Showing 18001 words to 21000 words out of 160450 words

Chapter 7 - LOKACI BAI KURE BA COMPLETE

M SHAKUR   

01 Oct 2025

143

Yaya ma tafini kyau ?Dasauri Momma tajawota jikinta Salma ta kankameta ashagwabe, Momma tace  wat are you saying Salma? Yarinya fara kal dake inake ina hada kanki da black skin Safeerah haba haba, ai sama taiwa yaro nisa saidai yadaga fuska ya kalleta shafa gashinta Salma tayi tace  Momma harda gashi tafini fa dasauri Momma tace  Kin fita keda kesa relaxer jibi gashinki common stop the comparison kina ragema kanki daraja ne, the kind money kike spending on your body why will you compare kanki damai shafa alayyadi ? Turo baki Salma tayi ta bala in jin dadin maganan mamarta tai blushing ta gyara zaman kanta a cinyan Momma tace  you re the world best Momma .

Dakinsu Safeerah tabude kofa ta shiga idanunta sunyi jaa, waje tasamu akujera ta zauna hawaye na saukowa daga idanunta tana gogewa da bayan hannu, ita kadai tasan metakeji azuciyanta, itafa da ace ita suke zagi, suke ciwa mutunci, suka maida jaka wlh bazata damuwa as long as iyayenta nada martabansu da kimansu, mesa Momma da yaranta this small Salma ke zagin mahaifinta da mahaifiyarta? Why? Wlh kawai tausayin su Mama takeji kuma harda bataso taja musu fitina dasaitama Salma dukan da akace ta zagi Baba bazata karaba, marasa tarbiya kawai da girmama na gaba dasu, she hated gidansu na Kano sabida yan daban anguwansu but yanzu she rather lives there sau dubu da wannan rayuwan gidan na Abuja wani kalan kaskanci iyayenta ke facing? Zata nemi aiki da zai taimaka mata tarike iyayenta da danta, saikuma tai shiru nawa ne kama haya? Nawa abinci? Asibitin Baba, abincin Waleed? How can she do all of those? Itada batada any qualification, takai almost 20min kuka take sannan ta tashi ahankali ganin seven yayi tawuce dakinsu tabude kofa ta kalli gado Waleed na bacci abinsa zuwa gaban gadon tayi ta duka takai hannunta tashafa kan Waleed murya chan kasa tace  Waleed pray for Ummy kaji! I don t want this life for you my Baby tai maganan ahankali takai dayan hannunta ta goge fuskanta sannan ta mike tawuce bayi ta watsa ruwa a gurguje tafito Vaseline nata ta shafa ta warware gashinta da sauri gashin yazubo saura baifi 2inches yakai waist nata ba gashin baki sosai ta shafa man kitso tadan taje sannan tasake packing tai donut da bakin sannan tabude sip din tanada tufafi ba laifi tun na akwatin ta na zamanin aurenta ne, wani blue atampa tadauko gown aka maga ta saka sannan ta dauki sky blue gyale mai duwatsu masu kyau babba taciro sannan tayi dauri taciro file na credentials nata datai photocopy tadauki bagpack nata tasaka sannan tasaka flat shoe tafesa body spray nata mai dadin gaske tafito, tajuyo ganin Waleed na bacci still tafito tabude kofa tafito tsakar gida tayi kyau sosai wlh gata da tsayi ba sosai ba dai, she looks so good, flat din tawuce tabude kofa ahankali Momma tagani da Shamsu suna zaune a dinning suna breakfast ya shirya tsaf cikin kananun kaya duk suka kalleta karasawa wajen tayi tace  Ya Shamsu ina kwana wayansa yadauka da car key yamike yace  muje ke I have somewhere to be kina batamin lokaci gyadamai kai tayi Mama tafito daga kitchen rikeda kula Safeera tace  natafi Mama Mama bata kalleta ba gudun kar ace tai laifi tace  adawo lpy Safeerah tajuya tabisa suka fito compound Baba ya wanke motarsa tsaf yana kara gogewa sai sheki motar take suka taho wajen, yayi murmushi yace  an fito sannu da kokari Shamsu nagode sosai, Safeerah sai an dawo ko, ayi addua, Allah bada sa a Ameen Safeerah ta amsa ciki ciki dan fushi take da Baba, Shamsu bai tankaba yashiga motan itama tashiga gaba yaja motan aka bude musu gate suka fice, saida suka shiga kan titi cikeda isa Shamsu yace  saura mukaje ki disgani! This is number one biggest construction company a Nigeria kaman irin su Julius Berger haka suke, suna gina titina, railways, estate etc, this people are bastardly rich, the Maradis kenan! Kudinsu gado sukayi tundaga zamanin kakannin kakanni and gasu all of them are bless, Babansu shine Maradi Jet co yana harkan jirage he s the only person a Nigeria dake kawo jirage yana saidawa yana bada shatter, sai dansa shine mai Maradi construction din nan Babban Soja ne kaman wasa yabude this construction company boom sun zama global, bama ya iya managing abokina dawani Indian Man Paresh ke mishi managing company, sai kanwarsu Layla tana auren dan shugaban kasan Nigeria sai sisters dinsa biyu da basuyi aure ba lemme even tell u I m trying to see yanda zan samu daya na aura sabida family mu yazama so powerful but that big brother nasu baya wasa and seems he doesn t like me, nafara magana da Lubna yahanata tacemin school zatayi she blocked me so dan haka banso ki kofsani, mind your business kiyi aikinki kibar wajen kidawo gida, wlh if you do anything dayasa aka kirani I will kill you Safeerah u hear me yadaka mata tsawa gyadamai kai tayi tace  naji Ya Shamsu company sukakai yanada girma tsaresu akayi a gate saida Shamsu yakira Auwal yasa aka barsu suka shiga company is so big ga manya manyan motoci na goni daban daban parked a big space din, parking yayi inda ake parking sannan yafito ahankali Safeerah tabude motan tafito wani iri jikinta yamata saitaji wani irin tsoro da anxiousness irin wanda kakeji din nan idan kaje sabon waje tafiya Shamsu yafara hakan yasa tabisa tana tafiya ahankali suka shiga building din, receptionist ne a lobby din saiga wani status na ginin gida da titi anyi komi me kyau is just a work of art ta tsaya tana kallo Shamsu yafara tafiya jin shiru yasa yajuyo ganin ta tsaya tana kallon abun yasa yaji kaman ya dura mata ashar amman ba dama a kufule yace  Safeerah! Firgigit Safeera tajuyo da kanta ta kallesa yamata wani mugun kallo ta taho da sauri kanta akasa suka wuce 2nd floor wani office da aka rubuta CEO suka wuce secretary tace  are you Mr Shamsu? Dasauri Shamsu yace  yes yes murmushi tayi professionally tace  welcome Sir, Mr Auwal is expecting you tayi maganan tana bude musu office
Shamsu yace  thank you ya shige Safeerah biye dashi ta shiga tana zaro manya manyan idanunta tana kallon office din da bata taba ganin me kyau dinsa ba ga wani mutumi zaune gaban table yana magana dawasu ma aikata dasuka karesa hakan yasa tashiga bin ko ina na office din da kallo kaman bakauya while Shamsu yasami kujera yayi zamansa comfortably, shikuma Auwal ya sallami ma aikatan suka juya sai alokacin idanunsa suka sauka kan wata yar yarinya dayabi da kallo tundaga kan kafafunta har zuwa saman kanta Shamsu yataso cikin murmushi yace  Boss Auwal mutumina suka wani kashe hakan yasa Safeerah ta natsu takallesu Auwal yace  Shamsu wai har yanzu kaki aure Shamsu yace  kai kayi ?Suka kara kwashewa da dariya sannan suka saki hannun juna Auwal yakoma yazauna yakalli Safeerah yace  Sister ka ce ? Kallon Safeerah yayi datazo wajen table din da sauri gabanta nadan faduwa tace  ina kwana shiru yayi yana kallonta saita sauke kanta kasa, murmushi Auwal yayi yace  you remind me of Lubna kanwata haka takeda tsoro, sit down please yanuna mata kujeran gaban table din zama Safeerah tayi ahankali, Auwal yace  give me the necessary document bagpack nata tabude taciro komi tadago kanta tamikemai karba yayi yashiga dubawa saiya dan dago yasake kallonta kanta akasa saiya kalli Shamsu yace  kacemin kanwarka dan sosakai Shamsu yayi yace  kaga surname dina da nata daban ba well kasan Momma da kwashe kwashe woman of people, wani brother ta tadauko daga chan Kano da iyalansa itane cinsu shan& .. katsesa Auwal yayi yace  I get she s your cousin Sister dan yatsine fuska Shamsu yayi baiyi magana ba, saiya sake murmushi yakalli Safeerah da kanta ke kasa yace  welcome to Maradi Construction Company Malama Safeerah dan dago kanta Safeerah tayi takallesa saita gyadamai kai anatse tace  thank you Sir zaro idanu yayi yace  wani Sir call me Yaya Auwal tunda ni abokin Yayanki ne can I see designs naki gyadamai kai tayi tasake bude jakan taciro wani files ta basa ya karba, to be honest she s an average designer bawai ta iya zanen hauka dinnan dazasuyi wowing naka bane, nothing special, Shamsu shima na ganin zanen yayi tsaki yace  danasan baki iya zane ba daban kawoki nan ba doluwa kawai dan kallonsa Auwal yayi yace  don t be harsh Bro! Duk ahaka muka fara muma ai it s okay! She will get better with time yakalli Safeerah da kanta ke kasa yace  don t mind Yayanki, you are trying, naga 6weeks zakiyi ko ? Gyadamai kai tayi yace  okay zansa secretary dina takaiki HR department zasu danyi magana dake sannan su kaiki inda yadace dake dazakiyi aiki pay, attention and learn bazaki samu problem dakowa ba, for me the only thing da zaisa nayi fada dake is late coming, this is one of the strongest rule na company nan we don t tolerate late coming, be punctual okay Safeerah gyadamai kai tayi ahankali, Shamsu yace  wai ke wawiyan inane baki iya magana bane ko bakinki na ciwo ? Dasauri tace  toh naji Yaya Auwal Shamsu zai kara magana Auwal ya danna wani bell yayi kara hakan yasa aka bude kofa secretary tashigo tace  I m here Sir files da komi na Safeerah yabata yace  take her to Mr Gorge HR, he will take it from there  yes Sir karba tayi takalli Safeerah tace  let s go beautiful Miss dan murmushi kadan Safeerah tayi tamike tsaye tabita suka fice, ganin Auwal yabita da kallo yasa Shamsu yadanyi gyaran murya dasauri Auwal ya kallesa, Shamsu yace  don t mind me I m grumpy sabida bacci bai isheni ba Momma tace saina kawota nan, ga yarinyar da shegen shirme dudda tayi aure harda d a dasauri Auwal yace  Matar aure ce Safeerah ? Girgiza kai yayi yace  no bazawara ce! Mijin ya saketa, tanada yaro that s almost 3 now ahankali Auwal yace  ayyah that s sad Shamsu yayi murmushi yace  but kasan Salma ba my BabySis she s still very single she s only 22yrs dan shiru Auwal yayi yana kallonsa part of the reason baiyi making Shamsu a close friend ba dudda tare sukai Havard University a kasan waje sabida halinsa ne yanada wasu halayya da ya tsana he s strongly against, this less than 5mins sitting yayi abubuwa da dama da bayaso from yanda yayi treating Safeerah, see rayuwan nan not all fingers are equal, akwai masu kudi akwai talakawa but why will u be feeling special sabida kanada kudi kaman kafi talaka? Look at the way yake treating yarinyar sabida yaga yana kallon Safeerah yadauka sonta yake shine harya faramai tallan sister sa taciki Salma, dan murmushi yayi yace  wooooh ahh ni inada Babe dina zamuyi aure soon ma jira nake agama na Ya Salim Shamsu yadanyi wani disappointing smile bai kara maganan ba sukayi hira kadan Auwal yasake yin baki hakan yasa Shamsu yatashi yamai sallama yatafi.
EPISODE 1?? 2??


Mr Gorge was so good to her, she must be special dan basu taba accepting yan IT ba, ko yan NYSC, he was kind to her yamata explaining komi tunda IT ne kuma 6weeks zatayi dau zata dinga yin one week a each department sabida tasami vast knowledge on how construction companies work, yace this week she will start with Marketing/Customer Care Service Department yatashi tabisa abaya suka koma first floor wani babban daki that looks like classroom yabude yashiga tana biye dashi mutanen office din sunkai 15, kowanne gaban laptop ga chair mai kyau ga coffee machine da water dispenser, ga TV, ga telephones dayawa wasu na waya, very fine office kaman wani conference room duk aka bisu da kallo cikin murmushi yace  we have newbie, she s here for 6weeks IT, her name is Safeerah Shu ibu let s welcome her tashi dukansu sukayi suna tafi duk kunya yakama Safeerah banda school nasu bata taba zuwa organization ko kampani haka ba, tayi murmushi kadan tadanja gyalenta tana rufe bakinta kaman wata yar kauye tama kasa magana balle ta gaidasu, wata mata tazo wajen yar babba haka tana sanye da abaya kafin tai magana Mr Gorge yace  meet head of this department Madam Maimuna ahankali Safeerah tace  ina kwana murmushi tamata takai hannu ta karbe gyalenta daga wajen baki tace  welcome to my dept Safeerah, don t be shy, lets go to your sit takama hannunta Safeerah tabita taja mata kujera ta nuna mata ga laptop awajen tace  zauna zama Safeerah tayi ahankali ta sauke jakanta Gorge yawuce yafita Madam Maimuna tawuce wajen coffee machine tasaka paper cup tamata coffee tadauki wani cookie daganan pantry takawo ta ijiye gaban table na Safeerah dasauri Safeerah ta kalleta murmushi tamata tace  have some coffee and calm yourself down i will be back to give you proper orientation nai assigning miki task gyadamata kai Safeerah tayi tawuce ta tafi, bakaramin dadi taji ba sai tadan fara natsuwa kowa kuma yacigaba da aikinsa babu mai wani kallonta.

Wuraren 11 ya shigo falon, Ammi natare dawata bakuwa makociyarsu ce, ahankali yace  ina kwanan ku Ammi tace  ka fito zokai breakfast girgizamata kai yayi yace  sauri nake Ammi I have meeting with Paresh and Auwal, where are the girls? Murmushi Ammi tayi tace  sun tafi school juyawa yayi yace  natafi Ammi  adawo lpy Allah bada sa yabude kofa yafita, anatse yake tafiya wajen wata black Lamborghini Urus yaje yabude motan yashiga yadauki black glases dinsa yasaka sannan yaja motan gateman dinsa na gaidasa rage gudu yayi yasa hannu a dayan seat na motan yadauki bandir daya na yan 500 dake Wajen yabasa sai godiya yake yawuce yatafi.

Wuraren 12 yakai company nasu kwata kwata shi baya parking anan waje, wajen parking motarsa yaje a kasan basement yadan dade cikin motan sannan yafito sai wani uban kamshi yake yawuce yafito direct wani elevator dake wajen ya shiga daya kaisa 3rd floor yafito yawuce wajen wajen wani off office dake wajen gawata secretary dake aikinta awajen bamata lura dashi ba, kamshin turarensa dataji yasa tadago kanta dawani irin sauri tamike tsaye tace  welcome back Sir, it s so good to see you batare daya kalleta ba yace  thanks I need coffee please  coming right up Sir office dinsa yabude yashiga that looks like a suite ya mahaukacin hadu wucewa yayi yazauna yashiga bude files da aka ijiye mai awajen dan ansan yau zaizo ya kunna desktop din yakalli agogon sa he needs to be in barrack by 2 yanada meeting yau da Lieutenant General, glasses na idanunsa ya zare akai knocking kofa yace  common in Auwal ne yayi wani murmushi yace  welcome Boss  thanks ya amsa yana duba files din, aka sake knocking wani dan india ne yashigo sanye da suit zai iyakai 45yrs yace  welcome Boss  thanks Mr Paresh yafadi still reviewing files din saiga secretary ta shigo tace  Sir your coffee just the way you love it ta ijiye agabansa yace  thanks Miss Becky murmushi tayi tajuya tafita, yadauki coffee yakai baki ya kurba ya ijiye sannan yakalli Auwal yace  mergin na gross profit namu yayi decreasing compare to last year, what happen? Yanda yake magana bazaka taba dauka Auwal kaninsa bane babu wani wasa is just a strict work conversation, bayani Auwal yashiga yi yana hadawa da report na accounting department, meeting din yakaisu har zuwa one but it was productive suka fito dan zuwa salla shida Auwal suka jera sai gaidasa ake duk randa ya shigo idan zai tafi he gives them lot of money araba so ma aikatan sa loves him die, nan masallacin su suka shiga dake nan cikin building din ga AC ga komi.

Tasowa Madam Maimuna tayi takalli Safeerah dake aikin shigar dawasu record a computer simple work ta bata as per new comer tace  tashi muje salla gyadamata kai tayi tamike tsaye wayanta kawai ta dauka suka fito tare, matar tace  sunana Maimuna yarana uku duka mata yata tafarko zakuxo tsara haka murmushi Safeerah tayi tace  ya sunansu ?  Aysha, Habiba, Maryam daidai sun iso restroom bayin very clean fitsari tawuce tayi tafito tashigayin alwala, ta gama ta gyara dankwalinta gashin goshinta ya kwanta lub she looks damn beautiful, Madam Maimuna sai kallonta take gyalenta tayafa akai da kyau Maimuna tace  muje tunda kin gama wucewa tayi suka fito suka sauka nan kasa hanyar wani door sukayi, Madam Maimuna agaba tama biye da ita, bude kofan sukayi dan corridor ne ga takalma awajen na maza da mata, suka cire nasu Hajiya Maimuna ta shiga masallacin ahankali itama tasanya kafanta ciki ta shiga wani irin sanyi taji ya ratsata sosai ko uban AC mosque dinne oho sai kawai ta kasa motsi ga wajen da few maza dake zaune dan an idar da salla yanzun nan, su mata sai sun shigo sannan zasu bude wani kofa su shiga side na mata asalin kofansu ana gyarawa so dole ta side na maza suke shigowa, Hajiya Maimuna hartakai kofan shiga tajuyo ganin Safeerah na chan kofa tsaye batai motsi ba ta kame yasa tace  taho mana Safeerah!
Hakanan sunan ya daki kunnensa da zuciyansa dummmm! Rabon dayaji sunan nan tun 5yrs ago! Tundaga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login