Showing 84001 words to 87000 words out of 107296 words
sauran wanda na gayyata duk nagansu awajen ina mi'ko godiata ta musanman...
Motoci da suka amsa sunan motoci ne suke shiga titin marhaba event center 'din da alama amarya da ango sun danno,cikin tent 'din tuni mc ya shedawa mutane cewar amarya da ango sun iso,Kuma amarya xata fara shigowa da tawagarta kamar yadda al'adar wushe wushen take,
•
"Bestie boo kwallina ya xaxxago kalla idona kiga"cewar Ummi Aisha dakewa Waliyya magana suna xaune cikin mota su ka'dai abaya da alama ango ashraf yana wata motar,
"Muga ba sosai ba"Waliyya tace hakan tana gogemata kwallin daya kwaranyo,
Mjay ce ta lek'o da kanta ta window 'din motar sanye cikin laffaya sak kanurin yerwa se kamshi take,
"Baxaku fito ba ga baffankican yace shi tafiya xeyi nibansan zaman me kukeba jan ran ya isa haka"
"Aunty kwalline ya xaxxago shine bestie take gogemin"
"Yayi Kyau to kufito"
Tsakiya aka saka ummi Aisha,gabanta Kuma bridal train 'dintane gefe da gefenta Kuma Waliyya ce da kausar 'kawarta,ciki hardasu batul mamman da khadija sidi,bayanta kuma dandaxon dangintane na kanuri da suka sha laffaya suma se bulbula kamshin khumra suke kanajiyo kamshin hakan xe tabbatar maka da cewa amarya ta iso,wani abin daxesa ke burge duk Wanda yagansu shine harda ammi da baffa da sauran luwali's d'inta aka shigo da ummi Aisha kamr yadda al'adar take hakan sukai,'yan uwan ammi maxan shigar kulwu sukai dasu gemage harda Wanda sukai dankiki da yange ciki hardasu arfaan da mus'ab...
Bayan amarya taxauna da yan uwanta tawagar ango yabiyo baya shigar ba'ki yai da fari 'kirar bauchi style seyasake fitowa sak ashraf 'dinsa su jay ansha fararen shaddodi shida sauran abokai se suka sake bada very colorful and exciting event,addua aka farayi,light music na wagge shiyake tashi abin gwanin sha'awa,jokes of the night ya biyo baya ciki harda na yaren kanurin anayi ana fassarawa Wanda basaji,Waliyya Ita tafito tabada tarihin amarya cikin harshen turanci,se babban abokin ango jay shima yafito yabada na ashraf,abinci kala kala na kanuri da normal shi aka dinga kawowa mutane,Kayan da'di abin ba'a magana,bayan anci abinci aka fara rawa inda aka kira couple da yan uwa da abokan arziki kan sufito ayi rawar 'ganga kuraa' kowa seda yayi rawar kamar yadda al'adar takanyi babba da yaro kowa sedaya taka harta dattijan yerwa dake wajen seda suka taka bayan an gama rawa ashraf yabawa amarya kyautar sulallen gold (gold coins)har 'kwara goma sha biyu kai guri seya sake kicemewa da murnar ashraf yayi kamar yadda al'adar ta tanadar,,yanayi yanasa babbar rigarsa yana goge wa Ummi Aisha gumin fuskarta duk cikin iya shegen ashraf ne,gashi yaki sakin hannunta duk inda xasu xaga awajen da shi ake xuwa har traditional abubuwa na wushe wushe su tulur da ta ru'da duk dashi akai yana wajen,
Conclusively haka aka dinga hidimar wushe wushen abin gwanin sha'awa,anci ansha an watsa naira antaka naira an raba naira,muna_b da magajiya dake gefe tagumi suka xabga ko 'dan hotan da ake xuwa aida amaryar basujeba kowa yagane ba'kin ciki suke shysa aka tattara lamarinsu aka watsar,savouniers kala kala haka aka dinga rabawa awajen,sama ko 'kasa tunda baby Kay tashigo da tawagar amarya ta ware waje wajen bobonta,zaune suke Ita dashi cikin motar sa bayan baffansu yahana xancen mota 'kirmishishi ta toshe kunnenta tabad'awa idonsa kasa don taga ba idon mutane awajen,
"Sweetest love yaushe xaka aiko?!"baby Kay tace da bobon hakan tana kallonsa
"Sugar pie nace maki su daddy sunje Qatar se sundawo tukun,Meyasa kike yawon kawo xancen nanne nace maki ke kadaice a xuciana trust me"
"Shikenan sweetest love Allah yadawo dasu lapia"
"Amiin"yace a takaice yasa hannunsa kan nata yana murxawa passionately
Da sauri tacire hannunta tana kallonsa,
"Why?!"yace da Ita yana dubanta
"Kabari idan munyi aure mayi hakan ko?!"
"Just a romance nothing beside the romance kinji sugar pie trust me kobaki yadda dani bane?!"
"Nayadda mana"tafadi hakan tana rufe fuskarta
Tashin motar yai suka bar wajen suka koma cikin dimlight dake gefen tent din suna shek'a alfasharsu(Allah ka karemu da kariyarka ameen),haka aka dinga event dinnan har wajen 12 na dare Sannan aka tashi fuskar kowa 'kal da Ita yana jin dadi gakuma tulin Kayan rabo fal a hannun jama'a,seda baby Kay taga amarya tashiga mota xasu tafi sannan tacewa bobo yakaita gidah kar anemeta,
Washegari;
Tun da safe ake shrye shryen tafiya bud'ar kai saboda xa'afara kaita gidan sirikanta kafin akaita gidan mijinta,ummi Aisha tasha kuka sosai da iyayenta sukai mata fa'da da Kuma jan kunne,sosai fadan I nayi bari nabari yashigeta ba ka'dan ba musanman inda baffanta ke cewa tabi mijinta Kuma karta kuskura ta tauye masa hakki saboda mala'ikun rahma xasuyi ta tsine mata wata ruwayar aka ce xasuyi fushi da Ita,shigar atamfa tai kalar blue and orange babban mayafi orange ta lullub'a light makeup aka mata,gidan su ashraf aka fara kaita nanma iyayen mijinta(Hajia sakeena da Hajia barira)sukai mata fa'da sosai tareda doriyar kome ashraf 'din yayi mata taxo ta fada tadaukesu iyaye ba surikaiba....daganan Kuma aka sake dawowa da Ita da Kansa captain adam yakaita har gidan mijinta dake unguwar sultan road inda alhaji kabeerun yabawa ashraf dank'areren gidan kyauta lakadan kyauta opposite the afficent duplex gidah sama da kasa komi yaji,yasha Kayan alatu irin na xamanin yanxu iyayenta sunyi mata fiye da tunaninta sunyi mata Kaya nagani na fad'a babu raini,captain adam ya dank'awa ashraf amanar Ummi Aisha sannan yasake masu fada me shiga kunne yai masu sallama yatafi,
A lokacin ne kuma kafin yan uwan amarya su fara watsewa abokan ango suka shigo da akwatuna guda 6,kyauta daga ango xuwaga amaryarsa sak irin yadda al'adar kanurin take haka ashraf yaiwa Ummi Aisha komai to wannan karenma akwatunan kwara 6 cike suke da Kaya,hudu dagaciki kususuram ne sekuma biyu daga ciki wato ra'aki shikuma rabin kususuram ne shikuma akwati biyu ne making it 6 duka,shewa da gu'da haka kanuri's dinnan suka dingayi,bayan manya suntafi se yammata kawayen amarya akai siyen baki sukai ciniki suda abokan ango Sannan aka watse aka bar amarya Ummi Aisha Ita kadai sunkife cikin wadataccen mayafinta...
•
"Dude nace maka anwatse fa anbar yarinyar nan Ita kadai da Allah katashi katafi kaxauna kana shegen murmushi kana taune wannan banxan pink lips din naka kamar na mace"jay yace da ashrf hakan
"Kana ba'kin ciki kenan?!beside niban huta ba kabarni na sake hutawa naga bawani nisa"ashrf yafadi hakan yana sake gyara kwanciyarsa,
Dundu jay ya d'umawa ashraf abaya,ashraf yamike yana sosa bayansa,
"Haba jay wannan childish stuff ne ba girman ka bane"
"Dole kafadi hakan mana tunda yanxu kanada iyali wai kaima kanada mata yanzu,kade siyi wani abin karkabar 'yar mutane da yunwa"
Tsaki ashraf yai Sannan ya xuri carkey dinsa akan stool yana cillawa jay harara wanda shikuma gwalo yake masa,ahnkali ashraf yake driving dede madallah suya yatsya yasai dakwalen kaji kwara biyar da drinks kala kala ya saka agaban mota yai hanyar gidansa 'kira'ar manshawi ce ke tashi ahankali cikin motar ha'de da turaren bahreinul oud da suka ha'du suka bada daddad'an kamshi,yana xuwa ya danna horn da sauri megadi yabu'de masa yashiga da motar,Ummi Aisha najin 'karar motar tai saurin lullube kanta cikin bargo tana munsharin 'karya kamar tayi nisa a baccinta........
•✨•
Gaisuwa mai d'inbin yawa xuwaga masoya littafin Ummi Aisha ,acigaba da hakuri dani makaranta tasani agaba ,amma Insha Allahu danasamu kaina sekungaji da karantawa ......
WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;NANA HAFSAT.........
[4/18, 11:59 PM] Asy Khaleel: •✨UMMI_A'ISHA✨•
(THE MAGNIFICENT)
84
©®MISS XOXO
👄
DEDICATED TO;
UMMI_A'ISHA👌🏼
nanahafsat.wordpress.com
•✨•✨•✨•✨•✨•
Ashraf nagama parking d'in motarsa yashiga cikin gidan hannunsa d'auke da ledojin dayasiyo Kayan k'walam da mak'ulashe,shiga d'akunan yai yana duba Ina Ummi Aisha take d'akin karshe na cikin corridor yaganta k'udundune cikin bargo tana munshari,daria abin yaso yabashi yasan sarai ba bacci take ba yaga side lamps d'in gadon a kunne kaf futulin d'akin ma a kunne suke,k'arasawa yai cikin d'akin yana bin d'akin da kallo sosai yamasa Kyau komai na d'akin k'irar royal ne gawani k'amshi dake tashi na khumra da turaren wuta,yajima yana kallon santala santalan cinyoyinta da suka fito waje kad'an gashi ne ajiki a kanannad'e ga wani sihirtaccen k'amshi dake tashe daga jikin nata,dak'yar ya iya seseta Kansa yasa hannu yana d'an dukan k'afarta ahankali,yitayi kamar baxata farka ba tacigaba da munsharin k'aryarta,
"Ke!"ashraf yace da Ita yana cigaba da tashinta,
"Uhm uhm"tace hakan tana ture hannunsa,
"Wake up abeg ko kuma na hau gadon natasheki"
Ummi Aisha najin haka ta mik'e tana murza idanuwa kamar gaske,
"Ga abinci nan kitashi kici"yace hakan yana mata nuni da ledar
"Na k'oshi nagode"
Murmushi ashraf yai da ke k'ara masa kyawunsa yajima yana kallonta kafin yasa hannu a aljihu ya ciro wayarsa yafara danna nambobi da alama kira xeyi,Ummi Aisha naganin haka ta ware ido tana binsa da kallo murya narawa take fad'in
"Mekake shirinyi hakan?!"takarashe maganar kamar xatai kuka,
"Baffa xankira nagaya masa tunyanzu munfara gardama dake kafin akai ko'ina nasihar daya mana bata shiga kankiba"
"To to naji zanci,naga ba yunwa nakejiba shysa"
"Haba wa y'ammta seda ruwan ciki akejan na rijiya ai"yafadi hakan fuskarsa ba yabo ba fallasa,
Itade shiru tai tana tunanin maganar dayai yanxu take jikinta yafara rawa,ahankali tasakko daga kan gadon tasa hannu a ledar daddad'an kamshin aroma na kajin ya bugi hancinta,hannu tasa taciro cinya k'wara d'aya tafara ci ahankali dakyar tacinye tasa hannu tafara rufe ledar alamar ta k'oshi,
"what the fu.."ashraf yace hakn yana kallonta Sannan yak'arasa kusada ita yasa hannu a ledan yabud'e ta duka yasake tura mata gabanta,
"Nak'oshi wallahi"tace dashi a shagwabance harda langwab'ar dakai wai dukdan yaji tausayinta ,
"Wallahi kinsan Allah sekinci dayawa waxakiwa yanga?!sannan ki bud'e yoghurt d'innan kishanyenshi tatass ba wasa nake dake ba inkuma baxakici ba sena fad'awa baffa"
Bayadda Ummi Aisha ta iya haka tadinga d'urawa cikinta kajin tana korawa da yoghurt,ashraf dake gefe se dariar mugunta yake mata ahankali gashi ko d'an tausaya mata yak'i yayi,seda yaga taci sosai Sannan yace tabarshi haka,dakansa yad'au wanda tarage yasa acikin mini freedge d'in dake gefen gadon,sannan yashiga band'aki gaban Ummi Aisha se dukan uku uku yake,bejimaba yafuto yacanxa kayansa xuwa pajamas(Kayan bacci)kashe fitilun d'akin yai yabar side lamps 'din kawai dasuka bada dimlight,ahankali yakashe d'ayar saura ta b'angaren Ummi Aisha jikinta se kyarma yake,ya lura da hakan yana sane yahau kan gadon ganin haka yasanyata ja baya yasake matsawa takoma c'an k'uryar gado yasake binta,har jikin bango suka Kai ahaka numfashinsu yana dukan na juna,dede kunnenta yai kamar Wanda xe bata side kiss sekuma yafara mata magana a kunnenta cikin wata irin murya me dad'in sauraro ga k'amshin mint da bakinsa yake ,ahankali yafara fad'in;
"Stop thinking negative 'yammata,keda kika tab'a yi menene na tsoro ?!after all ni ba abinda xanyi maki"yakarashe maganar yana taune pink lips d'insa had'e da girgixa mata kai Sannan yasa hannu yakashe fitilar data rage ya mik'e tsaye yafita,
Nannauyar ajiyar zuciya Ummi Aisha tasaki ganin ba abinda ya mata wani b'angaren na zuciyarta kuma haushin kalaman da ashraf yafad'a taji,ahankali ta mik'e daga kan gadon tashiga band'aki tajima tana kallon band'akin don tsaruwarsa komi pink ne harda jacuzzi d'in gashi ansa komai na Kayan wanka ciki,wanka tai,tayi brush ta kuskure bakinta da mouthwash na strawberry tayo alwala tafito,da sauri tasaka Kayan baccinta ta murxa mukulli a d'akin tahau sallar nafulfulinta tajima tana sallah sannan tad'an tab'a karatun alqur'ani tarufe tahau kan gado,bacci yak'i xuwa whatsapp tashiga sosai ta tarar da conversations kala kala Kuma duka messages ne na tayata murnar auren datai haka ma grps d'in ciki ,tabawa kowanne amsa sannan takashe wayar ta ajiye agefe,addu'oi tai tashafa ba ajima ba daddad'an bacci yai awun gaba da Ita,
Ashraf daya koma d'akinsa ba abinda yake se tunanin Ummi Aisha,daya rufe idonsa donyai bacci ba abinda yake gani se Ita da kyakkyawar surarta,wayarsa yad'akko yashiga kallon selfie d'in daya masu tare zooming fuskarta yai yana kallonta,yasa hannu yana shafa fuskarta,se juyi yake yakasa bacci dayaga abin bana k'are bane adole ya mik'e yashiga band'akinsa yayo alwala shima yatada sallah bashi yai bacci ba se bayan asubah bashi yatashi ba se wajen 12 shima wayarsa ce tafara ringing da sauri ya d'auka don ganin wake kiran?jay shine sunan dayake rubuce ajikin screen d'in,d'auka yayi yasa a handsfree don bacci ne sosai a idonsa,
"Yo dude"jay daya kira yake fa'din hakan dayake a speaker ashraf yasa,
"Yass jay"
" kan balai baku tashi daga bacci ba har shabiyu?!temaka kutashi mutumin banxa sekaje ka sukurkurta masu d'iya kafin wata shekarar kayo wata sabuwa tunda ita kamayar da Ita second hand"
Tsaki ashraf yayi kamar yasa hannu tawayar ya janyo jay don haushi,
"Kai wannan ya dama shine agabanka,ya akai yanxu??"
"Dama batun wannan construction 'dinne tetfund sun amince so xamuje around 12;30"
"Oh bouy"ashraf yace hakan yana dafe kansa,
" kaga babu takurawa anan idan you can't make it babu matsala ciki semuyi replacing da wani yanxu de are you in or out?!kalma d'aya pls saboda bansan abinda xasuxo sunajin haushi"
"I'm in"ashraf yace hakan atakaice sannan yakatse wayan batare dayaji abinda jay xece ba,
yafad'a band'aki yayo wanka within 15 mins harya gama shiryawa,sanye yake cikin yard ash and black yasaka komi black se k'amshi yake,futowa yai daga cikin d'akin yana d'aure agogon hannunsa,dadda'dan k'amshin turaren khumra ne yadaki hancinsa,atake ya lumshe idonsa yana shak'ar k'amshin ko'ina tatass dashi yajima yana kallon babban parlorn saman dayake tashin k'amshi kafin yasauka k'asan nanma k'amshin ne ke tashi daga k'wanyar Kansa ya tsinkayo sanyayyar muryar Ummi Aisha,
"Ina kwana?!"tace dashi tana k'arasa sakkowa daga saman sanye cikin doguwar riga k'irar a shape purple and black tayi ture kaga tsiya da d'ankwalin sosai tayi Kyau tulin gashinta yafito ta gefe kamar kasaceta ka gudu don kyau
"Lapia"yace a takaice amma yakasa d'auke idonsa akanta wani Kyau tayi masa ga lips d'innan sunsha purple jambaki yaso yad'auke kansa amma gangar jikinsa tak'i
" mama ta aiko ayush da abinci takawo tun da sassafe,
"I'm okay"yace da Ita yana cigaba da tafiya,har yaje bakin k'ofa yajiyo,yaceda ita
"Nafita"
"Allah yadawo dakai lapia"tace dashi tana langab'ar dakai
Ko kallonta beyi ba yasakai yafita amma har cikin zuciyarsa yaji dad'in adduar datai masa,sannan yace amiin cikin zuciyar tasa,fita yai yatafi gidansu jay daketa tsokanrsa sannan suka tafi branch na tetfund dake kano,se wajen to 5 suka gama abubuwan daxasuyi successfully anbasu aikin,wanda kwangila aka basu nasaka pipes a cikin k'asa ta federal university dake dutse saboda banbancewa tsakanin magudanar ruwa data kwata dake k'asan.A wahale yadawo gidah saboda sun cike documents yafi a k'irga dakyar yake driving d'in yai parking motar cikin compound ko takan megadin sa dake doka masa sannu da xuwa bebiba,yashiga cikin gidan dede lokacin da Ummi Aisha da Waliyya ke futowa da alama waliyyan ce taxo wajen aminiyarta ta jayai yatsaya donsu gaysa da waliyyan,gaysawa sukai inda waliyyan ke fad'in;
"Tunda nazo nake tambayanka tace kafita aiki tun safe"
"Ehh wallahi bade harzaki tafi ba?"yace da waliyyan hakan yana kallon Ummi Aisha da ita d'inma shi take kallo,bashigar safe ce ajikin taba wannan karon riga da skirt ne na atamfa ja tayi Kyau sosai,
"Tafiya xanyi aunty ce ke jirana xan rakata unguwa kuma ma na jima tun kafin d'aya nake gidannan"
"ai kamatayai Ki wunar mana har dare ko ba haka ba??"
"Hakane na amsa kuskurena sexuwa nagaba Kuma nagode"
"To bari musau keki"ashraf yafadi hakan dukkoda ba har cikin zuciyarsa yafad'i hakan ba don yagaji lik'is,
"Nagode sosai ango,amma antaromin d'an adaidaita yanxu xekaini gidah Insha Allah"
"To Shikenan kigaida aunty mungode "yace hakan,sannan yaciro kud'i yasakawa Ummi Aisha a hannu alamar tabiyawa waliyyan kud'in mota sobada bayasan waliyyan tagani,sallama sukai sannan yashiga cikin gidah sukuma suka fita wajen gate d'in taya d'an sahun daxekai waliyyan gidah,
•
"Ummah lapia kuwa meyasa kike acting very strangely?!"cewar baby Kay dake bin magajiya da kallo wadda tasa hannu biyu tana girgixa kanta kamar mahaukaciya,
"La..l..f,lafiya ta lau"magajiyan tafadi haka dakyar se rawa jikinta yake,
"To bakici abinci bafa nakawo maki tea?!"
Kad'a Kai kawai magajiyan tai,da sauri baby Kay tashiga kitchen tahad'owa magajiyan kakkauran shayi cikin kofi yellow tataho dashi takaiwa magajiyan dakanta asunkuye yake tasa hannu biyu tana girgixa shi,tana d'ago kanta tasa hannu tai fatali da kofin yatararratse a k'asa,
"Ummah are you okay?!"baby Kay tace haka damuwa k'arara ta bayyana a fuskarta,
"E"kawai magajiyan tace atakaice,
"No you are not kitashi muje asibiti ummah pls I beg of you"
"Lapiata lou"
"Kode kitashi ko kuma nafad'awa baffa kinada brain cancer/tumor"
Bayadda magajiya ta iya adole ta mik'e suka tafi asibiti gwajin farko likitan Wanda shine de yace tanada cancer yad'ago Kansa yana bin magajiyan da kallo sekuma yamaida dubansa ga baby kay yafara fad'in;
"Tun yaushe takeda Aspergers syndrome?!"
"Asper what?!"baby Kay tace hakan tana ware ido tana kallon magajiyan,
"Aspergers syndrome nace"
"I don't know dr abinda nasani kawai cikin week d'innan tafara acting so strangely tana magana ita kad'ai,jikinta was always shaking ga yawan nightmares datakeyi,kuma at times seta dinga maimaita magana ko abu nace to setaita repeating abun over and over again"
"Shikenan kawai abinda take?!"
"Yh shikenan yawwa sekuma throughout yau bataci abinci ba se nace barin had'a mata tea nahad'o mata tea d'in sekuma tasa hannu ta ture cup d'in yafashe"
"Meye color d'in cup d'in?!"
"Yellow ne"
Girgixa kansa yai yana rubutu a paper dake gabansa,
"Well abinda ke damunta de aspergers syndrome ne duk abinda kikace yanxu symptoms 'dinsane Allah ya kyauta kawai amma sekin d'an dinga binta a hankali saboda yanxu kwa'kwalwarta xata fara aiki da tunani kamar ta yara"
"Toh"kawai baby Kay tace a takaice,
"Yawwa sannan kidinga mata sadaqa abubuwan yanxu seda haka barin ita dakeda cuta kala kala akanta ga brain tumor ga cire mahaifa da akai ga aspergers syndrome kuma"yakarashe maganar yana girgixa kansa,
"Cire mahaifa kuma?!"baby Kay tace hakan tana kallon magajiya da kanta ke asunkuye tana girgixa shi batada maraba da tab'abb'iya
"Of course nan sukaxo suke fad'a itada wata lokacin da ake bata chemotherapy na cancer kidinga mata addua kawai"
Shiru baby Kay tayi tana tunani canta nisa tai ajiyar xuciya godia taiwa likitan daya basu takardar magungunan daxasu siya dakuma shara'do'din duk bayan sati d'aya suzo,sannan tatemakawa magajiyan suka tafi gidah,suna zuwa gidah bobo yafara kiranta awaya batad'au wani lokaci ba taci kwaliiya ta fita yana waje cikin mota daga bayan layinsu yana danna wayarsa;
"Honey boo"tace