Showing 1 words to 3000 words out of 136570 words

Chapter 1 - SARKI SAMEER 1 HAUSA NOVEL

xeemat   

26 Jan 2025

5400

[21/12, 3:00 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI SAMEER....💅
                             By
                ❤xeemat...love❤

             🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Edited🤗😎


   ....Ina ma'abota masoya makaranta littattafe kugarzayo nan domin kusamu naku rabon karku bari abaku labarin wannan litttafin me tafe da nasa sabon salon na daban wanda yasha bambam da sauran, wanada ya hada da sarkakiya me wuyar fahimta, tausayi😢makirci,mugunta😠san abun duniya,Son zuciya,Hassada babban ciwo gameyinta,bayan haka ba iya nan ya tsayaba ya hada da barkwanci da nishadantarwa da fadakantarwa da kuma wannan babban abun me gaba ɗaya watakon soyayya💞 hot romantic story💓
kude kubaza kunnuwanku da idanumku👀 domin ganin yanda wasan ze kaya gaba daya muje zuwa....

  Ina fatan Allah yabani ikon farawa lfy da gamashi lfy batare da wata matsala ba kuskuren da zanyi aciki Allah yayafe mina bani ɗaya,

Sannan ina f fatan zan samu hadin kanku baki daya Domin wannanne littafina na farko aduniya,Abun da yake me kyau mudauka muyi amfani dashi marar kyau kuma muyi watsi dashi.

ALLAH YAKARAWA ANNABI DARAJA DA FADILA ALLAH YABARMU DA SONSA HAR ABADA ALLAH YAKASHEMU DA SON ANNABI MUHAMMADURRASULULLAH(S A W)

DAGA SABUWAR MARUBUCIYARKU ME SUNA AZEEMA D AMINU.(XEEMA.....)

         BISMILLAH.......

Episode1

  "Mom! Mom!! Mom!!!

.....Wata yar budurwa da baza ta wuce kimanin shekara 21zuwa 22 ba tashigo cikin falon ko sallama babu, tana kiranta tana haurawa upstairs din dake falon after some minutes ta sakko tana ta kumfar baki tana zagaya falon tana mamakin ina mom din nata tashiga.

Bata gama tunanin ba naga wata mata da bazata gaza shekara arba'in ba zuwa da biyu ko ma da biyar tana shigowa ta fadada fara'ar fuskarta tare da cewa...

"A'a daughter yaushe kika shigo?

Bata bata amsaba takaraso inda take tare da ruƙo hannun tafara cewa.. "Mom wai kin san waccan yar iskar yarinyar can nagani tare da BOSSAY sai wani faman washe mishi baki take harda kyalkyala dariya shikuma ya wani tsaya yakura mata ido kamar ze cinyeta ta karasa maganar kamar zata hadiyi zuciya ta mutu tsabar bakin cikin da take ciki.

Mom ɗin da tundazu ta zubawa diyar tata ido batace mata komai ba sai ɗan murmushi datake yi wanda bekai har zuci ba tare da jan hannun ta zawa cikin falon ta zaunar da ita akan haddun kujerun falon da aka ƙawatasu da abubuwan more rayuwa wanda tsayawa ma faɗarsu bata loƙaci ne kawaide kana gani kasan bana qananun mutane bane saboda ya hadu iya haduwa yaji dukiya acikinsa,

Ɗan shafa fuskarta tayi batare da tace mata uffan ba ta tashi sannan ta wuce kitchen, bata daɗe da shiga ta sake dawowa da tire a hannunta cike da fruit sai cop da lemo me sanyi ta ajiye mata zatayi magana kenan yarinyar tai saurin katseta cike da rashin tarbiya murya asama tace..

"Wai Mom meye haka tun dazu ina tayi miki magana amma kinyi min banza ni banzan shaba ki dauke abunki banaso tafaɗa tana ƙoƙarin tashi tabar mata wajen, cike da rarrashi tayi saurin maida ita tazaunar sannan ahankali tace "Haba my daughter ki kwantar da hankalinki akan dan wannan abun nibanga abun tashin hankali ba kwata-kwata me akayi akai wannan kucakar yarinyar me kama da aljanun da.. marar asali marar gata watake da shi? Waye ubanta? Wacece ita da zata saki kiringa wannan tada hankalin akanta haba haba kamar ba jinin cikas family ba kamar badaga cikina kika fito ba tafada tana ƙara rike hannun ta, sannan tace "Kibar min komai a hannu na zata shigo gidan tasameni zanyi maganinta ne daga ita har waccan tsohuwar banzar, Tafaɗa tana kallon ɗiyar tata dataga alamun tadan saki fuskarta, Ɗorawa tayi da cewa to wai me yasa ma baki tsaya tun gaban nasa kinci mata mutun ci, kinyi maganin ƴarsa yarinya, har kika shigo gida kina sakawa ranki damuwa,

Kallon Mom ɗin tata tayi sannan tace "Mom wlh takaicine yahanani yimusu magana ma danji nai kamar zuciyata zata buga idan nayi magana shiyasa
kawai na shigo gida in fadamiki.

Karkaɗa kai kawai tayi sannan tace gwara da kika rabu da ita kar kijama ta ƙara renaki a gabanshi, intashigo za tamin bayani ne kisha wannan sannan kije kiyi wanka kishirya kifito kiyi lunch kafin tashigo, bata jira cewar ƴar ba, ta cigaba da cewa,  "Aikenta ma fa nayi amma shine taje ta tsaya hmm zatayi bayani badai ina cikin gidan zata shigo ta sameni....

Cike da jin daɗi yarinyar ta mike tana cewa "Mom bazan shaba bari kawai inje in watsa ruwa infito tafaɗa tana barin wajen ta haura upstairs inda dakinta yake tana tafiya, itama Mom ɗin ta tafi nata ɗakin tana ƙara jaddada hukuncin dazatayiwa yarinyar nan idan tadawo,

....Suna shiga, aka shiga turo ƙofar tare da leƙo da kai, wata yarinyar ce da tun farkon tattaunawar tasu tana gun atsaye duk ta gama jin tattaunar tasu, ƙarasa shigowa cikin falon tayi tana faman rarraba ido cike da fargabar abun dataji da tunanin kuma irin hukuncin daza ai mata yarinyace dabaza tawuce 14years zuwa 15 ba ita ba doguwaba ita ba gajeraba medium ce duk da banga gashin kantaba amma nasan tanada gashi sosai saboda gashin danagani kwance a goshinta da ya kusan hadewa da gashin girarta hakanne yabani tabbacin tana dashi, domin ance juma'ar da zatayi kyawu tundaga Laraba  ake iya gane ta, Ga wani uban saje da shima yake kwance luff luff awajensa ga uban eye lashes zara-zara meyawa, Ga tsayi tana da manyan idanuwa farare tass da su kwallon idonta brown color idonta kuma sexy ne idan tana kallonka sai kadauka bacci ne a idonta, fara ce tass kamar katabata jini ya fito amma saboda wahalhalun rayuwa ba aganin hasken nata sosai sai dogon hancinta me tsinin gaske idan ka matso kusa da ita sai kai tunani inkamatso dab ze iya tsokanema ido sbd tsayinsa sai bakinta dan qarami kamar gidan tsutsa gashi pink kamar ta shafa abu akai, sai kirjinta da ya dan fito amma ba sosai ba, sai bombom ɗinta da hips fin daidai jikinta basuyi mata yawa ba basuyi mata kaɗan ba, komai de yaji dede....

Bata gama tunane tunanen ba taji anbuga mata wata uwar tsawa, juyawa tayi zata kwasa aguje ta fita taji ankara daka mata tsawa tare da cewa "gidan ubanki zaki dan uwarki idan kikasake kibar falon nan sade uwarki ta haifi wata a lahira idan ana haihuwa, ko da yake ma na manta ashe baki da uwar ma, saidai ince waccan banzar tsohuwar ta haifi wata irinki idan zata iya shegiya me kama da aljanun da ido kamar na mayya waya sanin ko mayya ce bamu saniba cikin dan wallahi kinfi kama dasu...

Cikin jin ɗacin abun da tafaɗa mata ta juyo a hankali kamar wacce ba ƙashi a jinkin ta yayin da hawaye suke zubowa kamar ruwan sama suna wanke mata fuska tana ƙarasowa bata ankaraba taji anyi mata wawuyar shaƙa tare da ruƙe kunnanta kamar za acire mata shi, Da sauri tasa hannunta zata dafe wajen taji anriƙe mata hannun tare da murɗeshi tabaya cike da mugunta abun ya hadar mata ga wuyanta ashaƙe ga kuma kunne a murde tanaso tayi magana amma takasa saboda shaƙar da akai mata ba ƙarama bace tana kakari amma ta kasa furta ko kalma ɗaya sai da kyar tasamu ta sassauta mata ruƙon wuyan cike da tashin hankali da muryar ta data fara dashewa tace "Dan Allah Mom kiyi hakur......

"Bata ƙarasa bada hakurin ba tace "Dan ubanki ban hanaki kirana da Mom ba uwarki ce ni dazaki kirani da Mom ko ban hanaki ba?

Dasauri yarinyar ta shiga girgiza kai tana cewa "Kin hanani kiyi hakuri bazan ƙaraba na tuba wallahi bazan sake ba....

"Kima sake" Mom tafaɗa tare da cewa "Daughter saketa ki barni da ita ni kaɗai ma na isheta .

"Cike da jin daɗi ta sakar mata hannun tana cewa yauwa Mom kar kiraga mata wlh"  Ita kuma kamar wacce akeyiwa kirari haka ta daddage da iya ƙarfinta da Allah yabata ta kifa mata marin da saida taga star kafin tagama tantance zafin takaraji wasu marukan da saida tasaki wata razanarniyar ƙarar da ta karaɗe duka gidan tanasakin ƙarar kuma ta sume agurin, Mom naganin haka ta taɓe baki ta nufi wajen da fridge yake ta ɗakko ruwa me sanyi ta watsa mata, Agigice kuwa ta tashi zaune tana jada baya tana hada hannuwan ta da suke tafaman karkarwa tana kara basu hakuri amma basu saurareta ba kuma ko kadan basu tausaya mata ba sai ƙara ɗaga ta da tayi da gashin kanta tana janta har zuwa kaofar kitchen tana faɗar...

"yau saina yanka ki inga uban da ya tsaya miki kikeyiwa mutane rashin mutuncin dakiga dama acikin gidan nan, tana faɗa ta nufar ƙofar kitchen ɗin....

"Saidai bata kai ga ƙarasa shigaba wani saurayi yayi saurin ƙarasowa gurin yana riƙe hannun ta, tare da faɗin "Haba Mom mekike kokarin yine haka tundaga waje fa ake jiyo ihun ki duk akan wannan yarinyar me tayine?

Cikin masifa da take azalzzalal zuciyar ta, ta ɗago tana cewa "MUSBAHU sakar min hannu kafin indawo kanka ni kake cewa ina ihu ko? Watakon gani mahaukaciya, tafaɗa tana fisge hannun ta daga riƙon da yayi mata, Dagawa tayi zata ƙara kamo yarinyar, sai yayi saurin tsayawa a tsakiyar su yana cewa "Dan Allah Mom ki tsaya kisaurar......

Be karasaba ta katse shi da cewa "Anƙi a saurare ka ɗin ubana kamatsa min daganan ko sainayi maganin ka ai yau sainaga uban da yatsaya mata agarin nan be ankara ba tayi wani tsalle ta kamota ta rike ta gam, Sannan tajuya inda ƴar tata take a tsayaye, tana ta faman rarraba ido tawani ɓangaren tana me jin haushin zuwa yayan nata dayayi shikenan zesa aƙi hukunta yarinyar kamar yanda takeso, Tawani bangaren kuma tana jin tsoran zuwan nasa...

"Daughter zo kiwuce ki dauko min wuqa a kitchen, tafaɗa tana ƙara riƙeta da kyau saboda Musbahu da ya riƙeta shima yanaso yajanyeta daga hannunta...,

Cike da ɗarɗar ɗin yayan nata ta biyo ta gefen su zata wuce kenan..Yayan nata yada ka mata tsawa tareda cewa, "Ke..! "wlh RASHEEDA indan kika sake kika ɗauko ke zan yanka da ita, in kuma kina ganin wasa kuma bismillah...

Aikuwa da sauri taja burki ta tsaya cak, takasa motsa ko da hannun tane bare ƙafar ta tayi motsi alamun zata ɗin, tsayawa tayi tafara tunanin mafita yanzu umarnin waza tabi, ƴaƴan ko mahaifiyar........

"Please kuturawa ƴan uwa da kuma group group saboda Allah,
[21/12, 3:00 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI SAMEER.....💅
By
❤xeemat....love❤

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Epiesode 2

Edited..🤗😎

"Wacce aka kira da RASHEEDA ta juyo tana kallon mahaifiyar tata...
Itama ita take kallo tana huci ta ƙara yi mata magana da cewa "bazaki wuce kidauko min ba ko shi ɗin ubanki ne dazaki tsaya dan yace kar kije watakon yafini matsayi awajen ki ko?

"Girgiza mata kai tayi kawai sannan tayi sum sum sum tabi ta gefan sa zata wuce yayi saurin sama ta ƙafa ta faɗi a ƙasa jikake bummmm tafaɗi aikwa bashiri tasaki wata rikitattiyar ƙara,

Da sauri Mom tayi jifa da yarinyar da tariƙe, ta nufi wajen ƴarta cikin sauri ƙarasa gurinta ta shiga cewa nashiga uku na lalace ni SADIYA jama'a zai karairayamin yarinya, tana maganar tana ƙoƙarin ɗaga ta daga gun da tafaɗi....,

A loƙacin da take wannan bambamin shiko wanda aka kira da Musbahu tuni yayi sauri yaja hannun yarinyar ya fita da ita waje, ya barwa iska a jiyarta yana jinta tana kiranshi tana zaginshi ko waiwayowa ma beyiba bare tasa ran zai amsa ko zai dawo, data gaji da kiran nashi sai kawai tagirgiza kai tana cewa ai zaka dawo kasameni ne tana masifa tana ƙoƙarin cicciɓar yarta ta amma takasa saboda ita kanta nauyin kanta takeji saboda ƙiba ga rashin motsa jiki saide aci ajaɓe agu guda kamar buhun kwaki, dataga bazata iyaba kawai sai itama tazauna agun tana ta faman sauke ajiyar zuciya numfashinta harwani ɗan ɗaukewa yake sabo da tsabar gajiya sai kace wacce mayunwacin zaki yabiyo aguje.


"Saida ta ɗan ji dama dama sannan ta buɗe baki da ƙyar tace kiyi hakuri kitashi kinji my daughter kirabu dasu zasuzone har inda nake danni wurgice daidai nake da ƙugun kowa bana barin ta kwana wlh sai nayi maganin su...

Itadai Rasheeda jinta kawai take tana kallon ta saida tagama surutun nata, sannan ta miƙe da kyar tana shirin tafiya..

Da sauri Mom tace "Daughter Dan Allah ɗanzo ki tai maka min in tashi tafada tana miko mata hannu, kawai saitayi wani kasake tana kallon ta tana tunanin ita tayama zata wani iya riƙeta bayan buguwar da tayi data faɗi bama wannan ba gashi ita abu ba kadan shirgegiya da ita zata wani ce mata ta ɗagata tabbb...

Sai da taƙara maimaita mata sannan tadawo daga tunanin da ta tafi,

Kallon ta tayi tare da taɓe baki tace "Gaskiya Mom bazan iyaba Wallahi, kawai inje garin riƙeki ki ƙarasani shi inbe karyani ba aike kya Karyani, Tana gama fadar haka tajuya tayi tafiyar ta, tana ƙara cemata inkingaji da zaman gurin kya tashi dan kanki, daga nan tai wucewar ta upstairs"

"Itako Mom da ido kawai tabi ta batare da tace mata komai ba inda sabo ta saba da halin ɗiyar tata dan haka batare da taji komai aranta ba tayi ƙoƙarin miƙewa (niko nace yau naga ikon Allah mikewa kawai sai kace raƙumi ne ze tashi) Saida ta wani bubbuɗa ƙafafu sannan tayi goho da rarrafe rarrafe ta dafa jikin bango sannan ta mike da kyar bayan ta tashinma saida ta ɗan jingina da bango ta warwara hannuwa, saida ta ɗan yi jimm sannan tafara takawa da kyar ta ƙarasa tsakiyar falon sannan tasamu three seater ta barbaje dan ko hauka take bazata fara tunkarar bene ba tace zata hau dan tsaff zata iya runtumowa da ƙasa gawara tai zaman ta anan ko da daddare ta haura bayan tagama hutawa, (kujitafa yanzu wajen karfe biyu ko uku ma batai ba amma wai take kiran dare😅......


MUSBAHU kuwa yana fitowa da ita bece mata komai ba yanufi hanyar ƙofar gidan su da ita yana kaita bakin wani gida da yaji jiki qofar gidan ma akarye take saboda ƙanƙantar shima saikai tunanin ko shago ne, yana ƙara sawa yasakar mata hannu yajuya da nufin barin gurin.... sai ya tsinkayo sanyaryar muryarta me daɗin sauraro wacce in tanayin magana saikaji kamar waƙa take rerawa bazakaso ma tayi shiru ba idan tanayi.

Cakk ya tsaya tare da juyowa still de beyi magana ba yatsaya yana kallonta ita kuma sai taci gaba da cewa "Ya Musbahu nagode sosai da taimakon ka sanan kuma dan Allah kakara basu hakuri wallahi ba laifina shi yatsayar dani wallahi kuma ban....

Bata ƙarasa ba yasa yatsansa a kan lips dinshi alamar tai shiru kawai, shirun kuwa tayi tare da sunkuyar da kanta,

Idon sa a kanta yace mata kar ta damu tashiga gida kawai kuma kar tasake tadawo gidan su a yau ko wajema karta fito tabari sai gobe"

Buɗar baki tayi da nufin ƙara magana shima sai ya kuma saurin dakatar da ita, yace "kije kawai nace miki kuma kiyi abun da nafada miki kinjini?

Da to ta amsa mishi tukunna tajuya tashiga gidan.

Saida yaga shigar ta, tukunna shima yatafi yana tunanin kuma dramar dazeje yatarar wajen mahaifiyar tashi me rigimar tsiya be san meyasa batason zaman lafiya ba kwata-kwata a rayuwar ta, Da wannan tunanin ya karasa gida, Har ze shiga kuma ya canza tunanin gwarama kawai yayi wani wajen idan ta huce zuwa anjima yadawo yasan abun ze zo mishi da sauki bakamar yanzu ba idan ya shiga abun sai yafi tsamari...,

Tana shiga cikin ɗan ƙaramin gidan nasu tai ƙoƙarin kawar da damuwarta saboda kar DADDAN ta tagane halin da take ciki, Sai kuma aka samu akasi tana shiga tayi karo da ita, tafito daga banɗaki tunda ta fito kuma idon ta kuma ƙyam a kanta yake har taƙaraso cikin ƴar ƙaramar tsakar gidan, ƙasa tayi da kanta tace...

"Dadda sannu da gida tafaɗa tana ƙoƙarin shigewa ɗakin, Dadda bata amsa mata ba sai jefa mata tambaya da tayi da cewa "Me yasame ki a fuska ko ince waye yamare ki? har haka fuskar ki ta kunbura, tayi jaa?

Da sauri ta shiga girgiza kai tana ƙoƙarin mayar da hawayen da ya cika mata ido yana san zubowa tace "Bakomai fa Dadda faɗuwa nayi, ta ƙagare maganar da son wucewa dan tagaji da tsatstsare tan datayi.

"Dadda tace "hmmm naga alama ai wuce to" Da sauri ta wuce ciki tana shiga ta kwanta akan yar tatsitsiyar katifar ɗakin sannan ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciyar me sauraro ita sai yanzuma abun yake kara ɓata mata rai tana cikin yi taji muryar Daddan tata a kan ta tana cewa "Tashi kizauna"

"Bata tsaya ba wajen jinkiri ko yi mata musu ba kuwa ta tashi tazauna kai a ƙasa tacigaba da share hawayen ta amma sunƙi tsaya sam"

Dadda ma zama tayi a kusa da ita tare da kamota jikinta ta ungumeta saida ta bari kukan nata yadan tsagaita sannan ta dagota cike da kulawa takira sunnan ahankali tace "AMEESHA" ta amsa mata da na'am" sannan tace faɗamin abun da yafaru me sukayi miki?

A hankali tafara ce mata "Daman ɗazune Mom ta aikeni gidan su hajiya Rabi ina fitowa kuma sai na hadu da BOSSAY awaje niban ma ganshi ba fa shi yaganni yafara min magana yakirani ina zuwama nace mishi ai aunty Rasheedan bata nan sai yace ai tunda yaganni ma shikenan ko be ganta ba bashi da damuwa tunda duk ɗaya muke awajen shi, sai narufe bakina ina dariya ina cewa kai kai yaya Bossay

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login