Showing 81001 words to 84000 words out of 160450 words

Chapter 28 - LOKACI BAI KURE BA COMPLETE

M SHAKUR   

01 Oct 2025

125

banso ta batamin Salma Momma tadanyi shiru ganin yanda Salim ke kallonta yasa taji gwara tafitomai a mutum tace  kaga Salim nasan sojoji nasan yanda kuke mata daya daman sukan muku kadan i get that, bazan hanaka mata biyun ba but why not karabu da Safeerah tunda ba matar arziki bace ga Salma nan gabanka, innocent yarinya, very pretty saika aureta ita taje anabiyu wani kallon Momma yayi, is taking a lot from him dabai daura mata mari ba he hates nonsense ko gayamata kalamai masu zafi hakan yasa yamike tsaye yakalli kaninsa yace  let s go there s nothing to do here dasauri Auwal yamike shikuma yajuya zai wuce Momma tace  ka zabi zama da karuw& & ..  Kubura! Salim yajuyo yakira Momma da kakkausan murya mai zafi idanunsa sun chanza launi hardly kake gane ransa yabaci but today is was obvious! Ran Salim yabaci, da hannu yanuna Momma yace  mind your language whenever kike magana akan iyalan gidan Salim! Dakin har amsa deep husky voice nasa yake, Momma na kallonsa sosai hakama Salma dashi kansa Shamsu da gabansa ke faduwa! Sassauta murya yayi yace  be very careful! This is my warning! Yana fadi yajuya yafice Auwal yabisa abaya suka shiga mota Auwal yaja motan sukabar gidan, bini bini yana tuki yana satan kallon yayansa da idanunsa ke alumshe shi yasan ransa abace yake, maida kansa kan hanya yayi ahankali yace  Yaya I am 100% sure sheri kawai sukema Safeerah, cus rannan da Shamsu yakawota office dina the little 2min dasukayi I was able to understand they hated the girl, basason cigabanta, so kake kabar Safeerah ka auri tata yar baki yabude kadan yace  take me to my house .

Gidan barrack yawuce ya shiga yana duba komi cleaners ne agidan suna kara cleaning komi the interiors is beautiful Ya Allah, he spent money, he just wanna keep her here cus he loves yanada wife a barrack cus he s always here for work and other things unless basa Abuja, also those crazy family members nasu baiso suna zuwamai gida anyhow ko kashigo barrack babu wanda ya isa yashigo this particular estate nasu sai da izininsa, but nan gaba zatabar nan, gaidashi ma aikatan sukayi ya amsasu yawuce sama first dakin dake kusa da nata ya shiga dakin Waleed kaman akasan waje asalim children room anyi fenti har POP sama na space da astronaut ga bed nasa mai kyau an gyara ga shoe rag yazubama yaron shoes na banmamamki ga wani babban basket na toys cars Superman menene menen babu wanda babu aciki fitowa yayi yarufe kofa yashiga dakin Safeerah it looks so feminine yayi kyau sosai maida kofan yayi yawuce dakinsa shima yayi kyau zama yayi kafin yatashi ya chanza kaya zuwa na sojoji yatafi office.


Ahankali ta tashi zaune daga gadon takasa bacci Yasmeen dake bacci ta kalla dan hasken bayi na lekowa dakin kaman Yasmeen ne bata rufo bayin ba, data rufe idanunta tunani ke zuwa ranta takasa natsuwa, she s super worried, all this while da aka daura aurenta bata damu ba yanzu ne datasan for sure gobe zata tare gidan wani takeji gabanta na faduwa sosai, bala in tsoron aure take, har kasan ranta bataso takara sake aure ba, situation na iyayenta shine ya chanza mata lissafi, even though Salim seems like a good Man, he s taking care of parents nata, kayan kadai dayama _u Mama dazasu saka yau abin kallo ne, danta komi shike musu yanzu that doesn t mean tana sonshi, she don t feel anything about him, koda yake ko auren farko ma hakane, tana ganin yanda Yasmeen ke soyayya da saura yarinya iya baya tabayiba, ta wahala agidan Abbati sosai what is she made the wrong choice data karbi gidan mutumin nan iyayenta na zama aciki? Wat if yazo yanacin ubanta yana dukanta agidansa gasa soja iyayenta basu da karfin kwatota, gashi tanada kishiya budurwa ba kaman ita bazawara ba, she feels shima kawai ya aureta ne in form na taimako tunda ta taimakesa ada bawai dan so ba cus matarsa tafita komi ga kyau kaman balarabiya, shiru tayi, tasauke ijiyan zuciya zata iya daukan duk wani wahalan duniya as long as iyayenta and Waleed are fine, as long as bazai cutar da Waleed ba, bazai kori Waleed daga gidansa daga bayaba yace shiba ubansa bane she is fine, in sha Allah zata zama wani abu zata tara kudi incase of rannan da zai kore Waleed ko wani abu makamancim haka tasami dan kudin da zata kama gida tasa iyayenta
Ijiyan zuciya ta sauke gabanta sai faduwa take tana tuna abunda Abbati yamata dahar tai ciki yanzu shima wannan haka zaimata? Bata taba jin abu mai zafi kaman shi ba, anmata CS haihuwan Waleed but CS din baimata zafi ba kaman yanda tarayya da Abbati yamata zafi duka zagi da mari babu wanda baya mata idan yanayi dan dama abuge yake nemanta babu randa baya shaye shaye sosai gabanta ke fadi cus that s the only thing datamafi tsoro shi sex din is painful she hates it, how is this marraige going to be? Bazata iya maganan nan da Mama ko Baba ba bataso tasa damuwa aransu but she is worried, sauka daga gadon tayi ahankali tawuce bayi alwala tayo tafito tadauki hijab tahau sallan dare har asuba bata runtsa ba addu o i take.
Zuwa dakinsu Mama tayi da asuba dan tadasu tana bude kofa taganta zaune saita tsareta da idanu kawai tagane yarinyar batai bacci ba, tahowa ciki tayi ta duka gefenta tace  meke damunki? Murmushi ta kakalo tace  bakomi Mama shiru Mama tayi tace  bazaki gayamin gaskiya ba ? Baki tabude zatai magana sai maganar ta makale ta lumshe idanu da sauri tana hana kanta kuka wlh kawai tsoro takeji, abakin gadon Mama ta zauna saita kama kanta rungumeta Safeera tayi hawaye na zubomata tace  Mama gabana faduwa yake tsoro nakeji, wlh banson auren Mama, banso natafi nabarku, ya barni anan na zauna daku sosai taba Mama tausayi, Safeerah is just a small girl da all she needs is parents dinta around this age suna kula da ita banda condition mema zaisa amata aure at 16, wani mara tarbiya ya wulakanta mata rayuwa and dumped her da ciki, bayanta Mama ta shafa tace  shiiiii ya isa, dazaran kinji gabanki na faduwa ki dinga kiran sunnan Allah, as long as kin rike Allah bazai tabasa kiji kunya ba Safeerah, kin muzantu, an cuceki and wulakantaki an azabatar dake a aurenki na farko, I believe Salim zai kasance lullubi da rahama agareki sai nan gaba zaki gane kika zauna dashi, kiyakuri I know sabida mu kika fadawa aure haka amman Allah zai sakanya miki da alkhairi for wat you did for us kinji, stop worrying ina raye fa, and zan biki da addu a kema kidage da addu a kinji gyadama Mama kai tayi, Mama tacirota daga jikinta ta share mata fuska tace  maza ki gama kifito amiki gyaran jiki kisha magungunan ki, su Ummi zasu kai kayayyakin ki, da magungunan gidanki anjima ki dinga sha kullum kinji sune mutumcin diya mace gyadama Mama kai tayi, Mama ta mike tana tada Yasmeen da tai salla sannan tawuce tafita.

Kiri kiri Safeerah kinyin makeup tayi abun kunya yabata saikace wata budurwa amman tasa lace mai kyau da gold awuya kunne zobe da hannu, hannayenta da kafa sunsha lalli da akamata jiya, Waleed ma yayi kyau an samai shaddar da Salim ya dinkamai da hula da malummalum daidai jikinsa da takalmi sai kallon Waleed take kaman zata hadiyeshi tana son Waleed sama da yanda takeson ranta, su Salma da Momma sunzo Momma tahade rai sosai babu wasu outsiders haka, babu kuma mutane dayawa, ga abinci da chefs sukayi makota sun shigo anata sa alkhairi babu wani hayaniya hira kawai ake while Safeerah na sama da su Salma da Yasmeen, Safeerah duktai zuru zuru kaman auren farko, Salma taci uban makeup ranta fess sai dadi takeji har Yasmeen na tambayanta murnan metake haka tace ina ruwanta.
Wajajen asir makota suka watse and sun ba Mama gifts wlh some money, Baba shima yadawo gida abunsa yarage yisu yisu suka rage sai hira ake kowa yayi kyau, dayake kofan falo abude sabida baki nabarku shigowa falon wata hamshakiyan mata tayi tana sanye da lafiyayyen lace bayanta wani matashi ne da akalla he will be 33yrs yana sanye da jean crazy dayake a yayyage dawata shirt da botura uku na kasa kawai ya rufe sauran na saman a bude babu ko singlet a jikinsa yasa bakin glass a idanunsa bakinsa da cingam yana tauna doss doss doss kaman mace, dudda akwai glasses a idanunsa but kansa na kallon Waleed dake rike da ball a tsakiyan dakin ganin baki yasa ya tsaya yana kallonsu kaman yaga tv yana sanye da milk gizna mai kyau ba babban rigan a jikinsa just jumper yarage.

Kaman yanda matar tagaba itama ke kallon Waleed sosai dukansu babu wanda yayi sallama, mikewa tsaye Baba yayi, haka ma Mama tana kallonsa sai Zainabu, itakuma Momma nadaga zaune tana kallonsa tai wani smirking tareda daura kafa daya kan daya ta kada, gabaki daya fara a da walwalan Baba bacewa yayi daga fuskansa kaman ba Baba ba, babu walwala akan fuskansa yace  meyakawo ku gidana? Waya baku izinin shigowa gidana ? Taba baki matar tayi ta karaso cikin falon tazauna kan kujera tana kallon Waleed, shikuma guy din yakai hannu yazare glass din idanunsa, idanunsa sundanyi ja kadan sun kankance kaman wanda yayi shaye shaye yataho yana bouncing irin na niggas dinnan yazo gaban Waleed yaduka tareda yin murmushi yace  Hey Yhoo Kiddo Wassup Dan turo baki Waleed yayi ganin strange faces yayi rau da fuska zai fashe da kuka Baba yasa hannu yadaga Waleed ya daukesa cikin daka tsawa yace  nace mekazo yi agidana Abbati! Meya kawoka ? Mikewa tsaye Abbati yayi yakai hannu yana goge fuskansa yana yatsine fuska yace  damn! Kadinga matsawa baya idan zakai magana wannan yawu haka ran Zainabu baci yayi takalli matan dake zaune ta daura kafa daya kan daya tace  Hadiza meya kawoku gidan nan? Tayaya ma kukasan gidan nan? Idan da kunyi anyi hakuri not anymore talk to yaron nan yakama kansa yasan inda yake karyace zai raina Malam agidansa hannuwa Abbati yadaga sama yana daurewa a kunnensa yace  enough enough enough! I hate ihu guys! Yafadi yana yatsine fuska, Baba yace  get out of this house! Wani kallo yama Baba yanuna kansa yace  you think I enjoy being here?! Common nazo na karbi wat belongs to me ne? D ana nazo karba! Ba Baba kadai ba hatta Mama da Zainabu saida gabansu ya buga dim! Hadiza na daga zaune tace  before kufara this and that kome kuka kashe akan Waleed tundaga kan cikinsa, har haihuwa, har zuwa yau arubuta mana zamu biya but munzo karban danmu! Kuma babu uban wanda ya isa yahana tunda dai d a na Abbati ne, shi yayi cikinsa, shikeda hakki akan Waleed ba wani ba wani yar dariya Mama tayi takalli Hadiza tace  did you just say hakki?! Ku kunsan me hakki? Baku da d a a hannunmu, Waleed dan Safeerah ne kadai not dan Abbati bushewa da dariya Abbati yayi sosai yana tafi yana dan tangadi yarike cikinsa yanayi kafin chan yayi shiru yakalli Mama yace  idan kin isa yau ki hanani daukan d ana! Yajuya ya kalli Baba yamika hannunsa yayi murmushi yace  zonan Kiddo? Come to Pops Lamo Waleed yayi jikin Baba cus Abbati looks creepy and wired a idanunsa, haushi ne yakama Abbati dan baida hakuri yanuna Waleed da yatsa yana dakamasa tsawa da saida gidan ya amsa yace  kai zonan nace, ina wasa dakai ne! Dan Mace kawai! Fashewa da kuka Waleed yayi yakankame Baba atsorace Baba yace  wai mehaka Abb& .. fizge Waleed Abbati yayi daga hannun Baba yana hankada Baba yafadi haryana bugewa da table cus ya shammacesa daidai Safeerah na saukowa dan taji tsawan Baba dazu Salma da Yasmeen biye da ita while Mama da Mom na daga Baba up dasauri Momma tamike tace  Abbati mehaka? Ko yaronka kazo karba we do it in a civil way why are you being aggressive jibi yanda ka kayar da Shu ibu chak Safeerah ta tsaya tama kasa motsi jikinta kawai yahau rawa tana kallon yanda Waleed ke kuka yana ihu a hannun Abbati yana turesa yanaso ya sauka yagudu amman Abbati yarikesa gam Waleed yakasa motsi, Hadiza ta tashi tace  muje dasauri Mama tasaki Baba tamike kafan Waleed tarike tace  saidai kaje damu gabaki daya ture Mama yayi Safeerah tace  Abbati! Chak yajuyo, hada idanu yayi da Safeerah hakanan gabansa yawani irin fadi dummm! Tana sanye da wani black and red lace Ya Allah! Yamata kyau na bala i, tayafa red veil babu makeup a fuskanta but wlh ka kalleta saika kara kallo sabida yanda tai kyau da baitaba sani tanada shi ba, sak Amarya lallenta yayi kyau na bala i, lumshe idanu yayi yana tuna all his moments da ita, takara girma, lokacin nan kirgan dangi ne a kirjinta but look at how sexy and cute she is now, Safeerah is the only virgin daya taba ci arayuwan sa and he enjoy those moment yaso ya more da ita but takama tai ciki, sosai gabansa ke faduwa daya rasa dalili amman yadaure yahade rai kaman zaki yana kallonta, tahowa Safeerah tashigayi dudda tana tsoronsa da shakkan sa but akan danta she can do anything Wallahi a duniyan nan, tsayawa tayi agabansa tana kallon kwayan idanunsa, idanunta sun kada sunyi jaaaa tace  where do you think you are taking my Son toh? Kallon Safeerah Abbati yayi yakara kallo Safeerah dake fitsari a wando lokacin nan tsabagen tsoronsa ne ke ke kallonsa right into his eyes tana mai magana haka, cikin wani kaskantaccen look daya mata yace  who do you think you re dazaki questioning Abbati?  I am Waleed s mother! Tafadi azafafe, tace  ka ijiyemin d ana ka wuce kabar gidan nan cus you are not welcome Waleed daya matse gam yana kuka yace  Ummyyyyy comeeee, zoooo matso wa tayi dab da Abbati kaman mahaukaciya dan kukan Waleed yakara haukatata tace  nace ka ijiyemin d ana! Bakaga kuka yake ba he is afraid of you, ka ijiyemin d ana Malam hannu Abbati yakai akufule zai kaimata duka sabida yanda yaga tanamai tsiwa Baba yataso azuciye yarike hannunsa gam yana kallonsa ransa abace yace  as long as inada rai kagama taba lafiyan y ata! Ka ijiye mata danta Safeerah da hawaye na gab da zubomata ganin yanda Waleed ke kuka ya matse yaron he is hurting him tace  nace ka ijiyesa you re hurting him, drop my son and get out! Wani murmushi Abbati yayi yasake matse Waleed da gangan kaman zai kashesa yace  yaron nan d ana ne nina miki cikinsa kika haifesa, my blood runs in his veins, my DNA is all over him, ko a musulunci nafiki iko da Waleed! So listen very well to wat I m about to say to you Cikin kakkausan murya yace  wat ever kika kashe akan Waleed give me the bill I can even pay you here just sabida nafita daga hakkin ki, but as long as I am alife d ana bazaije gidan wani yayi rayuwa ba! Wani bazai tufatar da d ana ba! Ko wani ya ciyar da d ana ba, you have two choice kodai kije kiyi zaman aurenki Waleed natare dani! Koki fasa auren nan muyi aure mu raini yaronmu tare  Allah ya kyauta! Komai kama dakai bazan taba aura ba balle kai Abbati! Banama makiyini fatan aurenka balle ni! You re nobody dazaka gayamin mezanyi and Waleed bazai taba zama dakai ba, baka isa karabani da Waleed ba! Mutuwa kadai ne zata iya rabani da yaron nan not you, not your family, not anybody???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? aduniyan nan! Sosai yake kallonta wani wutan so hakanan yaji yana fizgansa ta mahaukacin masa kyau and she smells magical, gyadamata kafada yayi yace  okay then you make your decision loud and clear yajuya zai wuce azuciye Safeerah tarikeshi daidai kuka na zuwan mata hankalinta na tashi sosai tace  wlh bazaka tafi da d ana ba shima Waleed yakara rushewa da kuka ganin mamansa na kuka wucewa waje abinta Hadiza tayi ta kunna mota tai reverse abinta, Zainabu ta kalli Momma tace  wai bazaki magana ba Yaya kene kikasan mutanen nan, Hadiza ba kawarki bace Momma cikin fada tace  nace me? Ko kotu akaje shine uban Waleed kuma Safeerah bata isa ta rabasa da dansa ba wlh, yanda takeda iko akan Waleed haka yakeda shi they just need to find solution cikin kuka sosai Safeerah tace  baida iko akan Waleed da bayaso! Cikin dayaso ya hallaka! Yamin dukan bala i just sabida cikin yafita, ya tsani cikin ya tsani Waleed an kirasa an gayamasa na haihu yace ba nasa bane bayason yara, why is he coming back for him all of a sudden now?, idan kaga kafita da Waleed a gidan nan yau saidai idan na mutu! Abbati baiyi wata wata ba bayan hannunsa yakai gefen wuyan Safeerah yamata wani mummunan duka dayasa kowa na dakin saida yayi ihu Safeerah tai baya a sume Mama na tareta, Baba ya chakumesa yace  Abbati! Hankade Baba yayi da kyau Baba yafado kan Mama, Zainabu, Yasmeen da Salma dake kan Safeerah data sume tsabagen yanda Abbati ya watsar dashi yayi kofa yafice da sauri da Waleed dake kuka yashiga mota Hadiza tajasu sukabar estate din Baba har jiri jiri yake gani, Mom takamasa ya zauna Yasmeen na kawo ruwa ana watsama Safeerah amman shiru bata farfado ba, ahankali Baba yace 

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login