Showing 87001 words to 90000 words out of 160450 words

Chapter 30 - LOKACI BAI KURE BA COMPLETE

M SHAKUR   

01 Oct 2025

103

tafiya abinsa, sauka tayi daga gadon da sauri ganin yamika hannu zai bude kofa yafice yasa ahankali tace "Abeee!" Chak Salim ya tsaya jin sunan data kirasa dashi, itama batasan ya akayi ba kwai takasa kiran sunansa kai tsaye ne sai sunan da Waleed ke kiransa yazo bakinta kawai ta furta, gently yajuyo tareda zuba hannayensa cikin aljihu wandon uniform nasa yakalleta kanta akasa ta taho gyalenta data gani bakin gado ta dauka da sauri tadauka ta yafa gabanta na faduwa he could see yanda jikinta ke rawa rawa ta taho zuwa gabansa but still akwai dan tazara between them, bata kallon fuskansa but wani girma yamata agaba, yacika mata idanu, yamata balain kwarjini hakan yasa kai tsaye tai kneeling tasa duka knees dinta akasa dasauri yakalleta strictly yace "wat are you doing"? Abu taji ya tsayamata a wuya, baki tabude zatai magana saikuma bakinta yafara rawa hawaye na cika idanunta, iska ta fuzar ahankali kaman yar yarinyar datasan tai laifi dinnan batada gaskiya tace "I am sorry about all abubuwan dana fada jiya, I was so stupid for saying all of abubuwan nan, bazan karaba Wallahi, kayakuri dan Allah" tafashe da kuka ahankali, dan dauke kai yayi daga kallonta calmly yace "stand up! Don't ever kneel for me" wani raurau tayi da fuska cike da ban tausayi tace "namaka laifi ne, tunda na sanka you've been helping me, you've been so good to me, but jiya sabida an karbe Waleed inata maka rashin hankali bayan you're the only one that can help me" saikuma tadaura dauka hannayenta a fuska tana wani irin rera kuka mai shiga zuciya tace "Abbati is very wicked zai iya dukan Waleed, ya tsani yara, yaran yayarsa ma yana dukansu, he hates cry na yara, he can't tolerate Waleed, I'm sure Waleed baici abinci ba, I know he has been crying, maybe ma ba'a cire masa pampers ba, baida sabo idan mutanen waje yaga basa sonsa, I don't want anything to happen to Waleed nasan he's missing me, yanata nemana, I know beci komiba har yanzu, I know yanata nemana yana kiran Ummy, Ummy, banson wani abu yasami Waleed dina, karya mutu..." yanda take kuka tana maganganu ko he knows some abubuwa ma batasan tana fadansu ba, cikin wani irin murya mai balain rauni tace "Abee dan Allah ka karbomin Waleed dan Allah, dan Allah kataimakeni, ka karbomin Waleed, bring my Waleed back Abee kaji dan girman Allah, karya mut...
" shilli taji saukan yatsun Salim
akan lips nata ta kallesa dasauri shima ya duka agabanta.
EPISODE 48
Dayake hannayenta nakan idanunta tana kuka saukan yatsansa taji kan lips nata kafin ahankali taji saukan dayan hannunsa kan hannunta dake kan idanun, ahankali yasauke hannunta kasa yakama dayan ma yasauke kasa ya tsare fuskanta da idanu yana kallon long eyelash nata dasuka jike da hawaye sharkap cikin tattausan murya yace "how can this weak girl give birth to strong Waleed?" For the first time ta dago manyan jajayen jikakkun idanunta ta kallesa jin maganan dayayi, gyadamata kai yayi yace "is only fair a strong boy like Waleed ace strong mace ne ta haifesa not this weak cry cry Safeerah!" Dan rage murya kadan yayi yace
"listen thing good things don't come to the weak good things goes to the strong ones, idan you want Waleed back you have to be strong cus you have a strong battle ahead of you okay, where is that fearless Safeerah data boye soldier a wardrobe and put her life at stake just to save a soldier? Uhmm tana ina"? Shiru tayi tana kallonsa kaman yanda yake kallonta dawasu cool eyes, lumshe mata idanu yayi yabude su calmly yace "stop being weak!" Gyadamai kai Safeerah tayi kaman wata yar baby tana kallonsa tana sauke gurbataccen ijiyan zuciya, lumshe idanu yayi yabude su ahankali ya sauke akanta cikin wata yar kankanuwan murya yace
"I will bring our son back home today no matter what!" Wani sanyi Safeerah taji ya lullube ta gyadamai kai, gently yasauke yatsansa dagakan lips dinta, mikewa yayi tsaye yajuya harya bude kofa ya dakata yace "go to your room kiyi wanka, I don't want Waleed to see you this miserable it will break him kid can sense their mothers energy" yana maganan yabude kofa yafice tabisa da kallo takasa motsi daga wajen har saida taji karan rufe kofan falo mikewa tayi ahankali ta kalli inda ta kwanta ashe dakinsa ne nan, gadon taje ta gyara da sauri sannan tabude kofa tafito tawuce dakin dake facing nasa tabude akwatinan ta data gani tagane nan ne nata, dakin nata ma yamafi nasa kyau it feels like dakin mata, while simplicity dakinsa makes it feels like dakin maza, bayi tafada taga brush sabo tayi tai alwala tafito tazo tai sallan asuba ta zauna awajen tana tunani tunani, gabanta sai fadi yake, saikuma ta tashi da sauri bayi ta fada ta cire duka kayan jikinta tai wanka da hadadden shower gel dake bayin tadauki towel tadaura tafito wardrobe tabude taga duka kayan akwatin da aka dinka an jeramata plus abayoyin gabaki daya ga section na underwear suma acike, hannunta tamika tadauki black underwear pant and bra tacire tag tasaka kuma sun mata daidai tayi bala'in mamaki, wani black and red abaya tadauka da veil nasa mai kyau tasaka tamaida drawer tarufe tadawo ta zauna abakin gadon dakin tai zuru zuru kalle kallen dakin ta shiga yi wayanta takeso take takira su Mama saita tuna maybe yana gida dan tana tashi akasa ta biyosa tasake buga tagumi saikuma tasake fashewa da kuka she just can't help it tasan waye Abbati she knows him she's sure Waleed baici abinci ba tun jiya, veil na abayan tadauka takai fuska tana goge hawayen tabude kofa ahankali tafito tafiya tashiga yi tana sauka kasa wajen dinning tayi tabude kofan datake tunani na kitchen ne ahankali, jiya ta taba a kulle yanzu abude, kitchen din yahadu irin wayanda take gani a Tv, dube dube tashigayi still crying she just wanna cook incase Waleed yadawo tunda bataga abincin yara agidan ba, semo tagani a store tadauka, ga okra awani basket sai kawai ta debo tazo fridge tabude babu abinda babu ciki, kawai tashiga girki bini bini tana goge hawaye idanunta sun kumbura sosai, tuwo tayi da miyan kubewa dayaji kifi cus taga kifi a freezer neman abun kwashe tuwo take wani drawer tabude kawai saitaga abincin yara wanda she's sure na Waleed ne daban daban a jere sababbi,wani abu yakara taso mata arai, mutumin nan provides komi datake bukata dana danta kawai tahau kuka, tadauka baida abincin yara saisa tamai tuwo da miyan kubewa dan yanadan karba wani zubin but ganin abinci yasa tasake fashewa da kuka fito da abincin tayi tasa ruwa a heater incase yazo akwai hot water akasa, ta kwashe tasa a kula masu kyau takawo dinning ta ijiye sannan tawuce tazauna akan kujera a falo tana kallon kofa she looks bad but hakan bai boye wani glowing datakeyi na amarci ba.
**
Zaune yake abayan mota inda wani mutumin da akalla zaiyi 45 ke zaune tare dashi yana sanye da suit baki while wani sojan driver na tuki, magana suke but wayansa dake ringing yasa yaciro wayan yakalli mutumin yace "hold on Barrister!" Wayan yakai kunne yace "I'm listening!" Fuzar da iska yayi yace "follow him I'm right behind you" yazare wayan daga kunne yace "turn around Kay! We are going to Gaskiya!" Sojan dake tuki yace "yes Sir" Barrister yace
"an gansa?" Gyadamai kai yayi yace "yes!" Bai kara magana sai karkada kafa dayake, sosai driver ke gudu cikin 15mins suka isa Gaskiya, da yaransa yake magana awaya har ya iso inda suke wani hadadden unguwane na yan gayu sunyi parking motars na sojoji gaban wani gida, fitowa driver shi yayi yabudemai kofa anatse ya sauko daga mota looking damn charismatic yadaga hannunsa yana kallon agogon hannunsa this is 11:04AM, fitowa boys nasa sukai daga mota duk suna sanye da kayan sojoji suka saramai kai ya gyadamusu alamun ease yace "talk to me Hamza!" Hamza yace "kaman yanda ka rarrabasu mukaje Club 808, luckily around 10:20 yafito daga club din yashiga motarsa we followed him here yashiga this house" yanuna gidan dake facing nasu daidai Barrister nafitowa daga mota da papers a hannunsa, cikin wani kalan strange behavior na asalin mugu mara imani Salim yace "afitomin dashi!" Yayi maganan yana sa hannu a alfihun wandonsa yaciro kwalin taba yazaro daya zaikai baki dasauri Barrister yakai hannunsa ya karba wani kallo yama Barrister dasauri Barrister ya yar yace "kanakai abin nan baki ba alkhairi zaka aikataba, haba Salim! Calm down its public let's go by the rules" wani kallo Salim yamai saiya fashe dawani mugun dariya dayasa gaban Barrister yahau fadi cus yasan Salim batun yauba they've been friends idan Salim na dariya just cry kawai dan ka shiga uku, wani kallo yama yaransa hakan yasa kawai suka buga gate din dayake a kulle ganin daya na kokarin hawa gate yasa arude Barrister yace "Salim bamu da warrant fa dazamu fada gidansa, he can sue us for this mehaka?" Wani irin bitting lips nasa Salim yayi yakalli barrister da idanunsa dasukai ja yace "daya shigo har gidana and use his hands on my wife yayi using warrant?" Daidai soja daya ya dirka compound din Abbati na fitowa sabida bugun dayaji anama gate, this is new house baida gateman besides ma gate din uses remote ganin soja ya dirko yasa ya tsaya yana dan layi dan abuge yake yace "who da fuck are you"? Bude gate din sojan yayi, sauran sojojin guda biyu suka shigo kafin su gyara suwani kame suna sarawa Salim yashigo gidan yana wani irin tafiya yana kallon Abbati da hakanan Abbati yaji gabansa yafadi daya hada idanu dayayi da Salim but yadaure yace
"lafiya? Kodai batan gida kukayi officer"? Tafiya Salim yacigaba da yi yakai hannunsa yaciro kwalin taba yazaro daya yasa abaki dasauri daya daga cikin sojojin yazo da lighter ya kunnamai wani irin lumshe idanu yayi yana huro da hayaki ta hanci sojan yadauko wani plastic chair dake compound din yazo ya ijiye masa Salim yayi wani irin zama na basawa sannan yadaga hannu yakalli Abbati awulakance yamai alamu da hannu da yazo, daya daga cikin sojojin yadakamai tsawa yace "come here civilian" gabansa nadan faduwa yakalli door din entrance nasu saikuma yafara takowa yana zuwa wajen he was high before but saiyaji abun na clearing sai tunani yake sojoji daga ina kuma an gano yana deal na cocaine ne? Wait yanada any coke agida? No baya ijiyewa a gida ko an duba baza'a gani ba, he's clean bari yadaije yaji dame sukazo, karasowa gaban Salim yayi yadan kallesa yace "gani offi.....
" bai karasa maganan
ba sabida wani irin mugun kwashewa da Salim yamasa da kafa yawani zube akasa completely zai fadi Salim yawani kama bayan wuyansa da hannu daya da balain karfi yakawo kansa gaba while shi yanadan dukowa yana kallon kwayan idanun Abbati dake kallonsa arude looking damn confuse, keyansa da Salim yarike namai mahaukacin zafi yanaso ya kwace yakasa yana wani irin nishi da sauri sauri, idan kaga fuskan Salim tsaf kaga fuskan mugu mara imani, wani murmushin keta yayi yabusomai hayakin taban a fuskansa cikeda rashin mutunci yace "you've been making mistakes Allah baikamaka ba but you made the wrong mistake jiya!" Ahhh! Yawani kwashe keyansa da duka dayasa Abbati yaji wani radadi amman yadaure muryansa bata fita da kyau sabida zafi da tsoro yace "menayi Oga"? Sakin bayan wuyansa Salim yayi yakawo hannun saitin kumatun sa wani simple yet wicked mari yamai yace "hunnn baka sani ba!
Think" Tunda Abbati yake aduniya baitaba sanin akwai simple mari but mai azaban zafi ba sai yau kaman an zubama kumatunsa yaji idanunsa sunyi ja tsabagen yanda marin ya shigesa, Salim looking like a wicked bully yasakemai mari adayan kumatun yana huramai hayaki yace "me da me kayi jiya list them!" Ijiyan zuciya Barrister ya sauke he hates this part of Salim, Salim is very wicked saisa karma ka shiga gonarsa, don yasan kan yanda ake azabtar da mutum, baisan ko soja suka koyarda shi ba muguntan nan and he will be doing abun looking simple yana hira dakai ma sometimes but hes inflicting pain on you, nan da nan kumatu da jikin Abbati gabaki daya har yayi ja abunka da farin fata.
Abbati yace "club kawai naje jiya Yallabai" yarda taban daya kare Salim looking pissed kaman da taban yake fushi yayi yace "damn it I need another cigarette boys!" Yakalli Abbati yace
"how about that estate? Me kaje kayi awajen?"Dasauri Abbati yakallesa bakinsa yafara rawa jikinsa ma daidai ana bawa Salim taba a baki ya karba aka kunna, Abbati jikinsa na zabura yace "d'ana na dauko!" Kafa daya Salim yadaga yadaura kan kafadar Abbati da kyau yawani gyara fuskan Abbati ya kwantar baicemai komiba yafara slapping nasa tass! Tasss! Tasss!
Tasss! Kawai kakeji, Barrister ya runtse idanu is too much for him to look, kumatun mutumin har girgidi yake, yayi slapping nasa yakai 25 kumatun Abbati saida yayi suntum ya kumbura yayi jazur sannan Salim yasauke kafan kasa yayi murmushi yana huramai hayaki yace "you dare touch Matana har kana sumar da ita!" Wani irin bugawa kirjin Abbati yayi yakalli Salim da kyau zuciyansa na bugawa yakasa magana, daidai ana kara kawomai taba kara na uku sojan yasamai abaki aka kunna zukan taban Salim ya shigayi sannan yakalli Abbati yace "ina Waleed!" Muryansa har baya fita da kyau cus motsi da kumatu ma radadi yake masa yace "yana ciki!" "Dawa!"? Salim yamai wani azabar ihu, gabansa na faduwa yace "da Kuku na!" "The woman?" Bakinsa na rawa tace "tana gidanta" wani kallo yamai yace "inane gidanta"? Ahankali yace "Oakville estate house 21" kai tsaye Salim yace "pick her up Boys" yakalli Abbati yace
"waya baka address na gidan Matata?" Yanda kirjinsa ke bugawa yama kasa karya muryansa baya fita yace "Hajiya Kubra tabani Yayar Babanta" mikewa Salim yayi yace "we have extra candidate boys! GRA house number 10, take them to base" atare sojojin sukace Yes Sir!
V ni lumshe idanu yayi yace "kazo har gida ka raja yaro da mahaifiyarsa for you to just bring him here left him with Kulu kayi tafiya ka club tun jiya sai yanzu kake dawowa" ahankali Abbati yace "a??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????mini afuwa yallabai" dariya Salim yafara dayasa Abbati yaji kaman yanajin fitsari, yace
"I've not even started with you yet! Common Boy kabani 24hiyrs dakai kafin kafara neman afuwa" rawa jikin Abbati yafara cus all he sees a idanun Salim is tsantsan mugunta, kashemai idanu Salim yayi yace "we need to catch up and walk down memory lane koba hakaba"girgiza kai Abbati yayi hawaye na fita daga idanunsa, Salim yace "idan hawayen nan suka zubo sai ka ciro eye balls dinka kabani!" Abbati yarike kukan, dan ijiyan zuciya Salim yasauke yadaga hannu yace "give me the damn papers Barrister!" Dasauri Barrister yataho da papers a hannunsa karba Salim yayi yabude yana dubawa page by page yace "Matar daka saka and abandon bayan kamata ciki kace bakason ciki, spent most of her time a hospital, aka haifi yaro aka kiraka you refuse to acknowledge yaronka kace bakaso, ko suna su suka sama yaron, you didn't contribute anything for danka, rana daya kace zaka rabasa da mahaifiyarsa which did everything for him and dedicate her life for him kayi kadan! You're nobody arayuwan su!" Jefar da papers din yayi akasa yace "we filled for child custody! Let's meet in court! For now Waleed needs his mother! Waleed's mother needs her son, tashi ka daukoshi!"Salim yafada cikeda authority kokarin mikewa Abbati yayi but yama kasa kafafunsa sunyi sanyi ganin yakasa tashi yasa yatabe baki ya mike tsaye karan tabar ya yar akasa ya share hannunsa jikin wandonsa yadan kakkabe jikinsa sannan yawuce abinsa flat din, yace "take the useless boy to base Boys" sukace yes Sir akai sama da Abbati daya fara
?hu ina za'a kaisa? Inane base? Yace "I need my lawyer" wani bushewa da dariya sojojin sukayi sukai waje dashi.
Hannu yasa yabude kofa yashiga Kuku yagani yana fitowa daga ciki, hade fuska Salim yayi yace "where's the boy"? Atsorace kaman mara gaskiya ganin wani huge mutum da kayan sojoji ya nuna sama yace "upstairs second room" sama Salim yayi direct second room din yayi yasa hannu yabude kofa zaune yaga Waleed akasa yana sanye da tun shaddar jiya datai datti, ga majina da hawaye sun bushe a fuskansa, yana zaune akasan dakin hancinsa yayi jaa, idanunsa sun kumbura sabida kuka, ga abinci plates daban daban babu wanda yataba, chips, egg, rice, biscuits, juice, water duk yakici, fuskansa yayi red idanunsa sunyi red sun kumbura sai ijiyan zuciya yake saukewa yana haki sosai na kuka he looks pathetic, dudda yaji an bude kofa but bai kalli kofan ba, bala'in tausayin yaron Salim yaji ahankali yace
"Waleed!" Dawani irin sauri Waleed yajuyo jin muryan Abee dinshi, ganin Abee baisan sanda yashiga kokarin tashi daga zaune ba yafashe da kuka mai hawaye agalabaice yace
"Abeeeeeeeeeeeee" hannu Salim yabude masa yana murmushi farincikin ganinsa yace "come Son! Abee is here" dawani irin sauri baida ma karfi sabida yunwa pampers nasa namasa nauyi bama ya iya tafiyan da kyau da sauri yaje ya rungume Salim yana sake sabon kuka sosai harda tari sabon majina na fitowa duk ya gogamai ariga ko damuwa Salim baiyiba cikeda so yadagasa yana shafa bayansa yace
"it's okay! It's okay! I promise nobody will ever carry you away from us again kaji, stop crying now, stop crying" sake kankamesa yayi sosai cikin kuka da muryansa looking very weak and sad yace "Abeeee Um.....Um....Umyyyyyy" shafa bayansa sosai Salim yayi cike da kaunar yaron yace "Ummy is at home waiting for Waleed, let's go to Waleed Ummy, muje."
EPISODE 49
Juyawa yayi yafito daga dakin yasauka kasa kofa yabude yafito compound an fita da Abbati waje yayi waje yafito Abbati da ansa a mota yajuyo yakalli yanda Waleed ya kankame Salim gamgam yayi lamo ajikinsa sai ijiyan zuciya yake saukewa wani abu yaji ya tokaremai wuya da karfi, daya rike Waleed the boy was crying profusely amman jibi yanda ya rungume wanda ba mahaifinsa ba, wucesa Salim yayi cus he's carrying Waleed baiso yayi any improper abu gaban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login