Showing 63001 words to 66000 words out of 160450 words

Chapter 22 - LOKACI BAI KURE BA COMPLETE

M SHAKUR   

01 Oct 2025

132

finest girl diyar lecturer buzuwa an fasa bikinta ango yace ya fasa aurenta ayita gulmanta maybe ma blogs su dauka da wanne zataji a lokacin Salim ya barta ko trending dazatayi both in social media and off social media? Sai lastly Salim won against her kenan tahakura, ya ci amanarta ya yaudareta and he will just go free? Ai she will want to see uban waye bazawaran nan da Dady ya keta kira ya aura, so bazawara ma ya aura mai yaro yabarta budurwa intact, sealed sabida wata data taba haihuwa? No she wants to torture Salim ganinta kadai agidansu married to kaninsa can torture him kuma hakan can make him realize yana sonta cus dole yaji kishin ganinta da Auwal, banda haka she wants to use that love da kowa ke mata na gidan tai making sure nobody in that house will love bazawaran matansa, she wants to be close to him tana ganin rayuwansa da kyau sabida tasan dame zatai hurting nasa the most, sai lastly yanda yayi breaking aurensa da ita saitasan mezatayi tayi breaking aurensa da bazawaran she promised sai sunyi one one, maybe hakan yafaru she will be at peace tasa Auwal yasaketa tazo tanemi wani miji mai sonta ta aura, tasss tagoge hawaye ta tamike tsaye tafito.
Mommy dake wajen tace  kinyi making decision? Gyadama Mommy kai tayi, Mommy tace  Alhamdulillah Allah miki Albarka, I am proud of you, you are not alone Nanah na, I will always be here for you and support you in this difficult phase na rayuwanki, love comes and goes but a mothers love baya taba tafiya, and I love you my precious most treasured adorable Khadijatu wani sanyi zuciyanta yayi she don t wanna hurt Mommy amman tarasa yazatayi kasa suka koma aka zazzauna Dady yace  Masha Allah me nene final answer naki Nanah? Mommy Nana ta kalla, ahankali tace  Mommy I am sorry kiyafemin I don t think har ahada I can get Inlaw s dazasu soni sama da Dady and Ammi ba maida kanta tayi takalli Dady tace  Daddy na I will Marry Yayana Auwal sosai Anty Asabe ke kallon Nanah, itama Mommy kallon Nanah take kawai Dady yamike yazo wajenta yace  stand up stand up dawowa Nana tayi Dady yakama hannunta sai yashiga dan rawa yace  you are my African Queen, Daughter of my dreams sai Abba yazo yakama dayan hannun kawai suka shiga rawa da yarinyar iyaye mata na kallonsu da Baffa da Liman ma haka, wato boko yama Dad dashi Abban Nanah yawa, Nanah sai murmushi take na dole but kuka ne azuciyanta Babanta da Dady na farin ciki suna raye raye da ita ran Mommy yayi matukar baci.
EPISODE 3?? 7??




Around 2 na rana Auwal na zauna an office wayansa yahau ringing screen din ya kalla ganin Daddy ke kiransa hakanan yaji tsoro ya rufesa, are they back daga gidansu Nanah? Daddy yakira ya gayamai bata yarda ba ne ko? Tace tafasa auren gabaki daya dan idan shine Nanah I will never go for brother idan yaya rejected me gwara na hakura da auren duka, sake ringing wayan yayi hakan yasa yadaga muryan Dady so sharp awayan yace  dan albarka na! My champion! My Auwalulu, Yaron Babansa, kasan mene namaka order 5 luxury latest cars they will be here in 2weeks, nasaya maka yatch, Auwal fadamin kome kakeso and it s yours! Wani sanyi jikin Auwal yafara cus from yanda Dady is happy Nanah must have agreed sai kawai yaji jikinsa yahau zafi kaman zazzabi zai rufesa Dady yace  Auwal ahankali yace  uhnn Daddy yace  Nanah ta amince zata aureka, I ve sent my designer nasan kana company yazo yayi measuring naka amaka dinkunan biki, yanda kacireni kunya Allah ya biyaka da gidan Aljanna, I love you so much my Rahul Bayya, Choti Choti Chupke Chukpe Beta Auwalu duk yanda yakeji saida indiancin Daddy yasa ya murmusa Dady kam is happy, bakomi as long as mahaifinsa is happy, Yayansa is happy toh shima he is, he will treat Nanah well and respect her, he s okay with her idan she accepts him they will live normal and make babies other wise it s her call he is very much okay with her daman bawai yanada budurwa bane ahankali yace  Dady your Hindi sucks nidai bye I m working Dady yace  chalo my fine beta, bye ya katse wayan ya ijiye.
**

Jiya aka daura auren, jiyan Mama taje kasuwa and bought everything dazata bukata na ma yarta magunguna harda zabi, daganan tabiya gidansu mai magani ta biyata payment nata full zata dinga zuwa kullum daga safe zuwa yamma ta tafi though basu san kwana nawa Salim zai barta anan ba matan dai tace bill datama Mama na 2weeks ne Maman tace okay Mama tadawo gida tafara nata, zata mata nata magungunan dayan matan zatai mata dakuma gyaran fata da gashi.

Tsakanin jiya da yau da matar tazo Safeerah taci abubuwan da wasu har batamata rai suke, she knows menene kayan mata she knows wat they do ai ta taba aure, but kawai bataga amfanin bata ba, auren nan sabida su Baba tayishi shima kuma yace he s not marrying her for anything toh why all this stress kuma tun jiya da aka daura auren dudda ya aiko mata da waya bai kirata ba, yauma gashi yamma tayi bai kirata ba.
Karasa cin abun da mai gyaran tabata tayi da kyar tana batarai Matar tai dariya tace  Mama wannan Safeerah batason magani Mama tace  ai wannan dama sauki bazakiga tashin hankali ba sai ance Feerah tasha kwayoyin asibiti ko allura rannan zakiji kaman ki yankata Matar tai dariya tace  aiko Safeerah ki shirya shan magani yau day one ne, gyara zan miki na musamman, bakaramin dadi naji da mamar ki tacemin CS aka miki haihuwan Waleed ba aikina zai zama simple, dudda koda haihuwan ma d kanki kikayi still zan iya aikina kuma komi lafiya lau kawai CS is easier, zakisha mamakin gyara takalli Mama tace  nan da 3days zata fara chanzawa idan nutrients din suka fara bin jikinta, package din matan sanata kika biya zakuga aiki da cikawa murmushi Mama tayi tace  ko bayan aure idan akwai wani abu ki sanar dani sai adinga kaimata, gyara ai shine mace, ance duk kyanka ka kara da wanka, sai inda karfina ya kare akan wannan mai kan kwakwan turo baki Safeerah tayi Matar ta kwashe da dariya tace  haka kikeda shagwaba ahh gaskiya mai gida ya more mikewa Mama tayi tace  dan Allah koma zaki koya mata irin yan abubuwan nan ne Matar dasauri tace  ga M shakur Safeerah ai Coitus Junction class nata zata shiga kawai, kinga su shagwaba, iya kwanciya da miji wlh sai mijinta yayi kuka Dasauri Safeerah tamike zatabar wajen kunya kaman zai kasheta sabida Mama, Mama tace  sha zamanki nayi nan yimata maganan Hajiya Rakiya Mama tafice matar tace  kalli Safeerah kinsan mesa nake sonki? Sabida y ata itama ta taba rashin dace ita wata biyu tayi gidan miji ya sakomin ita but yanzu yarinyarata is the happiest girl agidan miji, and lokacin kaman ke take bata wuce 20yrs ba, na kalleta saina fara kuka inacewa this my small girl bata chanchanci zama bazawara ba at this young age, but as rayuwa yacigaba da tafiya nazo na gane cewa everything happens for a reason Safeerah, sabida aurenka na farko yamutu don t be ashamed, hakka Allah yaso, sabida mutane na kiranki da bazawara don t feel anything bazawara sunane da mutane suka kirkiro suka radama mata irinku just to make you feel kaman bakuda daraja or kaman taku takare kun shiga uku kun lalace kaman irin kunada bad luck, in reality you girls are just victims or marriage that didn t work! Or marriage that s toxic, or marriage da akwai rashin compactability, second marriage means second chance! Ki shiga second aurenki with everything you ve got! Tsoron Allah, biyayya, hakuri, juriya, kawaici dakuma yawan addu a cus babu inda ba jarabawa shiru Safeerah tayi maganganunta sun ratsata sosai matan tace  the only difference between ke da y ata is ita mijin datazo ta aura yanada wata matar kekuma tacemin kaman ke kadaine yafadi komi akansa amman baice yanada mata ba da yanada ita dazai fadi, so a irin auren nan you will face challenges wajen family sa cus yaro yakama ya auri wacce ta taba aure harda da as first wife ana bala i, zakiji maganganu daban daban, akiraki bazawara, ragowan wani, akira danki dan Angola but don t pay attention, remember cewa this aure kinshigo sa ne as someone with past experience, maganganun nan karma _u shiga zuciyanki balle haryayi affecting yanda zaki treating mijinki ko yaga bacin rai ko wani abu, magana daya nakeso ki rike tell your self inhar kina matsayin wacce ta taba aure, and harda yaro but this mutum yazo wup ya aureki you must be special! Very very special daya gwammace ke da budurwa, kuma ita mace wacce ta taba aure harta haihuwa tanada wani sirrin ni ima da yara kanana yammata basu dashi! Kome za a gayamiki na bakanta rai ki gayama kanki you are very special saisa har wane ya aureki ya mance dawasu kinajina you are not an ordinary person Feerah, kin iya shagwaba do it ma mijinki mamanki tacemin shekaransa 39 ba yaro bane kina 20 ya girmeki da shekaru sha tara, be feminine, let ur feminine energy flow, babu amfanin nuna ke strong Iron Lady ce, Koke gaki feminist, be under your husband, charm him with ur aura, your simple touches, sensational ones, caresses, soft kalamai, girmama wa, abinci mai dadi, iya kwanciya dashi akan gado, please ke ba budurwa bane don t come and be doing kaman bakisan menene sex ba hakan nasa maza suji an raina musu wayau, be good with him in bed, let him have you duk sanda yakeso, kisses him all over, feed him manyan nonuwan nan danaga kinadasu dawani irin sauri Safeerah tajuya mata baya Matar tahau dariya sosai dan yar duniya ce gadaita harda jikoki tace  ana kiran magrib kinga sarkin kunya gobe zamu cigaba, I will lecture you for 14days sannan zan baki magunguna bama wacce mahaifiyarki tabiya ba no wanda nakema y ata ta cikina cus I see you I see my Rumaisa she is 25yrs yanzu ta haifanmai yara biyu, yaranta uku in total daya na auren farko, saida safe Feerah akunyace muryan Safeerah kasa kasa tace  saida safe, nagode Umma murmushi matan tayi taji dadin magananta tabude kofa tafito tasauko kasa taga Baba da Waleed afalo Waleed na guje guje yasaka takalminta tahau dariya tace  tohh kai mijin baka bada sadaki ba sai adaumin takalma haka akeyi Baba yayi dariya yace  to kaji ko Waleed tsayawa Waleed yayi Baba yace  cire takalmin ahankali yacire Mama tace  Waleed, Waleed Allah yamaka albarka matar tace  Ameen duk randa nawa jikokin suka shigo gidana, gidan kansa kuka yake sabida Oganni sun zo daga Mama har ita da Baba sukahau dariya Mama tarakata har waje tashiga mota abinta ta tafi.

Tashi Safeerah tayi tawuce bayi kaya tacire batasan wasu kalan magunguna bane and just jiya tafara sha dasu pepper soup din but she keeps getting wet unnecessarily, wanka tayi tadauro alwala tafito saitaji sabon wayanta na ringing da sauri tai wajen gabanta na fadi sai yau wayan yayi ringing tun jiya screen din an rubuta Major Salim kaman wacce ke shakkan dauka takai hannunta tadauki wayan takai kunnenta murya chan kasa tace  hello shiru taji ba ace komiba, ahankali tace  ina yini ? Murya ciki ciki kaman ance yayi magana da ita dole yace  I m on my way! Faduwa gabanta yayi jin yace he is coming, me hakan ke nufi? Tafiya da ita zaiyi, racing kirjinta yafara batasan sanda tace  uhn d& .an& .Allah saikuma tai shiru kaman zatai kuka muryanta sounding like shagwaba tace  ni ban shirya tare& .wa ba takarasa maganan tana turo baki, bawasa kan muryansa yace  idan kuma nace saina tafi da ke yau dinfa? Can you stop that from happening? Yayi maganan da mugun isa, lumshe idanunta tayi kaman zata fashe da kuka ahankali tace  dan Allah kayakuri! To be honest he was testing her ne shida yau aka fara aikin cire kayayyakin gidan ana fitar dasu ma he knows yanda yace he is coming tadauka tafiya zaiyi da ita, but the way she apologized kuma saiyaji wani dadi and sense of yes nine mijin, kai tsaye yace  I will think about it! Gyadamai kai tayi kaman yana gabanta, calmly yace  ina Waleed? Murya chan kasa tace  yana falo tareda Baba  ke kina ina ? Asanyaye tace  ina dakina!  Wat are you doing? Shiru tayi tarasa mezatace yanda yake tambayanta kaman wani dan sanda, kusan 5secs tai shiru ahankali tace  wanka nayi  kinyi sallan magrib ? girgizamai kai tayi tace  a a yanzu zanyi strictly yace  banson wasa da salla, go and pray ya katse wayan ta ijiye tana wasu yan tunani yanzu wannan ne mutumin data taimaka that time? Daman haka yakeda hali so stricken kaman wani banatasan dame zata kwatantasaba, ba wasa no nonsense although ko lokacin somehow somehow she noticed ai baya wani kulata then yana shan kamshi but ta dauka ciwonsa ne dakuma ana son kashesa wata gown ?1k1n kayanta tadauki tasaka da hijab tahau kan dadduma tafara salla.

Tana zaune awajen akai isha i salla tayi tai shafa i da wuturi taji sun dawo sai wajajen 8:30 taji dan kukan Waleed sai chan taji yayi shiru saikuma taji budewan kofa wayanta na ringing at dsame time takalli wayan shine kai wayan kunne tayi.  I m outside yana fadi ya katse wayan tashi tayi takalli kanta dan gown nata ne ajikinta nawani soft material ba komi ciki sai this hijab data saka ta chanza kaya ne? Tai gayu ne? Tafesa turare ne? Dukta tambayi kanta but why will she when ba sonta yake ba itama ba sonsa take ba, he is just helping her sabida she helped him, juyawa tayi tafito a stairs taga Mama na hayowa rikeda Waleed da cheese balls ke hannunsa tasan shiya kawo tace  ai na dauka bakisan meya kamata kiyiba Mama ta harareta tawuce abinta takarasa saukowa Baba tagani a falo dan sauke kai kasa tayi tace  Baba yana kirana dasauri Baba dake kallon news yace  maza tafi abinki keda mijinki harsai kin gayamin kunya taji amman tawuce kofa tabude ahankali hada ido sukayi yana tsaye jikin motan yana sanye da yadi milk mai kyau anmai aiki a wuya tundaga wajen tana jiyo kamshin dayake ya tsareta da idanu da kawai taji ta burkice tasauka kanta kasa dasauri tana kalle kalle neman takalmin dazata saka kafanta, babuma takalminta awajen kawai tasaka na Mama yama mata yawa Mama 41 takesa takalmi itakuma 38 ne size nata tafito tajawo kofan, bayan mota yabude mata yana kallonta alamun tazo tashiga nan, yanda kirjinta yahau bugawa zaka dauka shidewa zatayi ta taho ta shiga ta zauna ya maida kofan yarufe yazagaya ya shiga ta dayan side din dawani irin sauri ta sake matsawa dab da kofa sarai ya lura hakan yasa yashigo cikin motan comfortably yadan matso kusada ita kaman baimasan yanayi ba yasa hannu yarufo motan yajuyo yakalleta duka duka space dake between them baifi Waleed yazauna ya cikashe ba.
EPISODE 3?? 8??





Faduwa gabanta keyi ga motan sanyi AC a kunne, dan dago kanta tayi jin shiru hakan yasa suka hada ido dasauri ta maida kanta kasa ahankali tace  ina yini bai amsata ba strictly yace  I am here to talk to you about auren mu! Faduwa gabanta yayi amman ta gyadamai kai hannayenta yaga sun fara rawa she is scared, lumshe idanu yayi ya sassauta muryansa sosai yace  dazu kince you are not ready ki tare ? Gyadamai kai tayi kanta na kasa, sake sassauta muryan yayi cu??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????s yanaso tadanyi magana dashi yace  how many days kikeso nabaki ki shirya and be ready? Shiru tayi tana shakkan gayamai wata daya, mugun mugun shakkan gayamai haka take for mutumin dayaso yatafi da ita yau hakan yasa ahankali tace  dan Allah kabani 3weeks! Kai tsaye yace  I can t! Dan dagokai tayi ta kalleshi wai wannan wani irin mutum ne, dasauri ta maida kanta kasa ganin sun hada idanu, calmly yace  I will give you 14days! Dasauri tadago kanta cikeda mamaki cus bamata dauka zai bata yakai hakaba wlh tadauka yace sati daya amman ganin yabata 2weeks for the first ever time tunda yahadu da ita saiyaga tai dan karamin murmushi tamaida kanta kasa, wani abu yaji yadaki zuciyansa that is very sharp numfashinsa na neman ya tsaya sabida murmushin datamai da kyar ya saita kansa yajuyar da kansa ya kalli waje na kusan 1min motan yayi tsit kafin anatse yace  as your husband Safeerah I have few rules danakeso na sanar dake, banso ki tsallake dokata inason ki kiyayesu! Gabanta faduwa yahauyi aranta tana cewa wani kalan mutum naje na aura ni Safeerah? Atsanake yace  banson kawaye idan kinada su ma yanzu kirabu dasu! You re staying a barrack inda nake aiki yawanci ina wajen inhar ina Nigeria, ban yarda kiyi establishing any friendship with wata awajen ba, bance kije gidan wasu ba and nobody should come to my house too, if needs be ko wani abu comes up I can take you muje tare, biki, suna or wani gathering just know bazakije ba, bason yawan waya, outside Mama and Baba and maybe nan gaba nasan few

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login