Showing 69001 words to 72000 words out of 160450 words

Chapter 24 - LOKACI BAI KURE BA COMPLETE

M SHAKUR   

01 Oct 2025

104

Safeerah ina Waleed kuma? Wlh bansan meke faruwa ba sai yau haka nabi mota tundaga katsina nazo da safiyan nan, kana ina eh? Wlh nadamu sosai kana ina? Dan Allah kafadamin Malam kuna ina iyye ? Yasan yayarsa Zainabu tadamun kam anatse yace  ina gidana Adda dayake wayan na speaker Momma ta gyara zama jin abinda yafadi cikeda mamaki, ahankali Zainabu tace  gidanka Malam? Gidanka ? Gyadamata kai yayi yace  kwarai yau nake shirin kiranki daman banji dadi bane, an mini aiki ne a idanu Alhamdulillah idanuna sun bude rass, saikuma na aurar da Safeerah to mijin data aura Salim shiya bamu gida, yakuma biya duka kudin asibiti na! Yarki zata tare nan da sati biyu Karaf a kunnen Salma dake saukowa daga sama, badai wannan hadadden guy daya dauki Baba bane Safeerah ta aura ba? Hope badai shi bane? Like hope badai shibane cus she picked interest in that man cus tana ganinshi she sees money, real money ba kalan nasu na gado dayakusan karewa ba.

Wani irin murmushi Zainabu tayi na farin ciki sosai takalli Momma data hade fuska tamau tace  Alhamdulillah Allah mungode maka, Malam Allah yabaka gida muhalli naka, kaga turomin address nazo na ganku Baba yace  yanzu kuwa dan muna bukatan zama atattauna kan shirye shiryen biki ya katse wayan, Zainabu takalli Momma tace  tunda yabar gidan ki ai shikenan komi yakare zakije ne ko bazaki je ba ? Wani mugun kallo tamata tace  ai na yafe Shu ibu ya aurar da Safeerah ban sani ba, ai na yanke sa amatsayin dan uwa, kadai kije ko ajikinta tace  eh zani, mu uku iyayenmu suka haifa, kina babba idan bazaki hada zumunci ba, ni zanyi zumunci daku daidai wayanta na ringing taga address ne tadauki wayan zata juya dasauri Salma tace  zan biki Aunt hararanta Zainabu tayi tace  ke din Salma? Sha zamanki tareda mamanki tana maganan tafice Momma tai tsaki tace  shashasha ki dawo ki tattara ki koma inda kika fito Zainabu tace  Alhamdulillah dan uwana nada gida tafice abinta, Salma ta taho tazauna kusada Momma tace  Momma indai mutumin danaga yadauki Baba ne rannan mijinta wlh bazan yarda ba, kinga yanda yahadu kuwa da alamu yama fimu kudi, irin mazan nan dani suka dace ba da ita ba, a ina tama hadu dashi? Momma this people munafukai ne fa when did they know this kind of person anata boyemana bamu sani ba Momma kafa tashiga kadawa bakin ciki yama hanata magana.

Saida Baba yayi magana a waya da security na gate akabar Zainabu ta shigo, Safeerah ne tafita waje dan tarota tana bala in son Zainabu, batada shi, she s divorced tana struggling a katsina da saida abinci, tasan datana dashi data taimakesu, bolt ya kawota daga nesa ta hango Safeerah parking tasa bolt din yayi tabasa kudi Safeerah tai wajenta da gudu batai wata wata ba ta rungumeta tace  Ummi naaaa Zainabu tace  laaaaa kaga yarinya wai ke bakisan kin girma ba yanzu harda da? Wannan kyau haka dakikeyi kinji kamshin dakike kuwa uwa na lasheki an fara gyaran jiki ne? Kin magana Safeerah tayi tacema mai bolt nawane kudinta yace 6k takirgo kudin tabasa Zainabu sai kallonta take, tace  ina wannan tijararren yaron mara mutunci mai halin turawa yaki abincin mu sai nasu dariya Safeerah tayi bata amsa ba sabida kofa da Mama tabude tana rikeda Waleed dake murmushi yana kallonta tace  ohhh wai fashewa zakayi Waleed da kiba? Aiko nazo kadingacin tuwo kenan dan kaniyanka turo mata baki Waleed yayi Mama tace  sannu da zuwa sannu da zuwa shigowa ciki sukayi duk falo tana kallon gida tace  Alhamdulillah, Alhamdulillah Alhamdulilah kaga ko Malam banasha gayamaka ba Allah baya bacci wlh, watarana sai labari yau ku dubi gidanku, ai Mama Kubra bataci sunan damuke kiranta dashi ba wai Mama, Allah wadaran naka ya lalace zama sukayi ana hira Safeerah tawuce kitchen takawo mata abinci lafiyaye tafito Zainabu ta kalli abincin saita kalli Mama tace  kinga rayuwa ko? Murmushi kawai Mama tayi batace komiba sukahau hira, Baba da Mama na bata labarin yaron da komidai hakan yasa Safeerah tamike zatai sama Zainabu tace  zonan takalli Mama tace  kekuma kira mun shi dan shiru Safeerah tayi, Zainabu tace  kiramin surukina nace gyadamata kai Safeerah tayi tace  bari na dauko wayan tawuce sama zuwa dakinta tashiga tazauna tadauki wayan daya sayamata hakanan kirjinta yahau bugawa, dialing number nasa tayi takai wayan kunne, zaune yake abayan mota sanye da uniform, wasu sojoji na jansa wayansa ne yayi ringing screen na wayan ya kalla ganin line daya saya yayi saving da Major Safeerah na kiransa yasa yayi jimm yana kallon screen din baya ko kyafta idanu saida wayan ya katse sannan yayi dialing number back, ganin kiransa back yasa taji kirjinta yasake bugawa takai wayan kunnenta, tana dannawa kawai taji magana ya makale mata a wuya, anatse da murya dake a kwance mai bala in taushi yace  how are you? Wani iri taji muryansa ajikinta he s always too serious shiwai baida raha da barkwanci, da kyar tadan saita kanta, kaman wata yar baby tace  Assalamu Alaykum, uhmmm ina yini ya aiki shiru yayi muryanta a waya da real baisan wanne yafi dadi ba, ahankali yace  how is Waleed? Batasan meba kodan tasaba duk duniya Babanta da Mamanta suke tambayan Waleed but ayanda yake tambayesa duk sanda zasuyi waya saitaji wani dadi da sanyi dakuma natsuwa aranta, ahankali tace  lafiya lau yana wajen Baba a falo, uhmmm& . Takasa magana, cikin isa da izza yace  me kike bukata? Dan rage muryanta tayi sosai kaman tana tsoron gayamai ko karyace a a hakan yasa tace  Ummi na tace nakira ka zatai magana dakai awaya shiru yayi chan yace  who is Ummi?  Yayar Baba Safeerah tafadi asanyaye gabanta na fadi karyace no, anatse Salim yace  that one GRA ? Yafadi muryansa sounding very strict, girgixamai kai tayi tace  a a ba itaba, su biyu ne wannan daga Katsina tazo yau tai shiru ganin yayi shiru baice komiba yasa ahankali tace  dan Allah! Kunya zataji idan bai magana da Zainabu ba, wani sanyi yaji but still yayi shiru, jin baice komiba yasa jikinta duk ya karaya kaman zatai kuka ahankali tace  she s nice  is that abinda zaisa kiyi kuka yanzu? Salim ya tambayeta ganin kaman tana gab da kuka muryanta harya chanza duk sai jikinsa ya mutu, ahankali yace  ok yafadi chan kasa hakan yasa ta tashi da sauri tayi dan murmushi tafice zuwa falo takai wayan taba Zainabu data karba tace  mijin naki ne Feerah? Kin magana Safeerah tayi tajuya tawuce ta tafi abinta takoma wajen Umma mai gyaran jiki.
Tana zaune adaki Zainabu tashigo rike da wayan tabata tace  gashi nan mijinki zaiyi magana dake turoma Zainabu baki tayi, Zainabu ta dungure mata kai tajuya tafice wayan takai kunnenta tace  hello dan shiru yayi chan yace  can you drive? Zaro idanu tayi tace  a a shiru yadanyi chan yace  zan aiko miki da mota da driver for shirye shiye dazaku yi, your Aunt tace zakuyi sayayya dake, I told her you can t go out ban zan tura mota taje ita baki tasaki yanda yake magana kaman irin shine me ita din nan, wai shi baida kunya yanzu Ummi yagayama bazataje ko ina ba, jin shiru batace komiba yasa yace  anything else dakikeso ? Kaman bazatai magana ba tace  babu komi asanyaye tace  thank you shiruuuu yadanyi zuciyansa yamai dadi sosai, ahankali yace  Ameen, my regards to Waleed ya katse wayan.
EPISODE 4?? 1??





Yau da sassafe ta tashi arayuwanta tanason Yasmeen dudda sau biyu kawai ta taba haduwa da ita, itada Yasmeen are age mate itama she s 20 but bata zama da Zainabu a katsina sabida tarabu da Babanta, Yasmeen kuma a hannunsa take saidai idan tasami hutun school ko yaga dama yakan barta tazo wajen Mamanta agidan, da suna Abuja Ummi tkawota gidansu suka hadu itama tanason Safeerah sosai sukanyi waya but ba sosai ba, Zainabu tace zatazo yau, girki tashigayi tun kafin kowa yatashi Mama ta shigo kitchen din tace  yau fa Yasmeen zatazo murmushi tayi tace  Mama Allah sa Babansu ya bari tadade this time Mama tace  sabida tazauna har bikin ki ? Dawani irin sauri ta kalli Mama dan kwata kwata ba wannan ne aranta ba kawai tai missing cousin nata ne simple hararanta Mama tayi tace  maza zo ga magungunan ki Mama ta bata cup data hada dan bata fuska tayi ta karba zata ijiye Mama ta harareta hakan yasa ta shanye, hannu Mama tasamata suka karasa girkin Zainabu na gidan Momma amman zata kwaso kayanta tadawo nan abunta, tawuce sama tashiga dakinta tana kallon Waleed dake bacci tai wajen gadon kawai ta rungumeshi tace  wai bazai tashi ba eh yaron nan tamai chakulkuli murmushi Waleed yayi yana mika tadago tamai kiss a kumatu tace  helloooo Waleely Baby bude idanunshi yayi ashagwabe looking so cute yace  Ummyyyyy kankamesa tayi tace  oyoyoooo Waleed, wlh inason yaron nan sosai sosai my fine boy Waleed yawani washe baki ya kankameta yakai hannu zai taba boobs takama tace  bana hanasa ba dariyan rashin gaskiya yayi yace  Ummyyyyy Safeerah tace  ko kaine kadai mai sunan nan sai haka kaman kai kadaine me Ummy, baraka fara magana da kyau ba saura 3months kayi 3yrs fa daukansa tayi tana mikewa tsaye tace  muje muyi wanka yahau kokarin guduwa normal drama wanka tarikesa gam tace  kazami kawai baraka gudu ba bayi suka shiga tamai brush da kyar ya yarda da wanka suka fito ta shafamai mai batasamai pampers ba yahuta ta shiryashi tafito dashi takaima Mama tace  Mama Alhaji Waleed yatashi natafi wanka kafin Umma mai gyara tazo Mama ta karbeshi tace  zo mijina .

Wanka ta shiga tana cikin wankan taji muryoyi akasa da sauri tashiga wankan da sauri chan taji muryan wata yar budurwa na.  Feerah wannene dakinki ? Ko fuska bata tsaya ta wanke da kyau ba taja towel tadaura tabude bayin tafito da gudu tabude kofanta tafito wata yar budurwa ce wacce kansu daya yanayin hasken fatansu daya ma dan Safeerah hasken Baba ta dauko Yasmeen hasken Ummi ta dauko tana sanye da abaya hannunta rike da handbag tana ganin Safeerah ta jefar da handbag din tace  Safeerah Safeerah tace  Yasmeeen suka wani rungume juna towel din Safeerah na neman faduwa dasauri Yasmeen tasake ta tana dariya tace  ni duk kin gogamin sabulu wlh baki fitaba muje ki koma bayi Safeerah ta kwashe da dariya ganin tasama Yasmeen kumfa ajiki, Yasmeen takoma tadauki jakanta suka shiga dakin Safeerah tafada bayi Yasmeen tafada gado tana kallon ko ina.

Fitowa Safeerah tayi daga bayi Yasmeen ta taso dasauri tace  ke Feerah an ina kika samo mai kudi haka? Wannan dankareren gida daya baki as sadaki ai yafi 300millions tabe baki Safeerah tayi tana daukan kayan dazata sa tajuya mata baya tana rufa da zani ta shirya tasa kaya tajuyo tazo gadon tana kallon kalaban da akama Yasmeen dayake itama tanada gashi Salma ma nada gashi but Safeerah dukta fisu Yasmeen ta kabar da hannunta tace  kibani labari zama da kyau Safeerah tayi tace  kin tuna wani dana cemiki an kusan kashewa a kano dana boye a wardrobe din Mama? Dasauri Yasmeen tace  eh ke shine? Ggyadamata kai Safeerah tayi, Yasmeen tace  kai to how come ya aureki ? Labarin komi tashiga ba Yasmeen suna ahaka Mama tabude kofa dauke da Waleed dayaci yayi nak tace  toh iyayen gulma an hadu ga Waleed mun tafi dasauri Yasmeen tadauki Waleed tace  Kai ina zaka da ci eh, nasayo maka mota tabude jakanta taciro wani mota mai kyau tabude a leda taba Waleed ya karba yana tsalle Safeerah tace  me kace Waleed dasauri yace  ahh ampana Yasmeen ta kyalyace da dariya tace  saifa Ahh ampana gwari kawai takalli Safeerah tace  yanzu kawai dan ya taimakeki ya aureki? Gyadamata kai Safeerah tayi, Yasmeen tace  karyane sonki yake hararanta Safeerah tayi tace  tashi muje falo kici abinci tashi Yasmeen tayi tadauki Waleed tana salati tace  wai me dan nan keci haka yaro kaman na dauki buhun doya Masha Allah hira sosai sukahau yi Yasmeen taci abinci tai nak Safeerah told her everything Yasmeen tace  tashi dan Allah mu zagaya wannan hadadden estate din maganan sa data tuna jiya yasa gabanta yadan fadi amman kuma ai ba zuwa zaiyi ba, kuma Umma mai gyara bata riga tazo ba, gyadamata kai tayi tace  ga takalmin Waleed chan a falo samai bari na dauko gyale sama Safeerah tawuce zip din atampan datasa skyblue da red flowers taja da kyau doguwan riga ne A shape ya zauna ajikinta sosai, ta kirjin shima ya kamata, most times bazaka taba gane Safeerah nada burst ba sabida kalan kayan datake sawa saika zauna da ita but yau rigan ya nuna cikan kirjinta sosai, parking gashinta tayi da kyau babu komi fuskanta banda wani dan makalen dankunne dake kunnenta daya karama fuskanta kyau sosai ta dauki karaman red veil kawai tajefa aka ganin ba fita zatayi ba suna nan cikin estate and again bata wani ganin mutane estate din kaman ba mutane ciki ai she can t even call this fita tunda cikin estate kawai zasuyi tafiya bata taba fita ba tun rannan data dauko kayayyakinta fa, gyalen iya wuyanta ya tsaya shima wuyan bai rufu da kyau ba, gabaki dayan kirjinta awaje, tasaka normal slippers na gida tana kamshi turare sosai abinta dan kullum sai an dafata da turare ba karamin gyara ake mata ba, tasauko kasa Yasmeen dake rike da hannun Waleed takalleta tai murmushi tace  wlh wayanda suka sanki ne kadai zasu yarda cewa kin taba aure harkin haihu cus u still look like yar secondary school, kawai nonon nan ne kesa asan kin wuce yar secondary school hararanta Safeerah tayi tace  yan katsina akwai batsa haba shewa Yasmeen tayi tabude kofa tace  zakiga batsa gun mijinki dasauri Safeerah tajuya Allah yasa bakowa a falo daga Baba har Mama na sama, Yasmeen tace  muje kaji Waleed Waleed na ganinsa awaje kawai ya fizge hannunsa daga rikon Nana yasa gudu, Yasmeen tace  laaaa kugan mini yaro tabisa da gudu itama Waleed najin dadi sosai estate din bakowa while Safeerah na dariya tafito tarufo kofan ta ga Waleed na gudu Yasmeen na binsa yana dariya sosai he s having fun sai kawai itama kaman yar yarinya tasa gudu tabisu iska na jan gyalenta kasa gashinta ya bayyana donut datayi ya warware yafado bayanta hakan yasa ta tsaya jin gashinta na bin bayanta na lilo da sauri tasa hannu taja gyalen tarufe gashinta ta mance da jelar batada lokacin gyara parking awaje.
Yana wajajen gate yana jiran motan dake gabansa yawuce ya shigo estate din yaji ance Waleed da karfi daidai motar ta wuce yaga wata na bin Waleed dake gudu yana dariya saiga Safeerah itama tafito tana binsu tana gudu gyalenta ya sauka abayan wuyanta, wani yirrr yaji tsigan jikinsa na tashi, ransa na bala in tsananin baci ganin matarsa like this a titi ance ya wuce fa dan shi ba a dubasa securities sun sansa but baima sani ba sabida kallon Safeerah dayake, horn da akamai yasa yaja motan yashiga dawani jaraban gudu, yana kallon sanda ta tsaya taja gyalen zatacigaba da gudu dan ta cinmusu yayi wani wawan parking da saida tires nasa sukai screeching making scary sound da saida Safeerah ta tsaya ta bala in firgice dan ta dauka an kusan bigeta ne ko hatsari akayi sabida yanda tires sukai kara takai hannayenta biyu tadaura a kirjinta tana wani irin nishi tana kallon motan da gabaki daya tinted ne batasan na waye ba, wani irin kallonta Salim yakeyi daga cikin motan tundaga saman kanta da gyalen ya zame yayi baya ana ganin gashinta zuwa wuyanta dayake iya ganin skin din, zuwa kirjin???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ta da shi yake abude gabaki daya babu mayafi awajen, jelan gashinta na lilo kawai yabude mota a zafafe yafito yamata wani kallo yana maida kofan yabuga saida jikinta yayi motsi sabida kara kirjinta yashiga bugawa ganin yanayin sa tama rasa mezatayi bakinta na motsi, tana tuna all abubuwan daya gayamata jiya, hannayenta suka shiga rawa takai daya tana kokarin jawo gyalen yarufe kanta da kyau tama kasa ja cus bamataji gyalen saman kanta ba tace  in& & ina& ..k& .wa& & n& &   get in the damn car! Ya daka mata tsawan da saida taji kaman cikinta ya hargitse batasan sanda tasa hannu tabude motan ta shiga ciki ba tamaida kofan tarufe bude motan yayi yashiga ya kunna tanaso tacemai su Waleed amman takasa magana yayi wani crazy reverse azuciye saida yabuge flower pot nawani gida yajuya zuwa kofar gidansu yayi parking yajuyo yakalleta cikin kakkausan murya yace  wani kalan shiga ce wannan? Yanuna kayan jikinta, kasa magana Safeerah tayi wlh gabanta faduwa yake sosai, idanunsa looks kaman zai kasheta tsabagen fushi.  I m talking to you Safeerah! Runtse idanunta tayi jikinta har zabura yake tace  a& ..t& ampa da gyale cikin zafin zuciya Salim yace  haka matan auren gidanku ke sa kaya? Kasa magana tayi, buga sitarin mota yayi yasaka mata tsawa sosai yace  magana nake miki, is this how matan aure ke sa kaya gidanku? I

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login