Showing 33001 words to 36000 words out of 160450 words

Chapter 12 - LOKACI BAI KURE BA COMPLETE

M SHAKUR   

01 Oct 2025

100

 bakowa!
Waleed ya kalla dake kuka sosai yana kallonsa kaman yasansa ga idanun bacci, ahankali Salim yamika hannunsa biyu dawani irin sauri taji Waleed yatafi wajensa daga hannunta hakan yasa tadago kanta da sauri cikin muryanta dake nuna kuka tace  kai Waleed daidai Salim yana karasa kai hannunsa jikin Waleed hakan yasa tasaki Waleed din, gently Salim yadaukesa Waleed yawani shige jikinsa ya kwantar da kansa akirjinsa yana rage sautin kukan Salim yashafa bayansa ahankali yadan jijijgasa yace  stop crying uhmm! It s okay! Lamo Waleed yayi batare daya sake kuka ba ko ihu, kallo daya yama yaron yagane danta ne yana yanayi da ita, kallonta yayi yanda take wasa da yatsunta kanta akasa yace  is it his father that beat you? Girgixamai kai tayi da sauri tace  a a mun rabu shiruuu yayi yana kallonta dagokai Waleed yayi yakalli Salim idanunsa na cikowa da hawaye sai yafara jiniyan kuka again dasauri Safeerah ta dago kanta takallesu tadan matso dab da shi tamika masa hannu tace  kawosa na goyasa mutafi, rigima zaita maka kaman badashi tai magana ba cikeda kulawa ya kalli Waleed kaman wanda ya fahimci yaron yace  are you hungry? Kanajin yunwa? Gyadamai kai Waleed yayi dasauri yace  yun aaaaa juyawa dashi Salim yayi yafara tafiya dasauri Safeerah tabisu gabanta na faduwa yayi waje, motansa yabude yashiga dasauri Safeerah tazo ta inda suke ta glass din Window tai knocking sauke glass din kasa Salim yayi strictly yace  zaki shiga ko mutafi mu barki ? Hawaye yaga sun cika idanunta gabanta na faduwa but still tace  ni kabani yaro na mutafi! .
EPISODE 1?? 8??



Kaman badashi tai magana ba kunna motan taga yayi abinsa ya danna wajen glass na window yadhiga rufewa ganin yana kokarin reverse ga danta acikin mota da sauri ta zagayo ta gaban motan tabude ta shiga ta zauna tana kallon yanda ya zaunar da Waleed ajikinsa ya rungumesa yaja motan da hannu daya, is the way Waleed yayi lamo ajikinsa ke bata mamaki kaman ba Waleed ba, da gudu yake tuki gaban wani super market na yara yayi parking ya kashe motan batare daya kalleta ba yace  wani abinci yakeci? Kin magana Safeerah tayi ita ya bata danta yaki ganin taki magana sai kawai yabude motan yafice rike da Waleed ya shiga ciki, yana shiga wani juice yafara budewa na yara yasa masa abaki tass Waleed ya shanye yana wani irin kallonsa irin kallon for the first time wani wanda ba Baba da Mama da Ummy ba yabasa abun dadi sai kawai yama Salim wani heart melting smile tsaresa da idanu Salim yayi shida baya murmushi sosai samin kansa yayi da sakinma Waleed full smile Waleed ya washe baki yana nunama Salim cheese balls, daukan masa cheese balls yayi yabude yabasa ya karba yafara ci sannan Salim yakalli matan dake wajen yace  I want kids food for him hadomai abinci akayi daban daban, yasayamai sweet da cheese balls pack, juice da biscuit yabada card yabiya, ma aikatan wajen na fitowa da kayan yazo yabude motan aka samai komi a back sit sannan ya shigo yazauna, Safeerah takalli su adan hankali tahada ido da Waleed dakecin cheese duk ya batama Salim rigansa kayansa masu haske amman duk orange orange na cheese ajiki, tama Waleed alamu da hannu dayazo yawani kankame Salim abun yabata mamaki, Salim ya rufo motan yadan kalleta maida kanta kasa tayi, ahankali yace  why were u at the company this night? Dan shiru tayi sai chan murya chan kasa tace  bakomi ijiyan zuciya yasauke yace  alright bari na maidake gidan na tambayi Baba meya faru aka miki duka haka a fuska basusan ke mace bace ya kunna motan dasauri tace  ni& & ni bazani gidan nan b& .. takasa karasa maganan sabida rawa da bakinta yafara kuka na neman kufcemata hawaye yazubo mata takai bayan hannunta ta goge fuskanta da sauri muryanta na breaking tace  ni& .nidai kabani Waleed nayi tafiyata thank you for everything takai bakin hijabinta ta daura kan fuskanta sabida bataso Waleed yasan she s crying yahau kuka shima, dan ijiyan zuciya Salim ya sauke yaja motan dasauri tasauke hijabin takalleshi ahankali tace  ina zaka kaini shiru yamata bai cemata kala ba takai hijabin tana goge idanunta, Silver garden estate taga sunje yana horn aka bude yashiga estate din yahadu sosai, parking yayi agaban wani gida number 17 dan gidajen duk iri dayane yabude motan rikeda Waleed batare daya kalleta ba yace  when you re ready come inside yazaga bayan motan yadauko ledan abincin yawuce yabude kofan yashiga tabisu da kallo a bude yabar mata kofan gidan yahadu na bala i.

Takai kusan 10mins a motan kuka take, kawai yamata hijacking yaro yakawota wani gida an gayamai ita yar iska ce? She s not even understanding wats happening, yanzu idan mutumin nan yamata wani abu fa? Dudda he doesn t look like a bad person but yanzu yazatayi? Inane nan ya kawota ya shige da danta? Meyakema Waleed? Idan shi maye ne ya cinye mata kuruwan d a fa? Ganin tana tunanin Waleed sosai yasa ta goge fuskanta tass idanunta harsun kumbura tabude kofa tafito tamaida kofan tarufe tashigo gidan, tsoro yahanata kulle kofa, babu kowa a hadadden falon, muryan Waleed taji ta around wajajen dinning datake kyautata kitchen ne hakan yasa tawuce wajen asanyaye jikinta yayi sanyi duka tabude kofan hakan yasa ta hangosu yadaura Waleed kan island na kitchen din shi yana tsaye yana basa abinci Waleed naci sosai yanamai murmushi tabi kitchen din da kallo garin abincin duk ya zube a kasa da kwalayen abincin, kitchen din looks so messy kana gani kasan bai saba yi ba maybe ma this is the first time yake bama yaro abinci, for the first time ta tsaresa da idanu tun shekaran jiya data fara ganinsa he s so gentle with Waleed, kaman yasan Waleed from somewhere, you Waleed means something to him, is not easy kabama stranger this care, who is he? Bata taba ganin Waleed ya yarda da stranger easily ba sai shi, yana basa yana goge masa kumatu yana masa murmushi hakan yasa Waleed nata murmushi, fresh hawaye taji sun zo mata dasauri takai bayan hannu ta goge su, ruwa yadauka na gora yabude yabama Waleed ya sha ya ijiye komi yasa hannu yadaukesa yajuyo ganinta yayi tsaye jikin kofa tana share hawaye da bayan hannu bamata san yana kallonta ba, wani irin radadi yaji zuciyansa namasa ganin the happiest girl daya sani back then is the saddest girl today and someone dares hit her, there s this thing he feels about Safeerah he feels kaman ya maida problems nata kansa and just solve everything for her, shafa bayan Waleed yashiga yi yaron yayi gyatsa tareda yin lamooo ajikinsa bacci yayi awon gaba da shi daman yunwa yasa ya farka, dagokai tayi ta kallesa suka hada ido dauke kanta tayi dasauri, tahowa ya shigayi hakan yasa ta matsa gefe wucewa yayi yafito tabiyosa yahau staircase saita kasa hawa kawai saita fashe da kuka dan at this junction takasa rikewa.  Please kabani d ana mutafi, I m not one of those girls dake kwana gidan maza, ni kabani Waleed natafi ni ba yar iska bace dudda yaji all she said but ko alamun tsayawa baiyiba yakarasa hawa tafashe da kuka da kyau tabisu da kallo takasa hawa benen karya mata wani abu, kwantar da Waleed yayi kan lafiyayan gado yaja bargo yarufa masa sannan yafito tareda rufo kofa har lokacin tana tsaye awajen tana kuka, saiya shiga saukowa akarshen stairs din ya tsaya yadan kalleta yace  I m going home you can stay here as long as you want ahankali tadago kanta ta kallesa hada idanu sukayi kasa jurewa tayi ta maida kanta kasa, anatse yace  idan na fita kizo ki kulle kofa ki sa key da sakata yazaro wani phone daga aljihun wandonsa yadan taka zuwa kujera ya ijiye wayan yace  my number na cikin wayan nan Salim call me if you need anything zan kiraki gobe da safe yasake yin shiru saikuma ya kalleta yace  put ice a face dinki, don t cry again is affecting Waleed gently tadago kanta takalleshi hada ido, komar da kan kasa tayi ahankali tana goge fuskanta da bayan hannu, ataushashe cikin murya kasa kasa that s so gentle and soothing yace  sorry! There is something she felt, batasan sorryn lallashi ne ko na menene ba oho but she just felt d word kaman ya daura hannu saman kanta yana lallashinta saitaji hawaye sun cicciko idanunta, wucewa yayi wajen kofa yadan dakata saiya sauke ijiyan zuciya yace  good night Safeerah! .
EPISODE 1?? 9??





Yafice yaja kofan da all this while yake abude yarufe, tana tsaye awajen taji ya kunna mota yaja yatafi, ijiyan zuciya Safeerah ta sauke tashiga dukawa a wajen kafin takarasa kaiwa kasa kawai ta zauna ta jingina bayanta da bango komi daya faru na dawo mata, jitake kaman an daura mata dutse a kirji, abun is too much for her, idan ita su Momma kema abinnan wlh wlh wlh she can take it but not her parents takasa bringing kanta tadanne zuciyanta, she s not crying because of abubuwan data gayama Momma wlh she s not regretting it, she is crying because of Mama da Baba data batama rai suke fushi da ita, ga Baba baida lpy, she is also crying tana tunanin inda zatayi yanzu cus she have only this night to make a decision dan ko sama da kasa zata hade bazata koma gidan nan ba kuma saita dauke Baba da Mama daga gidan, she can t believe gidan wani zata kwana yau, da kyar ta lallashi kanta tamike tsaye tawuce wajen kofan ta murza key tasaka sakata nasama dana kasa, tazo wajen window tadan daga ta leka taga motanshi baya wajen dan bata yarda dashi ba kar a sace su ko ayi rituals dasu, sannan tasaki labule tadawo tai shiru tawuce sama, dakin da Waleed yake taga kofan abude ta hango ta gansa kan gado yana shakan bacci hakan yasa ta wuce dakin ta maida kofan tarufe ta murza key shima tazauna nan jikin kofa ta jingina bayanta tabuga tagumi tana kallon Waleed, wani irin tausayin Waleed take he doesn t deserve this kawai tahau kuka wiwi saita daura hannu abaki cus yanzun nan Waleed zai tashi.
**
Jan motansa yayi zuciyansa cikeda damuwa baitabajin abu ya damesa kaman yau yanda yaga Safeerah, the way she was crying ba, he felt everything down to her born marrow cus Safeerah daya sani 5yrs back was the happiest and the brightest girl ever with love from both parents nata sabida from yanda tadingamai surutu he picked iyayenta really care about her and loved her, what happened? What changed a shekaru biyar dinnan da Safeerah tadawo haka, the way yakeji is even if it means going to karshen duniya ne he s ready to go just to see that genuine and innocent wholehearted smile dinta, and he will stop at nothing indai kan yasamo mata farin cikinta back ne. Kwana yayi da motan kawai yawuce GRA har zuwa unguwansu dan nesa da gidansu yayi parking ya kashe motan yayi shiru yana kallon gidansu wasu guys yagani a kofar gidan about 5 yayi shiru kawai yana kallonsu wayansa ne yahau ringing dasauri yakalli wayan dake jikinsa, ganin KB ne yasa yadaga yakai kunnensa KB yace  daha bari kaje gida an change kazo shikenan baka dawo ba? Are you afraid na maka lilis ne an arena eh Zer& &   I ve found her Kabir! Hardly Salim ke kiran sunansa jin yakira sunansa yasa dasauri yace  wa? Who did you find? Jingina yayi da kujeran ya lumshe idanunsa murya chan kasa yace  Safeerah! But I think I ve destroy her life Kabir! Yayi maganan sounding very hurt baitaba jin Salim hakaba cus Salim mutum ne da baka gane damuwar sa, farin cikin sa ko bakin ciki but yau muryan Salim sounds pretty hurt, dasauri yace  kaga Salim calm down, this girl helped you when you needed help the most I get it, I can clearly say Safeerah na part of the reason why you re alive today together with us, but stop blaming yourself for abinda ke faruwa in her life yanzu cikin dan fada sounding pissed yace  da ban fada gidansu make a little 15yrs old girl shoulder responsibility na boyeni ba da none of this would ve happened, I am a coward say it! The least I could do shine danaga small girl ce agidan dana juya cus I know everything about security, I know by being there I am putting her and her parents at risk cus yan anguwan nan are thugs but I stayed regardless and nabar gidan without fadin ayi protecting nasu or akaisu somewhere safe shiru duk sukayi KB yace  kasan sanda aka cireka daga gidan nan baka hayyacin ka? How would you have called all those shot? Banda haka you were in hospital for about 30days wat are you saying Salim, do everything you can to save her and help her if she s in need right now she deserve it, but helping you, hiding you was all her choice blame her good innocent heart! Shiru Salim yayi chan yace  I want to marry her KB! Dasauri KB yace  wait wat! Mekace? Calmly yace  inaso na auri Safeerah! Makes her my wife! Dan rage murya KB yayi yace  are you sure of what you are saying? Cus yau duka duka is 14 or 13days ne ma to your wedding da Nanah strictly yace  and I want to marry Safeerah tommorow or next max! Sosai gaban KB yafadi yama kasa magana, ahankali yace  she s not safe agidan da suke, dukanta ake that I can never ever and ever tolerate! An koreta this night and I believe the whole thing have to do with Yayar Babanta dasuke zaune agidanta she s not telling, I will sort her life out, she will never be alone again as long as ina raye I am Safeerah s Sheild yana maganan kawai ya katse wayan ya kunna motan yabar unguwan.
EPISODE 2?? 0??




Har aka fara kiran sallan asuba bata runtsa ido ba inama damuwa zai barta ta runtsa, she s extremely worried, takasa daina tunanin iyayenta, tayi kuka har hawaye sun dena fitowa, idanunta sun kumbura suntum bakindai yadan sabe but it s still there, gashi takasa tashi tai salla gani take kaman ta shiga bayi za azo a sace mata Waleed hankalinta yaki kwanciya agidan, ga kanta dake ciwo sosai yana saraw???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?a, ganin dai an fara salla yasa ta tashi tawuce bayi shima abude tabar kofan tayi komi tafito daure da alwala batasan inane gabas ba bangare daya kawai ta kalla ta kabbarta salla ta idar tafara azkar kanta na sarawa, hakan yasa ta kwanta kan dadduman ance ba a cheating nature bacci barawo ne yayi nasaran kwasheta.
Kadan kadan take bude idanunta dake cike da mugun bacci jin kara, bin saman dakin tayi da kallo kafin firgigit ta tashi zaune kanta na amsawa tuna inda take ya akayi tai bacci haka agidan mutane ta kalli gadon dasauri tuna danta, Waleed tagani yayi daidai agado abunsa yana bacci, jin ringing waya yasa tamike ahankali idanunta basama buduwa da kyau tafito da shiga sauka kasa da sauri ta taho falon inda ya ijiye wayan tasa hannu tadauki wayan da yana inda yabarta taga Major Salim a jiki hakan yasa takai wayan kunnenta cikin muryan bacci dakenan yar karama kaman tana whispering tace  Helloooo shiru taji anyi kaman babu kowa adayan side din da sauri takai hannunta ta goge idanunta da bayan hannu tazare wayan daga kunnneta takalli screen din again ganin the call is still on yasa tamaida kunnenta ahankali tace  Assalamu Alaykum cikin wani husky natsassiyan murya yace  I m outside open the door hakanan taji kirjinta na racing dagajin muryansa juyawa tayi tabi dakin da kallo, ganin basu bata komiba yasa ta ijiye mai wayansa back tai wajen kofan, sakatan tacire ta murza key tabude kofan ahankali hada ido sukayi yana tsaye gaban door sanye dawata yadi that looks soft and textures milk mai kyau dan yau Friday yana wani irin kamshi, he looks squeaky clean kaman ka lashesa, faduwa gabanta ya shigayi sosai, adan rude tasaki kofan takoma baya tadan tsuganna ahankali tace  ina kwana kallo daya yama fuskanta yadauke kai ya shigo this time around ya maida kofan yarufe dawani irin sauri abirkice ta mike kaman zai cinyeta tana kallon kofan daya rufe, kaman baiga yanda ta tsorace ba wuceta yayi ya shiga falon ya ijiye ledan wani super market akan kujera da basket na kuloli that looks like abinci, sannan yajuyo yakalleta batare dayama zauna ba tana tsaye chan wajen dinning sabida tsoro tana wasa da yatsun ta kanta akasa kaman yace woop ta arce aguje, hannuwansa yazuba a aljihu rigansa ya sassauta murya yace  are you feeling better today? Duk duniya ita kadai ne idan zaima magana saiya gyara muryansa, ya tankwara yakuma tausasa cus yaga tsoronsa takeji, gyadamai kai Safeerah tayi ahankali, yana kallonta still yace  Waleed fa ? Dan dagokai tayi ta kallesa suka hada ido dasauri ta maida kanta kasa, she felt wani iri dataji harya rike sunan danta sannan ya tambayesa kuka kawai taji yataso mata amman tadaure asanyaye tace  yana bacci shiru falon yayi bai kara magana ba itama bata sake dago kanta ba banda wasa da yatsunta datakeyi, gently tadan dago kanta ta kallesa hada ido sukayi yana mata wani kallo da takasa sanin na menene da idanunshi dake tsorata mutum, cikin wani irin yanayi na girmama mutum dakuma jin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login