Showing 93001 words to 96000 words out of 160450 words

Chapter 32 - LOKACI BAI KURE BA COMPLETE

M SHAKUR   

01 Oct 2025

116

misultuwa da baisan sanda jikinsa yafara bari ba yana vibrating kaman shine Safeerah, yana kokari yatura bakinsa cikin nata yakasa sabida yanda Safeerah ta datse bakinta gam bamata iya kukan danta kulle baki sai wani kalan nishi datakeyi kaman na mai asthma hawaye na fitowa daga idanunta jikinta yadauki shocking bata tabaji ana tabamata bombom hakaba sai yau, tana turesa da duka van hannaventa tanaso ta tashi tafita daga jikinsa takasa, shi kansa Salim saiyaji ma yana tausayinta yanda zuciyanta ke bugawa kaman wacce keda heart problem, mezai mata dazata dena tsoronsa hakane? Dazata dena shakkarsa? He wants her to be free with him, da kyar ya dakatar da kiss din danta hade baki ba amfani, yadan sassauta rikon daya mata hakan yasa ta tureshi da duka karfinta ta yunkuro ta tashi daga gadon tasauka sai kawai tai baya zata fadi tsabagen rashin karfi kaman kamata dayayi zuwa jikinsa ya hadiye mata dan karfin jiki da sauri Salim yataso yatareta kawai ta fado jikinsa kawai Safeerah tafashe da kuka ganin yasake riketa hankalinta yagama tashi, zata fizge kanta strictly Salim yace "shiiiii" shiru tayi tai lamo kaman marainiya amman abala'in furgice take hannayenta na rawa, adaburce cikin dan marayan voice tace "k....ka sakeni d....an Allah" lumshe idanu Salim yayi yana shakan kamshin datake kafin gently yasaketa tafita dagajikinsa tawuce da sauri tana layi tabude dakin tafito yabita da kallo ganin the way just body contact dashi yayi draining energy nata, kaf1n yakoma ya kwanta ahankali yana ruf da ciki ya fuzar da wata wahalalliyan iska shima what is wrong with him? Why is his body system changing all of a sudden? He thought yanada self control akan mace? Maransa da gabansa kawai ciwo suke masa, from the day akace an daura masa aure da ita in that parlor body system nasa kawai ya chanza, so many dreams, thoughts, imaginations babu wanda baya having, kaman ba soja ba, babu wani pain da bazai iya tolerating a duniya ba amman dan ciwon cikin nan sai yaji yana neman hallakasa, is he that bad da Safeerah ta kasa accepting nasa? Tashi zaune yayi yanaso yama tashi kozai iya zuwa kasa yadauko tea daga flask yasha ko zai rage masa jaraba yakasa, da kyar yatashi daga gadon yana dan duddukwwa bayi yafada yayafito daure da towel still having the boner kawai yaji zazzabi na neman rufesa yahau gadon yana fama.
Dakin Waleed Safeerah tashiga tamaida kofa tarufe da gudu ta tafi gadon wajen Waleed dudda gadon yarane but ya isheta tahau kawai tai hugging yaron gabanta na faduwa ta runtse idanunta da karfi tana tuna abinda just happened in few seconds dinnan a dakinsa, mesa jikinta ya mutu haka? She hates aure bataso takara yin wani aure ba, she is not ready for wani namiji yakara wannan abun mai azaban zafi da wahala da ita, daga tarewanta jiya mesa zai fara nemanta tun yanzu bazai ijiye alkwarinsa ba yace shi ba dan wannan ya aureta ba mesa yake nema? Wih wlh she is scared, she hates abun sosai baida dadi, babu komi cikinsa sai pain, sanda Abbati yasaketa the first thing da she was grateful for was dena abun cus wani zubin abun yamafi dana mata hankali kan dukandaga mata hankali kan dukan dazai mata, banda haka mema yake nema awajenta? Batada wannan confidence din yaganta ita data taba haihuwa, yaro duk yasha nonon ta menene menene, kawai kara rainata zaByi bayan yanada budurwan mata kyakkyawa, meyake nema awajenta bazawara? Mai da? With no so flat tummy, CS scar, saggy boobs masu manyan head da yaro yafito dasu waje? He will just use her ne darajanta yarage a idanunsa dan she has nothing to offer, jikinta na shaking har lokacin bata dawo daidai ba taji an danna door bell dawani irin sauri ta tashi zaune? Inama ta zubar da wayan sa daya bata? Kaman yana dakinsa, tashi tayi gabaki dayama ta mance gashinta abude kuma a sukurkuce tai staircase ta sauka kasa tana tunanin yanda zata bude kofan da bata iyaba amman dazu bayan yabata Waleed zai juya yafita wani botun taga yataba hakan yasa tazo ta window ta leka taga Yasmeen da Ummi dasauri ta danna botur din can ciki aiko saiga kofa yabudu Yasmeen na ganinta tai wani ihu ta rungumeta tace "ke kinga wani mahaukacin glowing da kyau dakika kara kuwa wai? From jiya zuwa yau, kinga yanda kikai kyau kuwa"? Dan tureta Safeerah tayi akunyace takalli Ummi takai hannunta ta karbi some abubuwa na hannunta tace "sannu da zuwa Ummi" "bani ruwa kishi nakeji wlh" rufo kofan tayi suna ijiye kaya suka zauna, Safeerah tawuce kitchen Yasmeen na binta while Zainabu tabisu da kallo fridge tabude tadauki tray tanasa ruwa da drinks ciki Yasmeen tace "kinga yanda gashinki yayi kyau dakika sakeshi kuwa kaman yar India"dasauri Safeerah ta taba kanta kunya yakamata tajuyo tafito Yasmeen tabiyota takawo ma Zainabu ruwan da lemu tace "Ummi akwai tuwo na zuba miki" girgixamata kai tayi tanashan ruwa tass ta shanye sannan tace "ke rabani muda ma muka kawo miki abinci akoshe nake, Yasmeen tashi ki tayata jejera abubuwan nan, amman wannan ciccibin rebanUmma mai gyara tace ki raba kashi biyar, kidinga cin kashi daya idan period yazo ki dakatar da ci.....
"juyawa Safeerah tayi ta kalli sama hakan yasa Zainabu takama baki kuma hakane fa taga motarsa saita tashi tace "kumuje kitchen mu jera miki muma daman yanzu zamu tafi" dasauri tace "dan Allah karku tafi yanzu wlh bacci yake, ku jira Waleed yatashi ku gansa" dasauri Zainabu tace "kinga ki barni maza su kaini ba mata ba" gwadamata yanda zatasha komi tayi tama hada mata wanda akace asha da milk taga sunada dano milk a fridge tabata tace "tamace karkiji komi ko al'ada yazo ita magungunan ta tsoka sukebi su zauna su ginu ba jini ba" Safeerah tasha tana sauke kai kasa sannan ta zauna kan daya daga cikin kujerun dake island tace "daman inaso namiki sallama gobe zamu koma katsina ni da Yasmeen" kallonta Safearah taui shankali lemmi Safeerah tayi ahankali, Ummi tace "Safeerah kinyi aure kinyi aure duk munasaran wannan gidanki ne na har abada, aure yariga ya dauru ina miki addu'a Allah yasa albarka a auren, Safeerah just because u are a victim of bad aure before baya nufin this is also a bad aure, you said alot jiya da banso nama tuna miki but dan adam always speak abinda ke zuciyansa a moment of tashin hankali, dan haka kinga zancen bakison auren nan, sabida su Baba kikayi kima zubar dashi and look at your husband kiga kyautan da Allah yamiki na sakayya, ki gode masa ba kiyi butulci ba, ki kiyaye hankinsa, sannan ina mai tuna miki da hakkokan mijinki dake kanki, dole kibi umarninsa, ya nemeki ga shimfidar sa dole ki amsa, mutane sukace MATAR SOJA soja ce! Dole ki zama jaruma" dakatar da maganan Mama tayi takalli Yasmeen tace "ke dalla bani wuri tafi falo" turo baki Yasmeen tayi tana murmushi tawuce falo, Mama ta tashi da kanta ta rufo kofan kitchendin tazo gaban Safeerah da kanta ke kasa tace "listen to me Safeerah sabida nasan mahaifiyarki bazata taba gayamiki this ba, aure ba wasan yara ake ba, duk wanda ya aureka ya aureka ne dan ya raya sunnar ma'aiki, mijinki ba yaro bane mutum ne dake neman shekaru arba'in, auren kalansu saika jure, Alhamdulillah shi kwanciya da miji da bakon abu ne awajenki, I believe komi zaizo miki da sauki kijure ki kama mijinki dan yamiki komi, bakisan yammata nawa ke addu'a Allah yasa ya kallesuba ya aura amman keya zaba wacce ta taba aure harda da dan haka Safeerah open your heart and eyes see Salim for Salim ki rungume mijinki take care of him and be the best wife, gay,u ado iya kirsa, magana mai dadi shagwaba da menene menene ki kashesa dazu haka ake zama da sojoji dam sunada taurin zuciya ina gayamiki so use your feminine energy kinajina" Gyadamata kai Safeerah tayi ahankali, calmly Ummi tace "nasan bazaki yardaba amman da zanso kibama Mahaifiyarki da Mahaifinki Waleed Safeerah!" Dasauri Safeerah tadago kanta ta kalli Ummi.

INA BIKI INA BIKI BUT I HAD TO DROP THIS NAGODE
EPISODE 52
Ahankali Ummi tace "kinyi aure, yanzu gidan zai kasance su kadai, ke kadai Allah yabasu,
Baba zai fara fita teaching, Maman ki will be all alone ke koma Baba yadawo gidan duk bazai musu dadi ba, I know ke da Salim kunason
Waleed but just think about it, basu Waleed baya nufin zaki rabu da Waleed of course zai dinga zuwa miki weekend duk sanda kikeso, zaki iya aikawa a daukosa duk sanda kikeso, yayi hutun school ma haka he can come, akwai another thing kuma dayasa nai maganan nan, kinga a musulunci idan uba wato mahaifin yaro yabude baki ya furta bai yarda kikai masa d'a gidan wani ba wih haramun ne kakai, koda babu kwandalan Abbati ajikin Waleed amman mahaifinsa ne so the right thing to do is kiba mahaifiyarki shi, they're lonely, Waleed na son su Baba sosai. bazai wani damu ba wih he is a big boy, just think about it kinji" gyadama Ummi kai tayi ahankali, Ummi ta mike tace
"bari naraba miki abun dakaina" deban 1/5 of ciccibin tayi tamata microwaving tabata tace
"cinye agabana" cinyewa Safeerah tayi dan bata wani ci abinci ba dama, tasha tsumin da Mama tabata, ragowan sukasa a freezer sannan suka fito, Yasmeen tace "Mama wayoyinta" Ummi tace "laaa nako manta suna jakana bari nakawo" bude handbag nata tayi tabata ta amsa Ummi tace "toh bari muje" wani kunya Safeerah taji hakan yasa tace "bari naje nagaya masa Ummi" Ummi tace "barsa ba bacci yakeba" sama tawuce abinta ai badadi bai gaidasu ba, dakinta tafara shiga tadauki wani sabon maroon hijab a wardrobe dayake nan har kasa tasaka sannan tafito wajen dakinsa tayi ahankali tai knocking murya ciki ciki yace
"come in" bude kofan tayi kadan amman koda wasa bata kallesa ba da fingers nata tashiga wasa cikin yar karaman murya tace "zasu tafi gobe zasu koma Katsina" tsareta da idanu yayi yadan sauke ijiyan zuciya kadan yace "ina zuwa" gyadamai kai tayi tajya takoma dakinta
wani slippers tasaka sannan tasauka kasa tace "gashinan zuwa Ummi" tazauna kusada Yasmeen suna kuskus abinsu, Ummi tace "aikin kenan" kusan 7min yabata dan saida ya shirya sannan yafito yana sanye dawata shadda mai kyau fara sai kamshi yake babu hula kansa but akwai takalmi kafansa na Hermes hannunsa rike da yar bag, he looks damn charismatic, dan daga idanu kadan Safeerah tayi ta kallesa da sauri ta maida kanta kasa, even in dreams akacemata zata auri this kind man bazata yarda ba, yahadu wih dan haduwa ga kyau, ga tsayi, ga kwarjini ga natsuwa ga rashin sake fuska, yanda yakeyi wih bazakace ya matseta daki dazun nan ba adaki yana kokarin mata kiss, saukowa falon yayi Ummi tace "yanzu saida ta tasoka Salim, cemata nayi fa ta barka kai bacci jiki da gajiya" dan murmushi yayi kadan yasami waje ya zauna amutunce yace "bakomi, ina yini Mom" dasauri tace "Alhamdulillah Salim, mun wuni Ipy, sannu da kokari fa, mungode Allah saka da Alkhairi" dan kallonsa Yasmeen tayi cike da shakkansa tace "Yaya Salim ina yini" duba daya yamata bawai akwai walwala kan fuskansa bane amman muryansa asake yace
"how are you Yasmeen" murmushi tayi tace
"Alhamdulillah l'm fine" Ummi tace "to Salim ga Safeerah nan zaman aure zo mu saba ne zo mu shirya sai ankai zuciya nesa zama ke dadi, mun yarda dakai sabida kai babba ne ga hankali da hikima Safeerah akwai shirme karka biyamata tayi ba daidai ba ka kirani, daga Katsina zanzo na lallasata namaka alkwarin nan" dan sauke kai yayi kasa, Ummi tace "Allah ubangiji ya albarkac???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?i aurenku, Allah yakawo kazantan daki to saduwan allhairi Waleed yatashi agaishemin dashi" mikewa duk sukayi Safeerah ta rungume Yasmeen da sauri idanunta na cicciko da hawaye, Salim yadan kalleta kadan feeling wani iri aransa shi ko mace baiso yaga ta rungume kawai yawuce wajen kofa yabude yafice rike da yar jakan dake hannunsa, sakin Yasmeen Safeerah tayi ta rungume Ummi hawaye na saukowa Ummi tace "wai kuka dai kike toh Safeerah lamarinki sai Allah saikace wata yarinya"? Sakinta Safeerah tayi takoma wajen Yasmeen, Ummi tai gaba while Safeerah da Yasmeen biye da ita abaya Salim na tsaye wajen motan yana magana da soja driver duk suka fito sai yanzu Safeerah ke kara ganin estate din wai daman haka barrack keda kyau ko dau ba barrack bane suke dan wih wajen kaman kasan waje, juyowa Salim yayi yakalleta baiji kunyan Ummi ko wani awajen ba strictly yace "go back inside" wani abu Safeerah taji ya tsayamata a wuya, sai kawai tasaki hannun Yasmeen tadaure tahana kanta kuka dudda hawaye na ciko mata a idanu taima Yasmeen waving bye, takalli Ummi tamata bye duk suka mata bye sume tajuya da sauri takoma ciki,Ummi murmushi kawai tayi the first day taji muryan Salim daya gayamata no bazata bisu shirye shirye ba tagane mutum ne shi mai ra'ayi da dokoki tagane dan kulle ne, funny enough abin ya burgeta barina yanzu kaman kishi ne dashi na bala'i dan akwai few maza sojoji haka a street din, gakuma driver daya kawosu, Safeerah kam zatasha fama dashi, da kansa Salim yabude musu baya Yasmeen tafara shiga sai Ummi sannan yasaka hannu ya ijiye mata bag dake hannunsa yace "Mama ki kama jari kika koma katsina, In sha Allah za'a kiraki akaiki gidan ki achan, this driver zai maidaku har katsina no need for public transport" Mama zata fara godiya da idanu yama sojan alamu su wuce aiko suka wuce few soja dake wajen suka tattaho suna mai congratulations na aurensa ya amsasu yayi godiya yakoma ciki.Anan bayin falo yayi alwala yasake fita dan zuwa sallan asir.
Dakin Waleed Safeerah tawuce bayan ta kwashe wayoyinta a falo wannan wani irin takura ne ko sallama batama yan uwanta ba haka rayuwa zai kasance mata ko waje bazata dinga zuwa ba? Wai dama akwai maza haka? Hawaye ta goge daidai Waleed na bude idanunsa ahankali dasauri takarasa share fuskanta tazo wajen gadon tana murmushi tace "Waleed Ayoyooo, Assalamu Alaykum yaron Ummy yatashi daga bacci" washe mata baki Waleed yayi yana tashi zaune yana kallon iPad nasa dake gefen gadon yace "Ummy IPad Abee" murmushi tamai tace "Abee yasaya maka kace Allah amfana" gyadamata kai yayi yace
"cartoon Ummy" dasauri tace "no muje bayl kayi fitsari" turo baki yayi sai kawai ta daukesa tamai chakulkuli tace "fushi zakai dani daga tashi daga bacci" dariya yayi suka wuce bayi basu wani dade ba tafito dashi yanuna ipad din again tace "no zomuje muyi salla" kuka yafara na banza tabude kofa tafito dashi suka shiga dakinta hijab tacire suka shiga bayi ta dauro alwala tafito ta shimfida dadduma tahau kai yahau shima amman sai yayi zaman sa yafara kukan banza wai shi fushi idar da salla tayi bata cire hijabin ba takama hannunsa tace "muje kaci abinci" make mata kafada yayi yace "babuu" girgiza kai kawai tayi ta tsugunna hawa yayi da sauri tamike suka fito bene tashiga sauka suka wuce kitchen tana goye dashi ahaka ta tsaya gaban heater tana dannawa dan yayi zafi aka bude kofan Salim ne dasauri daga ita har Waleed suka juyo Waleed na ganinshi yayi ihu.
"Abeeee" shigowa kitchen din Salim yayi yazo dab da Safeerah calmly yace "Waleed zaka karya mana Ummy ne? U are too big for this weak matar tawa" da dan sauri ta Safeerah ta kallesa jin abinda yakirata dashi saita maida kanta kasa asanyaye qabanta nadan faduwa,shikuma yadauki Waleed daga bayanta yace
"let's go and wait for Ummy takawo mana food ko" gyadamai kai Waleed yayi yace "yesssss Abeeee" dan dagokai tayi ta kallesu harya bude kofa zai fita murya chan kasa tace "an kawo abinci daga gida nasamaka?" Gently yace "yes" yafice, abincin Waleed tahada tasa a tray sannan tafito tazubamai jellof rice da pepper chicken da lafiyayyen salad da aka dafa komi tadaura a tray ta taho falo inda tagansu ya kunna ma Waleed a cartoon a big tv coffee table tajawo gabansa ta ijiye tray zata mike yace
"thank you" wucewa tayi takoma kitchen taga fruits kawai saitadauki water melon ta yanka tamai juicing a juicer data gani tasa a jug ta debi ice tahada a tray tafito ga mamakinta a kan carpet tagansu shi da Waleed, Waleed nacin rice tare da shi baima taba abincinsa dake gabansa ga katon chicken a hannunsa karasowa wajen tayi ta ijiye tajuya sai kawai ta zauna a dinning taduki plate tasama kanta rice din tasa salad tafara ci bini bini taba kallonsu wlh Waleed is eating rice sosai sai kallon Salim take dake basa though sunyi messing falon up fa, juyo da kansa yayi dawani kalan sauri ta dauke kai ta sauke kanta kasa tanacin abincin ahankali.
Tass suka gama ya cinye salad tass da nama but yarage rice, watermelon juice dinma sun shanye Waleed still yaci abincinsa amman yarage, daukan Waleed yayi yace "zakabi Abee zuwa gym?" Gyadamai kai yayi yace "yes Abee" daukansa yayi ya tsallake dattin yadan kalli Safeerah da kanta ke kasa yace "Ummy sorry for the mess" anytime yamata simple magana sai gabanta yafadi, tadan kallesa but yawuce stairs abinsa da Waleed, saita kalli carpet, carpet din kam duk shinkafa mikewa tayi tafara kai plate nata kitchen sannan tafito tazo tahada all plates nasu tamike takai kitchen tadawo hijabin na hanata aiki sai kawai ta duka ta zare hijab din ta ijiye kan kujera ta duka ta hada glass cup da jug tamike tawuce kitchen ta ijiye dudda ga vacuum cleaner tsintsiya tadauko da Parker tafito daidai yana fitowa shi da Waleed sanye da kayan gym Waleed na sanye cikin exact kayan yana rike da karamin towel dinshi ga sneakers nasa a kafansa dan kallonsu tayi Waleed yamata kyau but takasa kallonsa wajen kofa sukayi Waleed yace "Ummy byeeeee" dan dagokai tayi karaf sukayi hada ido da Salim yace "mun tafi gym, do you need anything?" Girgixamai kai tayi hakan yasa yabude kofa, ahankali tace "mezakaci da daddare?" Calmly yace "I take only tea, abincin dake kasa pack them a takeaway nazo zan fita dasu" gyadamai kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login