Showing 78001 words to 81000 words out of 120369 words

Chapter 27 - DAUDAR GORA COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Nov 2025

234

mulkarsu da fuska biyu ne .
? ? ? Yanda tai maganar kanta tsaye babu ko War ya sashi jin mamakinta. (Tabbas wannan abar ba mutum bace) zuciyarsa ta tabbatar masa. A zahiri sai ya Wauke kansa cike da basarwa. Shiru babu alamar zai sake tankawa har Iffah tama fidda rai ta cigaba da tsakurar abincinta kamar yanda yakeyi shima.
? ? ?  Wasa da rayuwarki kuskurene ga ?arfin halinki, ?in kasancewar ki tarihi a wannan safiyar bashi ke tabbatar miki nasarar tsallakewa ba .
? ? ? A yanzun kam zantukansa sun zama masu matu?ar tasiri a fitarsu da saurarensu gareta, jin bazata iya dannewa ba ta amsa batare data Wago ta kallesa ba,
? ??  Hakane shugabana, sai dai fa _Fate is some thing undeniable _
? ? ? ?? Ya basar babu alamar yanzu ma zai amsa, shayin sa ya kai baki cike da ?asaita. Itama sai bata sake cewa komai ba ta cigaba da cin abincin tana mai kallonsa ta gefen ido, sannu-sannu tabi sautin motsa plate Win gabansa da kallo har kan lallausan farar fatan hanunsa masu Wauke da tsaftatattun fararen dogayen farce, baya tai ?o?arin jan jikinta batare data yarda idanunta sun wuce kallon hanun nasa ba.?Yanda ya basar da ita Win kuma sai yay matu?ar sukar zuciyarta, dan bata bu?atar tattaunawar tasu ta tsaya iya haka. Amma sai bata yarda fuskarta ta nunaba. Sai ma mamakin ?asaita da tsantsar izzar wannan bawa da zuciyarta ke faman yi. A wani Sangaren ita kanta dakewa kawai take, amma kwarjininsa da gizago na firgita ta matu?a. Tana ?ara tsarkake sunan ALLAH akan yarda da jinin mulki gaskiya ne. Duk da ta shigo daular ruman da wani ?udiri a ranta hakan bazai hanata girmamashi ba, koda ace tayima yun?urin hakan kwarjinsa bazai bata damar yin saSanin girmamawar da kowa ke masan ba. So take taji tsanarsa a ranta kamar yanda takeji kafin ganin wannan fuskar matsayin shi amma zuciyarta ta?i bata haWin kai. Numfashi taja a hankali ta fesar a ?asan ma?oshinta.
? ? ? ??  Kokawa da ?addara a fuskar iyawa na nufin faWuwa! Kinga ko what you get is, what you have? .
? ? ? Ya faWa cikin katse mata tunani dai-dai yana Wagowa.......
'?

? ??  Fareedatu kibar danginmu su tsinkayi yini da kwana cikin sallama, Banda taro dutsen zuma inake ina kace nace da dodon may...>?q?

? ? ?

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*


_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*?AN ?ASAR NIGER
+227 96 09 67 63

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu=?-?=?O? .


5??5?2?5?)?5?"?5?'?5? ?=???


('5?o?5?l?5؀݊5?l?5?}? 5?r?5?z?5?}?5?l?('
(5?n?5؎?5ؐ?5؎? 5ؐ?5؆? 5ؘ?5؍?5؆?5ؙ?5؆?)



5???5???5???5??5??? 5???5???5???5???5???5??? 5???5???>??

*_34_*


........(Mi wannan mutumin ke ?ullawa?). Ta faWa a zuciya batare data motsa ba. (Keda ke neman kusanci da shi dama miye matsalarki da koma mi yake nufi) wata zuciyarta ta sake ayyana mata. tamkar wadda aka zaburar sunan Arfa da Fariha ya fara amsa kuwwa a zuciyarta har tana jinsa yana tashi bisa sararin samaniya.
? ? Kaifafan idanunsa masu nuna tsaurinsa ya zuba mata ganin ta basar da shi itama. Kusan mintuna uku babu alamar zata tankama zancen nasa har ya fara jin haushi. Ta taSe baki da kauda kanta gefe, cike da dakewa ta furta,  Da gizago na tsorata ?warin gwiwata da bazan amincewa shigowa ramin zakin da Wanyen nama shine abincinsa ba. Karka damu a kaina ranka ya daWe, dan a wannan gaSar *_cuta ce ta Wakko cuta, Sarawo ya Wakko akwatin maciji ._*
? ? ? Fuska ya Wan motsa kamar zaiyi murmushi, sai kuma ya basar.  Bana haWa ?wanji da mage duk da kamaninta na yanayi da nawa matsayina na ZAKI har a hallaya. Ki kama kanki dan kina bu?atar rayuwa mai tsaho wajen moran ?uruciyarki .
?? Ya faWa da muryarsa mai zurfi da ?asaita yana mi?ewa ya zagayeta ya wuce abinsa. Shiru bata motsa ba har ta gama jin Sacewar sautin takunsa a wajen, ta Wan cije bakinta  Zaki zako ka magantu fiye da haka . Ta faWa a fili cike da kwaikwayo salon maganarsa tana sakin wani lallausan murmushi da kai kofin shayi a bakinta, duk da zafinsa ta rumtse ido ta kwankwaWe abinta sannan ta juya taima hadiman dake tsaye har yanzu kallo Waya ta Wauke kanta batare da damuwar komai ba, dan tasan basuji komai Win ba da suka tattauna. A yanda suke maganar ma wani sai ya Wauka wani zancen soyayya ne ya haWasu. Komai batacema kowa ba itama ta mi?e tabar wajen, duk suka bita da kallon ?asan ido kowa da abinda yake?ayyanawa a zuciyarsa.
? ? ? ?? A tafiyar tata tana Wan kalle-kalle taci karo da camara, komai bataji a ranta ba, dan tayi tsammanin hakan tun farko, saboda babu yanda za'ai sashen mutum mai ?arfin iko kamar Tajwar ace babu wani tsaro makamancin hakan koma fiye da hakan. Da ?yar ta iya gane Wakin data kwana. Tana shiga ta zube a kujera da sauke nauyayan numfashi, Wakin da akaima gyara Wan gaske tabi da idanu, sai taga ma kamar ba'a cikinsa ta kwana ba, ganin akwatin kayanta kawai ya tabbatar mata da shi Win ne. Tunani mai ?arfin gaske ta faWa kusan kashi uku zuwa huWu musamman akan kawota da Malikat Haseena tayi, mi tsohuwar ke nufi da haka bayan su suka sanar mata an rasa matan baya ne a dalilin kawosu turakar Shahan-shan Win. Sai kuma akan Tajwar Eshaan Win, na farko waccan fuskar data gani a waje kafin shigowarta masarautar matsayin matarsa. Na biyu wannan fuskar ta yanzu da bata da banbanci da waccan Win, na uku hanyar da ya kamata ta cigaba da bi domin sanin ainahin wanene Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed a baWini da zahirin rayuwa. Domin da gasken gaske tana a cikin ruWani akan fuskokin nan biyu data gani a mabanbanta muhallai. Su ?an biyu ne? Kokuwa shi Winne ke Sadda kama yana fita?. Abu na uku kuma abinda ya faru a daren jiya da sai a yanzu yake bata matu?ar mamaki, tun a jiyan bawai ta ajiyesa a gefe bane dan bashi da muhimmanci ga haWarin da tasan ta kawo kanta ciki, kawai dai bata san dalilin da yasa bataji ko War ba a zuciyarta na tsoro, kuma har yanzu batajin tsoron sam, dama kuma tun asali bata da tsoron. Dan Iffah irin mutanen nan ne masu ?esashiyar zuciya mai iya tunkarar komai koda yanada haWari a garesu, tanada naci da zama kaifi Waya akan zimma da cimma buri duk da ?arancin shekarunta. Na ?arshe tattaunawarsu ta yanzu da shi da girman kalaman da yay amfani wajen jifanta da su. Ta Wan murmusa da cije lips Winta tana mai lumshe idanu a hankali......

? ?? &&.... &&.....

?? Zuwa yanzu tako ina maganar tsallakewar Iffah ce ke kaikawo a cikin masarautar. Kowa ya nutsu wajen tattauna abinda ke bakinsa da abokin maganarsa. Wasu jin daWine game da hakan, wasu ko ba?in cikine a ransu, dan mutuwar Zawjata-almilk Win kamar wani makamine a hannayensu na dukan nasarar Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed Win. Tsallakewar Iffah kuma zai kasance kamar damar ?alubalantarsa da suka ri?e ya kuSuce musu kenan. Ita kuma yarinyar kimarta da nunawa duniya tafi ?arfin masu ?arfin zai yi tasiri a zukatan jama'a.....

? ?? &Komai dake faruwa yana isa da shiga a kunnen manyan masu faWa aji ta bangaren iko da kusanci da Tajwar Eshaan Win. Wato Malikat Haseenat da Malikat Bushirat. Sai dai sunyi biris babu alamar zasu tofa nasu akan hakan bayan bayyanar farin cikinsu akan fuskokinsu daya gaza boyuwa ga kowa. Dan a dalilin wannan al'amari Malikat Bushirat har ?afiya tayi ga wasu firsinoni dake a cikin kurkukun masarautar akan wasu laifuka nasu da basu kai sun kawo ba. A cikin sunne kuma aka sallami harda Diwa a dalilin bincike daya tabbatar da bata da hannu game da abinda ya faru ga Iffah a waccan ranar.

? ?? &A Sangaren Malikat Haseenat kuwa maimakon bama abinda ke zuwama kunenta muhimmanci hankalinta ta maida wajen tantance hadiman da zasu koma aiki a karkashin Iffah ne bisa taimakon Daneen Ammarah da farin cikinta itama yake a bayyane. Dan itama dai har kyaututtuka na musamman yau ta bada ga hadimai tare da sakawa a tattaro mata dukkan malaman masarautar zuwa sashen Iffah da bukatar suyi saukar Alkur'ani mai girma. Ta kuma mi?e da karfin jikinta wajen shirya lunch na musamman ga Tajwar Eshaan da amarya Iffah Zawjata-almilk...

? ? ?? *_&BARRISTER&_*

?? Abubuwan da suka faru sun sakashi dakatawa a zahirance bisa shawarar Kaka. Sai dai yana cigaba da gudanar da wani binciken sirri dan yayma kansa al?awarin binciko duk mai hannu akan wannan al'amarin nasu Babiy da ma inda aka Soye su.
? ? ? Kamar yau ma tun jijjifin safiya ya fito daga gida. Kai tsaye hanyar jihar Hubab ya nufa inda bincikensa ya tabbatar masa nanne ainahin jihar da matar Abu Moosa ta fito. Jihar Hubab makwafciyar Dahab city ce (Daular ruman kenan) dan haka a cikin ?an?anin lokaci ya isa. Bai tsaya sanyaba ya Wauka hanyar ainahin kauyensu kuma. Kasancewar anan ma hanyace shimfidaWWiya a kan?anin lokaci ya isa. Da farko ya sha wahalar binciken inda gidansu yake, sai da yay dabarar nuna hotonta sannan.
? ? ? ?
? ? ? Kusan mintuna goma bayan isar da sa?on tanada ba?o gareta ta fito cikin irin shigarsu. Tayi Wan tsamm alamar shan jinin jikinta kafin ta ?araso a yanayin son basarwa. Barrister shi ya fara gaidata, tare da sanar mata sunansa. Lokaci Waya ruWani ya bayyana akan fuskarta ta shiga waige-waige irin na rashin gaskiya da ?o?arin ja baya daga garesa...
? ??  Bawan ALLAH ina baka shawara ka taimaki kanka ka bar ?auyen nan, babu wani abu da zaka iya ji a gareni dan ban san komai ba .
? ? ? ?? A fusace Barrister yay tsalle gabanta yana huci.  Baki san komai ba amma akaje da ke har gida aka kamasu. Karki sha mamakin bayan sanin inda kike har wasu abubuwa na sani a kanki Mss Farishta. Rashin bani haWin kai kuma na nufin na tonasu kowa yasan ke Win wacece har ma da dalilin auren Dawood, sani kankine wannan babban koma baya ne a gareki kuma harma da zuri'arki .
? ?? Yayu ta haWiya masu kauri tana kallon Barrister, sai kuma ta sake wawwaigawa tabbacin dai akwai abinda take shakka.  Naji Barrister zan baka dukkan bayanan da kake bu?ata, amma ina ro?onka kabar wajen nan, idan ma zai yuwu kauyen nan gaba Waya nake son ka bari. Wlhy na maka alkawarin zan zo na sameka na kuma faWa maka komai da kake bu?ata harma wanda baka sani ba .
? ??  Miyasa bazan sani ba a yanzu? .
 Saboda zamanka anan yana da matu?ar haWari .
? ?  Taya zan tabbatar da zaki zo Win? .
 Na baka dama kabi duk hanyar da zata bibiyi al'amarina .
? ? ? ?? KafaWarsa ya Wan Wage sama da faWin,  Okay inaga bana bukatar hakan, kije kawai ni na san ta hanyar daya dace na bibiyekin. Amma yaushe ne zamu haWun? .
? ?  Inasha ALLAH a daren yau ka sameni a ?auyen Jumna .
??  Garin su Abu Hanash da Dawood kenan? .
??  Insha ALLAH .

? ? ? ?? Tafiya yake zuciyarsa na faman masa kaikawo akan haWuwar tasa da Farishta (matar Abu Moosa datazo har gida da ?an sanda aka kama su Babiy. ALLAH yasa kun gane>?q?). Duk da yasan zata iya ?in aikata abinda ta faWa na haWuwar tasu a garin Jimna ya zaSi barinta su haWun can bisa lumana. A cikin Hubab ya tsaya yaci abinci tare da sallar azhar. Ya fito masallaci idanunsa suka sake sauka akan wata mota da tun fitowarsa ?auyen su Farishta ya lura da ita tana biye da shi, sai dai duk da ya ganta suna tafiya kafaWa da kafaWa bai kawo komai a zuciyarsa ba. Janyewa yay cike da rashin bama abin muhimmanci ya shige motarsa da zummar zai cigaba da tafiya kawai yaga an zagaye motarsa da bindigu.......

? ? ?? &&&.... &&.... &...

?
? ? A firgice ta farka a Wan barcin daya figeta bayan ta idar da sallar azhar. Ta dafe kanta dake sara mata. Irin mafarkin da tai da dare ne dai babu banbanci. Huci ta furzar da faWin,  Wace madara ce haka? Tabbas kodaga ina zata fito babu alkairi a cikinta tunda har mafarkin nan ya sake maimaita min kansa. Ya ALLAH . Ta furta a fili zuciyarta duk babu daWi, dan zuwa yanzu Iffah ta fahimci wani Soyayyen al'amari game da ita, tabbas in har zatai mafarki taita kuma maimaita irinsa sai wani abu ya biyo bayansa mai taSa zuciya, ta gane hakanne a Wan zamanta cikin masarautar nan, sai kuma auna abubuwan da suka faru a baya kafin yau Win. Sai dai tana ?o?arin ?in gasktama kanta hakan dan kar zuciyarta ta shagala kan abinda zai sakata kaucema umarnin mahaliccinta kuma. Ga kanta jingim kamar yanda yakeyi a duk lokacin datai mafarki makamancin haka, sai zufa data ji?eta sharkaf tamkar wadda tai wanka. Shigowar sa?o a wayarta da ke gefenta ya sakata tsurama wayar ido na kusan mintuna biyu, kamar wadda aka zaburar wani abu data shafa'a kuma sai ta jawo wayar. Data ta kunna a take tai downloading WhatsApp app..., Bayan ta kammala dai-daita komai tai searching number Sir Fawzan da zuciyarta ke ayyana mata ta fara nema, cikin rashin sa'a taga kusan kwana uku ma baya online ta hanyar lastsin Winsa. Duk da hakan bai mata daWi ba batai wani yun?urin kiransa ba ta maida akalarta kan number abokinsa Ajmaal. Cikin sa'a shikam dai yana online. Sallama tai masa a ta?aice ta tura, sai dai har kusan mintuna biyu babu reply (yana aiki) zuciyarta ta ayyana mata. Aminta da hakan ya sata cigaba da ajiye masa sa?o kawai a kan duk abinda ya sake faruwa bayan wanda ta tura masa ranar. Daga karshe ta aika masa da ro?on ya bincika mata iyayenta dan har yanzu hankalinta ya kasa kwanciya dangane da su. Ta haWa masa da adireshin gidansu, da faWin (In har kaci amanata ko yaudarata na barka da mahaliccin rana da wata yay maka hukunci da alhakin dukkan al'amuran ?asar ruman da zalincin mulkin wannan shaiWanin dodo ke tafin hanunsa). Daga haka ta fito shima Sir Fawzan Win ta tura masa gajeran sa?o ta goge WhatsApp Win gaba Wayansa ta ajiye wayar.
? ? ? ? Da Wan layin nauyin jikin dake tare da ita ta mi?e, tana ?o?arin shiga toilet taji kamar an gitta mata ta baya. Idanunta ta Wan rumtse sai kuma ta waigo. Komai babu dai a zahiri dan haka ta kaWa kanta kawai ta shige bakinta da addu'a....

? ?? Fitowarta kenan bayan ta watsa ruwa alerm Win ?ofar yay ?ara alamar ana knocking. Sai da ta zira doguwar rigar abaya data Wakko cikin kayanta sannan ta ?arasa ?ofar ta buWe. Hadimar dake tsaye ta zube ?asa cikin girmamawa tana kwasar gaisuwa. Amsa mata Iffah tai, zuciyarta babu daWi akan yanda suke ?as?antar da kansu, ta amsa cikin sau?in muryarta dake a sanyaye sakamakon mafarkin da duk ya sakar mata kasala..
? ?  Wani abu ya faru ne? .
Ta tare hadimar tunkan tace komai. Kai ta gyaWa mata tana sake rissinar da kanta.  A gafarceni ya Zawjata-almilk. Dama abinci ne aka kawo daga sashen mai Babban Waki .
? ?? Iffah tai Wan jim tana hasashen wace kuma mai babban Waki? Kamar hadimar ta fahimta tai saurin mata fashin ba?i da  Malikat mai babban Waki .
? ?? (Malikat Haseenat) shine abinda zuciyarta ta ayyana mata. Ta kaWa kanta da faWin,  Okay ba damuwa zan fito . Daga haka ta maida ?ofar ta rufe. Ciki ta koma, sai dai maimakon zama sai ta koma kaikawo kamar mai Safa da marwa abubuwa masu yawa na faman mata kaikawo. Ta jima a haka sosai kafin ta sake kimtsa jikinta cikin wata tsadadiyar abaya mai adon stones dake ta ?yalli da Waukar idanu. (Wannan yana cikin horon Daneen Ammarah data tabbatar mata koda wasa karta zauna da kazamar shiga ko fitowa da ga Waki a raguwar kwalliya. Dolene inhar zata bar cikin Wakinta ta tabbatar komai na jikinta ya isa a kalleta da shi. A tsarin masarautar hakan ba fariyya bane mutunta kaine ga kowa. A kuma Wan zaman Iffah cikinsu ta fahimci hakan sarai). A yanzu ma kamar Wazun turarrukan sa ta baza har ?amshinsu na rige-rigen fita kafin ita ta fita. Ta fito cikin takunta na nutsuwa da ?asaita kamar wata budurwar macen Wawisu (>?q?=? ?lol)..........
'?

? ? ??


? ? ?

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*


_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login