Showing 51001 words to 54000 words out of 160450 words

Chapter 18 - LOKACI BAI KURE BA COMPLETE

M SHAKUR   

01 Oct 2025

96

asace ta tura gaban gate tashiga ba kowa compound din wuf tafada dakinsu na gateman, ghana masgonta da credentials nata ta sunkuta dana Waleed dana Mama da Baba duka tafito dasu tafara kaiwa waje one one keke na tayata sawa daidai tadauki na Waleed Salma tafito tace  sata kikeyi ? Safeerah tace  bakuda abunda zam sata tadauki jakan zata fice Salma ta fizge tace ai mu muka sai kayan ki barsu anan kallon Salma Safeerah tayi batason rigima ga gidan gyaran hali data tuna saita barmata tajuya tafice fuuu tashiga keke yaja sukabar unguwan har layinsu da kyar estate din suka bari keke ya shiga.
Wuraren 11 tafito daga keken yatayata sauko da komi tana shiga dasu Mama kawai ta kalleta bata cemata komiba, sama sukakai komi Mama tawuce ta chanza kaya tasaka atampa mai kyau da babban mayafi, Baba ma ya shirya cikin shaddarsa mai kyau duk daga kayan da Safeerah ta kwaso musu, itakuma tasake wanke dan tayi zufa tasaka normal gown nata tasaki kanta danyasha iska tajika tai kwanciyarta tanaji anyi baki gabanta yafara faduwa.
Aminin Baba yamusu iso falon, Baffa yafara shigowa dawani abokinsa, sai mahaifin Kabir, sai Auwal da Layla data saka wani lafiyayyen lace, sai Salim yasaka shadda mai kyau fara kal tareda KB, duk zama sukai afalo aka gaggaisa Waleed dasauri yaje wajen Salim yadaukesa sai wasa suka da yaron barinma Layla dan Waleed akwai kyau gasa tuluki kuma yasa kaya masu kyau, anatse Layla tace  Mama ina Safeerah ? Murmushi Mama tayi tace  muje tana sama takarbi Waleed tace  taho Waleely kagani suka wuce sama ko kadan Safeerah batasan za a ganta ba Mama kawai tabude dakinta tace  Safeerah ga yar uwarki tazo ganinki dawani irin sauri Safeerah ta tashi daga gadon Layla tabi uban gashinta da kallo tai wani murmushi tace  Safeerah! Akunyace Safeerah ta sauke kanta kasa tarasa abinda zatayi sai kawai ta duka tace  ina yini dasauri Layla takamata tace  laaa mehaka yar yarinya dani kina dukawa ki gaidani, tashi tashi Safeerah tayi ahankali akuma kunyace tawuce wajen ghana masgon dake wajen tajawo wani gogaggen hijab tasaka Layla na mamaki wlh da za ace budurwa ce zata yarda batai kama da wacce zata haifi Waleed ba and she s damn beautiful, like extremely beautiful, ga flat tummy kaman bata haihuwa, ga hip ba chanchan sosai ba but yafi hips nata girma, ayanda ta ganta ko bra bata saka ba yarinyar akwai boobs manya a tsaye kaman Waleed baisha ba, ga gashi, ga idanu farare tass, ga pink lips, ga gira, the only abu da Nanah zata nuna mata is hasken fata wlh dakuma girman shekaru, da tsayi, sannan Safeerah nada natsuwa sosai ga kunya, unlike Nana that is lively akwai hira, dawowa tayi ta zauna akasa still kunyanta takeji tace  mezan kawo miki ? Dariya Layla tayi tace  wai kinamin haka haka kaman kinga Ammi mother Inlaw naki gabadaya, nasha ruwa a falo besides ai bazaki iya sauka bama maza na falo, sunana Layla ni sister Yaya Salim ce, nike bin Ya Auwal sai Ameera da Lubna, thank you for helping Yaya lokacin nan, my family is grateful sunnar da kanta kasa Safeerah tayi batai magana ba, Layla tace  bazaki min tambayoyi kan mijin naki ba ?
Sake sunnar da kanta kasa Safeerah tayi kunya takeji Layla tace  ai shikenan ta gyara zama tace  kinga Yaya yanada kirki na bala i amman bayason raini yanada fushi aka tabasa, sannan halinsa nada wuyan ganewa yanada wuyan ka karantasa amman he s easy going wlh, he is into diet so yanason healthy meals, bayason soye soye ko oily abu, he love vegetables, fruits, da proteins, Allah yasa albarka a aurenku yakada fitina & .
Baffa yace  nine yayan mahaifinsa, due to some unforeseen reasons Allah bai bawa mahaifinsa daman zuwa ba, ga Aminina, mahaifin Babban amininsa Kabir, ga kaninsa Auwal, sai kanwarsa Layla, danmu yamin bayani sun riga sun daidaita zancen sadaki da Safeerah ko ? Baba yace  kwarai Baffa yace  to za a bamu aurenta yau ne ko akwai abinda kukeso ayi Baba yace  adaura yanzu mun shirya nan take aka daura auren Safeerah Shu ibu da Salim 0brahim Maradi akan sadaki wannan gida aka shafa anata addu a ana samusu albarka, wani boyayyen ijiyan zuciya Salim ya sauke da saida KB ya lura, he s feeling kaman finally yabawa zuciyansa abinda yadade yana nema, yaji wani sanyi aransa, dawata natsuwa, da contentment
EPISODE 3?? 1??




Mama tai shiru like shikenan Safeerah tai aure, wannan aure ne da su sukamata ba wanda aka mataba a chan gidan ba, har kasan ranta takewa yarta addu a Allah sa this aure should be the best for her. Sunci abubuwan da aka kawo har cupcake Safeerah tayi, Salim ne kawai baici abu sosai ba dan he is really overwhelmed so cikinsa yacika, sallan azahar sukayi anan falo akai jam i sannan akai sallama za a tafi, Mama tace  bari na kira Layla wucewa Mama tayi sama tasami Layla adakin daketama Safeerah hira tana bata labarin duka yan gidansu tace  zaku tafi Layla tashi tayi tace  tom Safeerah saimun sake haduwa ko mikewa Safeerah tayi wlh kawai kunyan Layla takeji ta gyadamata kai tace  tom nagode sosai Anty agaida Meenal da kowa hannunta Layla takama ahankali, hannun Safeerah taushi kaman na karaman yarinya tace  tom byeee sannan tasaketa tawuce tafito suka sauka kasa tareda Mama, babu kowa a falon waje tafice sai chan tashigo tazo wajen Mama tabata wata yar jaka tace  gashi yace abawa matarsa atare daga Mam har Layla sukai murmushi, karba Mama tayi tace  tom zan bata kuwa yanzu, agaida yara dakuma Mama Layla Layla tace  zasuji Mama bye tawuce tafita Mama takoma sama tasami Safeerah zaune kan gado yarinyar duk tai wani iri Mama ta ijiye jakan gefenta tace  mijinki yace akawo miki ko kallon jakan batayi ba sai gyadama Mama kai kawai datayi ahankali Mama ta zauna gefenta ta kalleta tace  menene Safeerah? Girgizama Mama kai tayi tace  bakomi Mama, kaina naji yanadan ciwo kawai hannu Mama takai takamo kafadanta hakan yasa gently takai kanta tadaura kan kafadar Mama wani natsuwa taji saita sake gyara zama kawai ta kankame Mama, wani irin sassanyar kuka tasaki da batasan ma daga ina yazo ba, Mama tace  ke a aure na biyun ma still kuka zakiyi cikin kuka tace  Mama bansan mutumin nan ba, bansan komi akansa ba, satin nan na sansa, satin nan na auresa, Mama wlh banason nakuma aure na tsani aure, maza basuda kirki, all abubuwan nan dayakeyi idan he is worst than Abbati fa Mama? Bansan komi kansa ba, zai yarda Waleed ya zauna gidan? Idan ya yarda yanzu daga baya yace yaron yabar gidansa fa? Mama rike d a wanda bakai ka haifesa ba is not easy all this dayake yi da Waleed maybe kawai dan ya aureni ne danni bantaba ganin wanda yaso yaron dabashi ya haifa ba, ga Momma nan dudda yayar mahaifina ce amman bata kaunata sabida ba ita ta tahaifeni ba, ita kenan yar uwanmu na jini balle wani, Mama yara irinsu Waleed nada gundura, Waleed is selective wajen cin abinci kina ganin zai jure nonsense dinnan, Mama yafara dukansafa? Yafara kyaransa fa? Mama bazan iya jure any form of cutarwa ko takura ma Waleed ba, babu abinda bana tunani yau dinnan, kawai I m scared ne tafashe da kuka sosai Mama na shafa bayanta tai murmushi tace  kodan abinda kika mana Safeerah bazaki taba tabewa ba, i know badan kanki kika yarda da auren nan ba saidan mu, banda haka Salim seems like a good person, yanada hankali, gashi yanada natsuwa, wlh hakanan inaji ajikina bazai taba cutar da Waleed ba, idanma yayi muna raye fa zaki maido mana dashi daman ba kowa ke iya rike danda banasa ba rushewa da kuka tayi tace  Mama ni wlh duk auren dazanyi da Waleed bazai zauna dani ba saidai auren yamutu, ni bazan rabu da Waleed ba kawai tasama Mama kuka Mama tadanyi dariya ta jijigata tace  toh mara kunya naji mai d a zan tayaki da addu a, Allah ya sanya albarka a auren nan, yabaku zaman lpy kinji, Allah bazai wulakanta ki ba Feerah, share fuskanki kibude abinda yakawo miki gyadama Mama kai tayi tadago takai hannu tana goge fuskanta tass sannan tadauki jakan tabude ahankali waya tafara cirowa iphone 16 pink, saikuma bandir na yan 1k guda 30 sababbi that s 3million, ahankali ta kalli Mama, Mama ma takalleta saikuma tace  kudin maybe shirye shirye ne na abubuwan dazakiyi, zan dauk some of the money shima sabida matar dana sani a chan GRA dake zuwa yima yan unguwan gyaran jiki ne, yarinyar tacemin Mamanta na yin na amare yanakai 1m zamu biyata sai amiki gyaran jiki mai kyau sosai, nima kuma zan miki nawa, gobe zanje kasuwa na sayo duk wani abu danake bukata karki wasa da shan magunguna kinji yar kirki turoma Mama baki tayi she knows menene kayan mata sarai kawai bataga amfanin sha bane.
Sabida Layla yaje gidan yayi dropping nata dan she comes for wedding nasa sai bayan bikinsa zata koma gidanta, Ammi da Dad dukansu fushi suke da shi babu wani wanda ke kulasa cikinsu, sunsan anyi auren dan Baffa yakawomusu sweet da goro but babu wanda yace mai wani abu cikinsu saima fita dasukayi daga harkansa fitowa yayi daga gidan kawai yawuce barrack.

Dayake yau ake fara event, yau kauyawa day akayi ansha shagali agidansu, all he knows is yana bata everything datake bukata saidai in bata gayamasa ba but he won t participate shi baison parties ma so bazaije ba, ahankali yake driving kansa wuraren 9 cikin estate nasu dake da kyau, parents din Nanah are rich but not kaman su, Mahaifinta is a very good friend of Dad, horn yayi gidan gateman na ganinsa yabude gate da gudu yana dagamai hannu.  Sannu da zuwa Alhaji dan dakatawa yayi yaciro kudi masu yawa yabasa gateman din harda tsalle yace  godiya nake Ogana Allah taimaka wucewa ciki yayi yay parking yana kallon gidan acike da chairs masu shara haka na picking robobi da trash dai na event da akayi, wayansa yaciro yafito da number Nana she has been calling him for 2days baiyi magana da ita ba, ringing daya ta daga ashagwabe tace  Baby saiyau ko, wlh nagaji ansa nayi rawa yau sosai  I m outside kifito  kace wlh! Nana tafada while screaming cus bata taba tunanin zata gansa yau ba Salim akwaisa da abin ban mamaki tunda yadawo baizo gidansu ba sai yau, wajen window dakinta tayi tadaga taga motarsa dasauri tace  ohh my God I can t believe this it s really you, dan Allah kabani 5min nadanyi wanka na goge kwalliyan kauyawan fuskana nafito anatse yace  I don t have the time, sauri nake ahankali tace  okay
Ijiye wayan tayi tace  wlh sainayi hakanan kaganni looking like a clown Sister ta dake ciro wasu sarkoki daga akwati ta wanda zatai using tommorow na event tace  kije mana Nanah maybe he s really busy hanyar bayi tayi tace  he can t be busy for his wife to be tafada bayi abinta wanka tayi agurguje tafito tana kokarin sa kayan data ciro daga wardrobe Hamda dataji karan kunna mota taje window ta leka tace  ai gashinan zai tafi dawani irin sauri ta jefar da rigan datake kokarin sawa taja dogon hijabi tasaka akan towel na jikinta tafito har yayi reverse tafito da gudu bata taba ganin murdadden mutum irin Salim ba wai yanzu saiya tafi ko, gudun kawai dayaga tanayi yasa ta tsaya ta taho da sauri tabude motan ta shiga tazauna tana haki amman tai murmushi tace  kai Baby tafiya zakayi da gaske sabida na bata lokaci ? Wani mugun kallo yamata ransa yadan baci especially ganin saida tai wankan cus fuskanta duk ruwa ruwa, ahankali tace  I m sorry toh dan ijiyan zuciya yasauke yace  how are you ? Ahankali tace  I m fine kaifa mijina, ya kake? Ya shirye shiryen aurena? Dan kallonta yayi he s actually here cus he wants to tell her, atleast for the sake of she s going to be his wife she deserves to hear the truth from him, taji daga wani waje will hurt her more, he wants to try his best and be a good husband to her for the sake of yin abinda Allah yace and for the sake of iyayensa that chooses her for him su sukasan me suka gani danshi haryau baiga anything intriguing about Nanah Khadija ba, anatse yace  I m here to talk to you, I have something danake so nagaya miki inaso ki natsu jikin Nanah har wani tsuma yake cus baitaba magana da ita haka ba wlh tunda ta sanshi, dasauri tace  toh mijina I m all ears juyo da kansa yayi yakalleta sosai fuskansa ba wani tsoro ko shakkan yace  nayi aure Khadijah! Dummmmm! Gaban Nanah yayi wani mahaukacin bugawa tana kallonsa looking so damn confuse cus saita fara tunanin kaman ba abinda yace kenan ba maybe kunnuwanta ke mata karya, da kyar tace  k& ayi aure ko zakai& .au& re!? You mean auren mu ko ?
EPISODE 3?? 2??




Ganin yanda ya tsareta da idanu sosai alamun ba wasa yakawosa ba hakan yakara tabbatar mata da dagaske yake, bugawa zuciyanta yafara sosai tai shiru chan kuma tace  ba bikin mu saura 7days ba? Baby wallahi I am not understanding anything please explain ? Tai maganan muryanta yayi rauni sosai, ijiyan zuciya Salim yasauke yana kallonta da kyau yace  wani accident happens to me 5yrs ago that almost cost me my life, but wata yarinyar lokacin saved me, I ve been looking for the girl all this while, 5yrs kenan da faruwan abun ban ganta ba sai recently na ganta, na aureta today! Wani zafi Nanah taji kirjinta nayi saitaji kaman ma an rike mata numfashi idanunta suka cicciko da hawaye wani irin mahaukacin kishi na turniketa numfashi na gagaranta, wani zafi da daci jikinta ke mata tundaga kan dan yatsa zuwa brain dinta, duk yanda zatai bayan1n abinda takeji abin yawuce, mijinta fa, wanda zata aura, an fara event today just 6more days to go yazo yana gayamata ya auri wata magana kawai na saukan mata aka uwa aradu, takallesa sosai, shima ita yake kallo baice komiba cikin wata kalan murya mai rauni tace  ni zaka yaudara Salim ? Zuba mata mugayen idanunsa yayi batare dayace anything ba, dudda gabanta yafadi sosai bai hanata fashewa da kuka ba tace  mena maka da zakamin kishiya and baka gayamin ba sai bayan kayi auren? I ve been calling you nonstop for 3days but no response ashe kanachan kana auren?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? wata abunka, I suppose to be your first and only wife wata from nowhere tazo ta tunkude ni the waya kakeyi daman ko sun magana da mace bakayi daman kana magana da wasu matan? I thought you are this strict da kowa, kaci amanata ka yaudareni, few days to bikinmu saika auri wata, you re very mean Salim, u are a bad person, you are inconsiderate! Bakada Imani, how would you feel idan wani yama kanwar ka Ameerah ko Lubna hak& &   Khadijah! Salim yadaka mata tsawan da saida tadan matsa baya sabida tsoro, cikin kakkausan murya yace  don t ever bring sunan kannina into I and urs conversation sosai take kuka harda shesheka tajuya azuciye zata bude kofan tafita yayi locking yace  ban gama magana dake ba, idan nagama i will release you kitafi! Juyoda kanta Nana tayi tana kuka tace  I don t wanna talk to you ka kyaleni kariga kayi abunda kayi niyya ka barni in tafi tashiga kuka yadan lumshe idanu yabude, ahankali yace  I have something important to discuss ki saurareni pls dago kanta tayi takai bayan hannu ta goge fuskanta tajuyo takallesa ta turomai baki sosai cus ta dauka lallashinta zaiyi jin for the first time tunda ta sanshi yace mata please. Ijiyan zuciya Salim ya sauke yace  Nana Khadija you re a bright free spirited girl data taso cikin soyayyan iyayenta, yan uwanta da sorroundings nata, baki lacking anything ba as far as iyakan sanina a rayuwanki yadanyi shiru itakuma takara turomai baki ashagwabe still zuciyanta namata zafi, ahankali yace  recently I came across wani incident that left a question in my heart yasa inata tunani, is about aure daya mutu in just six month due to so many up and down from auren iyayene suka hadashi zuwa kan lack of soyayya which I believe yarinyar batason mijin, mijin bayason yarinyar, she s just like an item iyayensa bought for him he feeds on it, abuse it dump it, now basa tare she s left with a young innocent Baby a hannunta yakalli Nanah da kyau dake kallonsa ya tsareta da idanu yana sake mata kallon kurilla he wants to force kansa yaji ko yanason yarinyar but babu do ko daya, hakanan Nanah taji gabanta nafaduwa kawai taji kaman labarin daya bata da ita yake magana sako yakeson gayamata, calmly yace  I dont love you Nanah Khadijah!
Wani radadi sosai Nanah taji kawai ta kulle idanunta ta runtse su gamgam, anatse yace  I dont have feelings for you Nanah! I don t want to ruin rayuwanki because of our parents, just like labarin dana baki na incident dinchan yayi shiruuu ahankali yace  you re beautiful, you re unique, you re kind, akanme zaki wasting all this features akan someone like

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login