Showing 1 words to 3000 words out of 100561 words

Chapter 1 - BAKAR TUKUNYA hausa novel

07 Feb 2026

446

[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA*
Thriller
HUMAIRAH BULAMA
Yota 011.

*Shimfiɗa*

Bismillahirrahmanirrahim…


Da gudu mutumin ya fito daga cikin wata ƴar bukka ya nufi shashen wasu daga cikin mutanen wajen kamar kafafunsa za su tsinke..
Yana zuwa ya ja ya tsaya sai kuma ya d’an durk’usa ya kama guiwowinsa da hannayensa duk biyun yana haki.

Da sauri d’aya daga cikin su ya d’ago yayinda ragowar duk su ka yi kamar ma ba su lura da shi ba domin kuwa sun riga sun san me ke tafe da shi!

Yanayinsa na baiyyana y’ar damuwa mutumin ya ce “lafiya kuwa ka ke D’an Baba?”
Cikin haki wanda aka kira da ‘D’an Baba’ ya d’ago yana kallonsa wanda suna had’a idanu da d’anuwan nasu ya fashe da wani kalar kuka, cikin kukan sosai ya ce “ta kasa haihuwa wannan karon ma…
Ku taimake ni in kaita asibiti dan Allah…”
Shiruuu duk maza guda bakwai d’in su ka yi waenda suka kasance y’an uba a garesa..
Da kyar babban yayansu wanda shi kad’ai ne dama ya kulashi tun zuwan sa wajen ya ce masa “D’an Baba da ace Ina da yadda zan yi to da na taimaka maka…
Ka yi hak’uri…”
Durk’usawa matashin mutumin wanda ba zai wuce shekaru ashirin da bakwai a duniya ba ya yi, ya kamo
k’afafun d’anuwan nasa yana kuka sosai sannan ya ce “kar ka saka in sake rasa haihuwar nan da za a yi mini a karo na takwas!
Kar ka saka d’an da za a haifa mini shima ya koma kamar ragowar, ba iya haihuwa za ta yi ba….”
Cikin daka masa tsawa wani a cikin y’an uwan nasa ya kalle sa sanann ya ce “mu yi sata kenan mu baka? Ko ya ka ke so mu yi?
Bar nan kafin in yi kwallo da kai wallahi.”

Ganin yana ta b’ata lokacinsa gashi kowa ya k’i taimaka masa ya sanya ya yanke shawarar komawa wajen matarsa ya ci gaba da tofa mata addu’a ko Allah ya ji k’ansa, dan hatta y’an k’auyen ma duk sun k’i kulashi…
Tun lokacin da aka tabbatarwa da kowa shine ya kashe Mahaifinsu shikenan ya zama abun gudu ga kowa a kaff cikin k’auyen nasu….hatta y’an uwan nasa ma da kyar aka hanasu su kashesa shima sannan yayansa babba ne kawai yake kulasa….sai ungozoma wadda Mahaifiyarsa ce ta yi mata hanya ta koyi aikin..su biyu kacal ne suke kulasa a kaff k’auyen nasu. Mai k’auyen ne ma ya hana a jefesa a k’auyen saboda shi har gobe ya ce ‘bai yarda D’an Baba ne ya kashe Babansa ba’.

Yana nufar bukkar tasu ya ga ungozomar ta fito hannunta kacha-kacha da jini fuskarta babu annuri cike da damuwa…
Suna had’a idanu da ita ya fahimci mai ya faru dan haka ya sake rushewa da kuka.

Cikin rashin jin dad’i matar ta sauk’e wata zazzafar ajiyar zuciya sannan ta fara magana kamar haka…
“Ina mai bak’in cikin sanar maka da mutuwar d’anka wanda ya yi tun a kwanaki biyar baya da na daina jin motsinsa dama na gaya maka abunda nake zargi kenan..alamun rashes na sepsis da kuma symptoms d’insa waenda su ka baiyyana a jikinta ne ya tabbatar mini da gawar har ta fara rub’ewa a cikin cikinta kenan, dan duk wani symptoms na sepsis d’in sun baiyyana a tattare da ita ga kuma bleeding ta na yi na fitar hankali sannan Yaron kwata-kwata ya daina motsi tuntuni hatta alamun bugun zuciya ma da na auna duk babu tun kwanaki biyar da suka shud’e.
Har yanzunnan da nake yi maka magana ban kai ga iya fito da shi ba domin kuwa babu kuzari kwata-kwata a jikinta ballantana ta yi nishi…

Yunwa da rashin abu mai kyau a jinin matarka sune suka kashe maka Yaro tun farko, wanda da ace an kaita asibiti tun wanchan satin da ta dinga suma kafin ya rasu an had’a duk su biyun an ba su taimakon gaggawa to da Ina da yak’inin da ikon Ubangiji za su iya fitar mata da shi lafiya wala
ta hanyar aiki ko kuma su yi mata allurar nak’uda dukda jikinta babu k’arfin kuzarin da za ta iya yin nishi tsabar yunwa but na san ba za a rasa yadda za a yi ba…dukda kuwa na san Yaron zai zo da cutar yunwa da wasu negative abubuwan ko da ace sun yi nasu taimakon…


Ni dae na yi duk k’ok’arin da zan iya yi amma na gagara fito da Yaron kwata-kwata…
Na sha bak’ar wahala amma na yi ne domin Allah, kuma na san ko na ce ka kawo kud’in ungozoma cewa za ka yi babu..
Shawarar da zan baka itace ku dakatar da haihuwa tukunna dan Allah..
Babu wani abu mai gina garkuwar jiki a jikin matarka dan haka in har ta sake yunk’urin haihuwa gaskiya inaga da ita da Yaron tun a wata uku za su iya rasa rayukansu…
Sannan jini ya k’i tsaya mata kuma na duba akwai alamun mahaifarta ta samu matsala, sannan ga halinda take ciki dan haka ka nemo kud’i a duk inda su ke ka kaita asibiti a cire Yaron nan da nake
da tabbacin zuwa yanzu ya fara salub’ewa ma a cikin cikinta, a samu a yi mata gyaran ciki sannan a duba mahaifarta sosai itama in abun na magani ne a yi in na cirewa ne a cire tun itama bata kai ga rub’ewa ta zagwanye mata a cikin ciki ba….”
Ta na kammala fad’in hakan ta sa kai ta wuce a ranta ta na cewa ‘ae ko alhakin kisan ubanka da ka yi ba zai barka ba wallahi…’


Ta na wucewa ya zube a wajen ya yi zaman dirshen dab’ass!!
Kafin ya saki kuka mai tsananin sauti..kamar wani d’an k’aramin Yaro.
Mahaifiyarsa da Mahaifinsa ba su da kowa, cikin uk’ubar maraici suka taso.
Shima zuwa yanzu kam ya tabbatar ba shi da kowa domin kuwa waennan y’an uwa da Mahaifiyar da ta haife su ba zai kira su da nashi ba.

Matarsa itama da kyar ya sameta ya aura wadda ta kasance bata da kowa wannan dalili ya sanya suka ci burin tara y’ay’a da family a rayuwarsu sannan bayaga haka daga ita d’in har shi Ubangiji ya d’aura musu wani irin mad’aukakin masifaffen son y’ay’a!
Dukda kuwa jarumin talauchin da suke fama da shi hakan bai sanya ko da sau d’aya sun jii shakkar tara iyali masu tarin yawa ba…
In ana maganar talakan tukuff shi kansa ya san ya ciri tuta, a yanzu haka kwata-kwata a rayuwarsa kayan sakawar shi kala uku ne tsabar babu
Matarsa kuwa tun lokacin da ta auresa ya yi mata set biyu har gobe sune sai kunce da ta samu na hijabai domin kuwa kayan nata duk sun yi taushi sun yage shiyasa matar mai k’auyen take tausaya mata yayinda ragowar matan garin kuwa ko kallon ta ita da mijinta ba sa yi ballantana su tausaya musu..
Abinci kuwa wani zubin sai su yi kwana uku ba su ci ba!
Har abinci a bola ya sha d’aukowa ya kawo mata su gyara su ci….


Wani kalar tausayinta ne ya sake mamayesa domin kuwa shi a karon kansa ya san tabbas ya gana mata azaba da talaucinsa, mai karya zuciya.
A hankali
yana tangad’i sannan yana kuka sosai ya mik’e ya shiga cikin bukkar tasu domin ya samu su rarrashi juna sannan ya ganta kafin ya fita ya nemi kud’i a duk inda su ke kamar yadda ungozoma ta ce.

Yana shiga ya ganta kwance cikin jini ta na hawaye
dan haka ya k’arasa gareta da sauri ya d’agota ya rungumeta jikinsu duk su biyun yana wani kalar karkarwa…


Sama-sama ya fara jin sauti da murya kamar yadda ya saba jin ta ta na yi masa kuwwa a ka da kunne a duk sanda ta so tun kwanaki hud’u baya da suka shud’e….
Kazalika itama matarsa wadda take rungume a jikinsa suna kuka yashe cikin jini…kusan a tare suka fara jin komai su biyu kacal….
“Ku amince da mu, za mu dawo muku da Yaronku za mu baku arzik’i, za mu baku haihuwa bila adadin, amma kuma za ku bamu jininku guda d’aya tak! Ya yi mana bauta…
Wallahi in har ku ka amince da mu to tabbas duniya kanta sai ta yi alfahari da ku da ahalinku….”
Sai kuma firgigit su ka bar cikin duniyar muryoyin da aka tsunduma su cikinta suka yi snapping out a tare…
Da sauri suka kalli juna kusan a tare sai kuma kowannensu ya sunkuyar da kansa k’asa still suna rungume da juna har yanzun jikinsa ya na wani kalar karkarwa ya na haki sosai yayinda itanma ya lura gaba d’aya a tsorace take…
Tunda ya ke bai tab’a b’oye mata komaiba amma tabbas zai b’oye mata wannan abun kunyar, ba zai tab’a yin maganar ba ballantana ma ya saka abun a mizanin hankali domin kuwa kansa a gabas ba zai tab’a gwada shirka ba…
Itama abunda ta ke tunani kenan, Allah shi kad’ai ne mai rayawa da kuma kashewa duk wani abunda za a nuna maka makamancinsa wallahi k’arya ne sai dai a yi maka rufa ido daga baya ka zo ka na da na sani…
Duk su biyun a tunaninsu d’an uwansa bai ji abunda shi ya gama ji yanzun ba.

A hankali cikin son kawar da tunanin da banzatar da shi ya yi istighfari da ta’a’uzi sannan ya saka hannu ya sake k’ank’ameta zuwa cikin jikinsa.
Gaba d’aya su biyun jikinsu karkarwa yake yi, kafin cikin wata kalar razananniyar k’ara ta saki ihu sai kuma ta fara nishi….

Mintuna biyu ne kacal suka sanya shi da ita suka fahimci tabbas nak’uda ce ta ke yinta ganga-ganga…
Cike da curiosity ya shiga dubata domin har ta fad’i a wajen ta na nishi tun k’arfinta.
Ga mamakinsa sai ga kan Yaro nan ya taho gadan-gadan a take da shi da ita duk suka kid’ime suka shiga rud’ani..

Cikin duniyar muryoyin da aka saba tsundumasu suka tsinci kawunansu yanzun ma
“Ku bamu had’in kai ku haifi Yaronku lafiya!
Ku k’i bamu had’in kai kuma shima ku rasashi kamar yadda ku ka rasa ragowar y’a’y’anku.
Ya riga ya zama namu dan haka ku bamu had’in kai…”
(Astaghfirullah)

Ruwan sama aka kece da shi
a take wani nishin ya sake zuwar mata wanda ta na yi kan jaririn ya sake baiyyana..
Kallo d’aya zaka yi masa ka san yana cikin k’oshin lafiya sab’anin yadda ungozoma ta ce har ya fara zagwanyewa saboda ya dad’e da mutuwa….
A take daga ita har shi suka ji wani kalar masifaffen k’aunar Yaron ta dirar musu.

Wata mahaukaciyar dariya suka ji an fashe da ita kafin ace
“Mintuna biyu ne kacal suka rage muku! Ku bada had’in kai ko kuma ku rasashi…”
Yadda aka k’arashe maganar a tsawace ya sanya ta kid’ime!
A take ta ji k’arfinta gaba d’aya komai ya tsaya chak jikinta ya d’auki rawa….

A yadda kan Yaron yake a matse da yadda ta ji k’arfi da nishinta sun gushe ita kanta ta san in ba da kyar ba shima ba zai shak’i iskar duniya ba, dan ji ta yi ma kamar ta na shirin sumewa…

Ko kad’an ba su biyewa muryoyin da zuwa yanzu su ke yi musu kuwwar “ku bamu had’in kai” kamar za su tsaga cikin bukkar suna juyi a saman kawunansu ba!
K’arshema mik’ewa ya yi da niyyar fita domin ya je ya nemo ungozoma wata k’ila ita ta san dabarar da za ta yi a fito da jaririn dan shi a nashi ganin in ya ce zai janyo kan to zai iya raba kan da gangar jikin Yaron ne…
Amma sai dai yana mik’ewa kansa ya juye sam ya rasa hanyar fita, in ya yi gaba kuma sai dai ya ji ya k’ume, k’uumm!.

Cikin kuka ya ke iya jiyo muryarta a chan nesa da shi ta na cewa
“Shima wannan mun rasa shi!
Ba zan iya ba, ba na ganin komai na kasa nishi na san mutuwa za mu yi, ka yafe min..”
Chan k’asa sosai dan tsawar da ake daka musu ana cewa “ku bamu had’in kai”
Har kawo yanzun ta cika musu dodon kunne, kamar za ta fasa ne.
Da k’arfi ya saka dukkan hannayensa ya toshe kunnuwansa ya na kuka sosai wae ko zai samu ya daina jin muryar da ta rikitashi take shirin sanyashi tafka babban kuskure.
A zuciye ya juyo dan bai daina jin komai ba ko bayan ya toshe kunnuwan nasa kuma zuwa yanzu ya fahimci a bayansa ne yake jin muryar sab’anin d’azu da ya rasa daga Ina take fitowa..
Ko da ya juyo bai ga kowa ba kamar yadda ya tsammata dan
a kan matarsa idanunsa suka sauk’a ita kad’ai wadda take tsakiyar haihuwa dan kai da idanuwa sun fito da karan hanci amma abunda ya kama daga kan b’ulolin hancin da ragowar jikin Yaron duk suna cikin jikinta ne.
Kallonta ya ke yi ya na mai jin tsananin k’aunarsu ta na ratsashi…
Yayinda itanma ta ke kallonsa daga nan inda ta ke kwance ta na hawaye ta na kokwanton rabuwa da shi da Yaron da tun kafin ta gansa soyayyarsa ta shiga cikin ranta matuk’a.
****************

Zai fara zuwa muku very soon, in sha Allah.

BAK’AR TUKUNYA
Kar ku bari a yi tafiyar babu ku🙏
[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*

HUMAIRAH BULAMA

Yota

*01*

Bismillahirrahmanirrahim…

Legislative quaters..
Farawa, Kano, Nigeria.


La’asar sakaliya, mai sanyaya zafin da rana ta wanzar domin a lokacin ne ta ke d’auko hanyar fad’uwa sanyi da almuru su maye gurbinta..
Sama-sama flawowin da su ka yiwa garden d’in k’awanya su ke kad’awa daga ganyayyakinsu har reshensu su na bin duk inda iskar da ke wanzuwa a ta sanadiyyar Hadarin da ya ke had’uwa ta kad’a wanda yanayin wajen da iskar har ma da k’amshin da wajen ke fitarwa su ka zamto Abun k’ayatarwa da sanya nishad’i kwarai da gaske…
Tsaye ya ke ya k’urawa waje guda idanu kamar mai shirin haddace zane da duk wani tsari na wajen a cikin kwakwalwarsa..sai dai kuma a bad’ini sam hankalinsa ba a wajen ma ya ke ba.
A hankali ya ke zuk’ar numfashi ya na sauk’ewa cikin tsantsar kasala da rashin kuzari domin kuwa duk da kasancewarsa gwarzo kuma jarumi a fagen komai a yau d’in ya zamto rago…
A zahiri in ka kallesa ba za ka fahimci hakan ba amma a
Bad’ini ilahirin jikinsa a mugun mace ya ke sannan numfashinma kokawa ya ke yi da shi wajen gudanar da shi, sannan ga wani Abu mai tsananin tauri da tsantsar nauyi wanda ya tokare masa mak’ogwaro da kuma zuciyarsa baki d’aya….

Bai juya ba sannan bai ji ko da alamun motsin mutum ba amma ta na isowa wajen zuciyarsa ta sanar masa da hakan….
Ko a lokacin da yake Yaro k’arami sam kuka ba d’abi’arsa bace ba amma a yau a yanzun a take a wajen ya ji hawaye su na shirin cin galaba a kan jarumtarsa su na shirin tarwatsa dukkan wani kuzari nasa su na shirin tarwatsa jajircewarsa su bijiro ma sa da kasala da rauni da kuma gazawa…
Cikin sanyin muryarta wadda ta kasance d’aya daga cikin Abubuwa mafi tasiri wajen yin galaba a kan dukkan wani fushi nasa ya ji ta ce “Assalama alaikom”
A hankali kamar ba ya so
ya lumshe kyawawan idanuwansa a lokaci guda kuma tsantsar zazzafar k’aunarta ta shiga k’ok’arin korar duk wani fushi da alwashi da ya d’aukarwa kansa…
Ganin ya na shirin karaya ne ya sanya ya juyo gareta yana mai saka kwayar idanunsa a cikin tata…
Wani kalar yanayi na musamman su duk biyun su ka tsinci kawunansu a ciki yayinda kowa ya ke nashi nazarin a cikin k’asan zuciyarsa…
“Da gaske kwata-kwata bai sanni ba? Da gaske bai gane ni ba? In har idanu da kwakwalwarsa sun manta da ni shin ta yaya zan yarda da cewar zuciyarsa za ta iya mantawa da ni?”
Ta yiwa kanta tambayar a lokacin da hawaye su ke k’arasa taruwar mata tap a cikin kyawawa kuma sihirtattun idanunta….

Duk dauriya da juriya da kuma jarumtarsa kasawa ya yi, sam sai ya gagara ci gaba da kallonta a halin da ta ke ciki dukda kuwa yadda zuciyarsa ta ke azalzalarsa ta ke kuma sake tabbatar masa da abubuwan da ta aikata masa masu matuk’ar muni….
Cikin hikima ya yi amfani da wani yanayi wanda ya fi kama da jan aji da yanga wajen kawar da dukkan dubansa daga gareta sannan ya ce “Ina sak’on? Zan wuce yanzun….”
Ya yi maganar ya na mai kallon rolex watch d’in da ke d’aure a tsintsiyar hannunsa…
Cikin tsananin sanyin murya ta ce “Ya…..”
Da sauri ya katseta cikin cewa “ba ni sak’on mana AMAL, Ina so in wuce da wuri..na bar matata ita kad’ai a garin da ba namu ba….”

Duk dauriyarta kasa ci gaba da rik’e kukanta ta yi, wani k’ululun bak’in ciki da tashin hankali dunk’ule da takaici ne su ka ziyarceta a take, ba ta san lokacin da ta fashe da wani kalar siririn kuka ba mai tab’a zuciyar duk wani mai sauraronta…..

Ji ya yi kamar numfahsinsa zai tsinke yayinda hankalinsa ya k’arasa tashi sannan damuwarsa ta hauhawa b’acin ransa kuma ya nunku…
Da kyar da mugun kyar ya iya danne kansa ya saita kansa cikin son sake dilmiyar da ita ya ce “you are still a baby, aren’t you?”
Bai jira ta bashi amsa ba ya yi wani d’an guntun murmushi wanda ya fi kuka ciwo sannan ya ce “zan ce ki na gaisheta kuma ae za ku dinga waya…..”
Kasa ci gaba da magana ya yi jin ya kai aya a shafin duk wata jarumta da dauriya da zai iya yi a yau d’in, hakan ya sanya kawai ya saka hannu ya zame leda bag d’in da ke rik’e a hannunta wadda ya ke da tabbacin shine sak’on kawai ya wuceta ba tare da ya iya sake cewa komai ba….
Tabbas Amal ta yi destroying zuciyarsa sannan ta lalata masa abubuwa da yawa, sai waenda Allah ya tseratar amma kuma barinta d’in da zai yi a hakan it’s for her own good saboda ita ya yi wannan sacrifice d’in ba wai saboda kansa ba…
Ko hauka yake yi ba zai tab’a bari ciwon maitar da yake zargin yana tare da shi ya shafi Amal d’in ba ballantana ya tarwatsa ta…..


Har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login