Showing 15001 words to 18000 words out of 160450 words

Chapter 6 - LOKACI BAI KURE BA COMPLETE

M SHAKUR   

01 Oct 2025

139

wannan uban salary da kake biyaba how can I joke da wajen cin abinci na dan hararansa kadan Salim yayi yace  silly boy shiru yamusu bai kara tankasu ba yacigaba da cin abinci while Ammi da Auwal na hira, Dady da Baffa na nasu a falo, bai wani ci sosai ba yadauki mug na coffee yamike baice musu komiba ya wuce stairs yashiga hawa Ammi tabisa da kallo, anatse yake tafiya kaman yana inspecting ko ina dakin dake gaban na Ammi yawuce hannunsa yadaga yayi knocking so daya dudda kannensa ne baya taba fadawa dakinsu kai tsaye he respect privacy nasu, bude kofan akayi autansu ce Lubna batai wata wata ba kawai ta rungumesa tana washe baki dan tana bala in son yayanta tace  Yaya kadawo? Oyoyooo Ameerah da kanta ke a tsefe gashin kam acinye tazo itama tana murmushi akunyace gabanta na faduwa tayi hugging nasa tace  Yaya sannu dazuwa, Yaya kaga gashina duk yakarene saisa nasaka Calmly yet strictly yace  is that ur excuse na yin abinda Allah yahana ? Dasauri ta girgizamai kai, anatse yace  Allah ya tsinema mai karin gashi, get ready I will take you to supermarket gobe to get the best hair products that helps with hair growth gyadamai kai tayi tana murmushi tace  thank you Ya Salim suna mugun tsoron sa but again kuma suna mugun sonsa, he s just the best and very sweet but you need to be open minded before ka fahimce sa inba hakaba zaka dauka ya tsaneka ne, kusan 1min suna ahaka yace  ku cikani dariya dukansu sukayi suka sakeshi wucesu yayi yashigo dakin Lubna ta kulle kofa duk suka biyosa bai zauna kan gadonsu ba saiya wuce gaban dressing mirror nasu ya zauna yayi crossing leg yanashan shayin ahankali yanabin ko ina da kallo kaman wani invigilator this is just him haka yake, akwai observing environment nasa, he s very very security conscious, gadaje biyu ne a dakin daya na kallon daya ga bra da pants akan gadon Lubna kallo daya yamusu yadauke kai yace  wat are those underwears doing saman gadonki Lubna? Dasauri tayi wajen ta kwashe komi tawuce wardrobe nasu tabude tana sawa ciki tace  Yaya sunmin kadan ne Ammi tace nahada nafito dasu wayansa ne yahau ringing da sauri Ameerah tazo wajen tace  Yaya Anty Nanah ne? Kallonta yayi saiyasa hannu yaciro wayan ga sunan Nanah a screen din dasauri Ameerah tace  can I talk to her Yaya? Dasauri itama Lubna tace  Yaya nima I want to talk to her wayan yaba Ameerah yamike yace  idan kun gama ina wajen Ammi yawuce yafice daga dakin yashiga dakin Ammi, Ammi na zaune saman gado hannunta rike da wata yar takarda yawuce yazauna kan coach na dakin yace  ina yini Ammi murmushi tamai tace  yaushe zaka gidansu Khadija? Dan shiru yayi Ammi ta tsaresa da idanu ahankali tace  Salim dago kansa yayi yakalleta anatse yace  zanje Ammi tace  before this week runs out kaje, kudan tattauna kaji me da me take bukata da babu na biki, get to know her, Nanah yar mutunci ce ga hankali da kunya, this is duk abubuwan damuka duba ni da mahaifinka muka hada aurenku kajiko gyadamata kai yayi yace  okay zata sake magana Ameerah tashigo rikeda wayan tace  Yaya ga Anty Nana Ammi tace  Khadijah ce bani ita dasauri Ameerah tawuce tabama Ammi wayan, Ammi tasaka wayan a speaker tace  Yar Albarka akunyace tana murmushi kasa kasa tace  Ammi na ina yini ya gajiya yakuma karfin jiki? Ina Daddy na ? Ammi tace  Alhamdulillah duk muna nan lpy, Dadyn ki na falo, ya su Mama? Nanah tace  Alhamdulillah Ammi, Ammi daman gobe inaso namiki burabusko na aiko miki dashi Ameerah tacemin kina sonshi sosai da miyan hanta murmushi sosai Ammi tayi kana gani kasan maganan yamata dadi tace  gaskiya ne inaso kam sosai amman karki wahalar da kanki dasauri tace  duk abinda zan miki ba wahala bane Ammi in sha Allah gobe zan miki Ammi tace  shikenan Allah yayi albarka ahankali tace  Ameen Ameen agaida Abba, saida safe Ammi Ammi tace  Allah tashemu lpy tabama Ameerah wayan tace  ungo ba yayanki karba tayi tamike ta kaimai wayan karba yayi yasa hannu ya katse wayan yamike yayi kofa Ammi tabisa da kallo, hannu yasa zai bude kofa Ammi tace  I really love this girl Salim! Chak ya tsaya batare daya juyoba, Ammi tace  she s my choice and choice na mahaifinka, yarinya yar gidan mutunci, she s those type of girls that will keep familyn ka together, tanason kanninka da yan uwanka duka, tana son mahaifiyarka da mahaifinka, this is dream of Everyman yasami perfect wife that have no any problem or issues with his family shiru yayi baice komiba kusan 10secs kafin ahankali yace  good night Ammi yabude kofa yafice.
=ث?LOKACI BAI KURE BA=ث?



'

EPISODE =??
Bude kofa yayi yafito daga dakin ya sauko kasa Daddy kadaine a falo yana bude wasu files yana signing ga glass a idanunsa Baffa yariga yatafi, anatse yace  saida safe Dad dagokai Daddy yayi yakallesa yace  kaima saida safe Alhaji Salim bude kofa yayi yafice batare daya kara wata magana ba Daddy yasake kadakai yadauki files yacigaba da signing dayake yi.
Wayansa ne yafara ringing cirowa yayi daga aljihu Nanah ce, katsewa yayi yakirata back ringing daya ta daga tace  Baby dan Allah ka kulani wlh kewanka nake baice komiba ahankali chan yace  ya su Mama ? Ahankali tace  fine tanachan falo kasan yan uwanta har sun soma zuwa daga Katsina, Baby sai maganin mata aketa bani tayi maganan tana rage murya, yace  wat is that ? Yayi tambayan da zuciya daya, baya wani hira da ita itakuma babu abinda takeso kaman taga yana zance da ita, bala in mahaukacin son Major Salim take gani take she s the luckiest girl on earth, ga kudi, ga kyawu, ga gayu, ga ji dakai, ga aji ga ilimi, lankwasa murya tayi tace  Baby kagani ko idan za ama mace aure an samata rana ana bata magunguna haka dake gyara jiki, suna cire ciwon sanyi, suna saukar da ni ima ajikin mace kuma zaisa miji yayi na am da ita zakaga idan an tashi bikin Ameerah da Lubna za a basu maganin mata yace  I don t think Ammi tasan shi dan dariya Nanh tayi yau wlh yabata dariya wato namiji namiji ne, kasa daurewa tayi tace  Baby wlh I love you so much, ina mugun mugun sonka! You are so innocent, I can t wait to officially zama matarka, I promise I m going to be the best wife to you wayan na kunnensa baice komiba yakai dakinsa yacire wayan a kunne yasa a speaker ya ijiye kan gado yana rage kayan jikinsa jin shiru tace  zakazo ka ganni gobe?  No yabata amsa atakaice kafin ahankali yace  let s see within the week kaman zatai kuka tace  okay anatse yace  I have to shower, daganan zan shiga gym murya chan kasa tace  zaka kirani kagama? Ahankali yace  okay! Yasa hannu ya katse yawuce closet nasa ya ijiye kayan daya cire yadauki wani short na nike da singlet na nike black yasaka hand gloves yasa sneakers yafito yasauka kasa yabude wani daki gym ne yahau kan treadmill yafara gudu na bala i kaman a highest yasaka yakai kusan 20min sannan yasauka yayi press up yadaga karfe yadaga rope kafin yaje punching bag yasaka fighting gloves, one of his hubby is boxing he loves it a lot, yayi punching bag sosai kusan 2hours yabata sannan yagama yana zufa sosai yakalli agogo is 12:20 yafito yawuce sama, kaya yacire yafada bayi yayi wanka yafito he wants to smoke but bayayi agidansu kwata kwata out of respect for iyayensa kwanciya yayi agado alkawarin dayama Nanah yatuna hakan yasa yadauki wayan even though yana tunanin tayi bacci yakirata but harya katse bata daukaba hakan yasa ya katse wayan ya ijiye yayi shiru tareda lumshe idanu he s just seeing that little girl face data taimakeshi as usual dan babu ranan da baya gani yazo bacci, he s not sure takai 16yrs ma she will not pass 15yrs, this is 5yrs probably yanzu she s 20yrs haka, there s this guilt dayake feeling koma ina take yanzu aduniya itada iyayenta shiya sakasu in it, shi ya jazamusu, banda yaransa dayasa sukai bincike sama da kasa shi da kanshi saida yayi tattaki yaje garin yaje layin but gidansu is still burnt, even though that neighbor nasu ta sanar dashi ba a kona dasu ba but anma Babanta shegen duka sunje asibiti daganan ne basu kara dawowa ba he went to the hospital akacemai an basu bill but basu dawoba bakudi, his mind is not at ease baitaba samun abinda ya tsaya mai araiba sai this, murya chan kasa yace  where are you!? Nurse Safeerah! Yayi maganan ahankali yadan fuzar da iska yajuya gefe yakai hannu yana kunna side lamp yana kashewa lost in thought. Yarinyar is the most brightest girl he s ever seen in his life, the kindest, she has the most precious heart, she saved his life, zuman data shafamai was wat saved his hand not hospital, yakasa manceta the way she genuinely cried for him sabida taganshi in pain no one has ever done that ko iyayensa though baisani ba maybe dan baitaba wani major ciwo bane, but this particular guy makes a huge space a zuciyansa, sabida her kindness, free spirit and care, he just wanna know she and her parents are fine! He wants to take care of her! Support her, and gives her whatever her heart desires, gashi duk ba asan daga ina sukeba, har school da aka cemai Babanta na koyarwa wani primary school haka yaje school dinma basu da information na background na Babanta cus is not standard school principal din dai tacemai yan Maiduguri ne, ahaka bacci yayi awon gaba dashi.
**

Mama tashigo dakin ta tadata da kyar ta tashi zaune takalli Waleed dake bacci abinsa one thing about him baya tashi da wuri dan baya bacci dawuri itakuma bata samin enough bacci dan bata isa tayi bacci ba sai Waleed yayi duk kalan gajiyan jikinta yanzu ma da kyar ta tashi, bayinsu tawuce ta shiga brush tafara yi sannan tayo alwala tafito tasaka hijabi tayi sallan asuba, one thing is tunda suka dawo gidan nan batada karfi da ikon zama kayi azkar bayan salla saidai kayi a tsaye dan zasuje main flat girki da gyaran gida, mikewa tayi ta linke dadduma tana enchanting morning zikir nata tazo wajen gado tadan lullube Waleed sannan ta shafa fuskansa tana murmushi tamike tabude kofa tafito tabude kofa tafice, flat din tashigo duk suna bacci basa tashi sai around 9, 10, 11 wata rana har 12 ma ko 1 na rana, kitchen tawuce taga Mama awajen tafara hada abinci tace  Mama kibarshi zanyi komi murmushi Mama tayi tace  wuce kije ki koma bacci Waleed bai barki kinyi bacci dawuri ba murmushi tayi she has the best Mom wlh, Mama zata iya dauke duk wani wahalan duniya dan kawai ta huta, tazo wajen Maman tasa hannu ta karbi waken tace  kosai za ayi ? Murmushi Mama tayi tace  eh da kunu, sai pepper soup na kayan ciki gashinan cikin pressure pot, tunda kin karbe girkin bari na gyaro gidan ni dasauri tace  Mama duk zanyi w&  hararanta da Mama tayi yasa bata karasa maganan ba tadauki tsinstiya tafice itakuma tashiga aikin tana tunane tunane yanzu haka Baba na chan compound yana wanke cars, watering plant, gyaran grass and sweeping, tsayawa tayi gaban sink din takalli window gari yasoma haske takalli sama azuciyanta tace  Ya Allah baka bacci, I know Mahaifina baida sana a yanzu baima da hanyar yin sana ar sabida idanunsa baya gani sosai ko gidan nan sabida he s familiar with the sorroudings ne saisa yake komi, Mama na is helpless woman da batai karatu ba, I m all they got Ya Allah! Look at our lives slaving for people da basa appreciating namu ko mana godiya they said this is our payment na ciyar da mu dasuke tadan fuzar da iska tace  Ya Allah karka dawwamar damu ahaka! Ka yantar da iyayena, kabani source na taimakonsu, duk inda zanje IT Ya Allah kasa suna biya nasami wani kudi hawaye ne ya sauko idanunta takai bayan hannu ta goge tacigaba da aikin sosai, Mama tagama gyaran falon ta duka tana saka turare taji karan bude kofa dasauri tajuyo Momma ce sanye cikin wani bubu mai mayafi ga charbi a hannunta tanaja fuskanta ahade kaman wacce ke shirin dambe takalli Mama ta zubar, Mama tamata murmushi taduka cikeda girmamawa tace  barka da saukowa Mama Kubra, ina kwana  kiramin yarki Momma tafadi awulakance tashi Mama tayi tawuce kitchen tabude kofa tace  kizo Safeerah ana kira hannunta ta goge tarage gas tabiyo Mama suka fito ganin Momma tawuce ta duka tace  ina kwana Momma kallon banza Momma ta mata dasauri Safeerah tasauke kanta kasa, Momma ta tabe baki tace  anyways jeki shirya 8 Shamsu zai kaiki inda zaki fara IT, kibar aikin Uwarki takarasa wani abu Safeerah taji a kirji ta daure ahankali kanta na kasa tace  Momma zan iya gama komi before time aiki yama Mama yawa gakuma Wale& ..  Feerah! Mama takirata cikin kakkausan murya dayasa Safeerah tai shiru bata karasa maganan ba, Mama tadan gyara magana tace  yaran yanzu basu iya magana ba wani shirme kike gaya haka Safeerah ? Kada kafa Momma tayi tana kallon Mama tace  ke Amina nizaki gwadama makirci? Ohhh wato ke kin kasa gayamin a fuskana aiki yamiki yawa sai ki turomin yarki dasauri Safeerah tace  Momma wlh bahak& & . Hannu Momma tadaga mata sama sannan takalli Mama tace  na ciyar da mijinki na ciyar dake, na ciyar da yarku na ciyar da jikanku, nine tufafinku, abin shanku, kunzgunku, abincin jikanku, nine makarantan diyarku private university, kin dauka ina kashe uban kudin nan zan bar masu aiki agidan nan ne? Menene amfaninku? Shu aibu kanina ne jini daya kuma, da babuni da ina zaku? Sabida na rufamuku asiri namuku rumfa da sutura eh shine zaki bama yarki sako aiki yamiki yawa? Ahankali Mama tace  kiyakuri Mama Kubra kuskure ne kawai da shirmen yara yasa Safeera& ..  Shu ibu! Shu aibu! Momma tashiga kiran Baba ranta abace kaman daman jira take daga tsakar gida ya amsa yashigo gidan da gudu hannuwansa duk kumfa yana tsiyaya anan falon Momma tamai wani kallon banza da takaici tace  shashasha bakasan zaka goge hannu kafin kashigo min falo ba runtse idanu Safeerah tayi zuciyanta namata daci yanda ake zagin ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????mata iyaye agabanta, Baba dasauri yashiga goge hannuwansa ariga yace  yakuri Mama Kubra, gani kin kirani cikin fushi tace  Matarka Aminatu tayomin aike da yarku yanzu take sanar dani wai aiki yama uwarta yawa dasauri Baba yace  Subhanallahi wani irin magana ne haka nakeji Aminatu, Safeerah Mama zatai magana Momma ta dakamata tsawa tace  lemme finish Mama tai shiru, Momma tace  dan haka ka tattara matarka da yarka da jikanku kubarmin gidana yanzun nan faduwa gabansu yayi dasauri Safeerah takalleta tace  Momma dan Allah kiyakuri Mama tace  Mama Kubra dan Allah kiyi hakuri wlh aiki baimin yawa ba Baba ya zube yana hada hannu yace  Mama Kubra wanake dashi banda ke? Ina kikeso naje? Taya zan fara? Ga makanta? Bara kikeso naje nayi cikeda rashin mutunci tace  sai me toh akanka aka fara baran, sabida na rufamuku asiri sai ahaumin aike, mara mutunci kawai butulu daku marasa godiyan Allah matsalan talakawa kenan kamusu dare su maka rana lumshe idanu Safeerah tayi hawaye na zubomata this is the reason why she never talks take hadiye komi, cus everything she says affect parents nata more, they are being humiliated, abune ya tsayamata a kirji ganin yanda suke begging Momma tana duramusu zagi baki tabude zatai magana kawai sai zuciyanta ya karaya ta fashe da kuka sosai tace  Momma dan Allah kiyakuri, wlh wlh Mama bata aikoni komiba, baki fahimci maganata bane dan girman Allah kiyakuri Ijiyan zuciya Momma ta sauke tana kada kafafu tace  okay zan salllami masu gadina! Shu aibu ka tattara matarka da yarka ku koma dakin masu gadi dake gate dagayau kaine zaka dinga bude gate tunda na kore ka bawai kanada wajen zuwa bane dasauri Baba yace  naji na yarda zuciyan Safeerah ya mugun sosu, bude kofan sama akayi Salma tafito dawani mahaukacin kayan bacci ganin su Mama duke gaban Momma a falo yasa ta harari Safeerah tace  yarinya sai mugun hali kuma saidai aiki ya kashe Uwarki da Ubanki yanzu suka fara, yazama gateman your mother kuma our cook and maid die da bakin ciki, in kinyi zuciya ke nemo naki kudin kawai an dawo gidanmu ana cinye mana kudin gadon da Baban mu ya barmana, kai Baffa dalla tashi kafita tashi Baba yayi ahankali yajuya yawuce idanun Safeerah suka kada sukai ja.
EPISODE 1?? 1??




Momma itama ta dakama Mama tsawa tashi kibar nan kekuma wuce kije ki shirya kafin nasa Shamsu ya tattakamin ke da gudu Safeerah tayi kofa Salma tabita da kallo saikuma tazo wajen Momma tazauna tace  Wlh Momma I hate Safeerah, I hate her ta uban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login