Showing 30001 words to 33000 words out of 160450 words

Chapter 11 - LOKACI BAI KURE BA COMPLETE

M SHAKUR   

01 Oct 2025

141

ta tsaya dab da Mama tana huci tace  daman naga ke daidai kike dani, toh ki gayamin idan yarki ba karuwanci takeba a ina tasami kudi tasayo abubuwan chan nasan bata da kosisi? Mama takalli ledan sannan takalli Momma tace  nabata dubu ashirin yau da safe Baba yace  nakara mata dubu goma nima sabida Waleed baida abinci da pampas Momma tsayawa tayi kallonsu tace  ahhh lallai ni kuka tarunwa akai kuna kare yarku haka? Yau nataba muku yar gudaliya d aya d aya dinku ko, kiri kiri yarinya taje ta saida mutuncinta ayi amfani da ita abiyata amman kuhada baki ku shigan mata kuna rufa mata asiri okay fine Momma takoma tazauna tana kallonsu tana karkada kafa, Baba calmly kaman matsoraci yace  kiyakuri da nasan lamarin siyo abincin Waleed zai xama fada haka da ban bayarda kudin ma, amman yaron najin yunwa baida abincin dazaici gobe da safe eh Fisabilillahi Mama Kubra mu manya muna iya hakura da yunwa amman me karamin yaro Waleed yamana dazamu hanasa abinci ? Yadan matso dab da Momma yaduka ahankali gabanta just to make peace yace  dan Allah kiyakuri kinji bazamu karab& & .. tasssss! Momma ta yankama Baba mari da saida yayi baya zai tumbula Mama da mugun gudu ta taroshi Safeerah tai ihu tace  Babaa!!! Salma tace  ai dakinmai biyu Mom jikin Baba har wani rawa yake kaman marin ya mugun gigitasa baitaba tunanin yayarsa yar uwansa ta jini zata iya marinsa gaban iyalansa ba, idanun Mama suka cicciko da hawaye sosai tarikesa kawai takasa magana feeling yanda jikinsa ke rawa sosai na gigicewa idanunsa namai duhu yadena gani duka daman off and on idanun ke masa kaman switch, Safeerah takalli iyayenta takalli mahaifinta tasake kallon Mama da hawayen ma yazubo mata daga idanu kawai tarike Baba gam dake shaking but she s shattered completely, jitayi ina bazata iyaba enough please takalli Momma ido cikin ido tace  baki kira yarki dake kusada ke karuwa ba sai ni Momma! Maganan saida yadaki kunnuwan kowa adakin hatta Baba da Mama, Mama tasaki Baba tamike dasauri tazo wajen Safeerah zata kama hannunta Safeerah takalli iyayenta ta fizge hannunta da Mama takama tafashe da kukan takaici tace  ki banni Mama ki banni wat? Is she God? Ita Allah ce dazata dinga wulakanta ku? What gives her the right ? Takalli Momma dake kallonta kyur zuciyanta na tafarfasa tace  kawai sabida muna zaune gidanki, sai wulakanta min iyayena kike, me suka miki banda kyautata miki kullum suna miki bauta kaman bayi, kince bazaku sayama Waleed abinci ba, sun bani kudi naje na sayo to wat is there? Salma dake zuwa club sai tsakar dare, tana yawo da matan banza baki kirata karuwa ba saini da bana komi, me muka miki why are you slapping mahaifina meya miki this poor blind man? Kanninki jini daya, mahaifiya da mahaifi daya ya kawoku duniya kike wulakantawa haka sabida kinga kinada kudi ke waye Momma ? Safeerah tai ihu tafashe da kuka sosai ta mugun zuciya tana jijiga Waleed dake kuka sosai a hannunta tana kallon Momma dake kallonta itama, Mama takara kama hannunta tajata Safeerah taki motsi sai kallon Momma take kaman zata rufeta da duka, Salma tawani taso tace  sabida solobiyon wawan ubanki kikema Momma rashin kunya ko toh bari kigani sai kawai tayi wajen Baba takai kafanta zata haureshi wani yarda Waleed Safeerah tayi kaman zararra takai hannu tawani finciko kafan Salman, Salma ta taho a bare, jikake tass! Tass! Tasss! Ta dauramata maruka, Momma tamike ahaukace Salma na kurma wani ihu Mama ta taho zata shiga Momma ta fincike Safeerah ta daura mata mari jikake tass Safeera ta sunkuyar da kanta, Salma ta dunkule hannu tawani nushe bakinta sai jini batai wata wata ba ta naushi bakin Salma itama sai jini suakhau dambe sosai da Salma Momma nakaiwa Safeerah duka tako ina, Mama tafashe da kuka ganin yanda ake dukan yarta Safeerah both Momma da Salma dudda itama Safeerah ta jigbi Salma, Mama tace  Safeerah ni kikema haka? Have you seen condition na mahaifinki ? Chak Safeerah ta tsaya, Momma ma ta tsaya, Salma na goge bakinta taci bugu tace  ke waye ke har kin isa kitaba Salma? Ke da you are the one datasa iyayenta a condition dasuke yau shine kike blaming wasu Momma tace  think da bakiyi abinda kikayi ba da kuna gidanku yanzu haka a Kano, ke kika kawo bala i kika lalata rayuwan iyayenki! Because of action naki mahaifinki ya makance not because of us, all I did is save you guys in return kunamun bauta, after everything I did to you Safeerah ni kikama rashin kunya yau, nida na biya kudin aikin da aka miki kika haifo wannan yaron mara galihu na sayamasa sutura da tufafi da ubansa yace bayaso ni kika zaga yau? Ni da na ceceku bayan kin jawowa iyayenki balai? Nida na aurar dake ? Safeerah is feeling so bad cus some magana batai karya ba is all her fault but dudda haka azuciye tace  kika aurama mashayi ni mara tarbiya daya kusan kasheni dai, mesa baki aurama yarki shi ba? Kin tsanemu you don t want anything good for us? Auren zalunci kikamin fizge Safeerah Mama tayi ta daka mata tsawa tace  Safeerah! Is this tarbiyan dana baki? Kinsan Dawa kike magana kuwa? Yayar mahaifiyarki ce! Itace first Botn sai Harira sai mahaifinki! Are you okay, kika kara magana zan tsinka miki mari anan, dauki Waleed kuwuce daki Momma tace  wani dakin? Badai na gidana ba ko ? Mama da Baba dake numfashi sama sama suka kalleta banda Safeerah data duka tadauki Waleed dake kuka sosai tarike ajikinta tana goge hawaye gwanin ban tausayi, Momma tace  kidauki danki ki tattara kibar min gida this night inba hakaba wlh wlh saikunyi mamakin abinda zanmiki Safeerah! Yarinyar danama komi harda makaranta nizata zaga, wlh wlh bazata kwana cikin gidana ba, idan Safeerah ta kara kwana cikin gidana Shegiya uwata ta haifeni! Na rantse muku da Allah ita da danta sai sunbar gidana yau! .
EPISODE 1?? 7??




Dudda jikin Baba was shaking baya ganin at all saida ya yunkuro yana kokarin tashi jin maganan da Momma tayi, Mama ta taho tana kamasa takalli Momma tace  dan Allah kiyakuri Momma, dan Allah, Safeerah yarinya ce, batada wayau, ba hankali batasan me duniya ba, yarinyar da ko Salma ta girmeta ina zaki biyema kalamanta dan Allah kiyakuri zan hukuntata namiki alkawari Baba so yake yatashi yakasa cikin wani irin murya yana haki kaman mai asthma yace  Yaya Kubra kimin rai ina yar karaman yarinya ta zataje da daren nan da karamin yaro hannunta eh, kiyakuri kowani hukunci zaki mana kiyi amman banda koran Safeerah da Waleed ina zata ? Cikin ihu Momma tace  taje wajen karuwancin ta mana, koko taje ta nemo uban Waleed da ware haka nasan yana club yasha giya yayi tatil tadaga murya sosai tace  I don t want to count 5 na ga Safeerah da danta cikin gidana inba hakaba gardawa zan kira nasa su fitar da ita and zaku iya binta babu wanda nahana cikinku daman na dade da gajiya, ungrateful fool na taimakeku bayan Shegiyar yarinyar tajawo muku annoba yanzu tazo tana gayamin magana ke har kinada baki, One! Momma tafara counting jikin Baba yafara rawa sosai, Mama da hankalinta yatashi ga Baba ya birkice ga Safeerah ana koranta tace  Mama Kubra kimin rai, kimana rai, wa muka sani agarin nan? Ina Safeerah zata da yaro da daddaren nan? Ko bakiyi dan halinta ba kiwa Allah kiji tausayin Waleed, ina yar yarinyar nan zataje ta kwana ga Waleed ta ina zata fara eh ? Momma da zuciyanta fess ganin sun rude ga Safeerah na kuka idanu sunyi ja tace  two cikeda rashin imani, azuciye Safeerah takalli Mama tace  Mama kutashi mutafi! Momma dake kallon Safeerah sosai ta kalli Mama dake gabanta tayi kneeling tace  kalli wacce kike rokonma arziki, kalleta Shegiya mai zuciyan banza da wofi saisa Abbati yakusan kasheki butulu kawai kaza maici ta goge baki Mama ta taso cikeda bacinrai danyau Safeerah ta mugun bata mata rai bataga amfanin dan guntun zuciyan Safeerah ba, like yarinyar bata hango abinda _u manya ke hangowa all what Safeerah care about shine adena zagin mata iyaye akuma dena enslaving nasu, Mama tace  Safeerah muje ina eh? Are you okay do you know what is out there in the night ? Azuciye Safeerah tawuce kitchen batare data kula Mama ba, Momma ta kwashe da dariya tace  ku kalli yarku ooo zani Safeerah ta dayko na goyon Waleed tafito falo kawai tasa hannu ta daukesa tana daga hijabi ta goyasa tsaf abayanta, takalli Mama dake binta da idanu cikeda mamaki idanunta sunyi jajir bakinta ya kumbura amugun zuciye akuma kufule tace  Mama sa hijabinki mu kama Baba mutafi sangangan Mama ke kallonta mamaki yagama kasheta tace  you re very stupid Safeerah, nace you re very stupid Feerah, bantaba sanin girman banza ne dake babu wayau akanki ba sai yau, ina zamu? Can you see Babanki is sick is somet& & .. Momma tai ihu tace  three , fashewa da kuka Safeerah tayi dan she had enough ta duka wajen Baba tana kokarin kamasa ganin Mama taki supporting nata tace  ni bazan kara barinku anan gidan ana zaginku ana marinku ba, we are humans not animals, what gives her the right to me beating my sick father? Sai randa ta kashesa zaku bar mata gidanta? We are leaving gidanta for her, da mu kwana agidan nan gwara mu kwana a titi wlh tawani kama Baba da duka karfinta ya mike sai kawai yayi luuuu a sume Mama ta tarosa da mahaukacin gudu tace  Innalillahi Wa Innailaihi Raji un Five! Salma tai shewa tace  time up yau zamuga karshen fitsararra Momma tadaga wayanta takai kunne tace  kuzo gidana yanzun nan while Mama na faman jijjiga Baba daya sume sukaji ana bude gate wasu maza na shigowa guda biyar dasauri Mama ta ijiye Baba ta taho kawai takama hannun Safeerah taboyeta abayanta tana kallon mazan dasuka shigo dakin yan shaye shaye Momma tace  idan yarki batabar gidan nan ba wlh saina bawa yaran nan ita sun gamamin da ita ke kuma ba inda zaki zauna ki kula da mijinki dan kinsan babu wanda zai muku wahala hankalin Mama na atashe tace  kimana rai Mama Kubra, ina Safeerah zata, ke Safeerah bata hakuri cikeda rigima da taurin kai tace  ko wuka za a samin a wuya bazan bata hakuri ba make kanta Mama tayi tafashe da kuka tace  Safeerah ni kikema haka iyyee ni Momma tace  kucimin uban yarinyar nan in bata fita ba dasauri Mama takama Safeerah dake kuka gam abayanta tace  zata fita tafito da ita waje mazan na biyosu tayi kofar gida da ita takalli yarinyar sai tace  mesa kikemin haka Safeerah? Yau kin batamin rai i will not forgive you easily ? Cikin kuka tana shesheka da zuciya tace  Wlh wlh Mama saina cireku daga gidan nan, bazan taba yadena Matar nan ba she s very wicked shiru Mama tayi tana kallonta tace  yanzu ina zaki? I can t live Babanki haka baida lpy, kinada kawa a hostel na school dinku ne? Girgiza mata kai tayi alamun a a sai Mama tace  toh ina zaki dakiketa fada yarinyar sai shegen zuciya irin na su mutanen farko ? Shiru Safeerah tayi tana shesheka sai chan tace  zanje company danake IT akwai masallaci zan shiga na kwana awajen, Mama don t worry babu abinda zai sameni just take care of Baba, Allah zai bani yanda zanyi, I will arrange something mukoma Kano Mama tai shiru tana kallonta kaman ta rungumeta taita kuka, saita warware zaninta tamika mata 2k tace  kije Allah ya tsareminke babu abinda zai sameki, Allah ya kareku keda Waleed, kafin gobe Babanki ya farfado zamu lallaba Momma kidawo girgizama Mama kai tayi tace  Wlh bazan dawo ba Mama nagaya muku, kuma kuma saikunbar gidan nan hannuwanta Mama takama saita shiga dukan hannuwan bada wani zafi ba tace  taurin kanki da zuciyanki yayi yawa fa Safeerah kina mace, mehaka iyye kalli matsalan dakika sake sakamu ciki again  Malama ana nemanki ciki gardawan suka tsaya kan Mama, daya cikinsu ya kalli Safeerah yace  bar unguwan nan goge fuska Mama tayi tajuya takoma ciki Safeerah tajuya dasauri tashiga tafiya kirjinta bugawa yake sosai, tanayi tana share hawaye today is one of the saddest day of her life, take cewa company su inda just jiyan nan tafara aiki how sure is she ma za a barta ta shiga ciki? Jijjiga Waleed dake kuka abayanta tadinga yi harta fita tahau keke zuwa junction ta tare mota tashiga sannan Waleed yayi shiru kaman yayi bacci .

Around 8:30 tasauka bakin junction tashiga takawa da kafa tana addu a Allah sa abarta ta shiga, Allah daurata kan koma waye ke gadin, hartakai company wani dattijon security ne ke gadi ya tsareta agaban gate yana ganinta ya ganeta yace  Hajiya me kike nema? Me kikazo nema ? Ahankali tana saita muryanta daya koma kaman ta kamu da mura sabida kuka tace  na manta da key na a office namu dan Allah inaso na shiga na dauko kallonta yayi ga goyo dayagani abayanta yace  can I see baby dake bayanki ? Gyadamai kai tayi ta juya ta daga hijabinta sama tace  d ana ne Waleed ya kalla dake bacci yana kara haskasa da touchlight yace  okay zaki iya shiga yabude mata gate tawuce ciki yabita da kallo yana tunani, rayuwa sai ahankali mutane are fighting one battle or the other, ba yaune farko da zakaga wani ma aikaci yadawo company ya kwana ba, people are facing problem, from face nata yaga alamun mari ga kumburin baki harda dan jini idanu sunyi jajir hawaye ma basu gama bushewa ba, maybe mijinta yamata duka tazo nan ta kwana kafin gobe ta nemi option, if he can help her by letting her sleep why not, she s just lucky shine on post da abokin aikinsa ne da bazata shiga ba.

Wucewa reception tayi tabude kofa ahankali akwai wuta awajen tawuce kofar mosque tabude ahankali ta shiga ta taba bango ta kukkunna wuta tashiga masallacin tawuce bangaren mata shima ta kunna wuta tashiga daga hijabinta ta kwanto Waleed dake bacci sosai ta rungumeshi a jikinta ta zare zanin ta shinfida awajen sannan ta kwantar dashi ahankali tana sauke ijiyan zuciya tana kallonsa hawaye na cika idanunta yanzu zuciyanta ke kara breaking sabida Waleed, wat is she gonna do yanzu? Ta ina zata fara? Yaya zatayi da Waleed? Sai kawai ta rushe da kuka tana yaushe bakinta cus Waleed na ji zai farka.

Wuraren 8 yayi parking motarsa a compound dinsu yayi shiruu batare daya kashe motan ba ya lumshe idanu kawai, yakai sama da 20mins ahaka sai kawai yabude idanunsa yadan gyara zamansa yasa hannu yadauki wata iPad dake dayan seat na gaban motan kawai yayi logging in portal na company su yashiga CCTV to be honest baimasan mesa yayi ba wlh, yayi accessing all feeds na cameras din department by department yake dubawa, alamun mutum yagani a reception da sauri yayi clicking on camera mutum yagani da dogon hijabi tana tafiya ahankali tawuce masallaci babu camera a masallaci so baiga wayeba, bangaren details na ma aikatansa ya shiga yadauki number security gate yakira yakai wayan kunnensa ringing daya aka daga akace  Sir kai tsaye yace  wacece tazo company mu this night? Kunmasan da mutum aciki? Dasauri mutumin yace  Sir banine a gate ba I will resume post by 10:00PM Sir amman bari naje na tambayesa Abdullahi ne anatse yace  okay, no need to hang up dasauri da gudu yafito waje daganan waya Salim yaji yace  Kai Abdullahi Oga yakira wai waye yazo office da daddare haka? Dasauri mutumin yace  wannan sabuwar zuwan ce yar IT kaman she s having problem ne she looks like wacce akama duka saisa I let her in maybe she s not safe katse wayan yayi yawani yi mahaukacin reverse yabar gidan, tafiyan 20mins normally ke kaisa company daga gidansu but yau 13mins yakaisa budemai gate sukayi duk sunyi mamakin ganinsa karasawa yayi yay parking wajen da ake parking ya sauko yana sanye da manyan kaya yadi milk anyi dinkin jumper yana zuba uban kamshi, anatse yawuce wajen kofa yashiga yayi hanyar mosque yabude kofan slippers dinta yagani abakin kofa, daga wajen yanajin kukan yaro da kuma kukan babba duka atare, gently yabude kofan mosque din batare daya bari yayi kara ba yashiga tafiya ahankali towards kofar side din mata yakai daidai kofan ya tsaya jimm yana sauraron yanda take kuka da yanda yaron ke kuka shima hannu yakai asanyaye yabude kofan karan bude kofa yasa Safeerah tadago kanta afirgice tajuyo takalli kofan while Waleed ya tsala ihu yashige jikinta yana kuka yana kallon mutumin shima da idanun bacci da yunwa cus baici abincin dare ba, bayan hannunta takai ta share fuskanta da sauri jikinta har rawa yake ta yunkura tamike tasa hannu tadauki zanin goyon dasauri tana rike Waleed dake kuka ajikinta ta taho wajen kofan inda yake tsaye kanta akasa muryanta dukya hargitse tace  dan Allah kuyakuri na zo nan bada izini& &   who beat you!? Ya tambayeta tone nasa na nuna bacinrai sosai, tana jijjiga Waleed dayaki dena kuka yana kallon Salim dake kallonsu kaman ya sansa daga wani waje, yace  who slapped you and smacked your lips? Who did you fight with ? Yasake tambaya adan zafafe da saida gabanta yafadi sosai, murya chan kasa tace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login