Showing 102001 words to 105000 words out of 160450 words

Chapter 35 - LOKACI BAI KURE BA COMPLETE

M SHAKUR   

01 Oct 2025

136

baki before Dady ya yarda ayi welcoming Safeerah ciki harda Nanah dayake bala'in so tarokesa, Ammi calm down after deep magana da Anty Asabe tai da ita, hakan yada she invited her friends wih, makota da waye waye and they all came, anyi decorating compound din, ga chairs ga backdrop da akayi da ballons anda SAFEERAH WEDS SALIM #SS2025, wannan duk aikin Layla ne, Baffa na gidan da matayensa da yaransa duka, Anty Asabe, Ammi, kannensa su Nanah, kowa na nan, ga abinci ga rago ana gasawa, abunka da masu kudi ga drinks, ice cream dasu Mocktails station, Auwal ko ina Nana tayi yana binta da ido sabida the way she is getting involve in everything is shocking him ga gayun dataci kaman rannan bikinta, tun family na yi kaman basuso ta shiga sabida kartai getting hurt tanuna musu ita she is over that, Safeerah is family so she will join the ceremony, Dady dai yayi ficewansa abinsa yace bazai bada blessing nata ba, event biyu za'ayi this morning is presentation of gift da Waleema wata malama zatai wa'azi anjima da yamma kuma party za'ayi rawa.
Nanah tashigo falo daukan wasu party packs taji ihun Layla tace "gasunan sun iso, the S SQAURE are here" faduwa gabanta yayi dumm kawai taji kaman abu ya tsunguli zuciyanta, she's about to meet the girl da Salim yarabu da ita akanta. "Nanah" taji muryan Ammi da ke fitowa daga dakinta tana saukowa daga stairs looking damn beautiful itama cus itane zata tarbi sirikanta daga mota tamata lullubi that is the culture, tayi ado na lace ta zuba uban gwalagwalai a wuya, dasauri Nanah tajuyo tana kakalo murmushi tace "Ammi na kin fito"?
Ammi tace "why are you alone here?" Murmushi tasakeyi tace "party packs nazo dauka na kaima Ya Layla" ahankali Ammi tace "toh dauko muje" dauka tayi tana murmushi ta taho itada Ammi suka jera saikuma Ammi ta tsaya tareda bata side hug, cikeda so cus tana tausayin yarinyar after abinda Salim yamata tace "are you sure you are fine ko zakije dakina kiyi kwanciyar ki?" Dasauri Nanah tace "ahh Ammi na ja kwanta who will welcome sabuwar amaryan mu, muje Ammi ni wih l'm fine, Ammi bana gayamuku komi yawuce ba, besides Ya Auwal is just the best man in this planet I'm happy shina aura mai takuramin yanzu, muje Ammi ke ake jira" tabude musu kofa ita tafara fita Ammi biyeda ita daidai soja na saukowa ana ayyiriri mutanen dake compound din, yazo ta inda Salim yake yabude kofa, Salim yasauko a natse, tsayawa Nanah tayi chak tana kallonsa wani irin kallo that says alot, she missed him Wallahi tallahi, he looks damn handsome and charismatic bata taba ganin yamata kyau kalan wanda yamata yauba, yaci hula, exactly ango kusan kowa na family saida sukaga kyawun nan, basa ganin kowa na motan, hannu Salim yasa yadauko wani dan karamin kyakkyawan yaro fari tuluki da bazai wuce 3yrs ba yana sanye da exact same clothes as Salim hatta hulan ma iri daya, yaron namai murmushi yawani rirrikesa, kana ganinsu kasan akwai bond tsakaninsu kowa kallonsa yake bayako kunya ko shakkan nuna Waleed dudda ba dansa bane, kowa tsayawa yayi yana kallonsa har ita Ammi, saiya maida kofan yazagayo batare dayama kalli family sa ba yabude side da Safeerah take gabanta na wani irin faduwa, tanajin kunya, gata bazawara gashi ya dauki danta datazo dashi daba nasa ba, sunyi anko, how will his family look at her?
How will they treat yaronta? Saitaji inama batazo dashi ha ta barsa gida wajen Mama da Baba, Salim yakalleta itama dan kallonsa tayi for the first time yau tunda garin Allah yawaye, idanunta na cikowa da hawaye, tsareta da idanu yayi that looks like yana gayamata kartai kukan nan datake shirin yi, sannan yamika mata hannu alamun tazo wlh bata taba ganin mara kunya, mara tsoro kalan Salim ba agaban danginsa yake bata hannu, kunyan da jin nauyin basa hannu taji agaban uban jama'a da yan uwansa sai kawai tadan matso zata sauka batare data karbaba, hannunsa kawai Salim yasa cike da tsantsan kulawa yakamata calmly tasauko daga jeep din da taimakonsa kanta akasa, kowa kallonsu yake kaman an sami TV especially
Ammi, she thought zataga wata babban mace wannan da akace tanada d'a dan ta taba aure but to her suprise yar karaman yarinya tagani even Autan ta Lubna tafi Safeerah ma girman jiki da tsayi maybe ma Lubna ta girmi Safeerah wih da months, daidai lokacin kuma hawaye ke zubo ma Safeerah wani irin fargaba da tsoro take will they accept her? Will this rich people love her? Dasauri Anty Asabe tazo wajen
Ammi tace "muje Adda, you have to be the one to welcome her, she can't take another step without your approval" gyadamata kai Ammi tayi tadan sauke ijiyan zuciya sukai wajen kawayen
Ammi da sauran matayen su Baffa sukabi bayan Ammi suka fara wake suna tafi da hannu normal tradition dai, Ammi takarasa har gaban Safeerah while Layla ta taho dawani tray da Alkyabba kekai mai kyau ta tsaya Anty Asabe tace "ga mahaifiyar mijinki nan Safeerah" kasa dagokai Safeerah tayi ta kalli Ammi kawai saita duka har kasa, ba matan kadaiba har Salim dake gefenta saida ya kalleta yanda ta duka dan gaida mahaifiyarsa, ahankali tace "ina kwana Ammi" shiru kowa yayi ana sauraron muryanta, muryan Safeerah akwai dadi and it shows ita yarinya ce, hakanan Ammi taji muryan yatabata har zuciya wh, dan ijiyan zuciya tasauke, ba yanda zatayi her Son chooses her she must accept abinda danta ke so, dukawa tayi tasa hannu biyu takama Safeerah ta dagota ahankali fuskanta asake tace "Assalamu Alaykum Daughter Safeerah" lumshe idanu Salim yayi yabude yana kallon Ammin sa, kasa amsata Safeerah tayi kanta na kasa har lokacin takasa kallon Ammi, Ammi ta kalli Layla tace "ku warwaremin Alkyabban" da kanta Ammi tasa hannu ta yaye hijabin jikin Safeerah mutane na ayiriri wowwww! Ya Allah! Zamewa kallabinta yayi gashinta ya bayyana ga kirjinta awaje lace din yamata kyau matuka Salim ya tsare ta da idanu bayako kyaftawa, hijabin Ammi ta karba taba Anty Asabe, Salim yakasa daurewa juyawa yayi yabi gidan kap da kallo kaman yana scanning yajuya yakalli Soja dake wajen yahade rai ba imani kawai kai tsaye adikile yace "stay outside the gate, the guards should go with you, I don't want men in this compound" saramai sojan yayi yawuce, Baffa da Auwal daman sunje ciki dazu, ba sauran mutanen ba hatta Ammi saida tadan kalli Salim din ganin abinda yayi kawai ta dauke kai ta karbi kallabin taba Anty Asabe sannan ta karbi wani dogon sarkan zinare ta matso tasama Safeerah awuya tana shakan kamshin da Safeerah keyi dayamata dadi sosai kafin ta karbi Alkyabban ta warware tasamata aka sa hulan akanta sannan Ammi takai hannayenta biyu tadago fuskan Safeerah daidai hawaye na kara gangarowa hakanan kawai Ammi taji she feels the girl a zuciyanta, ita zuciyanta ma bazai bari tahau fushi da wannan yar karaman yarinyar sa'ar autanta ba she can't, banda haka Salim dansu yamusu laifi not this girl, calmly tace "welcome to our family Daughter Safeerah" kokarin dukawa Safeerah takarayi Ammi tariketa tace "come here" rungumeta tayi ahankali sannan tasaketa saita kalli Waleed dayayi lamo awajen Salim yana kallon Ammi tamai murmushi tamikamai hannu tace "ya sunanka fine boy"? Salim Waleed yakalla yace "Abee Ammi?" Gyadamai kai Salim yayi kawai sai Waleed yataho wajenta daukansa tayi yamata murmushi yace "Waleed" Ammi tace "Waleed aiko namaka kawa ina Binafa" da sauri Babyn Layla that is just around age na Waleed ta taho da gudu sanye da gown mai kyau tana kallon Waleed sauke Waleed Ammi tayi tace "Binafa ga Waleed, Waleed ga Binafa" washe baki Binafa tayi shima Waleed haka sai kawai takama hannunsa tace "let's go and collect ice cream from Anty Lubna" kawai Waleed yabita happily, Ammi takalli Anty Asabe tace "kuje da ita bari nai magana da shi nazo afara" kama Safeerah Anty Asabe da Layla sukayi suka wuce aka kaita kujeran Amarya ana wake aka zaunar da ita Layla na ijiye handbag nata da Salim yabata.
Ammi ta kalli Salim dayadan sauke kansa kasa tace "call babanka ka gayamai you guys are here, the fact that yama barmu to welcome her means yadan soma saukowa, ka shirya da mahaifinka Salim even if it means saying sorry, yarinyar nan needs to see mahaifinka ta gaidashi u know that right?" Gyadama Ammi kai yayi, Ammi kawia tawuce bata kara cewa komiba, Auwal yataho wajensa daidai yana
dialing number Dady bai dagaba Auwal ya kalla yace "give me ur phone" basa Auwla yayi wayan Dady yakira aiko yadaga yace "Auwal" ahankali yace "nine Dad, is Salim" haderai Ddady yayi yace "Ipy why are you using wayan d'ana kana kirana dashi" dan shiru yayi kafin ahankali yacd "I am sorry for everything Daddy" shiru Dady yayi, ahankali yace "Dad muna gida, ca you come back please" tsaki Dady yayi kawai ya katse wayan hakan yasa Salim yamikama Auwal wayan nasa yace "bari nadan kwanta l hate this nonsense da akayi" yawuce abinsa yana kallon Waleed dake wasa cikin yara ga sweet a hannunsa shida Binafa tunda aka bude gate ya hango Nanah amman tun bayan kallon nan bai kara mata na biyuba wucewa yayi ya gaida Baffa da matayensa duk suka samai albarka sannan yawuce flat nasa ko alamun kallon inda Nanah take baiyiba dudda tanata kallonsa shima Auwal na kallonta yaji wani abu a wuyansa yanda take kallon yayansa flat nasa yashiga yawuce sama abinsa.
EPISODE 56
Da kyar Nanah ta daure tahana kanta kuka sabida wani radadi dataji aranta ganin abinda Salim yamata, wato ko darajan kallo batada shi a idanun Salim? Batamakai matsayin da zai daga idanu ya kallo inda takeba? Sabida wanchan mummunan yarinyar da tulikin danta ya mata haka, ijiyan zuciya ta fuzar tana tahowa tawuce taje tasami kujera tazauna tana kallon Safeerah da kanta ke kasa ga su Anty Asabe ana kawo ruwan lalle za'a wanke mata kafafu hannaye da fuska tradition nasu ne wai cleansing Amarya naman miji keyi, daganan sai kowa yabata kyauta ayi waazi anjima party ayi spraying amarya, yanda Nanah ke kallonta haka su Ameerah da Lubna ke kallonta, zama Ameerah tayi kusada Nanah tace "she's pretty kam yarinyar ga gashi amman wih Anty Nanah ni duk kyan yarinya bazan iya aurenta as bazawara ba, especially ma auren farko, brain din Ya Salim is just wired differently from normal humans why will he leave you for a single mother"? Nanah dayake suna shiri da Ameerah tace "makirci mana bakiga yanda tawani duka tana gaida Ammi na ba ita gamai tarbiyya" Ameerah tace "munafuka kawai she ruin our family sabida ita no more peace tsakanin Dady da Ya Salim" murmushi Nanah tayi ranta fess suna kallon yanda Ammi tafara wanke mata kafafu da hannuwa saikuma gashinta Nanah tayi tsare kirjin Safeerah da kallo tanajin wani irin kishi ganin tafita boobs, tass aka gama aka goge da towel sannan akace kowa yakawo gift nasa, Anty Asabe tadauko wani kwali na wani foodflask dayakai 1M tabata tace "I'm Anty Asabe kowa anan na kirana Aunt, nice kanwar maman mijinki Ammi" akunyace Safeerah tace
"nagode Aunt" Matayen Baffa suka bata gifts masu kyau, Baffa ma yabata takardan fili as gift ahankali tace "nagode Baffa Allah amfana" Layla takawo wani box na mahaukatan lingerie set mai kusan 20 aciki tace "for my Sister" akunyace Safeerah ta ijiye tace "nagode Ya Layla" ta manna mata peck a goshi, Ammi ta kalli Nanah tace "saike" tasowa Nanah tayi tadauki wani jaka da abu keciki tazo wajen hada ido sukayi da Safeerah tsaf Safeerah tagane ta from blog yarinyar ko akwai kyau dasauri ta sunnar da kai kasa Nanah tace "ahh su Amarya badai kunya ba kalleni mana" takalli mutanen wajen tana dariya saikuma tace "I'm Nana Khadijatu ur sister inlaw, nike auren kanin mijinki Auwal" sake kallonta Safeerah tayi cike da mamaki Nanah tamika mata bag din karba Safeerah tayi ahankali tace "thank you" juyawa Nanah tayi takoma sai Ameerah tazo bawani murmushi fuskanta ta mikamata box na kayan makeup tace "sannu" wani iri Safeerah taji ahankali ta karba tace "thank you" Layla tace "don't mind her ita ke bina her name is Ameerah, Lubna sai ke" tasowa Lubna tayi tana murmushi da katuwar jaka a hannunta tazo gaban Safeerah tace "I am Auta Lubna, kinga Ya Ameerah is friends with Nanah can u be my friend too, ya gift naki" dan murmushi Safeerah tayi ta Gyadamata kai tace to
Set na Dior dinning set tabata so expensive tace "thank u we are friends" akahau tafi nan aka fara waka, kawayen Ammi suka bata gifts sosai, Waleed sai rawa yake da yara dasu Binafa Safeerah na satan kallonsa bini bini, cikinta nawani irin ciwo at same time tanajin fitan abu dan faduwa gabanta yayi cus sai yanzu tagane ashe period zatayi kaman ma yazo, abubuwa daban daban akeyi, everyone looks so happy, kujeran datake kai is white tsoro taji kartazo tama bata gashi bakuwa ce kunya takeji ta ma any one of them magana tace mene? Mezata gayama Layla, tace mata period nata yazo salon kowa yasani ai kunya zataji, jakanta ta kalla dake gefenta gabanta na faduwa tana feeling kaman jinin namata rushing itada on a normal day first day baya fitowa ma da kyau but yau datake cikin jama'a see what is happening, ko anxiety yasa period din ke rushing haka oho, ga maranta na ciwo kuma, kanta ma yafara ciwo, hannu tasa ahankali cike da dauriya tadauki jakanta wayan ta ciro all she could think of is just him batamasan mesa ba, message ta shiga tama rasa abinda xatace kawai saitace
"Abee" ko 5seconds batayi da turawa ba yamata reply. "Yes Wife wat is it?" Takai one minute batasan mezata cemai ba sabida jin nauyi ta maida wayan ta ijiye tana kallon yanda suke rawa harda Nanah, hada ido sukai da ita wani mugun kallo tama Safeerah hakan yasa ta sauke kanta kasa, wayanta ne yashiga ringing da sauri tadaga wayan ta kalli screen din
Salim ne rejecting call din tayi da sauri ta shiga message tace "uhn...da.ma.." Tai sending takasa gayamai yamata replying I'm listening dama me?" Daurewa tayi da kyar kaman yana gabanta tai typing "yazo and I don't know what to do ana event" Salim yakai sau goma yana karanta message din bai ganeba kwata kwata, saiya kirata tasake rejecting yamata reply da "me yazo?" Takai kusan 1 min sannan kawai tai typing "period" saikuma takashe wayan gabaki daya duk kunya yakamata gayamasa datayi, wlh ko 1min ba'a daukaba saiga Salim yataho wajen baya kallon uhan kowa kawai wajenta yazo direct tana zaune kan kujeran amare da akai decorating, Ammi dake magana da jama'a tadan kallosa ganinsa wajen, yana zuwa wajen kai tsaye kawai yasa hannu yadagata ita kanta Safeerah saida taji tsoro, ga cikinta daya kulle adan sace yakalli seat din everything is fine, sannan cikeda kulawa da shi baimasan yanayi ba yadanyi cupping face nata da hannayensa biyu, murya chan kasa just for shi da ita yace
"cikinki na ciwo? You look sick" Girgixamai kai tayi da sauri kunya kaman zai halakata tadan ture hannunsa daga fuskanta zata juya kawai yariketa wani dutse Nanah taji a wuyanta ya tsaya takasa numfashi da kyau, sai kawai Salim yadan kalli Ammi yace "Ammi she's coming" ko kallonsa Ammi bataiba sabida bakin ciki da Saleem ke bata, yaja hannun Safeerah da kaman zata fashe da kuka mehaka yake mata duk aka bisu da kallo kunyan duniya yakama Safeerah kaman ta nutse akasa, mesama tamai message itama tunda tasan bawai yanada kunya ko mutunci bane? Ba ruwansa da uban kowa, flat dinsa yabude yashiga da ita yamaida kofa yarufe kawai yadauketa runtse idanu Safeerah tayi hawaye na saukowa daga idanunta yayi sama da ita direct yabude dakinsa yashiga da ita yabude bayinsa ya ijiyeta yasa hannu yana kwance Alkyabban dake jikinta yazare da towel din daga jikinta yace "I will get you pad da mene kuma kikeso" batare data kalleshi ba murya chan kasa tace "shi kadai" fitowa yayi yajamata kofan yadaga wayansa Layla yakira tana dagawa yace "check dakin yaran nan bring me pad" ahankali tace "okay Yaya"dakinsu ta shiga amman wih taduba sama da kasa babu pad kodaya fitowa tayi wajen taje wajen Ameerah tace "kunada pad?" Girgixamata kai tayi tace "bamuda shi few ones daya rage bakinmu na bikin Nanah suka kwashe tass barayi" wucewa kawai Layla tayi tadaga wayan takira Ya Salim yana dauka tace
"Yaya wih babu yan biki sun kwashe musu" ahankali yace "okay" ya katse wayan Layla ma takatse Nanah dataji komi tayi kaman batajiba, knocking gaban bayin yayi yace "kin gama?" Muryanta chan kasa tace "kaya zan chanza" dan shiru yayi sai yabar wajen kofan yatafi closet nasa yabude wani shirt dinsa yazare daga hanger babba ne zai iya kaimata knee yadawo wajen bayin kai tsaye yabude kofa afirgice Safeerah tajuyo tana daure da towel nasa fari tacire gown din dan yayi stain tadaura kan washing machine idanunta har sunyi ja cus tayi kuka abayin, she's in their house for the first time za'ace tabar event tabi miji gashi kayanta sun baci tayaya zata koma waje yanzu?
Rigansa yamika mata, zuwa tayi zata karba sai kawai yajawota jikinsa kaman jira take fashewa tayi da kuka sosai jikinta yataba dan yaji zaft, jikinta haryadau zafi she's running temperature ahankali yace "meke miki ciwo Safeerah"?
Murya chan kasa tana shesheka tace "bakomi"
"then why are you running temperature"?
Ahankali tace "Ammi zatai fushi dani nazo nan wajenka kuma nadade ana jirana awaje" dan murmushi yayi yace "bari na sayo miki pad yanzun nan zan dawo zaki koma, Layla will get you another clothes stop crying" yafito da ita daga bayin yana maida kofan bayin yarufe yakama hannunta yasamata rigan yace "saka wannan" yawuce yafita, rigan tashiga sawa dan sanyi sanyi ma taji tanaji tabar towel din a waist nata dan she's rushing abinda baitaba faruwa da ita on first day ba in her life sai yau, sai kawai tahau gadonsa ahankali dan da gaske zazzabi takeji harda ciwon kai, rabon datai rashin lafiya ta manta, kodan rashin baccin shekaran jiya da jiya ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login