Showing 24001 words to 27000 words out of 160450 words

Chapter 9 - LOKACI BAI KURE BA COMPLETE

M SHAKUR   

01 Oct 2025

138

yace  excuse me stay in the car yabude motan yafita tabisa da kallo dasauri kawai ko is because he doesn t look like someone that can harm her ko ya cutar da rayuwanta ko yamata wani bad abu da tuni tagudu, almost 5mins yabata aciki yafito saiya zagayo ta kofanta bamata lurada shi ba kawai taji an bude kofan a firgice tajuyo hada ido sukayi tadauke kanta da sauri instead of yamika mata sai ya ijiye paper bags din agabanta akasa wajen da kafanta yake yace  next time eat a cafeteria a company, I don t want my employees staying with hunger am I clear? Gyadamai kai tayi batare data kallesa ba ya maida kofan yarufe yazagayo yashiga mazaunin dreba ya kunna motan yaja, kasa taba abincin tayi and bala in yunwa takeji bai sake magana ba har suka shigo GRA, sukaje first Avenue din kaman tace yasauketa daga bakin street nasu but takasa, haka yashige tun kafin sukai ta hango Baba dake zaune kofar gida kan wata yar plastic chair yasaka wata shadda brown data kode sosai, ta kafadan har yasoma zama kaman milk milk, kansa da hula ga yar radio karama rike a hannunsa yaja antenna sama yana saurara, baya gani sosai, sometimes baya gani kwata kwata, he understands environment nasa yasan sound kuma, jin karan mota coming towards kofar gidansu yasa yarage volume na radio kunnuwansa nawani budewa jin ba motan gidansu bane yasa yamike tsaye dasauri ya ijiye radio a kujeran yadaga hannuwansa alamun motan ta tsaya yace  wa ake nema? Parking Salim yayi ahankali batare dayamayi kwana kaman zai shiga gidan ba dawani irin sauri Safeerah tabude motan tafito bata dauki abincin ba tace  Baba nine wani murmushi sosai Baba yayi yamiko mata hannunsa yace  Mamana an dawo daga IT ya wajen? Kika tafi yau kina fushi da Babanki haka akeyi duk na damu saisa na zauna anan naga shigowan ki, an dena fushin ? Hannun Baba takama tamai wani cute murmushi tace  nadena fushin kawai ni banso Salma na zaginka agabana ne Baba ka kwadeta babu abinda zai faru Baba yace  waya kawoki? Motan waye anan ? Juyowa tayi da sauri adan rude Baba yasa hatta mance suna tare tarasa mezatace daidai Salim na fitowa daga motan rike da paper bags na abincinta, Baba yajuyo yana dan gyara kunnensa trying to read step na mai zuwa da kamshin yace  waye Safeerah ? Cikin mutunci da girmamawa yace  nine Abba, Salim ne dasauri Baba yace  Salim? Wani Salim? Salim daga ina? Safeerah maza wuce gida wucewa tajuya zatayi karaf suka hada ido hakan yasa ta duka tadauki paper bag din ahankali, Baba yace  wani Salim ne bawan Allah me kake nema wajen Safeerah ince badai cutar da ita zakayi ba ko? Koko fada ta nemo ? Dasauri Salim yace  a a Baba, narage mata hanya ne kawai, wajen aikin mu babu abin hawa dan ijiyan zuciya Baba yasauke yace  owooo toh Alhamdulillah, nagode Allah maka Albarka, mantuwa nayi dayake Yayanta yakaita ban ganta kafin ta tafiba so ban bata kudin mota ba, nagode nagode gyadamai kai Salim yayi yay shiru yana kallon Baba he felt very very terrible and responsible for condition nasa saiya kasa motsi, ahankali Baba yace  Salim tashi yayi daga duken dayake ahankali yabawa Baba hannu yace  sai anjiman mu Baba Baba yayi murmushi yace  mujima lpy, nagode Allah yayi Albarka .

BQ dinsu tawuce ga mamakinta saitaga furnitures na ciki na nan but kayan sawansu babu badai da gaske an maidasu wajen masu gadi ba, ko saisa taga Baba ma awaje har an sallami masu gadin? Wucewa tayi flat din tana bude kofa taga Waleed shi kadai yana wasa a falo ga remote a hannunsa duk sanda taga Waleed ahaka only means yan gidan basanan yana ganinta ya washe mata baki yataho da gudu itama haka tace  oyoyooo Waleeeeee tawani daukeshi sama yace  Ummyyyyy ayoyoooo fitowa Mama tayi tace  an dawo yan IT ? Dariya Safeerah tayi tana sauke Waleed tace  Mama nadawo ya kuke ? Mama tace  baki ganmu ba lafiyanmu kalau, jeki wanka, muna gate yanzu kallon Mama tayi dasauri zatai magana Mama kawai tajuya takoma kitchen alamun batason maganan, shiru tayi saikuma ta kalli Waleed tace  kawo remote din muje daki muci abinci ko bata yayi ta ijiye tadauki jakanta da paper bag din tafito tawuce gate tabude dakin tashiga falo ne da uwardaka sai bayi falon ga katifar Baba da Mama sai falo katifarta ga gwangwanayen abincin Waleed awajen ga kayanta a ghana masgo dan babu wardrobe anan jin ranta zai baci yasa kawai ta zauna tare da Waleed tashiga bayi ta wanke hannunta tace  at least I m grateful for this food ko Waleed yaron yace  eh murmushi tayi tabude Chinese rice ne sai Nan bread, humus da curry soup, sai turkey, salad da pinacolada murmushi tayi tace abincin yan gayu debo rice tayi takai bakin Waleed tace  ci kin ci yayi ya kauda kai sai ta gutsuro Nan bread tabasa ya karba yahauci tafara ci ba wasa yunwa takeji, ita da Waleed suka shanye juice din dadi tabar ma Mama Nan bread da soup din tawuce bayi tayo alwala tazo tai la asar ta chanza kaya tadauki Waleed suka fito sukazo kitchen ta taya Mama aiki suka gama komi suka kara gyara ko ina sukasa turare, sannan suka fito suka koma flat dinsu tace  Mama ganaki kallon abincin Mama tayi tace  waya siya miki abinci? Ahankali tace  Oganmu anatse Mama tace  mesa? Yasanki ne ? Girgizama Mama kai tayi tabata labarin yanda batada kudin mota da komi, Mama tace  inada 20k idan zaki tafi gobe saina baki saiki hada da 15k dinki ki samowa Waleed dan abincin daya sawwaka da pampers ko irin me guda goman nan ne shiru tayi ta tsare Mama da idanu tana kallonta, Mama tace  menene kike kallona haka? Hannun Mama takama ta jujjuya tana kallon uban shedan yanka wasu sun warke wasu basu warke ba, takai hannunta ta taba kashin wuyan Mama, da fuskanta da duk yayi wrinkles, sai hawaye yafado idanunta dasauri Mama takai hannu ta share mata tace  zaki fara yauma ko? Kina wani duddubani kaman patient, duk randa kike neman kuka abinda kikeyi kenan Lips dinta ne suka fara rawa tace  Mama na tambayi wajen IT ko zasu bani aiki parmanently na tara albashina na kama mana gida mubar nan? Tsareta Mama tai da idanu sai kuma tai murmushi ganin yarinta tace  yaro man kaza, shi aikin dakike magana akai ba su suka samo miki ba ? Ahankali tace  eh dudda haka amman ai basune masu kampanin ba Mama tai murmushi tace  ko dubu dari ake biyanki bazaki iya rikemu ba Safeerah mubar maganan ma dan Allah, kinyi tunanin makarantan ki? Mahaifinki duk wata wata yake zuwa checkup na idanu da hawan jini, ga Waleed very soon zai shiga 3yrs za a sashi makaranta dole, abincin sa fa, pampers waye waye, I know kin damu but u can t do this Safeerah! Rushewa da kuka sosai Safeerah tayi dayasa Waleed yazo wajen da gudu yana leko fuskanta Mama tace  wai me haka Safeerah kinga zakisa yaron nan kuka ko zo Waleed Mama ta daukeshi yafashe da kuka yana kallon Safeerah data kasa daina kuka, Mama tace  wlh banson wannan halin kawai saiki tasani agaba kina kuka ba a miki komi ba eh cikin kuka Safeerah tace  Mama nagaji da ganinki ahaka nagaji, kullum daga safe har dare aiki kike, kin zama yar aikin wasu da ba a miki godiya sai zagi da cin mutunci, while Baba an maidashi mai gadi da wanke mota ana zagin mahaifina kullum agabana, Mama mubar nan ko barane muje muyi yafimin da this life we are doing here, school din banaso lets leave Mama dan Allah Safeerah kuka Waleed kuma Mama tama rasa wazata lallasa sai kawai itama tafashe da kuka tace  Safeerah yakikeso nayi eh? Ina kikeso nasa kaina naji dadi? Ni yar rikoce banmasan iyayena ba Babana yarasu kafin ahaifeni mahaifiyata wajen haihuwana tarasu yar rikoce wajen yan uwan Babana, wahalan danasha wajensu bana shan kalansa anan, mahaifinki shiya ceceni ya aureni sukace sun yafeni banda kowa sai mahaifinki duk inda zaisa kafa zan saka tawa sabida yabani gatan daban taba samun kalansa aduniya ba, wannan shine hallaci duk runtsi duk wahala ina tareda shi, dagani har mahaifinki sabida ke muke zaune anan nothing is important arayuwanmu face ke da Waleed as long as zaman mu anan zaisa ki cigaba da samun education Waleed na samin abinci da kulawa fakat mu karmu samu mun hakura bakomi, stop crying we are doing this for you, no condition is parmanent watarana sai labari, zagi da cin mutunci baya kari, dan Salma ko Shamsu ko mahaifiyarsu sun zageni it s okay, watarana ko ance suyi bazasuyi ba, abinda nakeso is just focus on school naki, kigama IT dinki and become somebody, as for Waleed zan kula miki dashi as long as I m alive kinji, please karki bari Babanki yaji maganganun nan kar BP sa yatashi ya isa zo nan yarinya na nasan badadi ana zagin miki iyaye amman kiyakuri kinji Feerah na Mama ta rungumota zuwa jikinta lamo tayi jikin Mama haka shima Waleed yayi lamo yana kallon mahaifiyar tasa dake kuka Baba yadade gaban dakin tsaye dan yaji komi sai kawai yawuce yakoma waje yabuga tagumi, yasan watarana sai labari shi bayajin kyashin yima yayarsa Kubra komi sabida takula da lafiyarsa, tasaka yarsa a makaranta da sauransu, kawai baitaba sani yayarsa Uwa daya Uba daya zata iya maidashi mara daraja dan aiki mai wanke mota ba da gadi tana zaginsa da cimasa mutunci gaban iyalansa ba, shi yasan da shine mai hali Kubra tazo garesa bazai taba maida rayuwanta haka ba, zai iya kwashe iyalansa sunbar nan ba but tunaninsa shine aikin me zai samu baya gani? Tayaya zai rikesu? Mama Kubra ta cutar dashi sosai kawai baiso yayi magana ne sabida zumunci amman bazai taba mance lalata yaruwan yarsa datayi ba ta auramata dan shaye shaye mai duka.

Basu dawo gidan ba sai wajen 12 tuni Safeerah tai bacci anan falo shima Waleed haka, Baba yafito daga uwardaka yafito yazo yabude musu gate, driver ke tuka Momma da Salma dake baya suka shigo ya maida gate yarufe yabiyo motan Momma ta sauko yace  sannu da zuwa Mama Kubra kallonsa tayi sannan takalli driver ta tace  kai zaka koma BQ yanzu cike da girmamawa yace  toh Hajiya Salma tayi gaba batare data gaida Baba ba tace  ka daukomin kayan dinki na a boot Momma tace  ka tsaya kana kallona bakaji abinda Salma tace bane ahankali yace  naji bude booth yayi yadauki jakan dinki yawuce flat Momma biye da shi har bene yashiga hawa Momma tace  nasan ba hankali gareka ba ka ijiye agaban dakinta baka shigo ba daga ciki Salma tai kwafa tace  yashigomin daki bana gaura masa mari ba hmmmm Baba baice komiba yawuce ya ijiye gaban dakin Momma tayi dakinta tace  ka kashe wutan ko ina anatse yace  toh Yasauka yakashe wuta yawuce yafita.
EPISODE 1?? 5??



Washe gari da sassafe Safeerah ta tashi ance ba ason latti bayan tai salla ta taho flat tas tashiga share share tana azkar ahaka ta gyara ko ina tasa turare 7 har yayi Mama tace  maza jeki wanka wucewa tayi taje tai wanka wani black abaya tasaka yau is simple abaya babu wani kwalliya ajikinsa dan stones dake jiki sun dade da fita tun na akwatinta ne shima rigan, closed abaya ne black but a goge, tasaka wasu hook earings farare masu kyau Mamane tasayo mata su a kasuwa, batama tsaya gyara gashinta ba gyalen kawai tayafa aka tadauki jakan bayanta ta goya tafito she smells good very mild, Mama tries dasai mata yan turaruka da khumra haka da yan kudinta tasaka flat shoe black tafito, wucewa tayi zataje flat Baba dake shigowa gidan baiso yauma takara tafiya da bakin ciki yace  wuce kitafi dasauri tajuyo tace  Baba ina kwana hannunsa yasa a aljihu yaciro 10k yamika mata yace  gashi ki hada da wanda mamanki tabaki ki sayoma Waleed abinci da pampers saiki cire na mota kisai abinci kuma kici murmushi tayi tace  toh Baba nagode Allah kara bude, jama a Babana yafi nakowa principal Baba dariya Baba yayi yace  uhmm Principal da ba idanu yanzu murmushi tayi tace  da nazama Nurse dana maka magani yanayin fuskan Baba chanzawa yayi sabida burinsa kenan Safeerah tazama Nurse, wucewa Safeerah tayi tafice yabita ya tsaya a kofar gida tafiya tayi harta fita wajen layinsu tasami keke tahau yakaita bak1n junction tasami mota yakaita har layin wajen aikin sannan tatako daga junction zuwa company 8:05AM tashigo kampanin kafin takai ciki was 8:09 zatai hanyar office nasu receptionist tace  you need to sign in Miss Safeerah gyadamata kai tayi tazo tai signing receptionist din na kallonta ahankali tace  you re very pretty Miss, I love this plenty hair on your forehead kallonta Safeerah tayi sai kuma akunyace tace  thanks ta ijiye biro tajuyo tawuce zuwa office tabude tashiga Madam Maimuna na desk dinta, ahankali tace  morning sannan tawuce wajen Madam Maimuna dake kallonta tana murmushi adan kunyace tace  ina kwana Anty ? Murmushi tamata tace  lpy lau ga files naki jeki karasa sai na koya miki next abu, before then get coffee or tea, anjima da rana zamuje canteen muci abinci Oga yace kowa yadinga zuwa cin abinci bill on him, anytime Oga Salim ke gari enjoyment kawai akeyi a kompany, jiya yabada kudi araba naki na hannun Mr George gyadamata kai tayi ahankali tawuce ta zauna tafara aiki.
Wuraren 12 yashigo company cikin wata army green motan kana ganin motan kasan na soja ne tundaga plate number, Parking akayi chan aka bude kafansa na sanye cikin boot din sojoji me ruwan kasa yafito anatse yana sanye cikin wandon sojoji daya zauna ajikinsa tsaf, ba rigan sojoji mai common flag ne ajikinsa ba wani green riga ce mai v neck data kama jikinsa tsam har 6packs dinsa kana gani yayi stocking da rigan gawani arnen belt na sojoji a waist nasa hannun rigan gajerenne so kana ganin muscles dinsa a murde sosai, idanunsa sanye da bakin glases sosai, kansa ba hula sumansa sunyi wani irin kyau ka gansa sai kwarjininsa ya cika maka ido maida motan yayi yafara tafiya anatse few employees nasa na gaidasa instead ya shiga ta basement ta main entrance ya shiga dasauri receptionist din tace  welcome Boss dan gyadamata kai yayi yawuce yashiga hayowa staircase anatse yana bin ko ina da kallo har yaje fourth floor a staircase ko gajiya baiyiba office dinshi yawuce secretary dinshi na biyosa ciki tace  welcome Sir, coffee or tea Sir? Batare daya amsata ba yawuce ya zauna yasa hannu ya kunna desktop nasa sannan yace  none, excuse me dasauri tace  yes Sir tajuya tafice fuzar da iska yayi kawai yaja keyboard yayi logging into ystem din he have access to everything na company shi, direct CCTV camera file ya shiga yana shiga office office ya shiga office din customer care ya tsaya chak yana kallon Safeerah dake aiki ga file a hannunta tana cikawa, there s something he s feeling, he just wanna take care of this girl and repay her kindness, baitaba haduwa da y a mace data tsayamai arai like she ba, he doesn t know how to help, and also yanajin nauyi yaje yafara mata bayanin waye shi da yanda yasanta da menene menene, he just wanna get to know her first, zooming camera yayi yana kallonta da kyau kaman tana gabansa, ringing wayansa yashigayi batare daya jaye idanunsa daga screen dinba yadauki wayan yakai kunnensa yayi shiru yana kallon screen din.  Ina kwana Baby yaji muryan Nana, yace  how are you  gani nan banida lpy  meke damunki ? Yayi tambayan yana zoooming system din ganin Safeerah tamike yanabin ta tawuce wajen Madam Maimuna, Nanah tace  marana ke ciwo ahankali yace  sannu go and see Dr ki karbi magani murya chan ciki tace  Mami taje office, babu kowa agidan sai ni kazo ka kaini dan Allah hankalinsa gabaki daya nakan system din yace  I m kind of in the middle of something right now, but get ready I will send John yazo yakaiki muryanta ba dadi tace  okay nagode  Allah sawaka yafada ahankali yana zare wayan ya katse yadan cire idanunsa kadan daga system din yayi dialing wani number da akai saving da John yakai wayan kunnensa yamaida idanunsa kan System daidai Safeerah na juyowa rikeda wani paper a hannunta datake dubawa looking so serious daidai John yadaga yace  Sir murya kasa yace  I need you to pick up Madam akaita clinic anatse yace  okay Sir katse wayan yayi ya ijiye yana kallon screen din chan yadaga wayan office nasa yakai wayan kunnensa Hajiya Maimuna ta dauka zata fara gaidasa yace  I need report na feedback na client namu na last month dasauri tace  yes Sir anatse yace  give the newbie tasameni a parking space awaje I m going out dasauri tace  angama yallabai ijiye wayan yayi yakashe system din yadauki wayansa yafito daga office Secretary tamike tsaye dasauri, yawuce this time lift yashiga yasauka kasa yafice yaje wajen motansa ya jingina da motan yayi folding hannunsa a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login