Showing 75001 words to 78000 words out of 120369 words

Chapter 26 - DAUDAR GORA COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Nov 2025

257

ta faWa. Murmushin ya sake sakar mata. Sai kuma ya girgiza kansa da kwanto da kanta bisa kafaWarsa.  Bamu rasa su ba, ba kuma mu fidda rai da samunsu ba .
? ? ? A hankali hawayen da suka kasa fita a idonta tsahon kwanaki suka fara sauka a kafaWarsa.......

? ? ??
? ? ?? &&.... &&.... &&.....

? ? ?? Mummunan mafarkin da ALLAH ya bata ikon cin galaba a cikinsa ta farka a zabure, cikin amincin UBANGIJI harshenta ya ambato addu'ar tashi daga barci kamar yanda musulinci ya Woramu akai. Ajiyar zuciya ta sauke da saka gefen bargon data lulluSa ta yarce gumin da yay ma goshinta jalab, sai kuma ta sake lumshe idanu jin sautin kiran salla da take ?yautata zaton a masallacin cikin masarautar ne. Hasken Wakin ta kai hannu ta ?ara, ta bi ko'ina na cikinsa da kallo tamkar zataga munanan halittun data gani a cikinsa a mafarki. Rashin ganin komai a zahiri ya bata ?arin gwiwar sakkowa a gadon ta nufi toilet. Bata damu da rashin ganin Tajwar Eshaan a Wakin ba duk da taji Malikat Haseenat ta ambata nan Win matsayin Wakin barcinsa na daren jiya. ?arancin shekarunta da wautarta yasa bata Wauki tsallakewar komai ba. Abinda kawai zuciyarta ke mata kaikawo a rai shine ta tsallake daren na jiya dai koma yaya ne, ta tsallake tarihin mutuwa a daren kwana turakar dodon matsafa. Dalilin tsallakewar, ko barinta da yay da ranta ne bata sani ba, ba kuma tasan tayaya ya kamata ta sani ba. Abinda kawai take da damar yi shine buWe kunne da idanuwa taga mizai biyo baya ga kowa da kowa. A yanzu Win ma tayi zaton ganin jinin kamar jiya dai, sai dai babu alamar hakan har ta kammala uzirinta tayo alwala ta fito. Tana idar da salla wani irin nannauyan barci ya dinga fisgar idanunta. Dakewa tai cikin dauriya tai zaman yin azkar, da ?yar ta iya kammalawa barci yay mata baban fisga a wajen dole takai kwance tana ambaton sunan ALLAH. A hankali ta fara sauke numfashi alamar barcin nata mai nauyi ne....

? ? ? ?? &&....?? &&.....

? ? ?? A cikin masarauta tako ina an gama baza kunnuwan jin fito da gawar Zawjata-almilk. Hatta da Malikat Haseena bata tare da nutsuwarta gaba Waya. Tun ana ?irga sakanni a bayan sallar asubahi har aka koma mintuna, mintuna suka koma awanni babu wani labari. A take aka koma ?ar ?us-?us tun daga kan hadimai har manyan masu faWa ajin masarautar.
? ? Yayinda suma Hadiman sashen Shahan-shan suke zaune jigum-jigum na jiran tsumayen abinda kowa keda tabbacin zai kasance. bakunansu cike yake taf da abubuwan faWa akan abinda suka wayi gari da shi mai matu?ar rikitarwa da zai maimaita faruwa bayan ya faru ga duk wata Zawjata-almilk data kwana ta tashi a wannan sashen. Duk Wunbin yawan abin cewar iyakarsa zukatansu dan ko'a tsakaninsu bai faWuwa balle gulmantawa a waje saboda tako ina camara ce zagaye da su.....

? ? ?? *_&MALIKAT BUSHIRAT&_*

? ? Ba'a safiyar yau ba, ita tun ma a daren jiya tai hanun riga da nutsuwa. Gaba Waya a daren ko sau Waya bata iya ta rintsa ba. A maimakon barci ma idanunta akan sashen Shahan-shan da kowa ke iya gani daga nasa sashen a cikin masarautar suka kwashe mafi yawan awannin daren na jiya. Tayi yun?urin kiransa amma wayar a kashe, hakanne ya sake Waga mata hankali da jin zafin wann??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????an hukunci na Malikat Haseenat a karo na farko. A ganinta ganganci ne mi?a nagartacciyar yariya irin Iffah hannun gudan jinin nata bayan Mamma tasan minene makomar yin hakan ga rayuwar yarinyar. Duk jarumtarta a duk sanda ta tuna zuwa safiya gawar yarinyar ce zata fito takanji ?walla sun cika idonta. Amma takan danne ta hanasu fitowa har garin ALLAH ya kammala wayewa...
? ?? Tun idar da sallar asubahi bata iya ta motsa ba, ?irjinta ne ke matu?ar bugawa da jiran tsammanin mummunan labari.....

? ? ?
? ?? *_&DANEEN AMMARAH&_*

? ? ?? A Sangaren Daneen Ammarah itama a kwatankwacin irin halin da Malikat Bushirat ta kwana ta tashi take ciki. Dan ita kwana tayi ma tana hawaye. Har ?ar?ashin zuciya takejin matsanancin ?aunar Iffah. Tana jin yarinyar a matsayin cikon wani gurbi data rasa irin na kowace uwa mai shekarunta. Sai gashi Mamma da ta fara bata tsoro a daren jiya ta rusashi da maye gurbinsa da fargaba mai matu?ar tsanani da razani. Wani mutum saSanin jininta bai taSa mamaye zuciyarta da ?auna mai ?arfin haka ba kamar yanda yarinyar tayi mata. Sosai take jinta a rai da jinin jikinta. Itama dai tun daga sallar asuba bata sake iya kataSus ba tai zaman jiran tsammani irin na duk wanda ya kwana ya tashi a cikin masarautar.......

?? &&...? &&.... &&....

? ?? Harya gota Wakin cikin shiga ta blue Win jallabiya mai tsananin ?yau da ?yalli mai Waukar ido da nuna taushinta a zahiri dake nuna daga masallaci yake ya tsaya cak. Kamar bazai motsa ba sai kuma ya juya kansa a sannu yana kallon Wakin.?? Kallon kusan minti Waya da wasu sakanni ya motsa gaSSansa cikin takunsa na izza da kame kai ya tura kai ciki. Da farko rashin lura da ita ya sakashi yin tsamm, sai dai fuskarsa ta nuna dakewa kamar koyaushe. Ya Waga ?afa da niyyar juyawa ya fita idanunsa suka sauka a kanta. Yay tsai yana kallonta na tsahon mintuna kusan huWu tamkar mai rarrabe ita Win ce ko wata? Dan a kallo Waya zaka fahimci salla ta idar a wajen barci yay awon gaba da ita. Ya Wan furzar da numfashi da kauda kansa gefe ya sake bin Wakin da kallo kai kace ba?onsa ne har ya sake direwa akan fuskar Iffah dake ta barcinta numfashinta na fita a hankali.........
'?


? ? ?

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*


_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*?AN ?ASAR NIGER
+227 96 09 67 63

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu=?-?=?O?
5??5?2?5?)?5?"?5?'?5? ?=???


('5?o?5?l?5؀݊5?l?5?}? 5?r?5?z?5?}?5?l?('
(5?n?5؎?5ؐ?5؎? 5ؐ?5؆? 5ؘ?5؍?5؆?5ؙ?5؆?)



5???5???5???5??5??? 5???5???5???5???5???5??? 5???5???>??

*_33_*


.........?arfe takwas da rabi dai-dai agogon ?asar Waya daga cikin amintattun Hadiman dake gyara Wakunan barcin na Tajwar ta iso cikin faWuwar gaba hanunta Wauke da akwati da aka kawo yanzun nan daga sashen Malikat Haseenat matsayin kayan da Iffah zatai amfani da shi. Zuciyarta har wani zallo take na fargabar abinda take da tabbacin tozali da shi kamar yanda sukayi a baya ga sauran Zawjata-almilk da suka shuWe. Ta tura ?ofar cikin sanWa tana mai ambaton sallama da rawar harshe badan tana tunanin samun amsa ba. Ganin Iffah kwance a saman gado, lulluSe da lallausan bargo baisa taji ?warin gwiwa ba. Tai yun?urin ajiye akwatin hanunta, cak ta tsaya dukkanin idanunta na fitowa waje dan firgici ko sumar tsaye sakamakon juyi da Iffah tai alamar gyara kwanciya. Akwatin ta saki ?asa ta shiga jan jikinta dake Sari baya-baya harta dangane da ?ofa gab.....
? ?? Iffah dake ?o?arin gyara bargo idanunta rufe ta buWesu da sauri saboda jin ?arar bigewar hadimar. Da mamakin jinta kamar a gado ya sata shashshafa hannunta. (Tabbas gadonne) ta ayyana a zuciyarta tana sake buWe idanunta da ?yau tana mai yun?urin tashi zaune. Tuni hadimar nan ta sake firgicewa, da lalube ta murWa handle Win ?ofar ta fita a guje.? Kallon ?ofar Iffah tayi, sai dai hadimar ta gama ficewa bayanta kawai ta Wan gani kaWan da wulgawar mayafinta. da sauri ta yaye bargon da bata san ya akai yazo jikinta ba. Ta dire ?asa mamakin duniya na cigaba da dabaibaye ta.  Wacece wadda ta fita? Mi tazo yi? Wai ta yaya ma na dawo saman gadon nan bayan a ?asa na kwanta? . Ta shiga jerama kanta tambayoyin da bata san inda zata samu amsarsu ba. Sai kuma ta Wan kamo rigar jikinta ta kai hancinta.  Ya ALLAH, da gaske fa wannan mayataccen ?amshin a jikina ne? . Ta sake faWa a fili tana sake shinshinar rigar......

? ? ?? A Sangaren jama'ar masarauta dake a zaman jigum-jigum kam fitar hadimar nan ya isar da sa?on Zawjata-almilk na raye. Da farko duk wanda zancen yaje kunensa Waukewar numfashi na wucin gadi ne ke riskarsa, sai kuma rashin gaskatawa a zahiri ya biyo baya. Hatta da Malikat Bushirat da Daneen Ammarah yanayi da ruWanin jin hakan bai tsallakesu ba suma. A kusan tare suka Wauka wayoyinsu domin neman Iffah ko zasu samu jin gaskiyar zance. Cikin Sa'a kuwa ta Daneen Ammarah ta fara shiga....

? ? ? Iffah na zaune har yanzu cikin Waurewar kai akan wanda ya maidata saman gado da wul?awar fitar wadda bata sani ba wayarta ta katseta. Numfashi taja ta fesar da Wan ?arfi tana kai hannu akan wayar. *_Mamy_* ta gani rubuce Saro-Saro. Ganin zata katse tai ?arfin halin Wagawa ta kai kunne tana faWin,  Assalamu alaikum. Amincin UBANGIJI da rahamar sa su yalwatu a gareki Mamy barka da safiya .
? ? ? A matu?ar razani da motsuwar zuciya Daneen Ammarah taja numfashin dake neman ?wace mata.  Ibnati! . Ta ambata cikin son tabbatarwa.
? ??  Na'am Mamy .
Iffah ta amsa kanta tsaye babu alamar irin fargabar dake harshen Daneen Ammarah Win a tattare da ita. Dan ita wanda ya Wauketa daga ?asa ya maida saman gado da fitar macen data ganine kawai damuwarta a yanzu. Daneen Ammarah da taji al'amarin tamkar a mafarki ta lumshe ido hawaye na silalo mata saman ?yakykywar fuskarta a hankali. ?asa takai dur?ushe tana mai godema UBANGIJI ta hayar kai goshinta ?asa tai sujjadar shukur...

? ? ? ? Iffah da mamaki ta cigaba da ambaton  Hallo Mamy! Mamy kina jina kuwa? . Shiru babu alamar za'a amsa. Yanke wayar tai da yun?urin sake kira a zatonta matsalar network ce sai ga kiran Malikat Bushirat ya shigo shima. ?an jimm tai tana kallon wayar, sai kuma ta Waga takai kunne da sallama nan ma. Malikat Bushirat da idanunta ke cikowa da ?walla sakamakon jin muryar Iffah tar-tar a kunenta ta kai zaune tana ambaton sunan ALLAH. Iffah na son tambaya tana jin nauyi, sai kawai tai shiru tana sauraren kalmomin godiya ga ALLAH da Malikat Bushirat Win ke ambata daga can.
? ? ? (Ya rabbi! Wai mike faruwa ne haka?) Ta ayyana a zuciyarta da al'ajabi. Knocking ?ofa da akai ta hanyar danna alerm a dai-dai lokacin ya katse tunanin nata. Ta kai dubanta ga kofar babu alamar zata tanka har aka sake danna alerm Win sannan tai ?arfin halin amsawa da bada umarnin shigowa tana gyara mayafin data yanama kanta.. Hadimar Wazun ce dai ta shigo Wauke da ?aramin tray mai Wauke da butar shayi. Kanta a ?asa ta ajiye a inda ya dace tana mai zubewa ?asa durkushe.  Amincin ALLAH da tsahon rai mai albarka su kasance tare da Zawjata-almilk Barka da safiya .
? ? ? Iffah da ke kallonta ta amsa cikin motsa lips Winta kaWan. Sabo da hakan yasa hadimar bata damu da rashin amsawar Iffah ba. Cikin sake rissinar da kai tace,  Ya Zawjata-almilk yanzu lokacin wankanki ne, bayan nan karin kummalo na jiranki tare da Shugabana .
? ? ? ? ?? Yanzu Win ma kamar Iffah bazata amsa ba sai kuma ta jinjina kanta.  Kije abinki zan fito .
??  Umarninki shine abin jirana. Amma a gafarceni zan haWa ruwan .
? ? ?  Kije abinki zan yi komai da kaina .
?? Babu yanda hafimar ta iya dole ta mi?e domin bin umarni shine kawai huruminsu. Da kallo iffah ta bita abubuwa masu yawan gaske na son fara mata kutse a ?wa?walwa da zuciya. ?warin gwiwar da take bama kanta akan turesu ya sata mi?ewa ta nufin toilet tana mai ambaton addu'ai a bakinta saboda tuna abinda taci karo da shi a daren jiya a toilet Win.
? ?? Ko'ina tsaf, kuma cikin ?amshi irin na daren jiya. Sai da ta ?arema komai kallo fiye da jiya kafin ta Wage kafaWa irin na koma miye ta shirya masa. Tsabagen rigima da wuce wuri ko tsageranci za'ace ta haWa ruwanta mai Wumi da zuba duk wani nau'in turaren wanka da aka jera domin Shahan-shan ta shige cikin kwamin wankan tai luf. Sai da taji ko'ina nata ya mi?e yanda take bu?ata sannan ta fita a ruwan domin fara wanka...

? ? ? Tsaf ta kammala shirinta cikin doguwar rigar material sky blue da akaima Winkin daya fidda ainahin halittarta tamkar ?ar tsanar roba. Rigar ta zauna mata Was, siririn mayafin da aka haWa rigar da shi ta naWa tamkar yanda larabawa keyi, ta Wakko after dress shara-shara mai kamar al?yabba ta Wora a sama kalar blue sosai. Ta Wanji babu daWi na rashin turarurrukanta tare da ita, dan ko waWan nan kayan ganinsu kawai tai, cikin Wan taSe baki da Wage kafaWa a zahiri ta dinga kwasar turarrukan da taci karo da su a Wakin cikin wani ?ya?ykyawan glass dake kusa da mirror ta dinga zazzagama jikinta har sai da ta gamsu ?arfin kamshin zai kai duk inda mai rai ke numfashi a sashen sannan ta ha?ura. Idanunta ?yam a mirrorn ta saki ?ayataccen murmushi da kanne ido Waya a fili ta furta  Irin wannan haWuwa haka autar Ummu . Tai salute Win kanta....

? ? ?? ? Sautin ?arar takun takalman ?afarta da mayataccen ?amshin tiraren da shi kaWai aka sani da shi ya sashi tsayawa cak daga ?o?arin kai hannu a abincin da aka gama haWawa gabansa. Fararen idanunsa tar-tar tamkar madara ya Wago ya sauke a kanta. Hakama hadiman dake a tsaye ta gefe da gefensa kawunansu a ?asa cikin yanayin mutuwar tsaye data rikesu suka zube ?asa kan gwiyawunsu illahirin jikkunansu na ?yarma akan dalilai guda biyu. Na farko ganin tabbatar da wadda suka gama fidda rai da jiran tsammanin ganin an shigo fidda gawarta tamkar Zawjata-almilk na baya dai na raye Win kamar yanda Hadimar ta gano. Na biyu ?amshin turaren jikinta da ga mutum Waya tak ake iya jinsa a duk faWin ?asar ruman ma bawai a daular ruman ba...
? ?? Tamkar Iffah bata fahimci halin da suke a ciki ba ta ?araso cikin katafaren falon batare data dubi ko Waya a cikinsu ba balle mai gayya mai aikin. Cikin sauri Waya daga cikin hadiman ya mi?e ya gyara mata kujera, zaune ta kai tana mai dubansa? a karo na farko. Tuni shi kuma ya maida kansa ga abinda yake yi tamkar bai san da zuwan tan ba. Ta taSe baki da juya idanunta ta maida ga hadimar dake ?o?arin fara haWa mata abincin. Nunin abinda take bu?ata tai mata da Wan yatsa. Hadimar na kammalawa ta koma cikin ?an uwanta ta tsaya itama kanta a rirrine.
? ? ?? Gaba Waya jinta take a takure, kwarjininsa ya cika ko'ina a falon. Cikin dakewa da kaucewa gizago sa ta Wan Wago ta Wan saci kallonsa da nufin gaishesa idanunta suka shige cikin nasa da ya Wago da nufin kallon nata...
? ??  Who are you?
?? Ya fara faWa cikin basarwa yana kaWa idanusa da har yanzu ke cikin nata tamkar bashi yay maganar ba. Badan a idanunta tausasan lips Winsa suka motsa wajen ambaton wacece itan ba zata iya gaddamar hakan. Kaifin idanunsa sun neman sage duk wani ?warin gwiwarta. ?o?arin fara sassauta nata idanun tai yun?urin yi cikin ?an?ance su sannu a hankali. Shima sai ya kankance nasa kamar yanda takeyi, fuskarsa na sake tsukewa babu alamar sassauci tattare da ita. Nata ta fisga da ?arfi ta lumshe su, sai kuma ta buWe a kansa tana mai sake tsuke tata fuskar itama, bazata iya jure salon nasa ba dake neman ?one ?udirinta, dan haka ta kauda kanta gefe babu alamar zata bashi amsar da yay yun?urin ji daga garetan..
? ? ?  Barka da safiya .
?? Ta faWa a ?o?arinta na basar da tambayarsa ta farko.
? ?? Bai motsa ba, babu alamar kuma zai amsa ta. Hakan sai ya sake sukar zuciyarta harta Wan saci kallonsa, da sauri ta kauda idanunta, dan da gaske fuskarsa ruguza mata lissafi take, da gasken gaske shi ?ya?y?yawa ne, irin ?yawun dako a cikin ?asar tasu ake yabawa da shi, koda yake batai mamakin hakan ba, dan Malikat Bushirat ba'a magana, duk da girma ya fara zuwa gareta tsantsar ?yawunta a bayyane yake. Hakama Malikat Haseena dake matsayin kakarsa data haifi babansa tunda ita dai bataga baban nasaba ko'a hoto har yanzun, amma zubin Malikat Haseena dana Daneen Ammarah ya tabbatar mata shima Win dai zai kasance ?ya?y?ywan ne......
? ? ? ?  What is your goal in life? .
? Kalmomi guda shida suka katse mata tunani a bazata. Ta kallesa tana ?o?arin danne mamakinta kan waWan nan tambayoyi da yake faman yanko mata kai tsaye. Ganin yanda ya zuba mata ?asaitattun idanunsa masu firgita mara gaskiya ta janye nata tana yamutse fuska. (Damarki ce wannan) wata zuciya ta ayyana mata. Cike da gamsuwa ta sake kauda kai gefe dan har yanzu tanajin kaifin idanunsa a kanta.  Ni ban kasance kowa ba sai talakar dake a ?ar?ashin mulkinka ranka ya daWe. Abinda nake son cimmawa kuwa a rayuwata irin abinda shugaba ke fatan cimmawa ga talakawan ?asarsa ta hanyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login