamin describing din bae dinka wannan aitafi beyond yadda kace"
ASHRAF yawatsa masa wani kallo yana wurga masa harara,sannan yakoma ta 'bangaren baby kay yabude murfin motar yana kallonta,
"Ladies first"
Baby Kay tai fari da ido sannan tashiga ciki tana murmushi,jay yaiwa ASHRAF sign sannan yakoma yashiga tasa motar yatafi,shikuma yashiga yatada motar sukabar wajen,
"Yanxu naga sister 'dinki tabar wajen nan"
"Ohh haba?!,ko driver 'dinmune yaxo barin kirata"
Murmushi ASHRAF yaijin baby Kay xata kira UMMI AISHA,kiran UMMI AISHA tai tasa a kunnenta,
"Yeah hello!kina ina UMMI?!ina nemanki ance kinbar school din Yanxu,oh haba kina Ina?!banajinki ohh flavo...,"
Bata karasa fadaba ASHRAF yai saurin katseta
"Honey ai flavors dinmuma xamu,save ur credit"yai saurin fadin hakan kamar dagaske dukkoda dama soyake yasan inda xasu danya 'kunsa mata haushi,
"Okay sugar pie"Sannan takatse wayan batareda tamayarwa da UMMI AISHA reply ba
•FLAVORS
Flavors ha'dad'dan gurin cin abinci ne dake titin kan hanyar xuwa bayero university,kodah su MUHANNAD suka isa,wuri yamasu reserving su uku sannan suka zanzauna,daga bisanine waiter din yaxo da menu da notepad ahannunsa najin mexasu xa'ba,
"Mekukeso"
MUHANNAD yace dasu yana kallon UMMI AISHA,
Dede lokacin dasu ASHRAF suka shigo shida baby kay,waiter yaje wajensu inda ASHRAF yace abasu couple table,UMMI AISHA was highly surprised,daria takusayi amma tadanne ta kawai,
"Hot chocolate"UMMI AISHA tabawa MUHANNAD amsa,itakuma Waliyya milkshake taxaba se desert da aka kawo masu kafin abinci yai ready...
ASHRAF yanayi yana kallon UMMI AISHA,baby Kay tai waving UMMI AISHA itama waving 'dinta tai back,
"Sweethrt mekikeso akawo maki?!"
"Baby boo kaime kakeso?!"
Shide waiter yai tsuru tsuru yana kallonsu yanajiran abinda xasuce,
"Ka kawo mana coffee low fat decap da peanut butter sandwich"
"Okay sir yanzu kuwa"waiter din yafadi hakan Sannan yakoma ciki,baby Kay se juye juye ake harga Allah tadauka wannan abin dagske ne,basu wani jima suna hira ba wayar ASHRAF tai ringing dauka yai Sannan yacewa baby Kay yana xuwa fita yai wajen bewani jima ba yadawo hannunsa abaynsa,hardasu kneeling down yana kallon baby kay dede lokacin da UMMI AISHA tadauki hot chocolate dinta tanasha,yajuyo da hannunsa 'dauke da huge bouquet of lavender lilacs'sannan yamikawa baby Kay still yana durkeshe,
Rufe baki tai tana kallonsa,idonta ware tanabin hannunsa da kallo
"Baby boo"
"Sshhh"yace da ita in a romantic style,Sannan yasamata ahannunta yana binta da kallo "honeyboo say no more i got you lilacs because of what they represent"
•✨•
#teamASHRAF
AND MUHANNAD LOVERS
✨✨✨
WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;NANA HAFSAT.....
[4/18, 11:58 PM] Asy Khaleel: •✨UMMI_A'ISHA✨•
(THE MAGNIFICENT)
64
©®MISS XOXO
👄
DEDICATED TO;
UMMI_A'ISHA👌🏼
nanahafsat.wordpress.com
•✨•✨•✨•✨•✨•
"Awwwwwwm thank you lots,I'm so out of words,Nagode baby boo"takarashe maganar tanabin flower din da kallo,
"You like it?!" ASHRAF yace da ita yana mikewa daga dur'kushen da yai,sekace gaske..
"I love it honey,bansan ma mexance maka ba,best gift ever kenan,deepy appreciated"
"I'm glad you loved it"
Waliyya dake gefe ta tsaya tana kallonsu,abin 'kwarai yabata mamaki don tabbas tasan ASHRAF Kuma sau nawa take ganinsa yana nacin son magana da UMMI AISHA tun alokacin award giving dinnan amma ya akai haka?!"kai akwai wata a 'kasa"amsar data bawa xuciyarta kenan,
"Minti 'daya sisters barin amsa waya" MUHANNAD yace dasu UMMI AISHA sannan ya mike ya fuce,
"Bestie ya akai haka?!i mean how on earth naga wannan guy din da sister dinki?!"Waliyya kewa UMMI AISHA wannan tambayoyin,
"Tawan akwai ki dason magana to soyayya sukeyi ko ko hakan haram ne?"
"Nibance ba,kawaide naga kamar da kexenuna yanaso"
"That was then,this is now,hausawa sukace wai so tashi yake,to yakoma kanta,mexanyi da arrogant mutum irin ASHRAF?!he's not my type,Kuma ko'ajikina kece kika xuba idanuwa kina kallonsu,inkuma kina cikine toh"takarashe maganr tana daria,
"Rufamin asiri tawan,kinsan inada na 'karfen"
Muryar ASHRAF dayai magana da 'Karfi itace tahanasu 'karasa xancen da sukeyi ganin yadda yakewa baby kay,UMMI AISHA taxunguri Waliyya da hannunta
"Haba bestie kallon ya isa haka kinsa masu ido fa"
"Kyaleni inbawa idona abinci,baxan bari wannan moment ya wuceni ba"
Ware ido Waliyya tai ganin yadda ASHRAF yasake marairaice murya yana wa baby Kay magana kamar wata sarauniyar mata,batasan saboda yaga tana kallonsu bane yasashi hakan
"You are so beautiful soulmate"ASHRAF yace da baby Kay yana narkar mata da coffee brown eyes dinsa,
"Awwwwn baby you are to much,I'm very grateful,thank you for the moment I feel beyond blessed"
ASHRAF yai murmushi Wanda ba har cikin xuciyarsa yai hakan ba,
"The pleasure is mine soulmate,naji da'di dakika bani time dinki haka,xanwa waiter magana Idan da abinda kikeso se'ai ordering,mekikeso sugarpie?!"
Baby Kay fa gaba daya ASHRAF na neman sunce mata 'kwa'kwalwa dan da'di kowanne kira da sunan da yake gaya mata,muryarsa Ita tadawo da Ita daga tunanin da take;
"Honey boo,bakice komi ba,mekikeso dearest?!"
"Baby boo,cikina yacika,Nagode sosai.Allah yabarmin kai"
"Ba amin ba"yafadi hakan a hankali yadda baxata jiba yana sake sakar mata da 'tsadaddan murmushi...
MUHANNAD ne yashigo bayan yagama waya,yakarasa kusada su UMMI AISHA,
"Kuyi hakuri sisters,boss 'dinane yakira wai..."sekuma yai shiru,
"Laa kakka damu ya MUHANNAD,nasan bewuce yanasan ganinka yanxun ba,thank you so very much,munci munsha harda extra take away,Allah yasaka da alkhairi"UMMI AISHA tafa'di hakan tana murmushi,
"Ameen de Allah yasaka,Allah ya'kara bu'di"Waliyya ta fadi hakan,
"Nagode sosai,Insha Allah next time haka baxata faru ba,Allah yasoma mungama"
MUHANNAD yakarashe xancen yana mikewa tsaye,
Tashi sukayi su ukun sukai hanyar fita,ASHRAF kamar yajanyo UMMI AISHA gashi tayi Kyau cikin rigar abaya ba'ka,Se murmushi take me tafiyar da duk Wanda ya kalleta,,,take yafara fixgar da xaxxafar iska daga bakinsa yana fezarwa,yana taune pink lips 'dinsa,su UMMI AISHA basu da'de da tafiya ba suma su ASHRAF din suka tafi,dakyar ya iya sauke ta akofar gidansu Sannan yajuya kan motarsa yatafi gidansu jay dake unguwar court road,itakanta baby Kay tayi mamakin rashin magana da ASHRAF ya'ki yai mata tinda suka taho a mota,ko kallonta baiyiba gaba daya idonsa yaka'da Yayi jajir,Kansa har ciwo yake naganin abinda yasa Kansa ciki Ita kanta tayadda yau' gaskia ASHRAF arrogant mutum ne Wanda halinsa davan ne cikin mutane,
Yana shiga unguwar su jay yai parking motar awaje yashiga cikin gidansu jay 'din,bakinsa 'dauke da sallama ya shiga amma kwata kwata ransa a 'bace yake shikansa jay din ya lura,shiyasa bebi takansa ba sarai yasan halin abokin nasa ze'iya gaggaysa masa 'bakar magana shiyasa ya basar da shi shima yaci gaba da buga nintendo game dinsa shiysa halinsu yakusan xuwa 'daya...
•✨•
65
Seda ASHRAF yagama 'bacin ransa shi kadai Lokaci Lokaci yakanja tsaki,gaba daya coffee brown idansa yakoma jajir dashi,
"F*uck you"ASHRAF yace da jay Sannan yadau pillow ya wulla masa akansa,
"Godia nake baxande kula kaba"
"I'm damn serous,ba..baxan iya cigaba da pretending 'din nan ba,yarinyar nan bakaga yadda...,ohh what the f*ck,jay baxan iya ba I can't"
"Meyafaru,hope UMMI AISHA taga lokacin daka Bawa baby Kay huge bouquet of lavender lilacs?!"
"Jay,batama ko kallonmu hankalinta na gurin guy dinnan na neighbor 'dinmu,"yakarashe maganar yana taune lips dinsa
"You need plan b"
"To hell with your damn plan b or whatever it is,kawai xanyi approaching dinta I just can't wait any longer,jay my heart hurts anytime naganta da guy dinnan,yaxanyi na fada mata pls bansan me yake damuna ba?!"
"Arrogant shine yake damunka,kanasan yarinya kawai kasameta kagaya mata feelings dinka,Shikenan fa amma girman kai yahanaka"
"Duk lefin kane"
"Danayi me?!"
"Dakasa nai pretending Akan sister 'dinta don't you think yanzu nan gaba abin xe iya kawo matsala?!"
"Bama fatan haka,Insha Allah ma babu wani abinda xe faru"
"To Allah yasa,amma ni xan iya disgracing yarinyar nan cikin mutane Kasan halina Idan ta nuna wani abu"
"To ai dole seta nuna ta yadda UMMI AISHA 'din xataji haushi ai haka plan 'din yake"
"Ohhh bullshit,nikam baxan sake wani pretending ba,kawai kabani wani shawaran amma wancan plan 'dinde nayi cancelling 'dinshi"
"Nikam I'm out of ideas inde kafasa plan 'dinnan to Banda wata idea Kuma"
"Shikenan xanyi tunanin abinda xa...."
Be'karasaba wayarsa tafara ringing daga screen din yai ganin mekiran nasa yasa yakashe wayan gaba daya,
"Waye yakira ka kashe?!"
"Sister din THE MAGNIFICENT"
"Bakyau wulaknci dude,kadenawa yarinyar nan haka,jifa soyayyar daka nuna mata daxu yanzu kuma kamata haka?!"
ASHRAF ya ware Ido yana kallon jay,Sannan yasoma magana;
"What the f*ck kafa'damin idea 'dina ciki?!ba idea dinka bane kainefa kakirani Ina ciki kace naxo nakarba lilacs nakai mata,duk wannan lovey dovey stuffs din duk idea dinkane,sanin kankane mata ba damuna sukayi ba,haryanxu ma soyayyar UMMI AISHA doubting dinta nake a zuciata,nine ko ba ni bane,xaka kawomin maganr shirme ciki duk ba lefin ka bane,nakashe wayan karka cikamin ciki jay I'm not in the mood"
Shide jay shiru yai yana bin ASHRAF da kallo,ko kadan beji haushin saba,sarai yasan haka halin ASHRAF din yake kowama hakan yake masa,sede hakuri,shiysa yake ganin anya ma kuwa xasu dedeta da soyayya,sede Kuma ya lura UMMI AISHAn Itama kusan haka halin nata yake hayaniya dawani 'kyale kyale na dunia basu dameta ba,kusan Allah ne yakama ASHRAF din da kamuwa da soyayyar wadda bata damu dashiba,ya'dau mata a matsayin Kayan sawa yasa yacire yasa yacire haka yakeyi kullum cikin canxa 'yammata kosau daya 'betaba furtawa 'daya daga cikinsu kalmar so ba,kusan sune suke kai kansu gurinsa suna cewa suna sansa,hakan da sukeyi shiysa ya 'dauka haka 'yammatan suke,sefa da idonsa yafara tozali da UMMI AISHA yatabbatar da shayi ruwa ne,
Mi'kewa ASHRAF yai yana gyara pcap 'din kansa,
"Jay,I'm going kagayda mommy naso inshiga mugaysa banajin da'din jikina"
"Zataji Insha Allah,so yanzu ya'ke ciki?!"
"Yakwa xa'ai kasande duk abinda ASHRAF KABEER KAMILU yakeso Insha Allah yanasamu,to definitely bad boy game kawai xanyi playing and bet u senayi winning a 'karshe da yardar Allah"
"Nasanka dude,Allah yakaimu,don't play rough de babu ruwana"
ASHRAF ya kyalkyale da daria"Jay kullum tunaninka negative ne kasande baxanyi hurting abinda nakeso ba ever,"
Sekuma yakoma yaxauna a kan kujerar dakin jay da Ita kadai ce a madedecin 'dakin dake 'dauke da katuwar katifa kamar gado,se sauran karikicensa da set din kallo,
"Kasan me UMMI AISHA keso?!"
"Seka fada dude"
"UMMI AISHA batasan mutum yana xuwa school late ma'ana Se bayan lecturer yaxo kaikazo,Sannan tanasan mutum yadinga respecting lecturers dinsa da mutane da maida hankali a class,ko Kasan ban'taba note ba a school dinnan,Akwai wani lecturer dayake operation show me your note,wallahi jay kullum seya fito dani bana note and banjin wani haushi saboda nasan halinane,but yarinyar nan ta fuskarta xaka gane batajin da'din yadda nakeyi"
"Dude kana nufin xakai switching characters 'dinka kenan?!"
"Na makaranta ba,xanyi 'ko'kari Allah yasa na iya"
"Nagane kana nufin kenan hakan xesa kafara shiga ranta?!"
"Baxaka ganeba,already nasan tana sona Itama,baxata nuna bane"
"Okay nagane abinda kake nufi,Gaskia dude kanason UMMI AISHA"
"she's my everything"
ASHRAF yakarashe maganar sannan ya mi'ke tsaye da alama tafiya xeyi,atare suka fito da jay din har kofar gidah Sannan sukai sallama shi yakoma cikin gidah shikuma yaja mota yatafi gidah...
•✨•
66
•SARDAUNA CRESCENT KANO;
"Aunty haule baki 'karasa ban labarin yarintar tawa ba"cewar UMMI AISHA,da suke xaune a karamin parlor da jerin tum tum ne kawai se Kayan kallo da freezer dake gefe..
"A'ina na tsaya maki ma?!"
"Aunty haule harkin manta?!kin tsayamin inda kikace a wata takwas nafara tafiya"
"Yawwa,Sannan da wuri kika fara magana fa,Ammi ammi ko'ina kina takawa,se bafa dakikacewa baffanku,nikinsan mekike cemin?!"
UMMI AISHA ta kece da daria,"Wai bafa,Gaskia nayi abin yarinta,Aunty haule ke me nake ce maki?!"
"Aule kikacemin fa"haule takarashe maganar tana daria sannan tacigaba,
"Kuma bakiyo 'kiwa irinta yara ba,baruwanki kowa 'bangala masa daria kike kina mi'ka hannu ya'dauke ki"
UMMI AISHA tai murmushi "nagode aunty haule,ammi naita damunta taban labarin yarintata ta'ki gashi kekin bani,Yawwa aunty haule dama inaso natambayeki wani abu amma fa amana bansan ammi taji maganarmu ce nidake"
"Inajinki menene??"
"Aunty haule wai dagaskene hankalin ammi da ya gushe?!ummansu baby kay lokacin da Ina kaduna taita min gori tana kirana da 'yar mahaukaciya dangin mahaukata,Dan Allah aunty haule inaso kigayamin gaskiyar al'amarin yadda yake"
Haule tadafe kanta alamar maganar bata mata da'di ba,nannauyar ajiyar zuciya tasaki,sannan tafara fadin;
"Gaskia wannan maganar ba haka take ba,Kuma banso xanfada makiba,dande kin ha'dani da Allah ne da baxan iya fada ba,Tohh amma banida xa'bi,nide iya xamana da aunty shekara da shekaru banta'ba jin ko ganin wani daga cikin yan'uwanta me ta'bun hankali ba,sannan magana ta biyu tunda nake tunda Allah yakawoni gidan nan tunkafin asan xa'a haifeki ma banta'ba ganin