Showing 48001 words to 51000 words out of 120369 words

Chapter 17 - DAUDAR GORA COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Nov 2025

249

a wheelchair take komai. Hakama Daneen Ammarah tsaye take kan Iffah, yanda take kula da ita yasa Iffah jin ?aunarta batare data san dalili ba, ganinta take tamkar Ummu.?Yanda ake tsaye kanta da gata da kulawa yasa ko damar yin ?wa?waran tunani bata da shi, dan da tayi shiru Daneen Ammarah zata nuna damuwa taita jera mata tambayar mike damunta? Ko tamanin wani abu ne a jikinta har yanzu?. Dole take sassauta damuwarta, sai dai tayi matu?ar dagewa wajen ambaton UBANGIJI kamar yanda Babiy da Ummu suka dinga jaddada mata a nasiharsu ta ?arshe gareta. Labarin mutuwar hadiman da suka kai mata rigar nan ta saka yazo kunenta itama, sai dai jin sanadin mutuwar tasu ya tsaya mata a rai matu?a, harma ta rasa yaya zata fassara al'amarin...
? ? ? ? Bayan idar da sallar isha'i tana zaune tayi tagumi gaba Waya hankalinta ya tattara ga tunanin iyayenta da mummunan mafarkin daren jiya a kansu Daneen Ammarah ta shigo hadimai uku biye da ita. A bakin gadon takai zaune tare da kai hannu ta janye tagumin da Iffah tai. Nannauyan nunfashi ta sauke da Wan Wagowa ta kalla Daneen Ammarah Win, sai kuma ta maida kanta ta risinar da mata sannu da zuwa. Daneen Ammarah dake kallonta cikin damuwa taja numfashi ta fesar batare data amsa ba. Dai-dai nan Hadiman da suke tare suka zube gaban Iffah bayan sun ajiye kayan hanunsu. Gaisheta suke da tsantsar girmamawar da ko iya Waga kawunansu basayi su dubi sashen da take. Sam Iffah batajin daWin yanda suke matan saboda bata sababa, a ranta gani take kamar ?as?ancine. Hannu Daneen Ammarah ta kaWa musu alamar suje, zumut suka mi?e tamkar ?yaftawar ido suka fice. Iffah ta bisu da kallo cike da jin raWaWi a zuciyarta.? ?
? ? ?  Ibnati! .?
??  Na'am Mamy! .
Iffah ta amsa cike da girmamawa ga Daneen Ammarah. Sosai sunan da Iffah ke kiranta da shi ke raunanata da sake jin ?aunar yarinyar, dan a bakin mutum Waya tak take jinsa kafin ita. Taja numfashi da haWiye hawayen da suka cika mata ido ta maye gurbinsu da murmushi.? ?
? ??  Ibnati bana son cigaba da ganin damuwar nan a fuskarki, ki kwantar da hankalinki insha ALLAHU babu abinda zai sake samunki. Wanda ma ya sameki ki Wauka kaddararkice kinji, amma inaji a jikina insha ALLAH kece mabuWin nasararmu, ke ce hasken da zata haska mana duhun da muke a ciki a Daular nan kinji .?
? ?? ? Kai Iffah ta jinjina a hankali, haka kawai take jin matu?ar nutsuwar kasancewa da wannan baiwar ALLAH, sam batajin irin zafi da tsanar da takema duk wani mai ala?a da masarauta a kanta. Kallonta take tamkar wata katanga ta wani babban al'amari dake tunkarota.  Mamy bana tare da damuwa in har kina a kusa dani, duk abinda ya sameni kuma dama ALLAH ya ?addara sai ya sameni koda banzo nan ba. Ina tunanin su Ummu ne da jin tsananin kewarsu saboda mummunan mafarkin danai akansu jiya, ina tsoron kar wani abu ya samesu ne suma? .? ?
?? ? Cike da jin tausayita Daneen Ammarah ta shafa kanta,  Duk Wa na gari dolene ya kasance cikin kewa a lokacin da yay nesa da ahalinsa, da ace inada dama da a yau sai na kaiki kinga su Ummunki. Amma dokar masarauta ce Zawjata-almilki tana fitane kawai bisa ?wa?waran dalili, zuwa gidansu kuwa tana yinsa ne sau biyu tak a shekara, Waya a sirrance, Waya a bayyane tare da rakkiyar hadimai. Shiko mafarki ai na gaskiya bane Ibnati, MANZANNI ne kawai idan suka yisa yake gaskiya a garesu, amma mu namu yakanzo da wasu sigogi ciki harda sheWanu .? ??
? ? ? A hankali hawaye suka silalo a kumatun Iffah, bawai lokacin ziyarar bane yay mata nisa, rashin tabbacin kaiwa lokacin ziyararne ya sata zubar hawaye. Ita dake zaman jiran ?addarar mutuwarta taya zatai tunanin zuwan waWan can damarmaki guda biyu na ganin su Babiy, maganar mafarki kam ta san gaskiya Mamyn ta faWa, itama kuma ba tana dangantashi da zama tabbaci bane, kawai tana matu?ar jin tsoron faruwar wani abu ne a dalilin mafarkanta na baya.... Ganin hawayen Iffah ya matu?ar tada hankalin Daneen Ammarah, a rikice ta shiga tambayarta kamar yanda ta saba in har ta ganta a makamancin damuwar nan. Hannu Iffah tasa ta share hawayen nata da ?ir?iro murmushi.
? ? ?  Mamy ki kwantar da hankalinki hawayen sunzo ne kawai da kansu babu dalili .? ?
? ?  Haba Ibnati, dama ana kuka babu dalili ne? Ko baki faWaba nasan kinada dalilan yin kuka, amma idan kika zama mai ha?uri da juriya wataran ke zakiyi dariya a gaban waWanda suka cancanta suyi kuka. ? ? ?? (ALLAH ya tabbatar da wannan ranar) Iffah ta faWa a zuciyarta, a zahiri kam sai ta goge hawayen tana murmushi. Hakan yasa Daneen Ammarah yin murmushin itama, kafin kuma ta mike tsaye da kama Iffah suka koma kan dardumar da aka shirya abinci acan gefe na Wakin, dan Wakine ?aton gaske mai dauke da komai na jin daWin duniya. Tare sukaci abincin, Daneen Ammarah har tana bama Iffah wani lokacin a baki, jitake inama Iffah Wiyartace, dan da'ace tana gidan aurenta har yanzu Wiyarta ta fari zata iya kasancewa dai-dai da shekarun Iffah ne. Kulawar Daneen Ammarah ta sake saka sassauci a zuciyar Iffah harta Wan saki jikinta. Bayan sun kammala ta sakata shiga bayi tai wankan maganin da take amfani da shi, data fitoma da kanta tai mata haya?in turare. Iffah ta hau gado ta zauna, Daneen Ammarah a gefenta da littafin tarihin annabawa acewarta zata dinga karantama Iffah har sai taga tayi barci domin Webe mata kewa.
? ?? ??  Yauwa Ibnati kin shirya dai ko? .??
? ? ?? Fuskar Iffah da Wan murmushi tace,  Eh Mamy na ? ? ? ?
? ? ?  Masha ALLAHU ashe dai Habibty na tare dani .??
? ? Hannu Iffah tasa ta rufe fuska tana murmushi, itama dai Daneen Ammarah murmushin take. Ta fara buWe littafin. Iffah dake kallonta tai dauriyar finciko Waya daga Wunmbin tabayoyin dake cin ranta ganin zata fara karatun...? ?
? ? ?  Mamy dan ALLAH na tambayeki wani abu? .??
? ??  Oh Ibnati tambayeni mana kanki ma tsaye kuwa. ? ?
? ? Iffah ta jinjina kanta da sauke ajiyar zuciya..........
'?
? ? ?


*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*


_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*?AN ?ASAR NIGER
+227 90165991

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu=?-?=?O?

5??5?2?5?)?5?"?5?'?5? ?=???


('5?o?5?l?5؀݊5?l?5?}? 5?r?5?z?5?}?5?l?('
(5?n?5؎?5ؐ?5؎? 5ؐ?5؆? 5ؘ?5؍?5؆?5ؙ?5؆?)



5???5???5???5??5??? 5???5???5???5???5???5??? 5???5???>??

*_22_*


.......Iffah ta jinjina kanta da sauke ajiyar zuciya,  Immm Mamy dama... sai kuma tai shiru dalilin gargaWin da zuciyarta ke mata tunda har yanzu fa Bama wai tasan matsayin Daneen Ammarah Win bane a masarautar.
? ? ?  Dama mi? Kinga karkiji komai kimin duk tambayar da kike bu?ata, insha ALLAH zan kasance mai baki amsa, idan kuma bata dace ba zan baki shawara kodan nan gaba .
? ? ? Kai Iffah ta jinjina  Dama dan ALLAH zance ne yanzu mutuwar su hadiman can shikenan ta tafi a banza baza'ai wani bincike a gano ba? .??
? ?? Kallo na kusan sakan biyar Daneen Ammarah taima Iffah da har tama Wauka tai laifi, amma sai taji taja numfashi da maida kanta kan littafin hanunta.  Mutuwarsu bazai tafi a banza ba saboda dalili mai ?arfi Ibnati. Dan duk wanda ya kashesu yana gudun tonuwar asirinsa ne akan cutar da ke da akai yunkurin yi. A yanzu haka Shahanshan ya saka kwamitin bincike, muna fatan kuma ta wannan hanyar za'a gano koma wanene ya saka ki a halin da kika tsinci kanki. Kuma dama kema ana jiran ?ara samun lafiyarki ne aji ko akwai wani abu da kika sani, ko kuma bayan su ukun can da Wayar da aka samu nasarar ceto ranta ko akwai wasu..
? ???? Da sauri Iffah ta dubeta.  Mamy akwai wadda bata mutu ba dama? .??
??  Eh akwai amintacciyar hadimar Umm-Jasrah (haka take kiran Malikat Bushirat) mai suna Diwa. Ita an kaita asibiti kafin gubar da suka sha ta karasa katsa ?an hanjinta. Alhmdllh kuma an dace dan yanzu haka tana kan shan magani, tana kuma zagaye da tsatstsauran tsaro ? ?
? ? ?  ALLAH ya ?ara bata lafiya, sai dai kuma banajin tanada hannu a cikin al'amarin Mamy, dan da ganinta mutiniyar kirki ce .? ?
? ? ??  Gane mutanen kirki ba'a ido yake ba Ibnati musamman a wannan masarautar da kowa kansa kawai ya sani, a mafi yawan lokuta ma ba'a gane ma?iyi da halayya. Akwai rikitattun abubuwa dake a matu?ar cuWe a wannan Daular da gani da ido bazai wadaci mai kallo ba, dan haka nakeso ki nutsu kisa hankalinki waje Waya kafin ki koma sashenki ki koyi abubuwa da yawa na salon mulki da tsarin matsayinki na Zawjata-almilki. Saboda kunada matu?ar tasiri da girma a tsarin ?arfin iko na masarauta da kaikawon talakawan ?asan ruman. Fatana kuma kece Malikat a cikin Zawjata-almilki insha ALLAHU .? ?
? ? ? Sam Iffah bata fahimci komai ba ga kalaman Daneen Ammarah, amma sai bata sake cewa komai ba dan a ganinta tana bu?atar samun lokacin yin nazari na musamman a kansu kafin ta fahimcesu dallah-dallah.......?

? ? ? ? &&...? &...? &&....

? ? Ana idar da sallar asuba drivern daya kawo su Kaka jiya dan hanashi komawa yay saboda dare ya Wauka Iyyani da Ummu suka wuce. Kaka da Abu Zainab kuma sukai shirin fara neman inda zasu samo Babiy da Hanash.
? ?? Dai-dai suna shiga mota kaka ya dubi Abu Zainab da Wan murmushin ?arfin hali a fuskarsa,  To Zakariyya kai ne Wan gari, yanzu ta ina zamu fara kenan? .
?? Numfashi Abu Zainab ya furzar, tare da yin Wan jimm alamar tunani,  E to Baba banace ba dai, dan al'amari nada wuya, saboda bamu da tabbacin waWan nan jami'ai daga wane station suke. Amma ni yanzu a nawa shawaran ina ganin kamar mu nema gidan shi marigayi Win, tunda matarsa ita ta kawo jami'an tasan daga ina suke .
? ??  Hakane, wannan ma shawara ce mai kyau, sai dai inda gizo ke sa?ar kai koka san ina gidan Dawood Win yake? Dan ni dai rabona da shi ma kusan shekara biyar kenan tun suna tare da Muhammad Zayyan .
? ? ? ??  Ito baba banace ba, dan kusan nima hakan dai take, amma bayan tashinsa daga anguwarmu nasan inda ya koma, sai dai bani da tabbacin ko har yanzu acan Win yake zaune tunda ba wani huWWa muke ba gaskiya, dama dalilin Abu Hanash Winne ake gaisawa sai kuma idan wani zama na anguwa ya haWa kafin ya tashi kenan. Amma yanzu dai bara mu tafi can Win kawai rana ma nayi .

? ? ?? Cikin ?an?anin lokaci suka iso anguwar, kasancewar ma ta cika ba kamar da ba da kyar suka iya samo gidan. Duk da jikinsu ya Wanyi sanyi ganin ?ofar gidan babu alamar anyi wani abu daya shafi mutuwa Abu Zainab yay sallama har sau uku. Ana huWun wani mutum ya fito. Cikin binsu da kallon rashin sani ya basu hannu suka gaisa. Abu Zainab da shima dai jikinsa yay sanyi ya ce,  Kayi ha?uri nasan baka sammu ba. Muma dai munzo nan Winne neman wani bawan ALLAH daya zauna anan shekara kusan huWu haka baya. Sunansa Dawood, amma ana masa alkunya da Abu Moosa. Matarsa Waya bashi kuma da yaro ko Waya .
? ??  ALLAH sarki, gaskiya ban sanshi ba, dan nima dai ban wuce shekara biyu da tarewa anan Win ba. Na kuma sayi gidanne a hanun wani mutum Ibrahim Askari .
? ? Abu Zainab zai sake magana Kaka ya girgiza masa kai alamar kar yace komai. Godiya sukai masa da sallama suka wuce.

? ? ?  Baba ban san miyasa ka dakatar dani ba. Dama zan tambayesa ne ko zai faWa mana inda zamu samu shi Ibrahim Askari Winne .
? ? Numfashi Kaka yaja ya fesar,  Dalilin da yasa na dakatar da kai kenan. Kasan shi al'amari irin wannan yana bu?atar kasan dawa zakai maganar abu na gaba. Inaji a jikina waWanda suka haddasa tushen wannan matsalar dole suma zasu kasance suna bin bayanmu domin toshe duk wata hanyar da zamu iya bi. Dalili kuwa shine ina kallon lauje ne cikin naWi akan al'amarin .
? ? ? ?  Eh gaskiya hakane kuma Baba. To amma in har hakane mizai hana mu nema lauya, sai nake ganin cikin sau?i shi zai iya binciko mana inda suke ma, kuma koma minene sai yazo cikin sau?i tunda ana magana ne akan abinda ya shafi shari'a ko kuwa? .
? ? ?  Itama wannan babbar shawara ce a mahangar hankali Zakariyya, sai dai shi lauyan ne matsala musanma irin mu wanda muke bukata. Mai gaskiya da amana .
? ?  In dai dan wannan ne babu damuwa insha ALLAHU, akwai yayan matata data rasu, kwararren lauyane kuma mai nagarta da nasan zakaso aikinsa kuma zai taimakemu kasancewarsa babba. A yanzu dai nasan bazamu samesa a gidansa ba. Bara kawai muje ofishinsa ...

? ? ?? &&.....? &...? &&.....

? ? Kamar yanda Iffan ta nema alfarma a wajen Daneen Ammarah akan Wakko mata akwatinta da aka kawo ta gidan dashi ya iso gareta. Taji matu?ar sanyi a ranta da farin ciki. Hadimar data kawo na fita ta buWe akwatin ta shiga dubawa. Alhamdullah komai yana nan yanda yake, hatta takardar da malam Fawzan ya bata Winnan itama tana a inda ta Soye ta. Tana idar da sallar azhar littafin data sako a kayan nata kawai ta Wauka da biro ta fara rubutu. Anutse take rubuta komai daya faru daki-daki tun daga barowarta gida har zuwa shigowarta cikin masarautar, abinda ya faru da ita dama wanda ke kan faruwa bayan warkewarta. Da zarar taji motsi koda ma Daneen Ammarah ne sai ta boye, a haka ta kwashe kaf yinin har zuwa dare tana abu Waya. Da daddare bayan kammala shirin barci maimakon kwanciya zaman karatun Alkur'ani tayi, koda Daneen Ammarah ta shigo ta sameta a hakan bata katseta ba. Tasa Hadimar dake biye da ita ajiye mata madarar da suka shigo da ita. Daga haka ta fice taja mata ?ofar da nufin ta dawo zuwa anjima, dan yanzu tana son zuwa ta duba Malikat Haseena ne da yai batajin daWi.
? ? ? Iffah na ganin ta fice ta sauke ajiyar zuciya, addu'a tai ta rufe Alkur'anin ta mike, kofar taje ta sanyama key bayan ta le?a babu kowa a corridor Win. Ta Wan jingina da ?ofar tana mai ambaton  Alhamdullah da sakin Soyayyen murmushi. Cikin sassarfa tabar jikin ?ofar zuwa ga akwatinta, ta buWe tare da Wakko wayar Arfa da takardar da Malam Fawzan ya bata. Number da aka rubuta ta kwashe a wayar, ta haye tsakkiyar gadon ta kwanta tare da jan lallausan bargon ta shige ciki har kanta sannan tai dailing number. Gaba Waya a kage take da zumuWin a Wauka. Dan haka take bin sautin shigar kiran da zuciyarta. Sai dai harta yanke ba'a Waga Win ba. Kira ta sake yi, nan ma dai shiru, bata gajiya ba ta cigaba da kira har fin sau goma kafin a Waga a karo kusan na goma sha biyar. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tamkar wadda aka tsamo daga cikin ?an?ara. Sai kuma tai saurin faWin,  Assalamu alaikum .
? ? ?  Wa'ake nema? .
?? Aka faWa daga can maimakon amsa sallamar tata. Da lafiya lafiya ne sai tayi mitar ?in amsa sallamar, amma sai tai saurin faWin,  Sir Ajmaal .
? ? ? ??  Wa'ake nema? .
? ? ? Aka sake maimaita mata tambayar.
?? Zuciyarta ta Wan fara zabura amma sai ta danne ta sake maimaitawa itama.
? ? ?  Sir Ajmaal .
 Wa'ake nema? .
Still aka sake faWa kamar dai ba'ama jita ba.?
? ? ? Wayar ta janye a kunenta ta tashi zaune ta Wauka takardar, number dai dake a jikice dai-dai batai mistake ba. Sake maida wayar tai kunne aranta tana faWin (bara naga ?arshen ku dai) ta sake amsawa da  Sir Ajmaal .
? ?  Kin saSa lamba .
Aka bata amsa da yanke wayar lokaci guda batare da anjira cewar ta ba......

? ? ? ??
? ? ? ? &&.....? &...? &&.....

? Kasancewar Abu Zainab suruki ga barrister cikin sau?i suka samu ganinsa ta hanyar kiran waya. Har office yasa masinjansa daya fita yay musu iso ya shiga da su. Ganin lafiyayyen office Win nasa dama hukumar tasu ya sake tabbatar ma da Kaka babbane gaskiya. Sun gaisa cikin nuna sanayya shi da Abu Zainab. Ya kuma gaida Kaka da girmamawa kasancewar tsoho dama zai iya haifarsa. Basu saurari lemo da aka kawo musu ba Abu Zainab ya shiga masa bayani dalla-dalla. Sai da ya gama tsaf Barrister Abdallah dake rubuta wa ya ajiye biron yana jinjina kansa. Kaka ya fuskanta cikin son ?arin bayani....
? ? ??  Baba kaima kasan shi Dawood Win kenan? .
?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login