Showing 66001 words to 69000 words out of 107296 words

Chapter 23 - UMMI A'ISHA(THE MAGNIFICIENT) COMPLETE

22 Aug 2024

7703

yajanyo mata,sum sum ASHRAF ya'mike yafuta amma UMMI AISHA ta'ki tashi,

"Yass you in yellow"lecturer din yakara fadin haka yaneme nuni da UMMI AISHA,
Bashiri ta mi'ke tafuta,idonta yakawo ruwa saboda Allah tayi missing wannan lecture 'din kenan?!
ASHRAF naganin tafito yanufota yana murmushi,harara tawatsa masa tana maida note dinta cikin jaka

"Kaji da'di ba?!an koreni daga lectures"

"Haba nina isa?!"

"Ka'isa har kayi yawa,tunda kasa aka koreni saboda Kasan ba yin course 'din kake ba,"

"Haba life partner,wallahi ban isaba,baxan iya barin kixo lectures ke kadai ba without me,that's it kawai"

"Nide ya isa pls,gashinan kasa ana kallonmu"

Aifa kamar jira ASHRAF yake yafara magana da karfi

"everyone,she's mine if you touch even a piece of hair from her head I will hunt you down,now spread the words far and wide"yakarashe maganar yanabin students 'din dakebinsu da kallo,sunajin haka sukai gaba sunabinsu ASHRAF da kallo,sauran yammatan dake gurin se gulma suke 'kasa 'kasa,

UMMI AISHA tadafe kanta wannan abin kunya dayai har ina?!gaba tai abinta tabarshi abaya,da sauri yabiyota yai saurin ri'ko jakarta,

"Menene kuma?!bayan sawa dakai aka koremu daga class for the time in my life history hakn be isheka ba shine kamin wani disgrace 'din haba ASHRAF ka kyauta kenan?!to dan Allah ka kyaleni akwai inda xani pls"takarashe maganar tana jan jakarta,

"Pls life partner..."sekuma yai shiru yana neman tsugunnawa akasa UMMI AISHA tai saurin dakatar dashi

"Komai kace xakai kneel down haba kakka janyomin wani disgrace 'din dan Allah"

"To Kiyi hakuri pls"yakarashe maganar muryarsa na rawa gaba daya ASHRAF ya sururuce Akan UMMI AISHA Itamamaki ma take ko Ina arrogants 'din nasa yake oho,

"Na hakura"tace dashi tana tafiya,

"Ina xakije yanzu?!"

"Xanje coc village ne dunking pepper xanyi breakfast Kuma I want to be alone if you won't mind"don tasan seya biyota shysa tace hakan

"But..."

"No buts"UMMI AISHA tai saurin dakatar dashi tana gimtse dariar data taho mata,

Hartayi gaba setaga abinda tai bata kyautaba ,'dan daga murya tai dayake ta'dan masa nisa

"ASHRAF"takirashi

Da sauri yataho wajenta yana murmushi sekace Wanda aka biya masa aikin Hajji,dunking pepper ASHRAF yakaisu a motarsa sukai reserving waje su biyu suka xauna waiter 'din yaxo wajensu yana tambayr mexa'a kawo masu?!

"Coffee low fat decap,life partner me kikeso?!ni shikadai ya isheni"

"Tea nakeso da chips and egg"

Kafin waiter 'din yakawo suka shiga wata hirar kamar basu aka kora daga class ba,ASHRAF yafurtawa UMMI AISHA kalaman soyayya yafi a kirga itakam harta gaji ko Romeo and Juliet albarka,shiru yai yana kallonta can yace;

"Practice makes perfect now say I love you ASHRAF"

UMMI AISHA tai daria tana binsa da kallo ahnkali tace
"I love you ASHRAF"sekuma tai daria Ita duk a wasa ta dau hakan,

ASHRAF yai murmushi yana taune pink lips dinsa sosai yaji dadin hakn data fa'da dukkoda yasan bada gaske take ba,

"Now you get A distinction kalman dakika fada,now say ASHRAF is the best"yakarashe maganar yana jefa mata mayen kallon soyayyar da baya gajiyar yinsa

UMMI AISHA ta ware ido tana girgixa kanta
"What 'd you do that for mr two different eye colors"

"Now you gat a b minus"sekuma yai murmushi wanda dimples dinsa suka lotsa Sannan yace

"Ba two different eye colors ake cewa ba 'ca xakice heterochromia iridum ake cewa"

UMMI AISHA ta bu'de baki xatai magana kenan wayarta tafara ringing da sauri tasa hannu xata 'dauka ASHRAF ya rugata 'dauka 'ya MUHANNAD shine abinda yake yawo ajikin screen 'din wayar....'


•✨•

"Gaisuwa mai yawa gareku masoya littafin UMMI AISHA,Nagode 'kwarai"






WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;NANA HAFSAT.....
[4/18, 11:58 PM] Asy Khaleel: •✨UMMI_A'ISHA✨•

(THE MAGNIFICENT)
71

©®MISS XOXO
👄

DEDICATED TO;
UMMI_A'ISHA👌🏼

nanahafsat.wordpress.com

•✨•✨•✨•✨•✨•✨•

"Waya ke kira?"

UMMI AISHA ke tambayar ASHRAF tana mai nuni da hannunta,
Be'ce mata komai ba illa wayar tata daya mi'ka mata gaba 'daya yanayinsa yacanxa yakoma ASHRAF 'dinsa,Ita tsoroma abin yabata,kar'bar wayartai tai swiping ta'dauka,

"Hello ya MUHANNAD!na'am Ina kwana?!lapia qalau ya gidah?!,ehh Ina school,a'a bana class ina coc village naje cin breakfast,na'am..oh ina dunking pepper,to se kazo,okay bye"takarashe maganar tana maida wayarta cikin jaka,

Sannan ta maida dubanta ga ASHRAF,tana murmushi don sosai ta tsorata da yanayinsa,sedata nisa sannan tasoma fa'din;

"Yanzu de me 'kwayar ido kala biyu kaman naka me yau yakoma coffee brown anjima yakoma grey ba two different eye color ake cewa ba sede ace mema kace ??yauwa natuno' heteroncronia indium ko?!"takarashe maganar tana kallonsa

Yaso yayi daria saboda kwata kwata ba haka pronouncing 'din yake ba,sede gaba 'daya ransa a 'bace yake na daga abinda UMMI AISHA tai yanzu wato bata 'daukeshi abakin komai ba kenan da har xata cewa wani yaxo inda take,siririn tsaki yaja Sannan ya mi'ke a fusace yatafi inda ake biyan ku'di yana xuwa akai totaling ku'din ya biya sannan yai hanyar fita,dan baxe iya ganin UMMI AISHAn sa da wani ba,wannin ma Kuma wannan MUHANNAD 'din,muryar UMMI AISHA ce ta tsaidashi daga taku 'dayan daxeyi yafuta daga wurin cin abincin,

" ASHRAF "takirashi da muryarta cikin sigar lallashi,tsayawa yai be amsata ba bekuma fita ba hakan ya sake bata damar sake magana a karo na biyu,

"Menayi maka?! Meyasa xaka tafi?!"

Har cikin zuciyarsa yaji haushin tambayoyin datai masa okay bata masan metai ma ba kenan da har take tambayarsa,lalle abin renin wayo ne,fitarsa yai abinsa yashiga mota yafigeta a guje ya tafi gidah,a hanyar fita da ga gate 'dinne ya hadu da motar MUHANNAD 'din shikuma yana shigowa,wani takaicin ya 'kara tsayamai a wuya bashiri ya 'Kara wuta a motar yafigeta a 'dari kamar Wanda xeyi 'yar tsere haka yadinga kere motoci ko tsoro bayaji,

"To Menayi masa??"UMMI AISHA ke magana da kanta ita kadai don bataji da'din tafiyar ASHRAF 'dinba,

Tana cikin tunaninta MUHANNAD yashigo cikin gurin har yaja kujera yazauna batasan yana wurin ba ta lula duniyar tunanin abinda yafaru tsakaninta da ASHRAF, 'yan yatsunsa kwara biyu yasa ya murxa adede fuskarta firgigit tadawo hayyacinta,

"Sister lapiar ki kuwa tunanin me kikeyi haka??"

Murmushin dole ta 'ka'karo"ya MUHANNAD har ka iso??bakomai kawai tunanin duniya"

"Ki dena tunani 'karamar ki da ke kinji?!saboda yana haifar da matsala"

"Insha Allah ya MUHANNAD,Nagode"

"Yanxu mexa kici?!"

"Wallahi a 'koshe nake naci abinci,ya aiki?!"

"Bakyason de naga lomarki de,aiki alhamdulilah yanxuma gudowa nai nagaji wallahy"

"Ayyah se ha'kuri ai"

"Sosai,transfer ma nakeson nasamu baxan iya xaman garin nan ba"

"Hahah,habade meye da garin namu?! ai ko'ina xakaje be xekai Kano ba,na hausawa sukace kano tadabo tunbin giwa koda mekaxo anfika"

"Fa'dar hausawa ce kawai,kenan koda talauci mutum yazo kunfishi kenan?!beside ke ai ba 'yar Kano bace 'yar kaduna/hadejia ce ke"

"Ai inda aka haifi mutum nanne kawai garinsa,ni 'yar Kano ce,sannan bawai maganar talauci ba Allah ya MUHANNAD acire maganar wasa kano kam akwai komi se san barka"

"To inde yadda kikace 'dinne ni 'dan abuja ne kenan tunda can aka haifeni"

Sosai suka shiga hirar abin daria,kowanne yana fa'din garinsu yafi,sannan suka tashi suka tafi seda MUHANNAD yabiya ta bakery yasiya mata yummytreats sannan tace yasauketa gidansu Waliyya tunda amminta batanan taje wajen aunty mjay,gidansu Waliyya ya sauketa, sukai sallama da juna yatafi,Ita Kuma tashiga ciki sanin waliyyan batada lectures ranar,kai tsaye tashiga cikin gidan flat ne dayaji Kaya awadace auntyn waliyyan ce kawai a parlor da Ita suka gaysa sannan tashiga ciki 'dakin da waliyyan take,

"Salam alykm" UMMI AISHA tai sallama,da gudu Waliyya tatafi ta rungumeta bayan ta amsa sallamar,

"Tawan yaushe kika'karaso?!"tafadi hakan tana ri'ke da hannun UMMI AISHA

"Bestie boo,ban da'de dashigo waba mungaysa da aunty de a parlor"

"Ehh!nima ban da'de da shigowa cikin dakin ba,kika ce se 10 yanxu hka lecturer 'din beshigo ba ko?!dan last week abinda yafaru damu kenan"

"Wallahy yazo bestie, mutuminki ne yajanyo min,wani abin takaicinma ba ya offering course 'din dayake hake yake yanxu kobayayi seya min occupying sit ko 'karfe nawa yake xuwa oho?!sannan har se antashi seya tafi,shine fa yau 'din naje naxauna ya tsiri wani silly questions 'dinsa ashe malamin yaganmu shine yace mu fita daga ajin,bayan munfita yatsaya ya 'Kara wannan shirmen nasa aike kinsan hali de,aka tsaya ana kallonmu nide takaici yasa ko magana nakasa to bayan munje coc village cin abinci bayan munci nema shine ya MUHANNAD ya kira....."bata 'karasaba Waliyya tai saurin katseta,

"Kice de cin fuska kikaima ASHRAF,ma'ana MUHANNAD yaxo wajen kenan?!"

"Ai ASHRAF 'din bema bari MUHANNAD 'din yaxo ba yacanxa mood yatafi inata masa magana nace Meyafaru?!bebi takaina ba yai ficewarsa" takarashe maganar tana xama akan gado,

"Baki kyauta ba tawan,ai ba'a haka yaxa'ai kiyi haka,bayan Sarai kinsan mutumin nan sonki yake Bana wasa ba,sannan kinsande baxasu ta'ba jituwa da MUHANNAD 'dinba menene naki na inviting MUHANNAD yaxo wajen?!"

"Shiyace xexo bani nace yaxo ba"

"Ai da seki ce masa bake kadai bace xaki masa magana inkun gama,ze'iya xaton ma kedah friends 'dinki nema,gaskia de baki Kyau taba tawan,ki kirashi kibashi hakuri"

"Haba,habade,aji down kenan"

"Bawani aji down ai baki kyauta bane,kiduba irin abubuwan dayake maki,Wallahy seme son kane tsakani da Allah xe maka haka,ya hana idonsa bacci yasamar maki wajen daxaki xauna a lectures 'din dabayinsu yake ba,kiduba abinnan da idon basira,tawan wannan era 'din da muke ciki ba a'wa maxa haka,kaja ajinma katsufa gidan iyayenka opportunity comes at once,karki bari wannan damar ta wuceki kita addua Allah yaxaba maki abinda yafi alkhairi cikinsu,yanxu de 'dauki waya kiki rashi kinji?!"

Bayadda UMMI AISHA ta'iya adole ta'dau wayar ta kira ASHRAF ringing 'daya biyu ya 'dauka da kmar baxe iya 'dauka ba sede baxe iyayiwa life partner 'dinsa haka ba,da sauri yasa hannu ya'dauka,

"Hellurh"tace dashi tana kallon Waliyya,

"Hi"yafadi hakan atakaice,

"I'm sorry pls"

"For what?!"

"'daxu,I don't mean to hurt you,ban 'dauka xakaji haushi ba"

Har cikin ransa yaji da'din hakurin datake bashi Kuma sam damashi be ri'keta a zuciyar saba,haushin MUHANNAD 'din kawai yakeji,muryar UMMI AISHA ce tasake dagula masa lissafi cikin siririyar muryarta me da'din sauraro,

"Bakace komai ba ASHRAF"

ASHRAF seya tsinci kansa da ce mata"dole ne se ASHRAF xaki dinga cemin Kinga de ni bana kiran sunanki life partner nake cemaki"

"Shikenan xance ya ASHRAF,apology accepted?!"

"Baxan iya fushi dake ba life partner xuciyata takice,suna kawai nakeso kicanxamin banason ya ASHRAF ai ni ba yayanki bane"

UMMI AISHA tajuya ta kalli Waliyya dake daria kasa kasa sannan ta bude kofa tafice,

"To me kakeso nace maka?"

"Ke nakeson ki za'bamin dakanki"

"How about bae?!"

"Bae kuma?!"

"Yasss'bafore anything else'yake nufi"

"Yh i knw,but saura 'daya wannan yayi ka'dan acanxamin wani gaskiya"

UMMI AISHA tai murmushi "Shikenan xan samo wani unique name 'din nan gaba"

"Life partner"yace da Ita cikin wata irin murya

"Na'am bae"

"You are my first love and my last"

"What do you mean first love?!"

ASHRAF murmured softly in her ears"you are my everything"

UMMI AISHA tai shiru tabbas tasan duk abinda yafa'da hakan yake,sauri tai tacanxa topic din xancen dasuke don bataso suci gaba da wannan xancen,

"Meyasa ka keson coffee sosai?!"

"Saboda yanada amfani sosai ajikin mutum"

"Coffee 'din?!"

"Ehh shi,saboda yana increasing circulation Kuma yana stimulating liver,yana kare mutum daga alcoholic disease,Kuma yana increasing fat burning by as much as 10% in obese and 29%in lean people,Kuma yana improving brain function da memory mood and energy levels cognition amma bana yawan sha'ai saboda too much caffeine can overstimulate the body and burn out ardenal glands"

"Wow,gaskia yanada Kyau side effect 'dinsade caffeine ne kenan ba?!"

"Of course sweetheart"

"Bana gidah ina gidansu bestie Inna koma gidah mayi magana"

"Me kirki da'ita ai jay kusan kullum seyamin maganrta,shifa gaskia da aure yake sonta"

"Allah sarki jameel shima ai yanada kirki,Allah yaxaba abinda yafi alkhairi amiin"

"Ameen,se'ahada ayi tare da namu"

Sarai tagane meyake nufi shiysa tai saurin kashe wayar tana daria,shi'dinma ta bangaren ASHRAF kashe wayar yai yana daria shikam kunya irinta UMMI AISHA na birgeshi shiyasa take 'Kara shiga cikin ransa,ta jima agidansu Waliyya se bayan axahar sannan takoma gidah,tana xuwa tatarar dasu mjay da amminta da haule se hira suke a babban parlor 'din gidan,bayan ta gaishesu xama tai ana hirar da Ita,bayan kowa ya watse daga Ita se haule,UMMI AISHA ke fadin;

"Aunty haule baki karasa minba bamu ha'duba"

"Ayyo,ai na 'kare ma kawai de Wanda yakawo nonon daga kaduna magajiya ce"

"Bayan tasha shine se akai Yaya?!"

"Bayan nakawo mata sena koma kitchen inda kika biyoni kina ammi tace nabaki lemo to bayan nabaki ne futowar da xanyi babu Ita babu alamarta"

"Hakan yana nufin umman su baby kay itace ta gusar da hankal.."bata 'Karasaba mjay tashigo cikin parlor 'din da alama taso taji abinda suke fada

"Me kuke cewa ne se 'kus 'kus kuke nima a zanta dani"

"Bakomai aunty Mjay"cewar UMMI AISHA

"kinsan Allah baxan tashi daganan ba senaji 'karshen maganar"

Bayadda suka iya haka haule da UMMI AISHA suka fa'dawa Mjay komai,mi'kewa tai waisetaci uban magajiyan haule tai saurin riketa

"Haba murjanatu in hankali ya'bata hankali ke nemoshi,abar xancen nan Dan Allah tada husuma bakyau murjanatu,abu yawuce Dan Allah abarshi,wata shari'ar se a alahira"dakyar da nasihar da komai mjay ta hakura aka shafawa xancen lapia,
____Lokuta sunja ko ince kwanaki sun shu'de baby Kay tafara samun shiga wajen MUHANNAD yanxu kam suna xama har suyi hira a bangaren su UMMI AISHA,kullum tana tare da UMMI AISHA tana mata tutorials kamar gaske,harde suka saki jiki a ita,basau 'daya ba baby Kay tana xuba garin maganin a abincin MUHANNAD musanman dan wake dayake ma'abocin cin 'danwakene Kuma dama sau hudu akeson asaka Kuma tayi sau uku sauran 'daya kenan,

'Bangaren soyayyar su UMMI AISHA da ASHRAF yinta suke kamar wasu ba'ka'ken larabawa babu kama hannun yaro,suna Bawa soyayya hakkinta kamar cin 'kwan makauniya,kullum ASHRAF yana gidansu kokuma suna manne a waya, baby Kay ma tadanne kishi kamar gaske suna mutunci,

Ranata 'karshe itace ranar da baby kay taxuba 'karashen garin maganin da muna_b tace a abincin MUHANNAD wannan karon cikin lemon kwakwar da UMMI AISHA takawowa MUHANNAD baby Kay ta faki ido bayan UMMI AISHA tashiga daki ta xuba garin maganin aciki,sihiri ba karya ba MUHANNAD ya kwankwade lemo harda 'kari,baby Kay naganin haka ta saki shu'umin murmushi tai masa salllama ta koma part 'dinsu dama muna_b safiyar ranar tazo kano.Yana shanyewa idonsa yafara canzawa gashi gidansu MUHANNAD 'din xasuje dayake sister 'dinshi tahaihu ranar ne suna Kuma ammi ma xataje amma se anjima xataje shiyasa tace UMMI AISHA tai gaba itada baby Kay 'din datace xataje sunan Itama,UMMI AISHA nafutowa daga 'daki bayan ta shirya take tambayar MUHANNAD da idonsa ya ka'da yai jajir Lokaci 'daya yake lumshe su dakyar da alama maganin yafara aiki akansa,

"Ina baby kay kuma?!"UMMI AISHA ke tambayar MUHANNAD hakan.......







WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;NANA HAFSAT......
[4/18, 11:58 PM] Asy Khaleel: •✨UMMI_A'ISHA✨•

(THE MAGNIFICENT)
72

©®MISS XOXO
👄

DEDICATED TO;
UMMI_A'ISHA 👌🏼

nanahafsat.wordpress.com

•✨•✨•✨•✨•✨•

Kasa bata amsa yai illa fafutukar 'ko'karin bu'de idonsa dayake neman shirin rufewa ruf yakeyi,

"Ya muhannad kan kane ke ciwo ne?!"

UMMI AISHA ke tambayar muhannad hakan a karo na biyu ganin yadda idanuwansa ke rufewa gashi yasa hannu akai yana juyashi ahankali,kasa bata amsa yai illa kansa daya ka'da mata kawai,

"To ko mu fasa xuwa ne?!"

ta sake tambayarsa a karo na biyu,nan 'dinma bebata amsa ba illah mi'kewa dayai tsaye kawai yai hanyar fita
Wayarta tadakko takira baby kay ringing biyu ta'dauka;

"Salam alykm!kina Ina Khadija?!na'am,oh okay to Shikenan,will holla you inde ba'a tashi ba,to Allah yakymu"katse kiran tai Sannan ta maida wayar cikin jaka tafita wajen..

Kafin ta bu'de motar sedata fara lekawa ta window 'din motar setin muhannad 'din tafara masa magana,

"Ya muhannad wai Khadija xata biyomu daga baya tace muje frnds 'dinta ne sukaxo"

takarashe maganar tana 'ko'karin bu'de motar,gaba ta bu'de tashiga da damuwa 'karara a fuskarta ganin yadda ya muhannad 'din keyi da alama bayajin da'di.,Sannan yai reverse ha'de da jan motar suka fice daga gidan,

'Bangaren su baby Kay kuwa a jikin window suke suna kallon su UMMI AISHA basu dena kallon suba harse da suka ja mota suka bar wajen,muna_b tai murmushin mugunta tana kallon baby Kay da 'itama murmushin take mayar mata,Sannan muna_b 'din tace;

"Yanxu baby kay se ki bi bayansu ko?!kiga yadda abin xe kaya kintabbata kin'dau camera 'din?!"

"Na'dauka aunty"

"Yawwa to ki sauri karki rasasu kan hanya"

"Ina mukullin motar taki?!"

"Gashinan kan freedge"

Da sauri baby Kay tadauki mukullin tafita wajen parking space ta 'dau motar muna_b din ta kwasheta a guje tafuta,tayi sa'ar hango motar muhannad din cikin traffic jam 'din dake kan titin magaji rumfa da alama xagaye sukai ta tarauni,bin motar tasu take a hankali kada su gano ta,meyakwan muhannad 'din yai corner 'din layin su seya mi'ke titin hotels 'din tahir guest palace,muryar UMMI AISHA ce takatseshi daga shiga guest palace din ni'ima dake kan titin sulaiman by lamido cresent,

"Ya muhannad ba gidah xamuba?!"

Dafe Kansa yai yaneme son yahana kansa abinda jikinsa ke ingiza shi yayi,dukkoda ba so yake yai ba amma ya rasa Meyasa jikinsa ke xumu'din akaita hakan,juyar da Kansa yai da idonsa don bayasan su ha'da ido ma da ita,

"Xan kar'bi sa'kone wajen abokina dayaxo daga damaturu inasan Kuma kugaysa dashi shysa"dakyar ya 'karasa maganar don shi kansa yana mamakin abinda yake shirin aikatawa

"Oh okay toh"

'Karasa shiga ciki yai sannan yai parking aciki suka shiga cikin hotel 'din UMMI AISHA ba takawo komai a ranta ba sanin muhannad 'din duk inda descent mutum yakai muhannad yakai,suna shiga ciki baby kay tashiga da motar ta itama tai parking 'can cikin parking space 'din inda baxa'a hango motar sosai ba,sannan tashiga cikin hotel 'din itama...

Suna shiga ciki muhannad yanufa wajen hotel service 'din bayan yacewa UMMI AISHA taxauna a 'daya daga cikin kujerun wajen yana xuwa,yana xuwa yaiwa mutumin sallama;

"Wa'alykm Salam"hotel service 'din yabashi amsa,

"Kunada extra room ne??"

"Akwai oga kwanane ko kuwa??"

"Nida madam 'dina ne transit kawai xamuyi na kamar awa 'daya xuwa biyu sannan mu wuce daga tafiya muke"

"Ohh okay to Shikenan Bari a kimtsa maku dakin kubamu mintina ka'dan ga key 'din suite 20 shine naku"

"To Shikenan ba matsala mungode"

Komawa muhannad yai gurin UMMI AISHA dake jira a waiting area yaxauna gefen kujerarta,

"Wai yana sama antafi amana iso wajensa tunda shida iyalinsa ne se muje mu gaysa ko?!"

"Eh"kawai tace ata'kaice,

Bayan sun hau saman xuwa 'dakin,baby Kai tai saurin bin bayansu sede me bata samu damar shiga 'dakin ba don 'kofar a rufe take,gudun karta shiga su ganeta kuma muhannad ze'iya fasa aikata hakan akan UMMI AISHA yasa ta tsaya a wajen tana sa'ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login