Showing 24001 words to 27000 words out of 120369 words

Chapter 9 - DAUDAR GORA COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Nov 2025

227

da dattijan nan guda biyu da sai gobe zasu koma tare da kaka. Kaka kuwa na gefe zaune abinsa tamkar baima san mike faruwa ba a gidan. Yayinda Iffah ke can ?uryar Wakin Ummu kwance cikin zazzaSi data yini da shi.....
? ? ?? Washe gari su kaka suka wuce batare daya sake cewa uffan ga su Babiy ba akan komai. Yadai gargaWi Babiy akan karya kuskura yace zai yi wani yun?uri. Ya kuma sakasu killace dukkan kayan da aka kawo daga masarauta.....

? ? ?? &&&_______&

? ? Tamkar da gayya cikin kan?anin lokaci gari ya Wauka Shahan-shan zai yi aure, alamu kuma sun nuna ana shiryama auren da shiri na musamman duk da amaryar bata kasance ?ar kowa ba. Hasalima ahalinta nada tabon Shahan-shan a dalilin salwantar ?a?ansu biyu kafin ita. Dukkanin waWan nan ?ananun magana na faruwane a bakunan mutane da ?aramar murya, yayinda a kafafen ?aWa labarai da fejikan yaWa zumunta babu mai iya Waga murya yayin faWa sai fatan alkairi kawai. Mutane sun sake samun tabbacin wannan aure na musammne daya sha banban dana baya sakamakon fara shelarsa a kafafen yaWa labarai domin gayyatar manya-manyan ?asar kamar kowane Tajwar da jama'ar majalissarsa da talakawan garinsa. Da yanda ake wasu ?an gyare-gyare a daular ruman wai duk na tarbar zuwan ranar Waurin aure ne. Humm abin faWa taf bakunan mutane sai dai babu damar faWar. Idan kuma suke ganin zasu sami wani ?arin bayani an toshesa dan babu mai ikon shiga gidan Babiy a halin yanzu kasancewar zagaye yake da dakaru tako ina, acewarsu suna bama *_Zawjata-almilki_* tsaro ne. A cikin gidan kuma babu mai fita hatta da Hanash dake zuwa babbar makaranta...
? ? ? A haka kwanakin biki da suka rage suka cigaba da shurawa batare da wadda ake i?irarin zama amaryar ta sake tada kai ta dubi wani abu daya shafi auren nata ba koda da kallo. Ta dake matu?a tamkar ba itaba, hatta da ciwon dake cinta a tsaitsaye taki bada damar da su Ummu zasu fahimta. Ta ?e?ashe idanunta ?am ta hana hawaye zuba daga cikinsu. Ta tattare gaba Waya hankalinta ta maida ga rubuce-rubuce da babu wanda ya fahimci na minene a gidan, dan bata bari kowa ya duba mata shi. Sai dai ga duk mai hankali a duba Waya da zai mata zai fahimci tana cikin matsananciyar damuwa, mai busar da zuciyar mai ita da zai iya aikata komai da zai iya zama komai akan komai..
? ? ? Kamar ko yaushe yau ma bayan ta kammala ayyukan gidan da take taimakawa Ummu da su Waki ta koma tana kukan zuci daya zame mata abokin rayuwa. A idaniyarta kam babu alamar Wigon hawaye, sai dai raWaWin wanda ke kwaranya a zuciya ya maida launin idanunta sirkin ja har kana iya ganin jijiyoyi a cikinsa. Du?ufe take akan littafinta tanata rubutu da sakin ajiyar zuciya akai-akai. Ummu data shigo Wakin takai zaune a kusa da ita tana mai tsurawa rubutun idanu na wasu sakanni.
? ? ??  Ibnati! .
? ? Karan farko Iffah ta Wago ta kalla Ummu duk da tun shigowarta ta jita sarai. Wani irin miskilin murmushi ta saki tare da maida kanta a hankali ta du?ar..
? ??  Kina ganin laifinmu ko? .
? Cak ta tsaya da rubutun data cigaba, sai kuma ta saki murmushi. Tsahon sakkani uku kafin ta Wago ta dubi Ummu. Ta Wan girgiza kanta da ajiye biron hanunta.  Ummuna idan har zanyi zargin wani akan wannan al'amarin to kaina ya dace na zarga. Ku Win nagartattun iyayene abin alfaharin kowane irin Wa. Ni ya dace nazo muku da wannan maganar, domin nice na saka zukatanku a damuwa da Wunbin fargaba. Na tabbata a kowane sakan, a kowane minti, a kowane awa, a kowane kwana na waWan nan kwanakin kunayinsa ne cike da fargabar shuWewarsu da gabatowar su. Kuyi ha?uri ku ?ara ha?uri ku gafarceni. Koda baku faWamin ba, baku faWama duniya ba nasan irin raWaWin da kukeji a zukatanku domin nima makamancinsa nakeji. Sai dai ina muku albishir Ummuna, koda zakuyi kuka a wannan gaSar bazakuyi irin na baya ba. Na muku al?awarin kukan ku zai kasance tare da dariyarkune a lokaci guda. Dan ruhina sai ya amso muku diyyar su Nina Arfa kafin yabar gangar jikina. A duk randa sa?on mutuwata zai riskeku insha ALLAHU zai riskekune tare da na mutuwar azzalumai. Dan haka ina ro?onku kar kuyi ba?in ciki a wannan karon, zaku sadaukar da ruhin da zaije muku ya?in neman ?ancin kai ne ku da al'ummar ?asar ruman.....
? ? ? Kai Ummu ta shiga jujjuyawa hawaye na kwaranya a idanunta,  Ibnat...
? ?  Na ro?eki kar kice komai Ummuna, albarkarki itace mafi ?ololuwar bu?ata ga ruhin daya daWe da zama cikin tahin gawa. ?addarata rubutacciya ce tun daga al?alamin da idan yay rubutu babu wani duster dake iya gogesa ...........
'

? ??
ALLAH sarki Iffah, ALLAH ya baki damar ya?i irin wanda ya dace da fatanki na alkairi=?O?

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*


_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*?AN ?ASAR NIGER
+227 90165991

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu=?-?=?O?

5??5?2?5?)?5?"?5?'?5? ?=???


('5?o?5?l?5؀݊5?l?5?}? 5?r?5?z?5?}?5?l?('
(5?n?5؎?5ؐ?5؎? 5ؐ?5؆? 5ؘ?5؍?5؆?5ؙ?5؆?)



5???5???5???5??5??? 5???5???5???5???5???5??? 5???5???>??

*_12_*


.........Kalaman Iffah sun zama mafi ?ololuwar zama famin gyambo a zukatan Ummu da Babiy harma da Hanash. Sun zanu da zanen da zuciya ta killace koda tunasu zai zama mai raWaWi a cikinta. Sun karSa domin karSar ta zama tilas a garesu saboda rashin murya da ?arfin iko da suka rasa a hannayensu. Sun cigaba da kuka saboda kukan shine kawai mafita a garesu. A haka kwanaki suka cigaba da tafiya da raunin zukatansu har zuwan ranar juma'ar da masu ?arfin iko suka tsaida matsayin ranar Waurin auren ?arsu. Bayyana ko misalta kasancewar wannan dare da wayewarsa ma Sata lokacine game da halin da ahalin malam Zayyan suka tsinci kawunansu. Babu wani alamomin biki daga Sangarensu sai ma zaman makoki. Dan bayan Iyyani da Kaka da wasu dattijai da basu gaza biyar ba a cikin zuri'arsu babu wanda ya halacci wannan makahon aure hatta da ma?waftansu. Bisa tilastawar Kaka Babiy da Hanash sukai shirin halartar massallaci yin sallar juma'a da riskar abinda zuciyoyi ke tsananin ?una a kansa. Sun tafi sun bar Ummu da Iyyani da tazo itama a yanayi mai ban tausayi. Amarya Iffah kam idanunta ma babu wanda ya gani a wannan safiya abinci ma Iyyani ta bita da shi har Waki....

? ? ? ? ?? *_TAFARU TA ?ARE_*

? ?? Bayan gushewar wasu awanni, masu tafiya da ?arfin bugun zuciya busa irin ta sarakai da tashin tambura ya karaWe cikin birnin Daular Ruman dake cike da manyan ba?i tako ina. Dan kuwa sarakuna goma cif na ?asar Ruman duk sun halarta duk da suma akwai raWaWin rasa ?a?ayensu a zukatansu har yanzu. Koda yake wasu a ciki sun bada ne da kwaWayi na burin zamowar ?a?an nasu zama matan Shahanshan, suna ganin hakan wani Waukaka ce a garesu da samun wasu damammaki......

? ? ? Iffah dake kwance a Waki zuciyarta a bushe, idanunta dake zubda hawaye a Wazun a soye ta jiyo bayanin Waura aurenta da Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdull-Majieed daga bakin su Kaka. Wani irin dimmm taji a cikin kunnuwanta tamkar Waukewar wutar lantarki daga tashar gidan redio, ta koma ita ba wadda ta suma ba, ba kuma wadda ke a raye ba tsabar tsintar kai a wani hali. Ta jima a haka kafin ta dawo hankalinta kwakwalwata ta fara tantance abinda taji Win. Kenan abinda ya faru da yan uwanta a wasu watanni da suka shuWe itama shine ya faru da ita yau? Itama zata mutu mutuwar rashin gata da ?anci a hanun azzalumin mai mulkin Ruman da jama'ar cikinta. Daga yau za'a koma ?irga mintuna da da?i?un mutuwarta da suka rage mata, daga yau tayi bankwana da Ummu, da Babiy, da Hanash Akhi da su Kaka. Anya kuwa zata iya? Anya kuwa sadaukarwar nan ta dace da rubutattun burukanta? Anya kuwa zata iya jurewa? Kai ina bazai yuwu ba. (Mizai hanasa yuwuwa? Bayan zakije inda ko kuwwa kikai babu maijin muryarki?) wata zuciya acan gefe ta ayyana mata. A karo na farko hawaye masu zafi da raWaWi suka silalo bisa kumatunta da gudu.  Dole ma na jure, jurewa irin wadda a duk faWin duniya labarina zai karaWesa a lokacin dana hukunta Tajwar Eshaan ibn Haysam ibn Abdul-majeed . Ta faWa cike da ?warin gwiwa na tabbatar da burin mai Waukar fansa.
? ? ? Batare data goge hawayen dake cigaba da rige-rigen zubo mata ba ta sauka a gadon tana tangaWin jiri. Wayar data maida ta ajiye da ?udirin ta daina amfani da ita ta lalubo, haWata tai ta kunna, sai dai tai Wan jimm namai nazari kafin ta fara rubuta sa?o. Minti biyu bayan turawa kira ya shigo. Numfashi ta fesar, sai kuma ta saki murmushin takaici jin abinda aka faWa daga can.
? ??  Sir bamu da lokacin tattauna wannan a yanzu .
??  Na sani Fareedah, sai dai inajin matu?ar tsoro, tsoro irin wanda ko'a ido aka kalla an san tsoro ne. Nasan na rasaki na har abada a yanzu .
? ? ? Murmushin takaici ya suSuce ma fuskarta, sai dai ta hana hawayen da suka ciko mata ido zubowa.  Wannan shine tsoron dana gudar maka fuskanta tun farko dama duk jama'ar Ruman. Amma bazan gajiya ba, plan A dama ya?in sun?uru ne, plan B mafi haWari amma da ya?inin nasara .
? ? ? ? ?  Ta yaya Fareedah? Kin san kuwa waye Shahanshan? Kin san minene girman ikonsa?.....
??  Na sani mana tunda nima a ?asar aka haifeni. Sannan na zama cikin ahalin da sukafi WanWana Wacin girman ikon nasa da zalunci. Karka damu da haWari sir, taimako Waya zakamun a wannan plan Win wanda babu wani abu da zai shafeka da iznin ALLAH .
? ? ??  Amma Fareed....
?  Please sir .
Kakkauran numfashi yaja ya fesar cike da ?arfin halin son danne rauninsa a gareta.
? ? ? ? ?  Okay ina jinki .
? ?  Ka bani number abokinka .
 Fareedah mi kuma ya rage? .
? ? ? ?  Abubuwa masu yawa da amfani, hasalima yanzu ne za'a fara wasan na gaskiya .
? ?  Karki taurin kai .
 Na jima da zama mai busashiyar zuciya .
? ? ? ?  Ki fahimceni .
? ?  Ko kaina ma bana iya fahimta sir .
 Bana son na rasaki Fareedah .
 Iyayena sun jima da ha?urin rasa ni, kamar yanda na jima da sadaukar da kaina .
? ??  Miyasa kike da taurin kai Fareedah .
?  Shine izzata, ?arfin gwiwa ta wajen tunkarar ma?iyi na .
Wani irin cije lips yayi daga can, hawayen da tun randa labarin auren wadda ya fara so yake kuma kan so yazo masa da wanda yafi ?arfinsa suke kwaranya ya kasa sharesu suka shiga rige-rigen zubowa daga idanunsa, yasan ta ?are kuma, abinda ya rage kawai ?yautatama masoyiyarsa koda hakan zai kasance sadaukarwa ta ?arshe da zaiyi a rayuwarsa.
 Na barki lafiya, ki kasance cikin aminci da kariyar UBANGIJI . Ya faWa harshensa a sar?e da yanke wayar a lokaci guda.
? ? ?? Wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga gudu a fuskar Iffah, bata san tana son Sir Fawzan ba sai a yanzu. A yanzun da kowa zai iya kiransa ?urarren lokaci a rayuwarta. Zata cigaba da masa fatan alkairin samun madadinta koma wadda ta fita, jin kamar motsin ana tunkaro Wakin yasata saurin kwanciya taja bargo har saman kanta....
? ??
? ?? &&........

? ? ? ??  Muhammad Zayyan! .
?? Kaka ya kira Babiy tamkar yana gabansa cikin matsanancin damuwa da firgici na zahiri dake kan fuskarsa. ?ago kansa dake sunkuye yay a hankali shima tamkar yana a gaban Kakan. Hakan ya bayyana jajayen idanunsa da damuwa ta rinar. Sun rabu ne tun a wajen Waurin aure basu dawo nan gidan ba suka wuce Jumna.
??  Na'am Baba .
?  Kayi ha?uri. Karku zama masu ba?in ciki kai da matarka. Ku zama masu juriya da karSar ?addara rubutacciya daga UBANGIJI. Nasan akwai raWaWi, nima kuma makamancin irinsa nakeji a ?irjina. Sai dai bazan gaji da faWa maka *_Kibiyar ajali sulke baya tareta sai ta gitta ba_* kamar yanda babu wata duster data isa goge abinda al?alamin ?addara ya rubuta. Mu mun wuce yanzu, dan mungama namu ku ya rage kuyi naku mu barma UBANGIJI sauran, dan dama duka nasa ne. Iyyani itace zata shiryata kafin isowarsu Waukarta, nau'in turaren da yake a cikin gidanka kawai nake bu?atar fitar ?amshinsa daga jikinta. Ta kuma sha iya adadin madara datake gidanka kawai daga yanzun har zuwa wayewar gari. Ta kwana a Wakin daba shi aka ajiyeta ba. Karta karSa daga wanda zuciyarta tai rawa a kansa. Ta zama ?ar kallo a takun farko, ta zama kurma a shigar farko, ta zama mai rauni a tawagar farko, tasa a ranta kariyar UBANGIJI na tare da ita. Na barku lafiya .
? ? ? ? Ummu ta juya ta kalla Babiy dake ri?e da wayar a hannu tamkar dasashen gunkin da akai ado dashi domin tunawa a tarihi.  Lafiya kuwa? Baba ma baida wata mafita ko? Shiyyasa ya?i dawowa tanan ya wuce gida? .
? ? Idanu ya cigaba da tsura mata tsahon wasu sakanni harta fara kuka, ya ciza leSensa na ?asa yana mai haWiye abinda ya tokare masa ma?oshi. Gefenta ya kai zaune, tamkar mai bitar karatu ya shiga maimaita kalaman baba a zahiri _ Iyyani za ta shiryata kafin isowarsu Waukarta, nau'in turaren da yake a cikin gidanka kawai nake bu?atar fitar ?amshinsa daga jikinta. Ta kuma sha iya adadin madara datake gidank....... _
? ?? Kallonsa Ummu tai da share hawayenta a lokaci guda, cikin rashin fahimta tace,  Mi kake son faWa? .
?? Kansa shima ya girgiza mata.  Ba dagani bane ba, Baba ne. Amma na kasa fahimtar komai Jamaima. Ko ke kin fahimta? .
? ? ? ? ? ? Har zatace a'a sai kuma tai Wan jimm idanunta masu girma da su Iffah suka gada a kansa. Itama maimaita kalaman tayi kamar yanda ya faWa har sau uku,  Idanfa har na fahimta, Baba yana nufin _Iyyani ta shirya Iffah da kanata, idan sunzo da wani turare karmu bari tai amfani da shi, sannan ko taje can an bata wani abu kar taci......, Kaga kenan daga nan mu saka mata turaren, sannan mu bata abinci taci cikinta ya cika. Mu kuma......
? ? ? ? Numfashi ya ja daga hancinsa a hankali ya saukar a ?irjinsa, itama ta sauke numfashin mai haWe da zubar hawaye sakamakon dakatar da ita da yay da hannu alamar ya fahimta ba sai ta ?arasa ba. duk da bawai nauyin da zuciyarsa tayi ya ragu bane, ya dai samu sassauci daga kalaman Baba duk da basu san manufarsuba kai tsaye. Sai dai bin umarninsa a garesu tilas ne.......

? ? ??& Tsaf Iyyani ta shirya Iffah dake faman zubda hawaye har yanzu cikin shiga ta alfarma kamar yanda Kaka ya bada umarni. Wata haWaWWiyar riga ce da akanga irinta kawai a jikin hamsha?an matan gidan sarauta na ?asar ruman mai kama da al?yabba da ita kanta Iyyani bata taSa sanin a kwaita a gidansu ba Kaka ya kawo yace a saka mata. Duk da shirine bana daWin rai ba tayi ?yau matu?a. Ga wasu nau'in sirrika na ?amshi na tashi daga jikinta har suna hawa kai. Tsaff Ummu da kanta ta shirya mata wasu abubuwa masu muhimmanci nata duk da sun san zama ne na ta?aitaccen lokaci ga ?ar tasu mace tilo data rage yanzu. Daga Babiy har Ummu zama sukai suna mata nasiha, nasihar kuma gaba Wayanta tafi ?arfine akan addu'a, ta kula da addininta, azkar, karatun alkur'ani kar tai sakaci da su. Babiy da kansa ya Wakko wayar Fariha ya bata yace ta Soye kozasuna rin?a jinta, baima san ta Arfa ma na hanunta ba. Isowar jama'ar daular ruman ta katse zaman nasu. Inda mayan matan da suka shigo gidan tare da rakkiyar tawagar hadimai suka bu?aci a basu amarya da ruwa mai Wumi su shiryata. Kan Babiy a ?asa ya basu amsa da
? ??  A shirye take domin cika umarninku .
? ? Sosai mamaki ya bayyana a fuskokinsu dajin kalaman Babiy da kuma fitowar Iffah da Iyyani ta ri?o suka fito. Baki Waya daga cikinsu ta buWe zatai magana wata ta girgiza mata kai alamar kartace komai. Badan taso ba tai shiru, sai dai ta juya ta fita tana mai danna wayar hanunta da alama wani take ?o?arin kira.
? ?? Babiy da kansa ya kama hanun Iffah tare da akwatin kayanta ?arami har ?ofar gida gaban motar da aka tabbatar masa itace ta Waukar amarya.. Da gayya Iffah tai gaba zata kifa suna gab da fita a soron kamar tayi tuntuSe da rigar jikinta dake jan ?asa. Da sauri hadimai mazan dake tare da su sukai mata runfa da bayansu dan kar wanda yaganta, dan kofar gidan dama cike yake da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login