Showing 30001 words to 33000 words out of 107296 words

Chapter 11 - UMMI A'ISHA(THE MAGNIFICIENT) COMPLETE

22 Aug 2024

7691

take wuni"

Haka sukaita hira sukaci abinci Sannan sukai mata sallama xasu tafi,biscuits da sweets da chocolates dayawa Hafsat tabawa MUHANNAD,suma Kuma sunkawo katuwar Leda cikeda kayan jarirai na mata harda turmin atamfa,se bayan isha'i Sannan suka tafi bayan Hafsat tayiwa MUHANNAD alkawarin har gida xata kawo masa UMMI A'ISHA,dakyar yayarda yatafi waishi sesun tafi da ita,

Satin captain adam biyu yadawo dga abuja straight part din Hafsat yanufa dayake haryanxu xaman nasa da magajiya yananan yadda yake se abinda ya'karu ma,yana sallama ya'dauka UMMI_A'ISHA dake kicking 'kafafuwanta tana tsotsan hannunta,dagatayai sama yana mata wasa "honey boo boo I missed you sosai,se magana yake mata kamar wadda takejinsa kema kinyi missing baffa uhm?!"

Hafsat ce tafito daga daki tana waige waige,ganin UMMI_A'ISHA datai a hannun captain yatabbatar mata shiya 'dauke ta don taajiyeta kan gadonta se tashiga bandaki tawanko fuskarta tadawo Kuma batagantaba taxatama ko kukatake haule ta dauketa don bandakin can cikin corridor yake a gefen dakin,

Sannu daxuwa ta masa Sannan suka gaysa,sundan jima suna hira Sannan ya bukaci takawo masa abinci"Hayatee a'bangaren magajiya kake fa kada mushiga hakkinta kaga ba da'di"

"My hafsat kiyi abinda nace maki kawai nibaxanci abincin waccan matarba"

Batai musu ba don bata sabayi masa musun ba,takawo masa komi yaci yakoshi,da daddare ma haka yadage anan ze kwana anan seda Hafsat tai masa wa'azi meshiga ciki tareda tsoratarwar irin azabar da Allah xe masa dakuma kalamai masu dadi,haka captain adam yahakura yatashi yatafi don amatse yake sosai,

Haka kuwa akai,komai ya wakana tsakanin captain adam da magajiya ,wadda kamar ansata a aljanna don da'di,da safe hardasu kiran magajiya Sannan tayi farfesun kaji tabayar akaiwa masu gadi sukansu sunyi mamaki kwarai matuka don 'kwayar shinkafa daya bata taba basuba sefa yau'din,shide captain adam yayine kawai dankada yashiga cikin wani hali tunda yakasance mabu'kaci,

Haka lokaci ya'danja kamar wata 'daya kenan,sosai yanxu auratayya take shiga tskaninsa da magajiya dukkoda yanayi ne donbabu yadda xeyi 'din tinda Hafsat din babu dama,muna_b da magajiya sunshigo sunfita tahaka suka fara janyo hankalin captain adam yafara karkata xuwaga magajiya din,abin tunbaya damun Hafsat harya fara damunta dukkoda ko ka'dan soyayyar dayakewa baby UMMI_A'ISHA Dede da kwayar zarra bata raguba,

Da safe Hafsat tashrya xata tafi asibiti tayi mamaki kwarai datacewa captain adam xata asibiti yace jirgi yakaita don hakan bata taba faruwa ba,haka tashrya taje akai mata weekly shot,sannan nurse hidaya tace"Maman UMMI_A'ISHA akwai abinda yake daminkine don naji jikinki zafi?!"

Nan Hafsat tafa'da mata yadda takeji,bp dinta tagwada"Kai,bp dinki Yayi high Maman UMMI_A'ISHA,kirage damuwa gaskia karkijanyowa kanki stroke,Allah ya kiyaye amin....!"





WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;NANA HAFSAT..
[4/18, 11:57 PM] Asy Khaleel: •✨UMMI_A'ISHA✨•

(THE MAGNIFICENT)
31

©•MISS XOXO
👄

DEDICATED TO;
UMMI_A'ISHA👌🏼

nanahafsat.wordpress.com

•✨•✨•✨•✨•✨•✨•

"Amiin"abinda Hafsat ta iya fa'da kenan,sanann taiwa nurse hidaya sallama tatafi,ba gidah tawuce ba gidansu tawuce yiwa abbansu sallama dayake xasu koma berlin na tsawon shekara biyu don lapiar sa,

Tana zuwa tashiga ciki masu aiki suka fara haba haba da ita kamr yadda suka saba Sannan suka amshi baby UMMI_A'ISHA itade shiga cikin parlor dintai abban nasu da maman xaune suke suna kallon news atashar aljazeerah,bakinta 'dauke da sallama tashiga ciki,

Neman wuri tai taxauna agefensu bayan sun amsa sallamar"abba barkada rana ya 'karfin jikin?!"

"Alhmdlh Nana"(yadda yake cewa da ita kenan)"jiki da sauki sosai,ya mutan gidan?!"

"Sunanan qalau abba,suna gaisheku ma"

"Masha Allahu"

Juyawatai da kanta 'bangaren maman"mama barkada safiya,ya me jiki"

"Lapia qlau hafsatu,jiki Alhmdlh,Ina Kuma UMMI_A'ISHA?!"

"Ina shigowa kenan su farila sukakarbeta anan balcony"

"Ayyo nide ince bagida de kika barta ba"

Itade hafsat murmushi kawai tai,

Sun'dan taba hira sanann farila me aiki tadawo da UMMI_A'ISHA wacce ke sunkufe cikin over roll white and orange ga hulan sanyi ga over roll sweater ansa mata tayi kyau abinta ,tuni abba yasa hannu ya karbeta yana mata wasa,bayan yagama yatashi yatafi masallaci Ita Kuma mama takarbeta tacigaba da yi mata rawa,Sannan tabawa Hafsat Ita ta kwantar da ita a kan kujera tinda har bacci yadauketa,Maman taga dukyanayin hafsat 'din gashinan gashi nan ne"lapiar kikuwa hafsatu?!naga kamar bakya cikin hayyacinki wani abunne yafaru keda abokiyar zaman takine?!!"

"Babu komai mama kaina ke ciwo"haka hafsatun take dede da rana 'daya bata ta'ba Kai 'korafi gidah ba shekara ashirin kenan,dama Kuma haka akeso mace takasance bata maida gidansu gurin yaji dakai 'karar mijintaba,

"Toh shikenan Allah yasawwake,akwai wasu addu'oi da matar sadeeq tabani xandakko makisu inxaki tafi ..kidaure kidinga yi insha Allahu koma menene Allah xekawo karshensa,

"Allah yasa,nagode mama"

Haka sukaita hirarsu har abban nasu yadawo aka sake bude shafin xumunta,sosai shima yashiga yi mata nasihar da jajirtattun iyaye keyiwa 'ya'yansu,

Sallama tamasu cikeda kewar iyayen nata daxatai natsahon shekaru tinda adaren ranar xasu tafi 'kasar berlin, takoma gidah jirgi na parking tatafi part 'dinta....dama captain adam awurinta yake ranar kwana biyu biyun dayake masu taxagayo kanta...

Tuwon semo vita miyar karkashi tayimasa da zo'bo wanda yaji kayan kamshi se fruit salad dakuma soup na kayan ciki,shigatai bandaki tayo wankanta cikin shigar doguwar riga maroon ta material 'dinkin Senegalese tayi kyau abinta, light makeup tayi shiru ba alamarsa,se wajen tara da rabi yashigo ciki abinda 'betaba yiba,

Tararsa tayi kamar yadda tasaba,ignoring dinta yai tahanyar karbar baby UMMI_A'ISHA,yana mata wasa jiki sanyaye hafsat takoma baya tana wasa da yatsun hannunta ko kadan beso yake mata hakan ba yarasa meyasa wannan abin yake faruwa dashi tsakaninsa da hafsat ,da addua da komi yasamu yaci abincin data dafa Sannan yashiga 'daki kafa'darsa dauke da baby UMMI_A'ISHA!

Bandakin dake cikin parlor din tashiga tayo alwala sanann ta ziri hijabi tafara nafulfuli tana mekaiwa Allah kukanta ha'de dayin adduar da Maman tabata,Allah meyadda yaso kafin sati biyu tacika seda hankalin captain adam yadawo jikinsa har kuka yaiwa Hafsat dinsa nadaga abinda yake mata tayafe masa, nuna masa tai aibabu komai ba lefinsa bane tinda bahaka yake ba ba halinsa bane,

'A karshen satinne Kuma magajiya tatashi da matsinancin zazzabi asibiti captain ya sa jirgi yakaita awun farko yanuna tanada ciki positively gashinan arubuce ,tabbas captain adam yaji da'di saboda 'ya'ya rahamane shida yake nema gashi Allah yabashi yakuma sake bashi,Wayyo zokuga gwalli da gwatsarewa tuni magajiya tadinga tsurfa kala kala dukkoda captain adam din yanayi matane saboda kawai darajr dansa ko 'yarsa dake cikinta,

Babu wanda besan tanada ciki ba lungu da sa'ko na yan uwa duk sedata fada masu gashi Kuma ba haihuwar fari bace ballanatana ace,tunda 'Dayan gidan data fito tanada gartsetsen gardin 'danta baki wuluk kamar ita,,,,abinci se Wanda ta zaba cikin da ko wata daya bekaiba se zuzuta shi take,tuni takira muna_b tasheda mata yadda ake ci,washegari da safe muna_b taiwa gidan asubanci bayan sungaysa sunyi komi muna_b ke fadin"yanxu yaya captain 'dinnaki da hafsat din?!"

"Oho 'canta matse mashi,nide tinda nasamu ciki aishikenan dama haka maxan suke?!"

"Haba kawata kmar Wanda kikai auren farko ,barin Gaya maki hadisin maxa,yana daya daga cikin shika shiken maxa,Kinga namiji kamar gurjiya yake se an kasa akansan na kwarai,hmm 'kawata namiji kamar hankaka yake gabansa fari bayansa ba'ki...nifa Allah natuba bande yi auren ba amma babu namijin daxe 'boyen halinsa..kede tunda kinyi ciki Alhmdlh sekin cika gidannan da ya'yan ki yanxu Ita banzar tasan kinada shine?!"

"Nasan yafa'da mata mana aibaya boye mata sirrinsa"

"To ai bahaka tabarshiba,kede bari namana wani sabon catch na boka ance aikinsa kamar yankan wu'ka inde kinada farcen susa bakida damuwa,xan jonaki gareshi"

"Yawwa kawas shiyasa Kike da'da shiga raina kullum"

Haka sukaita hira muna_b nabawa magajiya miyagun shawarwari tana 'dauka,se wajajen 'karfe hudu na yamma Sannan tai mata sallama tatafi kanzata dawo nanbada da'dewa ba....

Kodah captain adam yasanarwa hafsat magajiya nada ciki tanuna murna kwarai tareda fatan Allah yasauketa lapia,har cikin zuciarsa yaji dadin kalaman da Hafsat din tafada!

'Kwanci tashi ba wuya awurin Allah UMMI_A'ISHA nada shekara 'daya da wata daya a duniya magajiya ta haifo 'yarta 'Baka Kirin kamar bayan tukunya ko kusa baxakace captain Adam ne mahaifinta ba,ba lefi yan Uwa suntaru sosai ,ranar suna raguna biyu da saniya daya captain Adam ya yanka amma magajiya tai kicin kicin tasa dole yakama mata fabs event center tunda boka yamata abinda kome tatambayeshi seya bata..akai hadadden suna kamar dinner 'yar gata su kansu su surayya basuji da'din kashin kudin da yayan nasu keyiwa magajiyan ba musanmn yanxu data Juya masu baya kamar basune sukai sanadin auren ba,yarinya taci suna 'KHADIJA'magajiya ta'dau son duniya ta'dorawa baby KHADIJA,ba lefi captain adam yanasan yarinyar tunda jininsace amma Gaskia yafison UMMI_A'ISHA...!

Baby UMMI_A'ISHA yanxu tana tafiya abinta ko'ina tana ammi wai hafsat dintake kira se bapa(Baffa)yar gwanin sha'awa da ita ga Kyau ga gashi Kuma doguwace kamar tayi shekara uku aduniya tubarkAllah!

UMMI_A'ISHA nada shekara 'daya da wata uku,hafsat tayayeta dayake tanada saurin girma ga garin jiki,asibiti taje don kwanakin nan batajin da'din jikinta,karo sukaci da magajiya abakin balcony din dake farfajiyar gidan magajiyan tawani yatsine fuska kamar taga kashi hannunta rike da KHADIJA 'yarta"to kekuma wannan saurin dakike haka Ina xuwa?!nide Nida 'diyarta kurwarmu kur"Sannan ta tsirtarda yawu akasa ta wuce,

Itade hafsat ko cikanki batace mata ba danyadda takejin jikinta koda dukanta tai baxata mata komi ba,saboda inka raina kasuwa ma ko sautu baxaka bayarba,asibiti tawuce jirgi yakaita tasamu dr NAUFAAL kuwa,gwaje gwajensa yai Sannan ya girgixa Kansa,hafsat damuwa karara a fuskarta take tambayrsa"dr akwai matsalane?!"

"Babu matsala"haka kawai yace da Ita a takaice,waya yakira captain kanlalle yaxo asibiti yanxu ,ba'adau lokaci ba kuwayaxo,inda dr yasheda masa hafsat nadauke da ciki amma yakoma bayan mahaifa yai sauri yasa hannu atakarda donsuyi mata aiki su cire inba hakaba komai xe iya faruwa,gabadaya captain adam a rikice yake se zufa ke ketomai,operation room suka nufa da Ita andau lokaci dr NAUFAAL yafito yana xare safar hannunsa,

Captain adam yatafi inda yake"yaya ake ciki dr?!"duk ya ki'dime

Dr NAUFAAL ya girgixa Kansa gaba daya jikinsa Yayi sanyi"captain munyi bakin kokarinmu amma Allah yayiwa......




WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;NANA HAFSAT.....
[4/18, 11:57 PM] Asy Khaleel: •✨UMMI_A'ISHA✨•

(THE MAGNIFICENT)
32

©•MISS XOXO
👄

DEDICATED TO;
UMMI_A'ISHA👌🏼

nanahafsat.wordpress.com

•✨•✨•✨•✨•✨•

Dr NAUFAAL ya girgixa Kansa captain munyi bakin 'kokarinmu Allah yayiwa abinda ke cikinta 'karar kwana dukkoda bekai haihuwarsa ba amma ya'dan girma bayadda xamuyi mun cire shi"

Captain adam ya girgixa kansa"dr kafa'damin gaskiya saboda daga ganinka nasan hafsat ta rasu" yashiga kuka ba 'kakkautawa,

Dr NAUFAAL yai murmushi Kawai hade dasa hannu yaja kafa'dar captain adam su shiga cikin office 'dinsa,harkan kujera ya xaunar dashi Sannan yakoma tasa kujerar yaxauna yaha'de hannuwansa,

"Captain kata'ba ganin anyi wasa da mutuwane?!sannan matan dake cikin operation room sunada yawa Wanda duk nine da temakon nurses mukeyin aikin saboda sauran doc 'din basanan,ayanxu haka mata masu ciki Wanda xasu haihu ma su uku ne suka rasa rayukansu agaban idona ta 'karshen data rasu ita jaririyar ta rayu kaji abinda yasa jikina yai sanyi kenan"

Captain ya tsaida kukan dayake Se ajiyar zuciya Kuma"yanxu xan iya ganin my hafst?!"

"Bari agama shryata tukun saboda ta jigata har wankin ciki akai mata nasa nurse ta mata allurar bacci daxan fito harta fara baccin ma itada baby UMMI_A'ISHA"

Captain adam yamike tsaye "kana nufin da UMMI_A'ISHA akai komai kenan?!"

"Abayan nurse hidaya take har aka gama komi,Sannan Hafsat din ta umarceta tabata Ita ta shayar da Ita to hakade sukai baccin tare,nanda awa daya xaka iya shiga bedrest mukeso tasamu dama"

Haka dr NAUFAAL yadinga kwantar mai da hankali harde awar tacika sannan captain adam yamike yashiga 'dakin da aka Kai hafsat din kwance take idonta biyu da alama ta farka tanawa UMMI_A'ISHA wasa dake kan ruwan cikinta azaune,

Bakinsa 'dauke da sallama yatura 'kofar yashiga,sallamar hafsat din ta amsa,UMMI A'ISHA najin maganar baffanta tafara murna tana Neman sakkowa daga kan gadon,da sauri ya'karasa yasa hannu yadauketa Se dadi takeji "'ammatan baffa yakike?!"itade se murna take tana tafa hannuwanta tana bapa(baffa)seda yagama mata wasa kafin yaxauna kusa da hafsat din yana kallon fuskarta dukta rame kamar ba Ita ba,"ya jiki my hafsat?!"

"Da sauki hayatee"

"Allah yakara sauki mekikeson ci yanxu insiyo maki?!"

"Banajin yunwa bakina ba apatite"

"Dole kici abinci ai my hafsat kalla yadda kika rame"

Itade hafsat shiru tai tana kallon baby UMMI_A'ISHA,

"Ina magana my hafsat"

"Shikenan hayatee asiyo yoghurt ma ya isheni"

Mikewa yai bayan yabata peck akumatu Sannan ya'dau UMMI_A'ISHA "bari muje mudawo xansa jirgi yakawo maki haule"

"Allah yadawo daku lapia ameen"

Futa yai daga 'dakin itakuma tajuya ta kwanta gaba daya jikinta ba 'dadi,siririn hawayene yake tsiyayowa daga idonta Wanda tarasa na menene,addua tacigaba dayi acikin zuciyarta har bacci ya'dauketa...

Sallamar da haule tai shiyasata sa hannu tai saurin goge hawayen datake,"Aunty yajikin naki?!"

"Da sauki haule"
"Allah yakara sauki ameen"
"Ameen"

Ba'awani jima ba captain adam yadawo da ledoji fal a hannunsa daya ,dayan Kuma UMMI A'ISHA ce ri'ke akafa'darsa hartayi bacci ,kwantar da ita yayi agefen gadon sannan yaciro wani pack da 'katuwar robar yoghurt ta L&Z,komawayai ta bangaren da Hafsat din take ya'dagota tareda sa mata pillow ta baya ta jingina,wanko hannunsa yai a bandaki haka yadinga 'dura mata roasted chicken soup 'din dakuma yoghurt batai musu ba don bata saba yi masu musun ba harta 'koshi Sannan ta goce xata kwanta yai saurin dakatar da Ita "my hafsat kakki kwanta yanxu,kibari abincin yai digesting inba hakaba xaki samu stomach upset"

Gyara xamanta tai akan gadon bata kwantaba tanata kallon 'yarta dake bacci peacefully abinta,captain adam ya mi'ke yashiga bandaki yawanko hannunsa sanann yadawo da roba da hand wash ahannunsa yatemakawa hafsat tawanke hannunta sannan yasa yatsansa cikin bakinta ya goge mata ha'koranta ha'de da zaro tissue yagoge mata baki Sannan yakoma bandaki yamayar "my hafsat bari naje wajen dr NAUFAAL"

"Okay hayatee take care"

Fita yai yatafi consulting room 'din da dr NAUFAAL yake,yaxauna sun'dan ta'ba hira Sannan captain adam yace"nikwa dr meyasa cikin my hafsat yaxube ko domestic issues na gidane yamata yawa?!"

Dr NAUFAAL yai murmushi "no not at all kasan lokacin datai wannan buguwan ta bugu sosai har mahaifan yaxama so weak shiysa data samu cikin seya koma bayan mahaifa Kuma hakan yanada hatsari gashi Kasan da akwai wannan ciwon haryanxu saboda haka Se ahankali don seda muka sake healing dinshi saboda ruwa yake fitarwa"

"To yanxu meya kamata ayi ko waje xanfitar da ita?!"

"dukde abin 'dayane de Insha Allah xata samu sauki xamu 'dorata akan magani"

"Allah yasa dr,godia nake"

"Yanzu xan rubuta mata magani,xaku iya tafiya ma tinda jikin nata da sau'ki"

"To shikenan Allah yasaka da alkhairi"

"Yawwa amma Dan Allah KO Yaya taji sauyi ajikinta akawo ta asibiti pls"

"Insha Allah hakan xa'ai"

Sallama sukaiwa juna Sannan captain adam yakoma wajen hafsat 'dinsa lokacin har baby UMMI_A'ISHA tafarka hafsat din na bata cereal,basu wani da'de ba aka sallamesu suka tafi gidah,

Tunda suka koma gidah tsahon sati biyu kenan hafsat ta warware ga kulawa datake samu na musanman nadaga wajen captain adam 'dinta ,UMMI_A'ISHA nacika shekara biyu cif aka yayeta ko ince tayaye kanta surutu babu kama hannun yaro ko'ina yawo take acikin gidannan babu sunan Wanda bata 'kokarin fa'da kaf gidan,Wutar 'Kinta kuwa kullum ruruwa take a zuciyar magajiya,musanman dataga UMMI A'ISHA din tafi 'yarta KHADIJA Kyau nesa ba kusa ba,

Kullum magajiya tana tatse captain adam kullum
Bani kaxa bani kaxa bashida bakin yace baxan bayarba tunda ankulle bakin,yanzu dukiyarsa cikin kashi 'Dari tadawo kashi hamsin,ranar wata lahadi suna xaune a babban parlor 'din gidan na captain adam ,xaune yake shida hafsat 'dinsa cinyarsa kuwa UMMI A'ISHA rike da biro se zane take 'kokarinyi a sketch book 'dinta,

Magajiya tai sallama tashigo tana zuwa ta'dora KHADIJA a'dayan gefen cinyar Capt adam 'din,fuskar yarinyar tayi fari 'kal kamar me bleaching Se 'kyalli take,Capt adam yabude baki"magajiya meyasamu yarinyar nan kalli yarda fuskarta tai fari ta'dashe ko batada lapia ne?!"

"Lapiar ta kalau lefi ne idan Fuskarta tayi fari bayan babanta farinne?!"

Captain adam yai daria Sannan yasa hannu a fuskar KHADIJAn aikwa ya lakuto foundation powder me 'maiko,ya ware Ido yana kallon magajiyan"menene wannan kika sa mata?!"

Magajiya tai dubi dubi se xare ido take kamar mujiya tana in'ina"i..inaga bansaniba ta..tasaka"

"Mtscew"captain Adam yaja tsaki tareda mikewa yaba kowacce 'yarta"'riketa Kuma kije kigoge mata koma menene kika sa mata,da fari da 'bakin duk Allah ne yayisu kada kisaka jahilci mana"

Sannan yafice fuuuu,magajiya da borin kunya ta isheta wucewa part 'dinta kawai tayi don kunya,

A 'bangaren hafsat captain adam din yake,kamar kullum part 'din yasha gyara se kamshi turare ke tashi dana abinci,sede dauriya kawai take yau 'din duk jikinta ba'dadi tarasa meyake mata da'di aduniya,sosai sukaci abincin ranar tare har nadare ma tare sukaci Sannan suka shiga 'daki kwance suke akan gado suna kallon news da ake rantsar da donald trumph,gaba daya hafsat 'din hankalinta baya wurinta captain adam yasa hannunsa cikin nata yana murxawa "my hafsat laifi nayine yau ake basar dani?!"

Hafsat tai murmushi sanann tajuya da kanta tana facing 'dinsa tasa hannu daya tana Shafa cyboc 'dinsa"ko'daya hayatee ni na Isa na basar da rayuwata?!kada Allah yakawo wannan ranar"

"To fada'min meke daminki?!"

Hafsat ta sauke nauyayyiyar ajiyar zuciya tana kallonshi"Hayatee Dan Allah kayafemin abinda namaka dunia da lahira"

Captain adam yasauka kasa down on his kneels yana kallon hafsat dinsa dake hawaye shima hawayen yafara"meya kawo xancen haka my Hafsat ?!sanin kankine Wallahy baki ta'ba min abinda xan ri'ke ki azuciataba kisani idanma kinyi Wallahy bansanshiba bayan Ma bakiyinba dawanda xaki yi nangaba da Wanda kike shirinyi duk nayafe maki dunia da lahira nima kiyafeni"

"Nagode hayatee Allah yabarmin Kai,dan Allah inaso arike min UMMI_A'ISHA tsakani da Allah abata ilimi both islama dana boko"

"Wai my Hafsat meya kawo wannan xancen kamar mebani will 'dinta"rungumeta yai tsam ajikinsa yana hawaye gaba 'daya jikinsa Yayi sanyi yarasa meyasa...

Kukan da UMMI A'ISHA take agefe shiya dawo dasu daga abinda sukeyi hafsat tasa hannu tadakko ta tana kallonta,,,"Ammi"abinda UMMI AISHA tace kenan tana kallon mahaifiyar tata,

"Na'am UMMI A'ISHA"









nanahafsat.wordpress.com


Ina me Baku hakurin rashin post danai na Kwana biyu hakan tafaru ne asanadiyar backup da wayata takeyi kusan kullum sena rasa chats 'dina ga mura danai fama da ita,Ina fatan xa'amin uzuri Kuma Insha Allahu xandnga posting akan Kari,nagode,
(Jameesh a'mika gaisuwata ga mama,Maman arfat Ina gaisuwa me tarin yawa)
Ga duk ilahirin masoya littafin UMMI A'ISHA aduk inda kuke inasonku Kuma Ina alfahari daku!!!!!



WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER NANA HAFSAT....
[4/18, 11:57 PM] Asy Khaleel: •✨UMMI_A'ISHA✨•

(THE MAGNIFICENT)
33

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login