Showing 138001 words to 141000 words out of 160450 words

Chapter 47 - LOKACI BAI KURE BA COMPLETE

M SHAKUR   

01 Oct 2025

110

karuwanci kaga tanayi, dukan mace Salim duka? Kataba ganin nataba mahaifiyarka? Wakataba gani a family mu yataba dukan matansa? Kama kanka and wlh tallahi idan banyi making naka pay for hitting this girl ba banine ubanka ba! Mara mutunci! Mahaukaci kawai shashaha Daddy ya kadakai yafice KB yace  Salim won t you talk? Speak Salim amman ko motsi baiyiba, Dady yawuce dakin azuciyw ya shiga bayin yakama Safeerah dake kuka da kansa ransa yayi matukar baci yace  samo mata lullubi wife mutafi tashi Mama tayi tafita daga dakin hijabinta tadauka nan tamaga bra da pant nata duka akasa akwatin data tabbata nagane kawai ta kwantar tasa aciki yadauki hijab da hand back nata ta taho yasamata hijab din da takalmi Dady ya karbi jakan suka fito da ita dasauri KB yace  Dady dan Allah karku tafinmai da matarsa all couples fight bamusan meya hadasu ba, dan Allah Dad kahadasu kamusu fada tukunna saki jakan nan Kabiru!
Daddy ya dakama KB tsawa, KB tasaki ahankali Dady yace  zai gane yatabamin diya he s very very stupid suka wuce da kyar ma Safeerah ke tafiya ga azaba gabanta nayi ga duka Ammi taji kawai ta tai ke da lamarin Salim suna fita suka sata a mota sai airport suka shige private jet nasu sai Abuja.

TOM JAMA A FOR THE FIRST TIME WE HAVE A NOT SO PERFECT CHARACTER DAMAN ANCE DAN ADAM TARA YAKE BAI CIKA GOMA BA!



SALIM YA KYAUTA FOR HITTING SAFEERAH???

SAFEERAH TA KYAUTA FOR YIMA MIJINTA KARYA???

ADVICE THEM CUS AKWAI MAZA DAYAWA LIKE SALIM TAYAYA MATARSU ZATA ZAUNA DA KALAN MAZA HAKA TAJI DADI???

A GANINKU SAFEERAH TABAR AURENSA TAHAKURA SU KOMA KANO KAWAI KO KATSINA KOMA MAIDUGURI??

KANA IYA KANASON MUTUM KA KUMA DAKESA HAR KANA FURTA XAKA KASHESA KAMAN YANDA SALIM YAYI???


RAYUWA ZAI YU YACE MATARSA BAZATA KULA WANI BA???

TAYAYA SALIM ZAI RAGE KISHI????

INADA MALARIA YAU MANAGE TWO EPISODES d'?

LETS DISCUSS A COMMENT SECTION!
EPISODE 8?? 2??





Harsuka sauka a Abuja Safeerah kuka take, like ta tsorata kalan tsoron dabata taba jin kalansa arayuwanta ba, cus she can t believe mijinta daya gama cewa he loves her shine ya mareta haka yana cewa zai kasheta, and his looks proves he s ready to kill her, mota suka shiga sai gida already Dr Maje da Dad yakira yana gida yana jiransu, parking sukayi Ammi tafito da ita tana tafiya ahankali tace  saitai wanka zai dubata fitowa Lubna tayi da Ameerah dan duk agabansu iyayensu sukabar gidan a haukace turus daga Lubna har Ameerah sukayi ganin Safeerah da fuskanta duk sheda ga kuka tanayi sosai duk yanda Ameerah takai ga jin haushin Safeerah da taya Nana kishi amman saida tazo wajen da sauri tana kallon Safeerah tace  Ammi meya sameta? Who slapped her haka Ammi? Safeerah meya sameki ? Anatse Ammi tace  tayani kamata muje ciki taya Ammi riketa sukayi itama Lubna tazo dasauri sai Ammi kawai tabar musu ita tace  dakina wucewa da ita sukayi dakin Ammi, Lubna saita fara kuka ganin yanda Safeerah ke kuka tace  Ammi who beat Anty Safeerah like this? Wlh Ammi bakinta ma na nauyi tace yayansu sabida kunya tace  kufita zata shirya, ku daukomin akwatin ta daga mota Ammi ta yaye lullubi kawai tashiga bayinta ruwan zafi tahada sosai tafito tazo inda Safeerah tashare mata hawaye tace  stop crying ahankali tace  Ammi zanje gidanmu da hannu Ammi ta nunata tace  kul karna karaji kin fadi maganan nan, babu inda zaki, nan ne gidanku, muje Ammi tawuce da ita bayi duk yanda Safeerah kejin nauyin Ammi saida ta gasata sosai sannan tai wankan tsarki bayan Ammi tafita daga bayin tadaura towel tafito bayan ta tsane kanta tafito daga bayin Ammi takalli wuyanta zuciyanta na mata radadi what if ya kashe yarinyar mutane? Meya sami Salim? Kaya tasaka sharp sharp Dr Maje yazo dubata yanda take kuka da za a samata drip saida Ammi tariketa sannan bacci ya kwashe ta akan gadon Dady yashigo dakin shima ya tsaya yana kallon wuyan Safeerah ransa yabaci Ameerah tace  Ya Salim ne yadaketa haka? Ran Daddy abace sosai yace  shine kowa jikinsa sanyi yayi basu kara magana Dady kawai yajuya yafita yana kiran Baffa awaya, ran Ameerah ba dadi indai haka Ya Salim yake gwara da Nanah bata auresa ba, Nanah da ma bayaso da ita kasheta zaiyi halan, kasa daurewa tayi takira Nanah, Nanah na fama da kanta dan Auwal bai sake dagamata kafa ba gasa hariji, mayen sex, bacci yasamu ya dauketa kenan saiga kiran tadaga Ameerah tabata labari batasan sanda tace  yanzu Matar dayaki aurena sabida ita yadaka Ameerah? Ameerah tace  wlh Anty Nanah, Allah yasoki sojoji basu hadu ba fa, mahaukata ne dudda Nanah hates Safeerah amman saitaga inhar zai iya yadaki yarinyar dayake so haka ita waye sai kawai taji gwara dabai aureta ba, dan bazata iya zama da mai dukan mata ba.
*

KB is one true friend da Salim ke dashi, yahadu da Salim tun sanda sukazo training na short service, Salim has always been this person dakeda zuciya sosai, but after incident daya samesa a Kano Salim ya chanza gabaki daya, yakara dawowa asalin mara imani, the only thing dayaga Salim yadamu dashi is yarinyar dayace ta taimakesa a Kano, but how come yau yarinyar yake duka? Barinsa yayi a bayin yafito yazauna anan bedroom na dakin yayi shiru kawai cus bazai barsa alone ba har aka soma kiran magrib yatashi yaje kasa yayo alwala yadawo saiya dawo saman yabude dakin Salim yagani tsaye a dakin yana cire rigan jikinsa daya jike idanunsa sunyi jazur kaman wuta ko kallonsa bayayi saima cire wandonsa dayayi yawuce yafita daga dakin yafita KB yabisa gaban dakinsu Salim yayi saiya tsaya ahankali yana kallon kofan kafin yawuce yashiga ciki out of respect KB bai bisa ciki fa, kusan 10min yayi aciki yafito sanye da jallabiya da dadduma a hannunsa ya shimfida dadduma yayi sallan asir da magrib yana zaune awajen idanunsa so reddish wlh yabama KB tausayi, tasowa KB yayi yazo gaban dadduman yazauna agaban Salim din sannan yakai hannunsa ahankali yadaura kan kafadan Salim ahankali yace  Salim! Dago jajayen idanunsa Salim yayi yakallesa batare daya amsaba, anatse KB yace  what is wrong Salim? Meya sameka? Why are you doing all of this? Murya chan kasa data gara gurbacewa yace  Safeerah ta karbi number John, and she called him KB na kallonsa sosai yace  duk wannan number akan karban number ne? Toh what are you trying to say Salim? Zargin matar ka kakeyi? Girgixamai kai yayi yayi wani huci da shi kansa KB saida yaji zafin dake fitowa daga hucinsa yace  I trust matana, bana zarginta and bazan taba zarginta ba cus ba mazanaciya bace, she s a woman of virtue, bazata taba irin wayan nan abubuwan ba KB yace  toh idan kasan duka all of this why are you acting like this eh? Wani lankwasa kai yayi jijiyoyi na fitowa a goshinsa sosai yace  I dont want matana tadinga magana da wasu maza, I don t want any man a rayuwna Safeerah, why will she collect Johns number? Mexatai dashi? Ubanme yahadata da John? What in this world zatai da number sa? Eh? Yanda Salim ke magana KB ke kallo but bai nunamai komi ba, a girma ya girmi Salim he s 43 while Salim be tsallaka 40 ba har yanzu, ahankali yace  Salim kishinka yayi yawa, and this is an unhealthy kishi, wannan bakin kishin baida amfani at all, inhar kanaso kayi xaman aure da mata you must reduce it inba hakaba you will never live in peace da iyalanka, mata ma basason maza masu wannan kalan mugun kishin, wannan bakin kishin will only make you loose Safeerah dakakeso with your entire heart and soul, and it will make her run for her life, sabida ka fara kishi bakasan me kakesa u run mad, baka da hankali kwata kwata, imagine you are fighting me today bama ka sani ba sabida kishi, you need to stop all this babu yanda za ayi ayi rayuwan aure miji yace kai kadaine namijin da zai kasance a rayuwan matarka a ina katabajin anyi haka? Why all this insecurities? What are u so afraid of Salim? Akwai wanda ya isa yarabaka da Safeerah ne? Dole matarka tai mu amala da maza daban daban that will enter her life one way or the other, Salim I know you da zuciya da fushi but dudda haka kai mutum ne mai hankali da hikima but today you totally lost it and I really think you need a professional help cus you ve lost it, gashi yanzu su Dady sun tafi da ita sabida abinda sukaga kama yarinyar mutane, Salim kalli kofan daka sauke kasa sabida bakin kishi? Kashe yarinyar mutane da zakayi eh? KB yanunamai kofan wani irin huci Salim yake zuciyansa na suya kansa na bugawa yace  I just lost it danaga ta karbi number sa and even called him and she lied to him, na tsani karya! Why will she call John? Ina mijinta akanme zatai magana da wani? How dare she? Auren mu is for life bazan taba rabuwa da ita ba! And bazata taba kara wani auren ba har abada, duk wanda zata aura saina kashesa ko ayi mutuwan kasko! Shiru KB yayi yana kallon Salim fan wlh wlh Salim is not okay amman kuma baisan Salim dawani mental disorder ba, every six month suna zuwa check up and psychiatric check up ba a taba cewa yanada wani abu a kaiba, see is it that soyayya na maida mutum mahaukaci? Wlh wlh baitaba ganin something like this ba? Wannan wani kalan soyayya ne? And he s suffering, he s hurting all because of karban number waya yana neman hallaka kansa da matarsa da John din, patting shoulder sa KB yayi yace  calm down Salim, calm down dan ijiyan zuciya Salim yasauke gabaki daya numfashinsa ya gurbace, he will talk to him about seeing a therapist but not now yanzu is not a good time, dan dago kansa Salim yayi yakalli KB da jajayen idanunsa muryansa bata fita sosai yace  did I hurt her sosai? Wani kalan tsinkewa zuciyan KB yayi ahankali yace  the only thing nagani was shaidan hannunka a fuskanta da wuyanta bansan ko akwai wasu internally ba sauke kansa kasa Salim yayi KByadafasa ahankali yace  Salim Safeerah yarinya ce she s only 20yrs old, yayi occurring to you cewa maybe kota karbi number sa akwai dalili? Cus babu wani abu da dam Adam zaiyi da ba dalili, also kace she lied to you bata gayamaka ba kayi tunanin it might be out of fear sabida tasan yanayinka tana tsoron tafada maka kayi fushi, lastly kayi thinking possibility of what if John is lying? Sheri yamata da yaushe ta karbi number sa? Kansa na kasa yace  I think yesterday
Dan shiru yayi yace  this is free advice zan baka as wanda has been married for more than 10yrs, don t ever believe maganan wani na waje than na gidanka, and whatever others say akan iyalanka investigate before jumping into conclusion, cus kabar mutane haka kawai, akwai wayanda baka taba musu komiba but burinsu kawai su kashe maka aure, so as long as maganan yan waje zaka dauka ka yarda bazakaga peace agidan ka ba

Put yourself together muna gama abinda yakawo mu nan for 5days we will go to your house apologize to your parents ka karbi matarka, but don t ever and ever hit matarka, zakaci abinci? Girgiza masa kai yayi sai kawai ya kwanta akasan yayi shiru ya lumshe idanu wlh sai KB yaji he can t leave him like that duk yama rasa mezai cemai shima ya kishingida da kujera sai wajajen 12 bacci ya daukesa ahaka KB nada minshari hakan yasa Salim yabude idanunsa ahankali yamike tsaye batare dayayi motsi ba ya tsaya yana kallon dakin daya fasa kofan saiya wuce ahankali ya shiga dakin yana bun kofan daya fadi ta cikin dakin a katsa da kallo yayi shiru what if kofan nan yafado mata? Bayan da kofan yake a bude ya kalla saiya wuce wajen ya tsaya yayi shiru yana kallon ciki kaman zaiga Safeerah hawaye masu zafi ne suka taru a idanunsa dasauri ya lumshe idanun batare daya bari sun saukoba, yajuyo yabi gadon da kallo pant dinta yagani aya karkashin blanket dake sanan gadon ahankali yada hannu yadauka
yabude box nasa ya saka sai yayi shiru kafain kawai yazauna akasa yana kallon gadon deep deep chan kasan zuciyansa he s regretting slapping here da shaketan dayayi, he s not regretting being angry with her tamai laifi she lied to him but he s regretting hitting her, kankame jikinsa yayi feeling kaman he s hugging her yarasa natsuwa wutan sonsa na kamasa sosai.
EPISODE 8?? 3??





Wuraren 7 na safiya ta farka bakaramin bacci tayi ba, ciwon kan yasaketa she s seeing everything so bright and clear kaman bacci yasake wanke abu a idanunta, hannunwanta takai tashafa a kumatunta tana tuna marin da Ya Salim yamata da duka karfinsa bugawa kirjinta yayi sannan ta shafa wuyanta tai shiru, wayanta ta kakkalla tana nema batagani ba tasan su Mama da Bbaa sun kirata back, bude kofan dakin akayi Ameeeah ce jikinta duk yayi sanyi kallon kofan Safeerah tayi tai shiru shigowa tayi har zuwa wajen gadon ta tsaya tana kallon Safeerah kaman yanda itama Safeerah ke kallonta cus tasan yarinyar bata sonta, hannunta Ameeeah takai tashafa daura kan kumatun Safeerah cikeda kulawa tace  kumatun ki ya washe sosai wuyanta ta taba tace  wuyan ne yana nan jajir yanda yake, sorry ko Anty Safeerah, muje kije bayi kiyi wanka da brush da alwala tashi daya takao hannu tadauki Safeerah tasowa itama Safeerah tayi tana mamakkin mesa Ameerah ta chanza da taimakonta taje bayi Ameerah ta tsaya agaban bayin shigowa dakin Ammi tayi ganin Ameerah Sauda tai mamaki tace  me kikeyi adakin nan ? Ahankali tace  nazo dubata ne Ammi Kai tsaye Ammi tace  thank you but ni kadai na isa wuce kije dan kallon Ammi tayi sai kawai tawuce tafita, Ammi ta tsaya Safeerah ta tafito daure da towel kanta akasa Ammi takamata ba kunya tace  zoki shirya kiyi salla baban _u yanaso ya ganki ahankali tace  ina kwana Ammi dan dakatawa Ammi tayi tace  lafiya lau yarinyarana yaya jikin ahankali tace  fine kaya Ammi tabata tasaka simple gown na Atampa tai salloli na jiya da ake binta sannan taia asuba Ammi takamata tace  muje ana nemanki faduwa gabanta Safeerah yadingayi suka fito bedroom na Daddy Ammi tabude ahankali lafiyayen bedroom ne mai shegen kyau akwai gado gakuma set na hadadden kujeru Dady na zaune sanye da jallabiya da Baffa shima yana sanye da jallabiya yana ganin Safeerah Daddy yamike yataho wajen kofan dasauri cikeda bala in kulawa shima yataya Ammi kamata from other side yace  be careful wife, yauwa gently haka kunga yanda suka riketa shida Ammi suna tafiya da ita kaman suna tafiya da kwai sai kawai jikin Safeerah yayi sanyi kuka na taso mata har kujera Daddy yakaita kujeran dayake kai two sitter ya zaunar da Safeerah dawani irin sauri Safeerah ta salubo tai kasa tace  Dady ina kwana takalli Baffa tace  ina kwana Abba dasauri Daddy yakamata yace  tashi ki zauna keda baki da lafiya kike dukawa haka zaunar da ita yayi shima ya zauna Ammi saita zauna akan one sitter tana kallonsu Dady ya tsare wuyanta da idanu zuciyansa na tafarfasa yadan gyara murya yace  Daughter na kalleni nan dan dagokai Safeerah tayi ta kallesa saita maida kanta kasa takasa ahankali Daddy yace  I am a man that is guided with rules da principals, naje makaranta nayi karatu har saida nakai matakin Doctor, one of the creatures nakeso nake tausayi is women! Wato mata, you people are the weakest abu a duniyan nan, imagine ko Annabi cewa yayi an halicci mace daga one rip out of all the rips dake jikin d a namiji Daddy yayi shiru sannan yace  yarana biyar wanda biyu ne kadai maza ukun duk mata ne, I watch my girls grow agabana, Safeerah kinga yarana mata I can protect them with my sweat and blood, zan dawo gidan nan naga Auwal ko Salim sunji ciwo amman wlh ko ajikina, but naga daidai da kurjewa ne ajikin Layla ko Ameerah ko Lubna nan fa za aga tashin hankali Daddy yayi shiru yace  komene kikayi Salim baida right na tabaki baidashi! Daddy ya buga hannun kujerah yace  baisan struggles da iyayenki went through just to give birth to you 20yrs ago ba, suka daukeki fes fes dake tsaf lafiyanki kalau ba tabo jikinki suka basa aurenki yau shine shi zai samiki tabo a fuska dakuma wuya wlh wlh sainasa Salim yayi nadaman abinda yayi sau dubu tambayesu kiji nine daidai dake agidan nan Daddy yayi shiru yana kallonta kanta akasa, ahankali yace  daughter! Dago kanta Safeerah tayi yace  calm down ni mahaifinki ne tell me everything that happens banso ki boyemin ko abu daya ko da ko laifin ki ne feel free ki gayamin ina bayanki, as long as ina bayanki kuma ko kene mara gaskiya kin dawo mai gaskiya tell me karkiji tsoro murmushi Baffa da Ammi sukayi jin abinda yace, ahankali tace  jiya mun kai mundan huta yace zai fita yasayo abinci, to ni ina sama namayi bacci tai shiru kaman mai tunani Daddy yace  saime yafaru daganan ? Ahankali tace  cikin bacci nahi muryansa yayi ihu shine na fargita kawai natashi daga gado zumbura nafito ina sauka daga bene nazo kasa kafin nama bude kofa sainaji wanda ake duka yana cewa your

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login