Showing 48001 words to 51000 words out of 160450 words

Chapter 17 - LOKACI BAI KURE BA COMPLETE

M SHAKUR   

01 Oct 2025

131

Waleed nawani irin dirlowa daga hannun Mamansa yakama hannunsa yace  ayoyooooo juyowa yayi yakalli Waleed dakawai ganinsa yasa yaji bacinran yabace dan karamin smile yasaki yace  Hello Finest boy Waleed, come here yawani daukesa ya rungume yana kallon Safeerah daharta sauke kanta kasa, murya ciki ciki tace  ina yini bata jira amsar sa ba tawuce dasauri ta tafi ta shiga ward din binta yayi da kallo she still walk kaman da.
7 aka fito da Baba an saka bandage a fuskansa.
Yana asibitin har isha i awajensa Waleed yayi bacci sannan yadawo dashi yamusu sallama yatafi koda Mama tace taje tamasa sallama fitowa tayi but taki zuwa chan tadawo daki, kallonta Mama tayi tace  zo Feerah zuwa tayi ta zauna gefen Mama, hannunta Mama ta kama tace  Salim yagaya miki waye shi? Girgizama Mama kai tayi alamun a a, ahankali Mama tace  dazu kina masallaci Babanki ya tambayesa mesa yake taimakon mu, shine yake gayamana shine mutumin da kika taimaka kika boye lokacin nan! Tunda Mama tafara maganan kirjin Safeerah ke bugawa none stop, Mama tace  yanuna ma ni da Babanki hannunsa gabaki daya hannun tabon kunane haryau bai dawo daidai ba wani irin kallon Mama Safeerah take, murmushi Mama tayi takai hannunta ta kama fuskan Safeerah tace  yace yanemeki sama da kasa bai ganki ba not until rannan dakikazo company sa aiki Mama tai shiru tace  ni da mahaifinki mun aminta da auren mun yarda, and mun yanke shawaran zamu shiga gidan tunda sadakin ki ne, da kyautane da munji wani iri, ga idanun Babanki anyi aiki yana warkewa zai nemi koyarwa we will live good babu wanda zai kara zaginmu, abinda nakeso dake yanzu is kidage da addu a, Allah yasa Albarka a auren, Salim ba yaro bane abinda yasa muka karajin natsuwa dashi kenan, thank you Safeerah for saving us Mama tayi rungumeta kankame Mama tayi tunani sunmata yawa aka daman shine mutumin nan? Saisa yadinga kallonta the first day daya ganta in his company, daman shine? But yanzu yafi girma.
**

Yau kwanan Baba five a hospital din Alhamdulillah yaji sauki ras idanun dazu aka bude da safe yana gani ras saidai sun kankance but Alhamdulillah, tun after rannan operation din Salim baizo ba sabida wani work trip daya tafi to France na just 3days but kullum yana aiko sojoji akawo musu daily need, yasayama Safeerah 5abayas yabada akaimata saida Mama tai da gaske sannan tasaka kayansa.
Yau aka sallami su but Dr Isa yace Salim yace ajirasa zaizo yakaisu gida duk suna zaune, Safeerah tasaka daya daga cikin abayan daya sayamata black yanada stones yamata kyau ajiki sosai dankwalin abayan ta yafa, Waleed short ne ajikinsa na jean dawani blue riga mai kyau da takalmi yayi kyau sai wasansa yake a tsakar dakin sun hada komi nasu tsaf, suna zaune akai knocking tareda sallama hakanan gaban Safeerah yafadi jin muryansa dasauri ta gyara gyalen kanta da kyau tana rufe gashinta, Mama tabudemai Waleed na ganinsa ya jefar da Cheese na hannunsa yadaga hannu yazo dagudu yace  ayoyooooo daukan Waleed yayi dasauri yayi murmushi kadan yace  Finest Boy Waleed kankamesa Waleed yayi Mama tace  ai sai ka barsa ko hannunka duk cheese zaka bata masa kaya dasauri yace  Mama barsa bakomi yashigo dakin batare daya kalli Safeerah da kanta ke kasa ba yayi wajen Baba yana mika masa hannu cikeda respect yace  Abba ina yini, idanu sunyi kyau Dan dariya Baba yayi yana feeling very free with Salim yace  ai saiyau nake ganin ka da kyau, Salim kam Masha Allah dan sunnar da kansa kasa yayi maganan Baba tasa yadanji kunya kadan yace  bari nasa akai kayan mota sai mu tafi yajuya yakalli kofa yace  come in Boys sojoji guda biyu suka shigo suna daukan yan kayansu Mama tazo inda Safeerah take zaune kan kujera, duka ta dakamata a sace Safeerah ta kalleta da sauri, wani harara ta mata irin bata iya gaisuwa ba, adan hankali Safeerah tace  ina yini batare data kalleshi ba, shima bai kalleta ba yace  lafiya lau yace  Abba Bismillah muje Baba yace  asibiti ba dadi jama a yasauka ahankali yake tafiya Salim dake rike da Waleed na je rawa dashi suka fito, Mama ta kalleta tace  ke da bakin hali baki iya gaisuwa ba ko kaman zatai kuka tace  Mama magana fa yakeyi saisa ban iya nai gaisuwan ba fa Mama tace  muje mai kunnen kashi murmushi tayi suka fito itada Mama.
Sunakai wajen motan ijiye Waleed yayi akasa shiya rike Baba cus baida karfi sosai yasaka sa abayan mota Safeerah da fitowansu kenan tareda Mama tadan saci kallonsa he s so gently da mahaifinta, Mama ma tabisa da kallo sai tadan sauke ijiyan zuciya wlh she loves Salim for yarta sosai, karasawa wajen sukayi itama ta shiga baya, adan kunyace Safeerah tashiga gaba, shima yashiga Waleed na jikinsa ya kunna motan yaja har zuwa estate din Baba da Mama nata kallon ikon Allah sabida basu dauka a irin waje haka yabawa Safeerah gidaba, wlh estate din yafi GRA su Momma kyau sau dari, ga gidajen iri daya sak, saima dayayi parking gaban wani hadadden gida ga flowers anyi decorating wani mini garden, ga bike na yara da ball yasa awajen wanda she is sure bata gani the other day ba, yanzu wannan hamshakin gidan Safeerah ta karba jama a? Kashe motan yayi yabude yafito yazagayo ta bangaren Baba yabude masa kofa, fitowa Baba yayi Mama ma haka, itama Safeerah jikinta yadan mata wani iri amman tadaure tabude motan tafito taciro key dake yar jakan hannunta ganin ko kallonta Salim bayayi wasa yake da Waleed abinsa yasa tai wajen kofa su Baba na kallonta tabude tajuyo ta kallesu saikuma takasa magana, Salim yace  mushiga ciki Abba shiga Baba da Mama sukayi duk suna kallon gidan this is the moment of disbelief awajen gidan nan nasune yanzu? Su? Suka zauna afalon dayake a gyare, Salim yasauke Waleed yace  remember don t cry zanje office okay gyadamai Waleed yayi, gently yace  je Ummi tasa maka cartoon dan satan kallonsa Safeerah tayi jin abinda yafadi yamike tsaye yace  sai anjiman ku Abba har yayi kofa Baba yace  Salim dasauri Salim yajuyo yace  na am Baba ahankali Baba yace  gobe kazo da magabatanka adaura muku aure ba amfanin bata wani lokaci tunda nasami lpy faduwa gaban Safeerah yayi sosai jin abinda Baba yafada, Salim yadan gyadamai kai yace  toh Abba .
EPISODE 2?? 9??



Wani haske kalaman Baba sukasa yaji aransa, deep down yanaji kaman yawani fizgo gobe tayi, he just wanna hear those golden words an daure tsakanin Salim Ibrahim Maradi da Safeerah Shu ibu, rabonsa da gidansu yau kwana nawa dayana France ko sau daya Ammi bata kirasa ba maybe Dady yafada mata, sai kawai yawuce gidansu, parking yayi yafito flat nasa yawuce shower yafada tun yana ciki yaji wayansa na kuka karasa wanka yayi yafito jin wayan na kuka again yasa yatafi wajen wayan, ganin Ammi ke kiransa yasa yadaga wayan muryanta ba dadi kwata kwata tace  kazo ina dakina bata jira amsawan sa ba ta katse wayan, ijiye wayan yayi shima yacigaba da shiryawa, wani 3quater yasaka wando yasaka, yasa t-shirt mai dogon hannu, slippers yasa sai kamshi yake yafito, flat nasu yashiga yaga Lubna da Ameera a falo suna tattare souvenirs dasuka hada na bikinsa dasauri sukace  sannu da zuwa Yaya wucewa yayi bai amsasu ya gyadamusu kai ganin abubuwan dasuke hadawa yasa yatuna da auren da za amai yawuce dakin Ammi yayi sallama yabude dakin Ammi ya shiga, Auwal yagani aciki da Layla kanwarsa datai aure yarta daya Meenal, Ammi yagani tahade rai sosai tana kallonsa, Layla tamike da murmushi sosai kan fuskanta tace  Yayaaa yau kwana na biyu ina gida banganka ba wayanka baya shiga hancinta yaja yayi murmushi yace  i was in France Auwal yace  ya hanya Yaya ? Anatse yace  Alhamdulillah yana tahowa cikin dakin rike da Layla data basa side hug yasami waje yazauna yakalli Ammi yace  ina yini Ammi Ammi bata amsasa ba sabida yanda ranta yake abace tace  kullum rannan duniya complain na mahaifinka is baka girmamasa, bakada respect menene menene, I see complain nasa baseless kawai yacika korafi ne but slowly na soma yarda da maganar sa yanzu tai shiru, cikin tsantsan bacinrai tace  me nakeji haka daga bakin Dadynku Salim? Dan lumshe idanu yayi yabudesu yace  me yaran nan keyi anan Ammi ? Yayi maganan yana musu wani kallo hakan yasa duk suka tashi zasu fita Ammi tace  nina kirasu kudawo nan cus enough is enough tsayawa duk sukayi Auwal yazauna kan hannun kujeran da Salim ke zaune kai din, Layla tazauna gefensa ahankali, Ammi tace  wat kind of embarrassment is this Salim? Few days to your wedding, gobe zasu fara events one week to wedding, Bazawara zaka auro ana zaune lafiya harda d a fa? Sauke kansa yayi kasa, Ammi tace  I m talking to you kamin banza menakeji me hadinka dawata bazawara datazo IT company? Because she saved you and so? Da dan zafi kan muryansa yace  wat if sonta nake Ammi? Wat if all this years I ve fallen for her tun sanda ta taimakamin I ve beeen searching for her? Dan naganta yanzu ta taba aure tanada yaro does that change anything Ammi? I am a Man yaushe karin aure yazama wani laifi ko wani abu? What am I doing wrong Ammi ? Cikin fushi Ammi tace  everything you are doing is wrong Salim, mahaifinka daya hada auren nan zaka kunyata? And yes it does matter sabida you are too small ka auri bazawara not to even mention ta taba haihuwa bayan ga budurwa wacce bata taba aure ba ce zaka aura dan runtse ido yayi he hates d name da ake referring Safeerah dashi, Ammi tace  inba magani tamaka ba ga budurwa zaka aura yarinya danya shakap yau biki saura kwana takwas kace kai bazawara zaka aura kuma ? Ahankali yadan dafe kansa dake sarawa yace  wat do you want yanzu Ammi? Why did you call me here ? Cikin fushi Ammi tace  kabar maganan wani aure, Salim ran Babanka yabaci sosai, already kullum cikin damuwa nake da yanda baku jituwa kaidashi kun dawo goshi da keya, ka kama kai auren nan he will never forgive you, saisa na kira kanninka su saka baki, don t ruin relationship dinka da Mahaifinka sabida wannan auren kaji Son Ammi tadan sassauta murya tace  I hate yanda baku jituwa dakai da mahaifinka please respect his wish, give this girl kome takeso ka rabu da ita and face Nana Khadija kaji ahankali Salim yace  I can t Ammi! Ba Ammi ba har kannensa kallonsa sukayi, Ammi tace  ni kake gayama you can t? Ahankali yace  da ace zan iya da tun last five years na hakura da nemanta, not a day goes by da banayin tunaninta, now that I ve finally seen her kuma I can t let her go, I m really very sorry Ammi but I can t grant this wish naki, Daddy needs to accept I m a man, and I own my life, he should respect wish dina and yadena dictating mini my life! I am 39 Ammi not 13 yamike tsaye yajuya zai fita Ammi cikeda mamaki Salim tace  Salim! Tsayawa yayi chak batare daya juyoba, Ammi tace  tun yanzu kafin ka aurota kafara nunamin ban isa ba ko? Wani iri yaji sosai ahankali yace  baku taba kawo abu kuce nayi nakiyi ba, even Nanah ban muku gardama ba dakukace na aureta, but ni nakawo kunce a a, and it s too late nariga nabiya sadaki! And gobe za a daura auren so I can t back out now! Kowa na dakin kallonsa yake da mugun mamaki ran Ammi ya matukar baci dataji yarinyar ma zai fara aure before Nana, da kyar ta daidaita muryanta tace  okay shikenan kaje kai aurenka dayake zabinka but kasani ba yawuna ciki, and as long as ina raye ni matarka daya nasani Nana Khadija, bazan taba accepting koma wace yarinyar da zaka auro ba shiru yayi yay jimmm maganan ta tabasa sai kawai yabude kofa yafice daga dakin Layla tai wajen Ammi da sauri tace  Ammi please calm down dan Allah, Yaya baitaba disobeying dinku ba, ku fahimce sa kadan, haba Ammi kinfi Dady fahimta fa kinji Ammi na Ammi da ranta yabaci tace  karki gayamin maganan banza Layla ahankali Auwal yace  but Ammi Layla is right, Yaya baitaba gardama da ku ba, even though bayason Nanah I saw it but ya yarda sabida zabinku ce, ni banmasan Safeerah ce yarinyar ba but rannan daya ganta naga yanda yake kallonta, bantaba ganin Yaya yakalli wata mace aduniya like that ba wlh, ku barsa ya aureta, Ammi tsakani da Allah bai kamata kuna gayama wanda is approaching 40 wat do and wat not to do ba, yanzu idan kuka hanashi aurenta shaidan ya shiga ransa da aurensa yaje yanabin yarinyar fa eh Ammi? Kunada kason zunubi, kidena biyema akidan Dady dan boko bayason aure aure, as long as zaiyi adalci, he s capable bamu zamu tayasa ciyar da su ba let him have his way, Ammi badan yarinyar nan ba da yanzu kullum muna kukan rashin Yaya yarasu? So koma menene he owe her his life Ammi kinji shiru Ammi tayi jikinta yayi sanyi tace  Nanah fa? That girl is so innocent she s just 25 ina zata iya dawata bazawara? How will she feel 7days to bikinsu rannan da ake event na kauyawa day wanda zata aura na chan yana auren wata eh, Small girl zai aurowa Bazawara Auwal yace  to ai Nana ta girmi Safeerah ma Ammi, Safeerah is just 20, kuma Nana tafi Safeerah girma da wayewa da komi ma babu wanda zai cutar da Nanah Layla dake shafa Ammi tace  toh kinmaji Ammi calm down, yariga yasa ransa look at how serious he is da maganan so unlike Yaya, kika hanasa zaiyi abinda dukanmu bazamuji dadi ba, Ya Salim ba yaro bane let s respect him Ammi please, and ki lallaba Dady, stop supporting Dady blindingly let s call a spade a spade Ammi shiru Ammi tayi tana kallonsu saikuma tace  dallah kutashi daga gabana munafukai kawai ta watsa musu harara Auwal yafice Ammi is kind laslas she will come around, Dady ne dan bala i Layla tabisa abaya suka fice, flat din Salim suka shiga baya falo sama suka wuce knocking Layla tayi gaban dakinsa tace  Ya Salim murya ciki ciki yace  wat gently tace  can we come in? Ni da Ya Auwal ne, mushigo ? Shiru yayi chan yace  come on in bude kofan tayi ahankali ta shiga yana zaune bakin gado wucewa tayi ahankali ta zauna kusada shi shikuma Auwal yazauna kan kujera, ahankali Layla tace  Yaya you re the best brother I trust with my own life, I know you Yaya, you are such a critical thinker, bakada garaje, kome zakayi nasan bazaka taba abunda zakai bringing shame to our family ba, I don t care idan mata hundred zaka aura you have my support, nasan zakai adalci Yaya, Ammi will come around i promise Dady ne dai sai Allah shiru yayi yana kallonta saikuma yadanja hancinta yace  remind me how old is this girl again Auwal ? Murmushi Auwal yayi yace  28yrs Salim yace  and she s this smart are you sure bazan gayama Habib yakaro kudin sadakiba wanda yabiya abaya yayi expire dariya sukayi Layla kawai ta rungume shi tace  I just love you Yaya so much and I trust you, I trust your decision, you deserve Safeerah! A selfless girl mai taimako da jarumta da kirki only deserves a selfless Man mai taimako da kirki like you bayanta ya shafa calmly yace  thank you Layla anatse Auwal yace  but Yaya just from kawota wajena da Shamsu yayi is like akwai issue a family su he treats the girl like trash at a point saida namai magana ma nakasa daurewa dan shiru Salim yayi gently yace  that s why I wanna take her away yayi shiru chan sai ya gayamusu komi dake faruwa yace  that s why I wanna keep her by my side, she kept me hidden then even though nace zan tafi murmushi Layla tayi tace  Yaya zan iya binku gobe idan zaku? Gyadamata kai yayi yace  yes! Baffa zai bini ko bazai bini ba I m not sure but i called him, sai Kabir KB da mahaifinsa incase Baffa bai bini ba Auwal yace  zani nima gyadamusu kai yayi sai suka zauna dashi he was sad actually sabida Ammi but sunsa almost 70% na damuwansa is gone.
**
EPISODE 3?? 0??



Babu wani kayan abinci da babu agidan, everything ansa agidan, hankalin Safeerah yawani irin kwanta ganinta da iyayenta cikin gidan, Baba da Mama sun saki jikinsu sosai they re very happy wlh, babu abinda yakai runfa akanka taka babu mai zuwa ya zageka ko yacimaka mutunci.
Safeerah tadafa lafiyayyen abinci tanaso taje ta kwaso kayanta agidan nan da komi nata but batasan yazatayi ba haka dai har washegari girki sukayi itada Mama na tarban bakin ita batada number sa yakira Baba yace zasuzo shabiyu, Baba yakira wani amininsa yamai kwatancen gidan yazo tacema Mama zataje gidan nan ta kwaso kayansu tafice bata saurari Mama ba layin taje gabanta sai faduwa yake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login