Showing 36001 words to 39000 words out of 160450 words

Chapter 13 - LOKACI BAI KURE BA COMPLETE

M SHAKUR   

01 Oct 2025

109

nauyi ahankali tace  uhmm nagode! Thank you for everything! Dama uhmmm idan Waleed yatashi zamu tafi ? Idanunsa na kanta bayako kyaftasu har yanzu yace  ina zakuje? Dago idanunta tayi ta kalleshi suka hada ido zata sauke idanunta strictly yace  don t try it! Kasa maida idanun kasa tayi ta tsaresa da kallo kirjinta nawani irin bugawa none stop his eyes are wild Ya Allah! Sai kawai lips nata yahau rawa takasa daina kallonsa takuma kasa magana this is the first eye contact dasuke having tunda ta sanshi dayakai na kusan 30seconds, he noticed saiya kara tausasa murya yace  I said ina zaku Safeerah! ? Wani irin blinking idanunta suka shiga yi he s too much for her eyes kaman yamata asiri kasa karya tayi tace  nim& ..ma ban sani ba! idanunta suka cicciko da hawaye sai kawai ya dauke kansa, kaman yasaki kuruwanta wani ijiyan zuciya ta sauke itama ta sauke kanta kasa, ahankali yace  okay yanuna mata table din yace  have breakfast, take drugs that are here sai ku shirya, call me when you re ready to go gyadamai kai tayi ahankali tace  thank you wucewa yayi wajen kofa yasa hannu yabude yafice saikuma yajuyo hada ido sukayi dasauri ta sauke kanta kasa, ahankali yace  zanje wajen Baba and talk to him you need to go back to your parents da sauri ta sake kallonsa sai kawai tafashe da kuka sosai tana goge fuskanta da bayan hannu batare datai magana ba, ya tsaya jimmm yana kallonta kafin yasa hannu yazare key tabaya yajawo kofan yasa key cus ya lura gidansu ne batason komawa something is definitely going on, yanda yace zaije yaga Babanta karyazo kafin yadawo tagudu tabar nan what if tafada in the wrong hands ga yaro karami tareda ita, dasauri tai wajen window tana kuka taga yaja mota yabar wajen.

Rolex din hannunsa ya kalla is 11AM, he needs to help his helper whatever it takes, yarinyar that helped him a death row he will go to the end of the world just to see that smile in her face not cry or sorrows. Cikin 20min yakai kofar gidansu yakashe motan wuraren 11:30, babu kowa a kofar gidan yayi jim sai yafito a natse yazo wajen yakai hannunsa ahankali yayi knocking ya dakata shiru, sake knocking yayi na biyu ya tsaya shima shiru, yakai hannunsa yasake knocking akaro na uku, karan bude kofa yaji hakan yasa yadan koma baya kadan sai yaga an dan daga wani marfin lekowa yaga idanu hakan yasa yace  Assalamu Alaykum ganin ba yan gidansu bane yasa anatse Mama da duk tayi wani iri tabude kofa tafito kallo daya Salim yamata yagane itane mahaifiyar Safeerah, Safeerah really looks like her but tanada haske Baba though Baba yafita haske, Mama kuma baka ce, saisa Safeerah is not black she s caramel, anatse yadan duka cikeda kunya dakuma girmamawa yace  ina kwana calmly Mama tace  lafiya lau wa kake nema? Dagowa yayi yakalli Mama dake kallonsa ganin bata sansa ba calmly yace  Abba nake nema, Baban Safeerah! Dasauri Mama takara kallonsa tana tunani dan unguwan nan ne? Tasan Baba na gaisawa da yan layin ko zaman dayake awaje saisa ma yake dan samin kudi sukan masa kyauta once in a while, ahankali tace  bayajin dadi ne yana kwance, waza a gayamasa ? Dasauri Salim yace  meke damunsa Mama ? Kallonsa Mama tayi da kyau jin yanda yakirata Mama, hakan yasa Mama tace  wayekai bawan Allah? Dan shiru yayi kafin ahankali yace  sunana Salim nine Ogan Safeerah a inda take aiki, jiya tazo company mu da daddare da signs na duka toh daman maganan nazo yima Abba kenan, zan iya dubasa Mama in yaso sai nayi maganan dake sosai Mama ke kallonsa tanajin wani natsuwa dashi especially natsuwansa sannan ba yaro bane irin su Shamsu, babba ne kuma kamili wanda yasan kansa, ganin batai magana ba yasa ahankali yace  Abba yasanni mun hadu so daya dan ijiyan zuciya Mama ta sauke, sannin Momma bata nan hakama Shamsu Salma ce kadai agidan kuma tasan tana bacci war haka yasa tace  shigo Bismillah tajuya yabi bayanta a natse, ga mamakinsa dakin dake gefen gate na masu gadi yaga sunyi a babban gida haka da base on the little info he daya samu jiya this house na yayar Abba ne cus ance Shamsu yakawota yaron sister kenan, and mahaifin Shamsu is tsohon gwamnan Jigawa he s late, why will her own blood brother be living a side na masu gadi?
Bude kofan Mama tayi tashiga ciki saiya tsaya agaban dakin, juyowa Mama tayi tace  shigo ahankali ya shiga dan karamin falo ne ga yar katifa awajen dake a gyare tsaf ga ganamasgo da jakan school din Safeerah ke kai, ga gwangwnayen abincin Waleed a wajen sai few kayan wasan yara da ball, babu komi falon, dadduma Mama takawo ta shimfidamai ya zauna ahankali tace  bari nafito dashi tawuce ciki taduka gaban Baba da baya gane wanda ke kansa idanunsa ganin ya bace gaba daya, ahankali tace  Malam Malam motsi yayi yace  na am Mamana na dawo? Waleed fa ? Shiru Mama tayi tun jiya kawai Safeerah yake tambaya ahankali tace  kayi bako sunansa Salim, yace ka sansa shine Ogan Safeerah, kampaninsu Safeerah taje jiya dasauri ya yunkura zai tashi yakasa kamasa Mama tayi suka fito tazaunar dashi Baba yace  ina Safeerah Salim ? Ruwa Mama tasa a plate mai kyau pure water ta ijiye masa ta zauna gefen Baba, anatse Salim yace  ina kwana Abba da kyar Abba yace  lpy lau ina Mamana Salim ? Shiru Salim yayi he s feeling very sad seeing how sick Baba is yace  she is safe Abba, namaso nataho tareda ita nadawo da ita amman taki yarda, meya faru, waya daki Safeerah haka? One thing about Salim is bayida tsoro ko kadan kokuma irin kunyan nan da jin nauyi bai iyaba unless idan bai damu da abuba shi ba yaro bane he is here for something and he will sure do that.
Kafin Baba ya bada amsa Mama tace  rashin kunya tayi da dambe da dan sauri Baba yace  Salim kasan kowani family nada one or two issues haka, yar matsala aka samu jiya, one thing da Safeerah shine dan banzan zuciya ne da ita inhar aka tabani ko mahaifiyarta bata daurewa Baba yayi murmushin manya yace  Safeerah ta taso ita kadai bata da siblings so kwata kwata bata understanding cewa Yaya da kani can fight, that is basically abinda yafaru nasan nai magana da ita na lallabata zata dawo Mamana akwai rigima kam Masha Allahu Mama data kasa daurewa tace  Malam kasan dai koka lallaba ta tadawo yan gidan ba barinta zasuyi ba ko, itama kuma rasakunyan bakinta ba mutuwa zaiyi ba kasan dai Safeerah cikeda damuwa Baba yace  zan bawa Mama Kubra hakuri da yardan Allah zata barta ta& ..ta& t& . Hannunsa yadaura akirji kawai yayi baya Mama tace  Malam Malam dasauri Salim yatashi kama Baba yayi yarike yaji jikinsa zafi rau yace  he needs hospital Mama daukan Baba yayi yace  muje asibiti chak yadauki Baba, Mama da already tasa hijabi tabiyosa tasaka slippers fitowa sukayi daidai Salma na zuwa wajen tana sanye da Shedanun kayan bacci tawani kalli Salim dake dauke da Baba daga sama zuwa kasa tace  wa kuka kawo mana gida batare dakun nemi iznin Momma na ba? Wlh sainasa kuma takore ku kaman yanda takori Safeer& &  wani black kallo da Salim yamata yana saukowa daga few staircase dake wajen yasa tahadiye maganan ganin bata taba ganin hadaden guy irinsa ba damn he smells incredibly good, duk yawonta duniya bata tabajin kamshi mai dadi irin nasa ba, wuceta yayi yay gate yabude Mama tabisa itama Salma tabisu da sauri wata jeep urus tagani kofar gidansu aranta tace  who is this Man! A ina suka sanshi? Baba yasa abaya Mama ta zauna kusa dashi yazagayo ta gaba ya shiga yaja motan da gudu Baba yafara tari sosai tana wheezing yakama hannun Mama cikin wani kalan murya yace  ina Safeerah ? Cikin damuwa Mama tace  na shiga uku Malam meke damunka iyye? Malam why are you confuse, kaga calm down tana kampanin datake IT lafiyanta kalau Oganta ma shiyazo nemanka kunyi magana, Malam kadena magana kaji asibiti zamu cikin wani irin murya yace  ki rikemin Safeerah amana, ta wahala wannan mutumin yakusan kashemin y a! Mama Kubra ta cutarmin da yarinya amman bakomi akwai Allah akwai kuma rannan gobe kiyama, banso Safeerah takara wahala, agabana jiya an mari y ata, an doketa, an fasamata baki duk agabana, da Safeerah ta zauna inda za a cigaba da dukanta kaman jaka gwara na daukeku munje muyita bara a titi, kicemata nace tazo bazamu koma gidan ba, munbarsa, na yarda, bazan kara zama inda za a dinga zagin mahaifinta agabanta ba kinji, kucemata tadawo Mama na goge hawaye tace  zan gayamata kadena magana ya isa kaji, babu abinda zai sameka Malam yana wani nishi yace  ku saida kaya duka asaima Waleed abinc da kudin daidai sunkai wani military hospital nan da nan aka karbe Baba anan emergency akai ciki dashi nurse tace  Sir zoka cike form yakalli Mama dake kuka yace  muje Mama .
EPISODE 2?? 1??



Binsa Mama tayi jikinta yayi wani irin sanyi ganin condition na Baba, she s regretting dama ta tsaya tabar Safeerah tai haukan nan data kwakkwadeta, yanzu ga jikin Baba ya birkice ta ina zata fara idan Baba ya rasu? How? Cike komi tayi tamike musu sannan takama bakin hijabinta takai saman idanunta tadaura awajen wani huci tafarayi sai kawai Salim ya sauke kansa kasa cikeda tausayin Mama kana ganinta kasan tayi bottling so many things aranta but yau takasa, ahankali Salim yace  he will be fine Mama, babu abinda zai sami Baba da izinin Allah bakin hijabin tasa ta goge fuskanta tass tasaki hijabin she s very sad da jijiyan goshinta harya fito takada kai tace  nagode Salim muje he felt really bad ta wuce yana biye da ita har zuwa wajen dakin da Baba yake ta zauna a kujeran wajen tabuga tagumi tana kallon dakin gabanta faduwa kawai yake jijiyoyi na bayyana na fuskanta, hawaye suka sauko takara gogewa dasauri ita kadai tace  Safeerah bataji, bataji, bataji, yanzu abinda ta aikata wani fa ida ke tattare dashi? Saidai tashin hankali look at where Baban ta yake yanzu Mama tai shiru saikuma tajuyo takalli Salim da kyau ranta abace tace  tasan mahaifinta baida lafiya Salim mesa kome aka mata bazatai hakuri ba, eh? Kallon Mama yayi asanyaye she is really angry kana ganinta kasan she s feed up tace  Babanta baida kudi but muna rayuwan farin ciki da muna Kano, abu yafaru dayasa aka kona gidanmu bayan sunma Malam duka shine har yau baida lafiya, ga baya gani da kyau, nine nakira yayarsa Kubra wannan damuke gidanta na sanar da ita ga abinda ke faruwa haka ta aiko da kudi dubu dari da bamu dashi muka biya a asibiti aka dan bawa Baba taimako na gaggawa kafin drebanta ya iso yadaukemu muka dawo Abuja wajenta Mama tai shiru saikuma tafashe da kuka sosai Salim ya sauke kansa kasa, Mama tace  nasan the reason Safeerah ke all abubuwan datakeyi sabida she had enough, kullum tana ganin ana zagin iyayenta ana cimana mutunci between Kubra da yaranta but nasha gayamata ke haka masu kudi suke barinma yan Abuja, society yakoma wani iri da me kudi ake respecting banda talaka, yau da ace Malam na da idanu yana aiki nasan rashin mutuncin bazai taba kaiwa haka ba sabida yanada nasa yanada na rike iyalansa no ita takiji takasa ganewa shashashan kanason kaga fadan Safeerah azageni ko mahaifinta agabanta bata iya hadiyewa, kasan mi Safeerah tayi rannan kuwa ? Mama ta share fuska da hawaye ke kwance tace  rashin kunya da rashin da a ta sufafawa Yayar Babanta, wacce ta girmi mahaifinta fa sannan ta kama Salma da dambe, aiko Kubra tasa hannu da Salma suka bata kashi ban hanaba maganin mara kunya ai kenan fitsararriya har lokacin bai dago kai ya kalli Mama ba, Mama ta fuzar da iska tace  Salim kaga nasan waye Mama Kubra nasan metakeyi amman no matter what ba abune mai kyau karamin yaro ya kalli tsabaragen idanun babba yayi rashin kunya ba bahaka iyayenmu suka taso damu ba, Mama Kubra tamana abubuwa da dama ciki harda lalata rayuwan Safeerah kaga bayan dawowan mu Abuja dayake anata fama da kai Malam asibiti tace tagaji zata aurar da Safeerah ga mai kudi ayi amfani da kudin a kai Baba asibiti tagaji da kashe kudinta wai kudinta gadon yaranta kasan marigayi tsohon gwamnan jigawa take aure Mama ta hadiye wani abu awuya tace  ninasan harda jin haushi da tsanan Safeerah cewa sukayi wai abinda yafaru ita tajawo mana fitinan so she just wanted to teach the girl a lesson shine tasamo wani yaro mara tarbiya wai Abbati dan kawarta Malam na tsaka da ciwo tace aurar da Safeerah zatayi da ni da Malam babu wanda ya isa yace wani abu, haka ta aurar da yarmu agaban mu yabiya sadaki miliyan biyar Mama tafashe da kuka sosai kaman maganan was very personal for her kana goge fuskanta da bakin hijabi kana ganinta kasan she has been swallowing this pain aranta, Mama tace  yarinya ta was just a little girl ko zance basu tabayi da yaron ba banda so daya da aka nuna mana yaron atare da mu da ita muka gansa yazo wajen Mama Kubra bata taba kebewa da yaron sunyi wani magana ba, rannan da akakai Safeerah rannan takirani tana kuka yamata duka sosai tana nishi kaman zata rasu! Dunkule hannu Salim yayi ahankali kansa akasa har lokacin, Mama tace  haka na mike zumbur cikin daren nan hankalina tashe naje flat dinsu natadasu ina kuka wiwi na gayama Mama Kubra ga abinda Safeerah amman kiri kiri tamaidani shashaha tace idan banyi shiru nakoma na kwanta ba sai raina yabaci taso Safeerah nake kota lafiyan kaninta Mama tai shiru tana kallon tiles na floor na wajen looking lost a tunani tace  kullum rannan duniya for good 6months sai yaron nan yama y ata duka ba dare ba rana amman dukan yafi faruwa da daddare idan yayi shaye shaye yadawo haka watarana asibiti suka kiramu ita Mama Kubra wai Safeerah na asibiti batasan inda kanta yake ba mukaje muka tarar ya mata shegen duka yasaketa saki uku wai shi bayason haihuwa kuma tayi ciki, watanta daya a asibiti tana jinya babu ko sisinshi Mama Kubra tabiya komi Baba yaso yaje police station tahanasa wai haka yaran masu kudi suke, karmu damu tunda tanada ciki zai dawo menene menene ahaka yarinyar ta haihu Mama Kubra takirasa yace kar akara kiransa ba dansa bane, he is not ready for kids, mu mukai komi, ganin anata surutu shine last 2yrs tasaka yarinyar a school, shima Safeerah tayi kuka dan nursing takeso da kyar na lallabata ta tafi architecture din Safeerah nada taurin kai wani abun sabida mu take shiru ga fada, nadade banyi fushi da itaba amman abinda tayi jiyan nan bazan hakura dawuri ba saitaga fushina this time around&  Mama ta fuzar da iska. Dr neyafito yataho wajen Salim hakan yasa yamike tsaye yace  Dr Isa ? Anatse Dr yace  Alhamdulillah he s stable for now, BP sa yayi sama sosai any further damuwa can push him to having stroke, Madam ya akayi BP sa yayi raising haka yanada damuwa ne? Fuska Mama ta goge zatai magana Salim yace  zata iya shiga ta gansa?gyadamai kai Dr yayi yace  of course Mama Salim ya kalla yace  Mama je wajen Baba bayan nagama magana da Dr zanje nakawo Safeerah gyadamai kai tayi tace  toh nagode Salim, Allah ya sakamaka da mafificin alkhairi gyadama Mama kai kawai yayi tawuce ya shiga dakin shikuma yajera da Dr Isa dayace  who are this people Major? Why are you so ordinary dasu? Ina escort naka ? Wani kallo dayama Dr yasa Dr Isa ya kame tareda saramai yace  Sir! Wani banzan kallo yamai yace  give my patient your best I will be back yajuya yabar wajen yafita daga hospital din yashiga mota yaja.
EPISODE 2?? 2??





Bayan fitanshi tadade tsaye anan wajen dinning din kafin daga bisani ta wuce wajen ledan tabude kaman mai tsoro taga kayan yara sabbabbi riga da short masu bala in kyau da takalmi da pampers sai Chicco cream na yara da powder da soap, saikuma ledan maganin H-medix drugs ne aciki, tsayawa tayi tana kallon komi tana tunanin why is he so thoughtful? Yasan kome suke bukata kaman tabude baki ta rokeshi, wani bakin sealed leda dabata budeba tasa hannu ta dauka tabude ahankali ta ciro abinda ke ciki Saudi abayane mai kyau black ta warware dasauri size nata ne kuma 58, abayan smells kaman turaren sa it doesn t look like shi wannan yasayo a shago ne kaman daga gidansu ya dauko, maidawa da sauri tayi ta ijiye komi kawai saita wuce kitchen abincin daya zubar shida Waleed tasa broom ta share ta wanke bowl and spoon dayayi amfani dashi and keep everything a waje daya saita dawo falon tabude ledan, kayan Waleed kawai ta dauka da man shafan da sabulun tahada sauran abubuwan tamayar ledan chap itane zatasha magani, she hates magani ita chan magani shine ma abinda ke sata zazzabi, tawuce sama kawai daidai Waleed natashi daukansa tayi tawuce bayi ta tara ruwan zafi tamai wanka tafito ta shiryasa cikin kayan kuma daidai jikinshi yayi kyau tasamai takalmi sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login