Showing 48001 words to 51000 words out of 107296 words

Chapter 17 - UMMI A'ISHA(THE MAGNIFICIENT) COMPLETE

22 Aug 2024

7700

ASHRAF brother din ayush din shine yake mata"

"Aunty ita kadai kuma?!"

"To ARFAAN idan beyi mata ba waaxe mata Karka manta ba field dinku takeba"

"Hakane" abinda ARFAAN yace kenan ransa duk a jagule,yanzu tarin dakon soyayyyar dayake mata abanxa xata tafi kenan?!,haka yamike yabar parlor din kotakan abincin data xuba masa bebiba,yana tafe yana shrya abinda xeyi akai kafin damarsa tawuce,yana fita suka hadu da UMMI AISHA a bakin kofa xata shiga ciki,tana ganinsa tafara fara'ar da fararen hakoranta suka bayyana"yaya ARFAAN! "Tace tana me fa'da'da murmushinta

" na'am"yace atakaice sannan yabi tagefanta yawuce,

"To yau lapiar yaya kuwa?!"
UMMI AISHA tafadi hakan tana karasa cire takalminta me igiya sannan tai sallama tashiga cikin parlor din tana kwala kira" ammi nadawo....!"


#teamUMMI_A'ISHA
(THE MAGNIFICENT)



Nasan yayi ka'dan ayimin afuwa banajin da'dine,Nagode da sa'kon gaisuwarku Allah yasaka da alkhairinsa ameen.....




WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;NANA HAFSAT......
[4/18, 11:58 PM] Asy Khaleel: •✨UMMI_A'ISHA✨•

(THE MAGNIFICENT)
53

©®MISS XOXO
👄

DEDICATED TO;
UMMI_A'ISHA👌🏼

nanahafsat.wordpress.com

•✨•✨•✨•✨•✨•✨•

Daga kitchen hafsat tafuto tana mewa tilon 'yar tata murmushi,kindawo UMMI AISHA?!..

"Nadawo ammi,mama tace tana amsawa wai kwanaki taxo layin nan dahar xataxo sekuma tace kai dare yayi tawuce gidah nace Kuma Wlhy bamuyi bacci ba"takarasa fadin hakan tana dora kanta akan cinyar Hafsat din..

Hannu hafsat tasa tana shafa mata kanta"Allah sarki aida tashigo,Yaya tutorials din hope komai goes on smoothly?!"

"Alhamdulillah Ammi Gaskia ya'iya tutorials Allah yabashi"

"Sosai kuwa danma yayi wasa da damarsa aida tuntuni ya kare karatunsa"

"Ayyah,such is life"

"Ga abincin kican akitchen a foodflask"

"Wannan na plate dinfa?!"UMMI AISHA tasa hannunta tana nuni da plate din dayaji shinkafa da wake wasar wasar da Ita gefe daya Kuma salad ne dayaji yankakken kwai da lemon tsami ga robar yaji kusa dashi,

"Abincin ARFAAN ne yasa naxuba masa Kuma yatashi yabarshi awajen ko yakoshi ne Allah kadai yasani"

"Kila yanada uzurin davan,barinci wannan 'din shi idan yazo se a dakko masa na flask din"ta karashe maganar tana sakkowa daga kan kujerar hade da janyo plate din gabanta tana juya abincin da cokali,

"To hakanma yayi,barin koma kitchen girkin baffanku nake karasawa idan kingama seki xo kitayani da wani abin"

"To ammi"

Haka rayuwa tacigaba tsakanin UMMI AISHA DA ASHRAF ita takasa gane Kansa kwata kwata yau yamata mutunci Gobe idan taxo xe nuna duk duniya besan an halicceni ta bama,haka xe kare mata tutorials din KO kallo bata isheshiba wani lokacin Kuma yaita janta da hira KO xata tafi seya janyo topic din daxata dan Kara jimawa,ta tabatar a arrogants dinma shi first class ne sekace me bataliyar aljanu akansa dake bukatar ru'kiyya...

Kamar kullum lecture din 12 ne dasu,around 11 dede suka fito itada baby kay dan yakaisu school,cikin sauri suka bude mota suka shiga,UMMI AISHA tabude jaka tana neman wayarta kenan taduba taga babu littafin ta babu alamarsa gashi lecturer din no nonsense ne kullum cikin operation show me your note yake,inbaka da note dinsa Bakada attendance dinsa kenan cikin rawar murya UMMI AISHA ke salati"menene Kuma?!"baby Kay tace da Ita taname rage volume din wakar datakeji tacikin earpiece,

"Littafina,naman tashi gurin coach dina"

"And so?!"

"KO...koxamu biya na karba Dan Allah?!"

"Wallahy a'a,wallahy baxamu koma bayaba,kinsande yadda xaki kawai amma Wallahy baxaki makarar daniba kinji Allah"

"Shikenan barin sauka anan kawai"UMMI AISHA tasauka daga motar kamar xatai kuka ,bawai tsoran baby Kay takeba,tashin hankali ne bataso kawai,

Napep tahaye yakaita har 'kofar gidansu ASHRAF Sannan tasa kai tashiga bakinta dauke da sallama,babu kowa a parlor din se me aiki dake faman goge goge,bayan sungaysa ne UMMI AISHA ke fadin,

"Ayush nanan kuwa?!''

"Da sassafe suka fita itada mama amma inaga sunkusa dawowa dan mama tace bada'dewa xasuyi ba,kijira su mana"

"Bakomi sauri nake makaranta xani dama littafina namanta jiya anan 'din ko kinga shi?!"

"Gaskia babu littafi anan,jiyan de dare mama tabawa ASHRAF wani littafi nakejin nakinne"

"Too nagode...barin karba yatashi kuwa?!"

"Yananan dinning kiduba"

"Nagode"UMMI AISHA tafadi hakan a takaice tareda jan kafafuwanta dasukai mata sanyi Lokaci daya ta Isa dinning area din gabanta se dukan takwas takwas yake,ta dade abakin kofa tana kame kamen yadda xata shiga ciki,Kai tasa tana leken ASHRAF din dake sanye da 'kananan kaya wando jeans baki se riga ja kirar polo tareda blazer sanye ajikinsa,gefe daya kuma coffee cup ne agabansa da plate da waffles akai,hankalinsa kwance yana danna waya se murmushi yake,dakyar ta iya hadiye yawun dayatsaya mata tayi sallama ciki_ciki,seda ta sake wata sallamar kafin ASHRAF ya amsa da"wa alykm salam"

"Ina kwana?!"tace dashi haryanxu tana jingine ajikin 'kofar itabata shigo ba bakuma takoma ba,

"Yana kwano"yabata amsa yana cigaba da danna wayarsa hankali kwance,

"Nace littafina da mama ta baka xan karba"

Shiru yai da Ita yana cigaba da taunar waffles dinsa,

"Kaji"takara ce masa hakan nanma yai shiru da Ita"makaranta xantafi sauri nake"takarashe maganar muryarta se rawa take,

"Mtscewww "yaja siririn tsaki"ni 'dankine?!daxaki dinga kirana da kaji magana nake dakai,inada suna bawai 'dan farin dakika Haifa bane Kike boye sunansa,mexanyi da wannan littafin naki da rubutunki kamar jerin tsutsotsi dake chanjin sheka,it's somewhere around this place"yafadi hakan tareda sa hannunsa yana nuni da wajen tv stand"ki nutsu kiduba littafinki hajia inkika makara ni babu ruwana"

Dukkoda maganarsa ta daki UMMI AISHA hakan be hanata karasa shiga ciki ba,ahankali tadinga dubawa lungu da sako tana neman inda xata ganshi,'can ta hango littafin kusada gidan cd carriage dake cike da Korean series kala kala,hamadala tai Sannan tasa hannu ta dauki littafin nata me cin ten subjects,da sauri tasashi cikin jaka tareda zugewa cikin sassarfa take dosar hanyar fita hartasa 'kafarta daya awaje muryar ASHRAF ta tsaida Ita cak
"Hold on"yace da Ita yana karasa sipping coffee dinsa,bayadda ta iya tsayawa tai batare da ta juyo ba,haka kawai yatsinci Kansa ya rasa meyasa yatsaida ita bayaso tatafi...






•✨•
54




"Lecture din nawa kike da yau?!"yafadi hakan yana kallonta ko kiftawa bayayi,tagane yana kallonta domin jikinta yabata gashi bataso tahada idonta da wannan shegen sleepy eyes din nasa yana magana yana lumshe su,

"12"tace dashi tana gyara tsaiwarta tabaya,

"12"Yamaimaita hakan tareda kallon agogon hannunsa 11-12,"kedah driver ne?!"yasake fadin hakan yana kallonta dukkoda bayanta ajuye yake sosai shigarta tayi masa Kyau sanye takeda doguwar rigar abaya 'baka me torches blue tasha jakanta blue da covered shoe blue shima,

"Uhm uhm ba driver bane yatafi yakai khadija kartai late"

"Lemme drop you"yafadi hakan tareda mikewa yadauka carkey dinsa agefen coffee cup,

"No thanks,zantafi da kaina nagode"Sannan ta cigaba da tafiya,muryarsa Ce takara tsaida ita

"Nima bawai so nake nakaiki ba hajia kada ma kikawo hakan a zuciyarki no not at all,Nima xanyi attending lectures din,sannan yanxu haka 12 ya kusa temakonki xanyi bawai....shikenan de kawai"

Sosai maganarsa ta ta'ba xuciyarta batada tacewa,shiru tai tana naxarin kalmominsa Wai temakon ta xeyi duk Ita tajanyo wa kanta dataxo wajensa in the first place,amma komai yaxo karshe baxata sake xuwa ba,abinta tai tamaimatawa kenan cikin zuciyarta ,dakyar ta'iya Jan sayyadar kafafuwanta tabi bayansa dayake Yayi gaba abinsa,motarsa 'kirar Mercedes Benz suka nufa yabude yashiga yatada motar,harta bude gaba xata shiga yai saurin dakatar da Ita dukkoda so yake taxauna agaban yana kallon kyakkyawar fuskarta amma ya kasa hakan"Noo Ki koma baya kixauna,bakisan sit din gaba only meant for special person ba,Ki koma baya tunda temakonki xanyi I will be your very own driver yau"

"Wannan cin fuska har ina?!"UMMI AISHA tafadi hakan a zuciyarta,bude kofar tayi takoma baya taxauna,sosai hawaye yafara ambaliya a fuskarta takuma kudiri niyyar daga yau baxata Kara xuwa yai coaching dinta ba,yana kallonta ta fuskar mudubi soyake yabata hakuri amma arrogant dinsa yahanasa dukse yaji ba dadi gefe daya Kuma yanema farin cikinsa yarasa,ciki asanyaye yatada motar yafara tafiya yanayi yana kallon UMMI AISHA amma kotakansa bata biba sema regrets dataketayi data sanshi arayuwa....!

•BAYERO UNIVERSITY KANO;

___suna xuwa department of political science ASHRAF ya nemi gurin parking yai parking motar,dede da futowar baby Kay da kawarta daga cikin department din,da sauri UMMI AISHA tasa hannu a fusace tafice,beyi niyyar futowa daga motar ba ganin hakan tafaru yasashi futowar shima Dede lokacin da kawar baby Kay ta dora idonta akansa,"OMG osheey Kinga wani THE CHARMING ?!"tafadi hakan tana taba baby Kay dake faman magana dawani a gefe..
Da sauri baby Kay tadago kanta dan ganin the charming din da ake fada,gaba daya she was totally speechless naganin ha'dad'dan gayen datayi tsaye ajikin motarsa yana waige waige da alama wani abin yake nema,
Kawarta ce takatse mata kallonsa datake"kinsan dawa naganshi kuwa?!"baby Batai magana ba illa kada kanta datayi,

"Da UMMI AISHA naganshi"

Ware Ido baby Kay tayi"wacce UMMI AISHA Kuma?!"

"Sister dinki mana"
Basu karasa magana ba ASHRAF yaxo yawuce tagefansu yashige cikin department din inda lecture hall din suke,

"Osheey wannan dake yadace fa"kawar tata tafadi hakan tana kallon bayan ASHRAF din dake tafiya,

"Kede bari kawai xatai bayanin inda tasameshi,daxu hardamin karya wai tamanta note dinta,ashe haduwa xashi well he's not her type ai"hannu tabata suka tafa sanann suka koma cikin department din dan ganin wannan ha'dad'dan guy haka..,





•✨•
55



Suna xuwa suka shiga cikin hall din na yolamu dake cikin dept of pol sci,Neman waje sukai suka xauna cikin kujerun basuda yawa yan ajin dayake elective course ne,UMMI AISHA dake gaba batasan wacce wainar ake to yawa ba,hamdala tai ganin se alokacin lecturer din yaxo,bawani 'bata Lokaci yafara masu lectures akan 'scientific management theory' gaba daya hankalin ASHRAF da gangar jikinsa tatafi ga UMMI AISHA dake jotting abinda lecturer din yafada,baby Kay kamar ta fashe donganin irin kallon da the charming din yake jefar UMMI AISHA dashi,sosai lecturer din yamasu lectures Sannan yafara tambayar questions kamar yadda yasaba"who was the founder of scientific management theory??"

Ajin akai shiru masu buya suka fara masu sunkuyar dakai kasa suma suka fara,da sauri UMMI AISHA tadaga hannu don ASHRAF abinda yagama mata tutorials akai kenan shekaran jia,"go ahead UMMI AISHA I'm all ears,some people sat down shamelessly looking,idiotic morons,Allah yakyauta yakarashe maganar yana girgixa Kansa naganin kusan kullum itake amsa questions a ajinsa kamar Ita kadaice student,
Tashi UMMI AISHA tai tafara magana"scientific management theory was a concept coined by Lois d Brandeis in 1910,but it was popularized by Fredrick Winslow Taylor in 1856_1915 because of the fact that Taylor was an engineer at midval industry"

Professor tajuddeen yai murmushi hade dasa hannunsa ya tafa mata,"that's very good,very very good,,,class a very loud round of applause to one of the bestest student in the department"nan ajin akahau tafi,shide ASHRAF dake gefe murmushi yai Kuma yaji dadi sosai har cikin zuciyarta naganin yabonta da akai,

"Thank you UMMI AISHA may you be forever blessed,keep it up the sky is your starting point..."professor tajuddeen yace da UMMI AISHA da kanta ke asunkuye,karaf idanuwansa suka hadu dana ASHRAF gashi betaba ganinsa a ajinba

"The man with the blazer stand up"yaceda ASHRAF,ba musu ASHRAF din yatashi yana Sosa keya,

"Are you part of this class?!"

"Yasss sir"

"No you are not,kindly check out"

"Yass sir I'm part of this class"

"If yasss show me your id card,any slightest mistake consider your self withdrawal"

"Okay sir"Sannan ASHRAF yaciro ID card din nasa ya mikawa malamin"

"ASHRAF KABEER KAMAL"professor din yafadi sunan a hankali,"you better be serious,ya akai Baka xuwa makaranta?!"

ASHRAF yai shiru yana tunanin can idea ta fado masa"sir credentials dinane na nemasa na rasa har lokacin screening ya kure,se daga baya nagani har academic office sukace xasumin changing of course to kumade basu canxa ba..."

"Ayyah,okay sit down"professor yace da ASHRAF hakan Sannan yakoma gaban podium yatsaya yacigaba da lectures dinsa kusan one hour da thirty minutes sanann ya rufe littafinan"okay class let's call it a a day"

Yammatan ajin akahau juyawa ana kallon ASHRAF dake yamutsa fuska kaman yaga kayan wanki soyake yaba UMMI AISHA hakuri amma ya kasa bakinsa Yayi masa nauyi,mikewa akafarayi ana tafiya dama lecture daya ce dasu aranar ta professor tajuddeen,
UMMI AISHA tahada Kayan karatunta tasa a jaka tafice tabar ajin,da sauri ASHRAF yabi bayanta,baby Kay naganin haka itama tabi bayansu tana sauri,lokacin har driver yaxo daukar su da sauri UMMI AISHA tabude mota tashiga kotakan ASHRAF dake binta kamar jela a baya batabiba,itama baby bude motar tai tashiga driver yaja suka tafi,ganin haka yasa ASHRAF yaji hannu hade dasa hannu yadaki gefen motarsa"damn it"yace da Kansa yana Kai kawo awajen....

A mota baby Kay tajiyo tana kallon UMMI AISHA tarasa mexatace takawo topic din ASHRAF"muga note dinki"bamusu UMMI AISHA tadakko note din tabata,bayan baby Kay takwafa tamayar mata"gashi Nagode"da sauri UMMI AISHA tajiyo tana kallonta don bata taba jin wannan kalmar tafito daga bakinta ba koda suna kanana,murmushi baby Kay tayi"I was worried daxu da bakixo ba kada professor yashigo bakinan"

"Why are you acting so strange?!"UMMI AISHA tacewa baby Kay hakan dan itakam bata yadda da Ita ba,baby Kay tayi shu'umin murmushi "to cut the story shot ,who's that charming??"

"I knw right ashe"UMMI AISHA tafadi hakan tana daria,"ASHRAF sunansa shine tutor din da mus'ab yace muje wajensa"

"Seriously?!"baby Kay ta ware ido,

"I'm damn serious"UMMI AISHA tabada amsa a takaice,

"Nacuci kaina oh boy nayi falling for guy dinnan he's too cute Kinga pink lips dinsa lets keep it a deal ba kinaso muyi kirki dake ba?!well xamuyi mutunci dake nikuma ki barmin ASHRAF dinnan plssss"baby Kay takarashe maganr kamar xatai kuka,

"Base munyi deal ba khadija,niba boy frnd na bane kawai yana coaching dinane beside ma ni be yimin ba at all,idan kina sonsa kije nabaki shi Wallahy ni nama dena xuwa tutorials din"

"Meyasa??"

"He's arrogant,bashida mutunci at all"

Daria baby Kay tayi harda rike ciki,hakan yasa UMMI AISHA kallonta sosai takeson tilon 'Yar uwartata tajini inama ace su dawwama ahaka suna hira abinsu cikin so da shakuwa irinta 'yan uwan juna,"nikam ina sonsa,yaxa'ayi?!"

"Kawo kunnenki kiji"UMMI AISHA tafadi hakan,da sauri baby Kay takai kunnenta UMMI AISHA tarada mata mission din daxasu hada,




•✨•
56



Weeks passed haka rayuwa taja ARFAAN gaba daya yakasa fadawa UMMI AISHA abinda ke cikin xuciyarsa,bangaren ASHRAF kuwa yadamu matuka narashin ganin UMMI AISHA da bayayi,koyakirata bata dauka yarasa meyasa kanwarta baby Kay ta like masa kamar super glue Yayi Yayi tarabu dashi taki saboda UMMI AISHA shiyasa baya mata rashin mutunci amma basar da Ita daki mata magana tana shansa kullum gata da nacin bala'i kamar ba mace ba,
A satin ne akai saukar qur'anin su UMMI AISHA da baby datasha da kyar akai da ita tanada kokari amma idan ta maida hankali,a Kuma satinne akai fixing wani satin xa'ai taron debate na top 5 universities a a nig kowanne university takawo students dinta kwara 2 kawai mace da namiji,tashin farko senates na Buk sukai taro kan Wanda xa'a bawa ganin UMMI AISHA nada 5;00 a exams din dasukayi gashi duk wasu tests da debates setaci idan akayi tunma ba a university na iya north region ba,shiyasa suka xaba UMMI AISHA amatsayin representative ta Buk gaba daya a mata,while a maxa Kuma wani Muhammad Salem suka zaba dake medicine a old site,xa'a gudanar da debate dinne a coronation hall dake govt house kn..

Ranar Monday kamar kullum su UMMI AISHA sun shirya driver yakaisu makaranta harta shiga lectures akace professor tajuddeen yana nemanta office dinsa tanufa gabanta se faduwa yake "Allah yasa ba wani lefin naiba"tafadi hakan a zuciyarta,bayan tashiga suka gaysa da malamin batare da bata Lokaci ba yafara mata bayani kamar yadda senate na makarantar suka xartar da hukunci,shiru UMMI AISHA taitana tunanin wannan abin bawai baxata iya ba kawai de acikin dubban mutane xata futo tai bayani?!

"Don't be scared of your potentials UMMI AISHA,I knw you can do it"professor tajuddeen yace da UMMI AISHA hakan,itade shiru tai tana tunani,Kuma intai hakan atleast Ammi da Baffa xasuji dadi ace 'yarsu tayi hakan cikin billions of students Ita aka xaba,

"Tohh malam"abinda tace a takaice kenan,murna gurin professor ba kakkautawa dadi kamar yatashi yataka rawa,nan yafada mata yadda xatai komi da coaching din daxasu dinga yi mata kullum har weekend xa'a mata,Sannan yabata takarda da mini project din daxatai yake aciki a rubuce boldly;1_multinational corporations and sustainable development in Nigeria,na biyun Kuma shine;
2_man power planning and development in the public sector...
Kafin tabar office din sedaya Kara coaching dinta wasu abubuwan sosai,koda takoma gidah Ma Ammi da Baffa suka Kara karfafa mata gwiwa Kuma tayi addua kan idan alkhari ne wannan abin Allah yasa tayi,sosai take addua har ranar debate din taxo a coronation hall akeyi yacika Yayi makil da mutane dukkoda card admits ne,batare da bata Lokaci ba aka fara kira students daga first university wato nsukka(Nigerian university)bayan sun kammala suka koma judges dake rubuta scores suka fara aikinsu,gaban UMMI AISHA se faduwa yake,Se university of Lagos nanma suka fito sukayi nasu,followed by Ahmadu Bello university Zaria nanma suka fito sukayi,then Se wata university a ogun,se bayero university kano,seda namijin yafarayi kafin UMMI AISHA tafita gabanta se faduwa yake tana addua jikinta Se rawa yake,da hannu professor ke mata nuni da "calm down take a deep breath"

Gefe daya Kuma ASHRAF ne yaxuba mata arrogant face dinsa tareda sleepy eyes dinsa yana kallonta,sekuma yasakar mata murmushi,gaba daya UMMI AISHA seta nemi fargabar gabanta ta rasa,sosai tadaga murya tafara kwararo jawabi cikin muryarta me da'din sauraro da tafiyar da hankalin duk Wanda ya saurara,...ta jima tana jawabi kowa yanutsu yana jinta musanman yadda ta'iya turanci dakuma fitar dashi yadda yadace,bayan tagamane a kadau tafi,judges suka fara completion na scores,cikin sauri Wanda xe fadi makarntar dataci yafito yana kallon takardar Sannan yakalla audience din dasuka xuba ido suna sauraron Wanda xekira,
Award din me taken"MAGNIFICENT PERFORMANCE"
"Okay fine I wll like to call on stage.......!"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login