Showing 15001 words to 18000 words out of 120369 words

Chapter 6 - DAUDAR GORA COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Nov 2025

228

Jeki ki cigaba da karatunki dama motsi naji kamar, amma fara duba kosu Hanash sun bar mana ?ofa buWe ne .
? ? ? ?? Da to Iffah ta amsa tana nufar hanyar soro da sauke ajiyar zuciya...

? Tana shiga Waki wani uban tsalle tai ta dirga saman gadonsu dan farin ciki. Mulmula take tana dariya irin wadda ta jima batayi ba, wauta da ?uruciyarta tafi hango mata nasararta na Waukar fansar ?an uwanta fiye da tunanin idan wani abu ya faru Babiy ne na farkon wanda za'a tuhuma kasancewar zumar daga hanunsa ta fito. Haka Iffah ta ?arasa wannan dare cike da zumiWin ganin wayewar gari Babiy ya kai zuma masarauta.
? ? ? Bayan ta idar da salla yau ko fama da ita Ummu batai ba akan shirin tafiya makaranta, a da kuwa saita tasota da?yar kasancewarta mai son barcin safen tsiya da tayi salla take komawa barci. Babiy kansa saida yay mamakin wannan sammakon tashi nata yau, Hanash kam kasa ha?uri yay saida yay magana. Sai cewa tai ai sunada program ne a makaranta yau... Koda taje makaramtar ma dai bawai ta nutsu bane, rabin hankalinta ne kawai ga duk malamin daya kasance da su har aka tashi.

? ? ? &A Sangaren Babiy kam duk da tabon da masarauta daular ruman ta bar masa a zuciya bai taSaji koda wani zai bari ya cutar da su ta hanyarsa ba ko shi ya aikata hakan ta damar dake hanunsa na kai musu zuma. Tsaf yay shirinsa kasancewar yau juma'a ce ya Wiba tulunan zumar nan guda uku ya nufi daular ruman. Idan yaje ba kaitsaye yake Waukar zumar nan ya kai ga Tajwar ba, dan ganin Tajwar kam babban abune da sai wanda ya cika ya tumbatsa keda wannan damar. Akwai wanda keda alhakin amsarta shi ya isar da ita inda ya dace har ta isa ga sashen Tajwar Win. Bayan ?an bincike a kansa na kullum da basa ?arewa ya shiga daular ruman iya ?ofa ta biyu. Dattijo da kamanni da suturar jikinsa kawai ta isa tabbatar maka da shima wanine ya iso ga Babiy bayan zaman jiran kusan mintuna goma da yayi. Cikin girmamawa Babiy ya gaidashi duk da zasu iya zama kusan sa'anni da shi. Shiko ya amsa yana hura hanci irin na masu dama ta mulki a hannu. Umarni ya bama Babiy akan ya WanWana zumar, Babiy da yasan babu wani abu na razani ko shiga dogon tunani kafin WanWanawar kansa tsaye ya kai hannu ya Wauka cokali dake bisa tire a hanun hadimin dake biye da dattijon nan. Tunda dama haka ba sabon abu bane garesa duk sanda ya kawo sai ya WanWana Win. Tulun farko ya kwancema baki kasancewar a Waure bakin yake da ganyen ayaba, yasa cokalin nan ya Wibo zumar da bismillah ya nufi bakinsa.........
'

? ?? *_=?,?=?,?=?,?Iffahhhhhh!!!!=?F?

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*


_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*?AN ?ASAR NIGER
+2290165991

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu=?-?=?O? 5??5?2?5?)?5?"?5?'?5? ?=???


('5?o?5?l?5؀݊5?l?5?}? 5?r?5?z?5?}?5?l?('
(5?n?5؎?5ؐ?5؎? 5ؐ?5؆? 5ؘ?5؍?5؆?5ؙ?5؆?)



5???5???5???5??5??? 5???5???5???5???5???5??? 5???5???>??

*_8_*


..........Zaune takai a kujerar dake duban tasa tana mai kallon agogon hanunanta. Ya saki murmushi cikin kafeta da idanu.  Daga zuwa sai duba agogo? .
? ?  Hakan dolene Sir, domin ko lokacin islamiyya zan cinye anan. Kaga kenan sai da tsantseni .
? ? ? ??  Okay .
Ya faWa yana gyara zamansa.  Ba bu?atar maimaita abinda ya faru baya, na gaba kawai yanzu shine zanyi iya ?o?arin ganin na haWu da abokin nawa koda ta waya ne, kin san aikin nan nasu yana hanasu samun isashen lokaci matu?a kasancewarsu manya dake tare da babbar kafar yaWa labarai mai aiki da kamar duniya gaba Waya. Ke yanzu a gareki miye shirinki? .
? ? KafaWa Iffah ta Wan Wage cikin jan iska da hurowa.  Kusan dukan shirina a kammale yake, burina kawai nasamu yin hira da African Aye=?A??
=??? .? ? ??? ? ??  Indai hakane haWuwa da abokina kawai ya rage mana, fatana dai bayan ni kar wanda yasan wannan hatta a gidanku, inba hakaba zamu iya shiga haWarin da har burin rayuwarmu ma bazai cikaba bayan wannan. Nikuma zanyi duk yanda zanyi insha ALLAHU wajen hana wannan sirrin fita daga gareni....
? ? ?  Shi abokinka Win fa? .
 Baki da matsala da shi domin shi aikinsa ne .
? ?? Kai ta jinjina masa fuskata cike da murmushi. Sai kuma ta rissinar da idanunta alamar jin kunyarsa saboda kallon daya kafeta da shi. Kunyar nada nasaba da tuna yanda ta dinga wancakalar da shi da manufarsa a sanda yake malaminta. Sai gashi shine na farko data fara tunkara da matsalata a yanzu duk da kuwa tana kallonta a kan matsalar data shafi kowa na ?asar Ruman ne. Sautin murmushinsa ya sakata Wagowa ta Wan kallesa, sai kuma ta sake kauda kanta gefe itama tana murmushin.
? ?  Hummm!
Ya faWa yana mi?ewa. Itama mi?ewar tayi batare data yarda sun sake haWa ido ba.  Kije gida zamuyi waya .
? ? ? ? ??  Nagode sir, ALLAH ya tsare gabanka da bayanka .
? ? ? Jin sautin murmushinsa ya tabbatar mata jin daWinsa, amma sai tai gaba da sassarfa tunkan ya sake cewa komai........

&__________________&

? ? ? ? *_DAULAR RUMAN (MASARAUTA)_*

? ? ? ? ??? Katafaren Waki mai Wauke da ?ayatattun kayan more rayuwa, kwance take bisa lafiyayyen gado da dukkan nau'in shimfiWunsa suka kasance na alfarma. Sautin dariyar dake tashi cikin kunnuwanta tamkar mafarki ya sata buWe idanu, cikin tsumar jiki ta ture lallausan bargon da take ciki, tamkar wal?iya ta dire ?asan lafiyayyen kafet Win dake malale gaban gadon tai kneel down tamkar mai neman gafara, kanta a risine alamar nuna tsantsar girmamawa.....
? ? ? Tamkar shirin film ko labaran almara tsohuwa tukuf sanye cikin jajayen kaya ta bayyana bisa ba?ar kujerar ?arfe mai Wauke da adon gold a cikin Wakin. Ba?ace matu?a mai tsananin muni da jajayen idanu, yanda ta zauna ?afa a harWe kai ka Wauka itace Shahanshan Win.....
? ? ? ?  Lafiya da tsahon rai su ?ara kasancewa a rayuwar *_Uwa_* mai share kukan masu kuka . Hamsha?iyar matar ta faWa cikin tsantsar girmamawa ga tsohuwar dake harWe saman kujerar tata tamkar sarauniyar ingila.
? ? ? Cike da isa da ?asaita tsohuwar taja wani kakkauran numfashi da sake faWaWa girman ?ofofin hancinta ta hanyar hurashi, ?ara harWe ?afafunta tai tana mai motsa yatsun hanunta, idanunta jajaye kafe akan matar. Cike da isa da ?asaita mai Wauke da rashin daWin muryarta ta tsufa ta fara magana.  Ta-?urya kin kusa cin nasara wajen cika sharaWi na biyu akan al?awarinmu. Na tayaki murna, saura sharaWinki na ?arshe, mafi wahala a cikinsu .
? ? ? ?? ?asa ta ?arayi da kanta cike da girmamawa a gareta, da dukkan ?arfin zuciyarta ta furta,  Kece madubin nasarata Uwa!, duk inda akaga naje da jagorancinki na isa. Yanda na cika na farko shima na biyu zan cika sa, nayi al?awarin cika na ?arshe ma fiye da yanda kike tsammani.....
? ? ?? Jajayen idanunta masu kama da garwashin wutar gidan biredi ta Wago tana kallon ?ya?y?yawar kuma hamsha?iyar matar dake gurfane a gabanta. Ta ?yal?yale da wata dariya mara daWin saurare ga kunen kowa, sai kuma ta gimtse tamkar ba ita tayi ba tana zaro manyan jajayen idanunta kamar na dodanni.  Ta-?urya nasan zaki iya, sai dai akwai wani babban ?alubale dake tunkaro cikar nasararki ta biyu, kuma gab yake da cimmawa, idan baki gaggauta datsesa ba, zakiyi biyu babu .
? ? ?A razane ta Wago tana kallonta cikeda bushewar zuciya, sai kuma ta maida kanta da sauri ta rissinar  A gafarceni Uwa, a kawar da ko miye mai son yima cikar burina kutse. Na rantse da ALLAH daya halicceni, koda cikin yankin ahalina ne bana bu?atar numfashinsa Uwa!! .
? ?? Dariya ta sake ?yal?yalewa da shi sai kuma ta gimtse fuska. Kanta ta shiga girgiza mata da dukkan isa.  Ta-?urya wannan karon akwai banbanci da koyaushe, dama na taSa faWa miki bayan cikar nasararki ta farko akwai ?alubale dana gani akan cikar ta biyu, sai dai ba'a buWe mun komaiba a wancan lokacin, alamar haka na nuna ?arfin taurarin mai yun?urin, amma a daren jiya dana tsananta bincike akan mafarkinki na gano wani yanki da ?yar. ?ar shilar suda na ?o?arin yin cara irin ta gawurtattun zakaru a kunnen bututu da taimakon wata zuciya mai son kusantar tata.
? ??  A taimakeni a kawar mun dasu gaba Wayansu Uwa. Ko a bani damar kawar da su da kaina . ? ?
? ?  Hhhhhhh!!!! ?addarar ?ar shilar bata mutuwa bace cikin sau?i. Tana kuma da ?arfin taurarin da zata iya cin nasarar dusashe naki .
? ? ? ? Bugawar da ?irjinta yayi ta zata zuciyarta ce zata fito ta bakinta dan tsabar razana. Ta kafeta da idanu cikin wani irin yanayi mai wahalar fassara. Sai kuma tai saurin maida kanta ?asa ta rissinar tana faWin,  A gafarceni Uwa .
? ?? Wani irin kakkauran numfashi mai cike da gargaWi tsohuwar taja, cike da ?asaita tana yamutse mummunar fuskarta ta cigaba da faWin,  Zamu iya samun mafita sai dai akwai ruWani a cikinta. Har zuwa yanzu kuma ban samu buWewar ruWanin ba kai tsaye. Dan haka kina da zaSi biyu. Kodai ki ?ara yin duk yanda zakiyi igiya ta ?ullu tsakanin Malik-alMuluk da wannan ?ar shila muyi duk yanda zamuyi tazama cikamakin aikinmu na biyu, ko kuma ki barta ta cimma burinta....... ? ? ??
? ? ? ? ?? Idanunta da suka kaWa jajur tai ?o?arin Wagowa, sai dai ta maidasu da sauri zuwa ?asa.  Uwa amma kin faWamin na cinye jarabawa ta biyu da zarar ya aura cika makin matansa shine matakan nasarata, yanzu haka akwai su su biyu da suka rage Wauke da aurensa a kansu, zasu mi?asu garesa a karshen watannin nan kamar yanda na samu tabbaci. Taya zamu shigo da wata bayan aikin ya cika. A yanzu ya rage kawai samun cikar burina na ?arshe ne a kansa. Miye dalilin shigowar wannan yarinyar abinda bai shafeta ba? Mizai hana ai mata wani hukuncin daya dace da ita?...
? ? ??Hannu ta Waga mata cikin tarar numfashi da ?ar hasala-hasala, da kakkausar murya tana mai nunata da Wanyatsa  Amma har yanzu ban sanar dake wadda ta dace ba, kuma damun san cutarwace na umarninmu gareki bazamu ce ta shigo ba .
? ?  Hakane Uwa, a gafarce ni. Sai dai Mahaifiyar Zak....... .
Ta faWa da alamun shiga tashin hankali mai girma, amma kallon da Uwa ta watso amata ya hanata ?arasawa.
? ? ? ?? Bata tanka mata ba, sai dai yanayinta ya nuna a hasale take, dan cikin kaushin murya da zunzurutun jin zafi ta kaWa ?ahon hanunta mai kama da kwarkwaron gidan dodon koWi. A take haske ya gilma, sai ga farar takarda a hanunta.  ?ar shila burinta shine Waukar fansa, domin biyu a cikin masu Wakin Malik-alMuluk da suka shuWe jininta ne. Burinta shine bin kadin jininsu ta hanyar bayyanama duniya ko kawar da shi. Bayyanawar tata kafin cikar burinki faWuwarki ne, a yanzu haka kuma ta haWu da mai taimaka matan harma sun gama magana .
? ? ? Sosai zuciyarta ta ?ara harzu?owa.?Amma sai batace komai ba saboda ganin Uwa a hasale take da ita. Cikin yin ?ara ?asa da kai? tace,  Da ace bayan cikar burina ne kauWi da ?udirin Waukar fansar wannan yarinya ya shigo haske ne ga cikar burina. Dan zata ?arasamin aikin ?arshe da zanyi. Amma tunda ta shigo a tsakkiyar labarina do??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????lene ta fuskanci hukuncin daya dace da ita. Idan ita bazata mutun ba shi a kawar min da shi mana Uwa .
?? ??  Hakan mai sau?i ne, sai dai shima babu bu?atar mutuwarsa, dan zai iya mana amfani a gaba. Sannan shi rabata da shi shine mafi ?ololuwar hukuncinsa. Dan haka daga nan zuwa safiyar kowace juma'a ta ?arshen shekarar nan ki tabbatar an zarga igiya tsakaninta da Malik-alMuluk, a dakatar da kai masa matan da suka rage a kaita garesa bayan tarewa, dan da ita zamu cigaba da amfani har samuwar cikar burinmu ga kowa!!.
? ? ? Da sauri ta Wago kai jin muryar nayin nesa da ita, sai dai kafin ta iya furta wani abu Uwa ta Sace daga Wakin tamkar guntun girgijen hadari a tsakkiyar fararen gizagizai. Zumbur ta mi?e tana mai dafe kanta dake sara mata, wani irin tu?u?i da ?ai?ayin mai zafafa ruhi zuciyarta ke mata. Sai dai sanin wacece Uwa ya sata jin Wan sassauci kaWan, amma ruWani mai Wauke da abubuwa masu matu?ar yawan gaske da fassarasu a Wauka shekara dubu bisa dubu ba'a kammala ba na neman danne wancan ?warin gwiwar. Taya ruhin ?a?an sarakunan ?asar Ruman basu bata matsala ba sai ?ar talakawa ?as?antattu? Dolene yarinyar nan ta WanWana kuWarta na hukuncin shiga gonar daba tata ba ?warai da gaske, sai tayi wasa da ita a tsakkiyar titi wasa irin na Sera a hanun mage, dan ko ita Malikat bata isaba.....

? ? ? (Tofa masu karatu, ita kuma wannan wacece ita? Iffah fa ta taro match Win da babu players. Kumuje zuwa dai muga yaya wasan zai kaya=ش?
? ? ? ?? &__________________&

? ? ? *_IFFAH_*

? ? ? ? ?? A Wan firgice ta buWe idanunta tare da tura hannu ?ar?ashin filon data tada kai ta sake danne wayar dake faman Surari cike da tsoron kar Ummu ta jiyo, dan tasan Babiy da Hanash basa gidan. Ajiyar zuciya ta sauke mai matu?ar ?arfi da zaro wayar, cikin rawar jiki ta dannata a silent. Tamkar jira kiran ya sake shigowa kuwa. Idanunta masu matu?ar girma da haske ta waro sosai ganin mai kiran, ai batama bari tayi ring na biyu ba taa Waga tare da kaiwa kunnenta tana direwa a gadon.
? ?  Kina jina? .
Aka faWa daga can. Kanta ta jinjina masa tamkar tana gabansa dai-dai tana le?awa tsakar gidansu. Daga can gefen da Babiy ke kiwon tsuntsaye ta hango Ummu, dan haka ta sauke ajiyar numfashi da fara magana cikin raWa.
? ??  Ina jinka Sir! Ta samu ne? .
 Babu lokacin dogon magana Iffah, kiyi ?o?ari daga nan zuwa awa Waya ki sameni, dan kuwa mun tsinta dami a kala Ajmal ya shigo Ruman, kuma a yanzu haka mun gama magana da shi sai dai ban sanar masa ainahin zancen ba, ya kuma bu?aci haWuwa dake.....
? ??  Ya ALLAH! Alhmdllhi. Naji daWi matu?a wlhy Sir. Insha ALLAHU duk yanda zanyi kuwa zan fito ka saurare ni .
? ? ? ??  Okay .
? ?? Kawai ya faWa yana mai yanke wayar. Itama shiri ta shiga faman yi a gaggauce, tare da tattare takardun dukkan bayanai data tattara waje Waya. Bakinta Wauke da addu'ar samun nasarar amincewar Ummu abisa ?aryar data shirya akan fitar ta? fito. Daga inda Ummu take tako zubomata ido na alamar tuhuma. Gareta ta ?arasa cikin danne komai da karsashin data aro.  Ummu kiran gaggawa na samu daga Ikram. Inaga dai abinda muka jima muna jirane ya fito .
? ? ? ? ?  Amma Iffah....
? ?  Ummu dan ALLAH kar kice a'a . Iffah tai saurin tarar numfashinta cike da marairaicewa.  Ni ba hanaki zanyiba, sai dai wannan yawan fitar taki a kwanakin nan bana zuwa makaranta ba ya fara damuna Iffah. Shin kin manta halin da muka shiga da wanda zamu iya shiga a yanzu? Ina jin tsoro wlhy, matu?ar tsoro a duk sanda kika fita koda makaranta ne .
? ?? Sosai tausayin Ummu ya sake mamaye zuciyar Iffah, ta haWiye hawayen da suka taru mata a ido tana ?a?aro murmushi.  Insha ALLAHU Ummu babu abinda zai faru, wanda ya farun ma a baya bazamu taSa mu yafe ba. Fita ta kuma ta daina baki tsoro, tunda kinga duk sanda zan fitan ina suturta dukkan jikina .
? ?  Shike nan ALLAH ya tsareki, dan ALLAH kiyi maza ki dawo kafin Abbin ku ya dawo gidan nan ko Wan uwanki .
? ??  Insha ALLAHU Ummuna . Iffah ta faWa tana rungumeta. Shafa kanta Ummu tai tana murmushin ?arfin hali itama, dan ba wani zuciyarta ta samu nutsuwa bane ita dai, ta bartane kawai saboda tace fitar ta shafi karatunta. Amma zata cigaba da rakata da addu'a harta dawo.........
'


*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*


_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login