Showing 12001 words to 15000 words out of 122205 words

Chapter 5 - BUZU BOOK2 COMPLETE 2

18 Jan 2026

636

cikin garin Buda. Sai dai shigar su garin ke da wuya, Nana ta fara jin sanyi yana ratsa ta.
Addu'a ta din ga yi, a kan Ubangiji Allah ya rufa mata asiri, ya kawo musu ɗauki, ya shiga tsakaninsu da su Ƙaisar.

"Ma vie" ta ji ya yi magana.

"Na'am Sayyid" Sai kuma ya yi shiru, bai sake cewa komai ba. Yara suka firfito suka tatstsaya bayan ganin mota ta tsaya a ƙofar gidan Uwani.

Uwani da kanta ta fito tana tafa hannu, tana "Maraba da mutan birni. Ina yayar tawa take?" Nana ta buɗe motar ta fito tana murmushi.

Ummi ta sallami mai motar, Uwani ta ce "Ina mai gidan?"

Nana ta buɗe taxi ɗin, ya fito a hankali, kansa rufe da mayafi.

Uwani bakinta fal magana, amma ta haɗiye ta yi musu maraba, zuwa cikin gidan. Babban gida ne mai ɗauke da ɓangarori. Ta kai su sashen ta, aka yi shimfiɗa Sayyid ya zauna ya jingina da bango.
Abin da dai ba ya ƙauna, ya sake tararwa a garin, kallo. Ba ya son a zura masa ido, amma ya lura da yadda ake ta kallon sa.

Uwani ta karrama su da ruwan pure water, da abinci shinkafa da wake.

Ummi ta ce "Kafin cin abinci, Uwani a ina za su zauna, a gyara musu?"

Sai da Uwani ta sake yi wa Ummi ta tas, tamkar ita ce Baban, sannan ta kalli Nana ta ce "Yayata, kin ga cikin gidan nan, akwai ɗakuna, idan ma ba zaku zauna a nan ba, nan baya tafiyar babu nisa, akwai gida da ɗakuna biyu da tsakar gida. Babu kowa a gidan idan za ku zauna".

Nana ta ce "Gara su zauna a inda babu kowa"

Ummi ta ce "Maimakon ku zauna a cikin mutane, yadda ko wani abin ne, a taimaka muku"

Nana ta ce "Akwai dalili gara mu zauna inda babu kowan" Nana kuwa ta yi hakan ne, domin samun rufin asiri na larurar da suke fama daga ita har Sayyid. Ga uwa uba takura da Sayyid ba ya so.

Uwani ta saka yara, su ka je su ka share gidan tas, aka wanke.

Nana ta ce "Sayyid, bari mu je da Ummi, a gyara gidan, sai mu zo mu tafi da kai" Ya saka hannu ya riƙe nata, tare da girgiza mata kai alamar a'a.

"Mu tafi tare za ka iya tafiya?" Ya jinjina mata kai alamar eh.

"To ta so" Ya yinƙura a hankali ya tashi tsaye.

Uwani ta ce "Nana, ku bar shi a nan mana, tun da ba shi da lafiya, ke ku je, ku gyara gidan"

Nana ta ce "Ai ba zai zauna ba, ya ce bin mu zai yi"

"Ikon Allah, ni da bita zai-zai, to Allah ya taimaka" Nana ta yi murmushi kawai, tare da jin nauyin abin da Sayyid ɗin ya yi.

Sauran yaran gidan Uwani, suka bi su Nana, su taya su shirya kaya. Wanda galibi Nana ba ta ma san su ba, saboda ba zuwa garin suke yi ba, domin ita rabonta da garin ma, har ta manta.
Gidan ƙasa ne tsura, da zunzurutun turɓaya Ɗaki ɗaya ne gyararrre, sai aka yi masa siminti, da plasta, aka shafa farar ƙasa, da ƙofar langa-langa. Sai wani ɗakin kuma, si kuma ko rufi babu, sai banɗaki.
Duk lalacewar gidan su Nana ya fi nan nesa ba kusa ba, Ummi jarumta kawai take yi, zuciyarta a cunkushe babu daɗi, biyo bayan tuna cewar a nan Nana za ta rayu. Sai dai ta ga tsantsar tawakkalli a fuskar Nana. Su ka gyara ɗakin aka shimfiɗa leda, sai katifar su. Sai kuma tarin kayan su, na girki sai na sakawa a cikin bagco.
Uwani ta aiko musu da Abinci. Da la'asar bayan Ummi ta yi salla, ta ba wa Nana kuɗin barkononta da aka sayar, ta yi ta mata nasiha da kwantar mata da hankali, sannan ta yi musu sallama.
Ɗan gidan Uwani ya ɗauke ta a kan babur, ya tafi da ita.

Nana ta ƙarasa gaban Sayyid, da ya zuba mata idanu tamkar bai taɓa ganinta ba.

Ta riƙo hannayen sa ta ce "Sayyid, duk da ban san wace irin rayuwa ka yi a baya ba. Amma wadda muka yi, mun yi ta ƙarƙashin kulawar su Habu, ba mu taɓa neman abu mun rasa ba. Amma Allah shi ne abin godiya. Wannan yanayin da muke ciki, ba zai dauwama ba in sha Allah. Ina fatan Allah ya baka lafiya, ya kuma baka haƙuri da juriyar a yanayin da muka tsinci kanmu a ciki".

Ya sanya tafukan hannayen sa biyu, a fuskarta laɓɓansa na rawa, amma magana ta gagara.

Ta girgiza masa kai tana murmushi, ta ce "Ruhinka yana cikin jikina, kar ka damu kanka lallai sai ka yi magana. A jikina ina jin abin da ka ke son faɗa" ɗan guntun murmushi ya yi, duk da yadda yake matuƙar son ya furta wani abu.

Da daddare Uwani ta aiko musu da tuwon dawa, da miyar karkashi, ta sha daddawar kalwa har ɗaurin yajin daddawa.
Ta san ba lallai ya iya ci ba, ta ba wa yaran da suka kawo kuɗi, ta ce su sayo mata buredi da shayi, na gurin masu sayarwa, da kuma maganin sauro, saboda azabar sauron da ke ɗakin.
Sai dai ya ƙi shan shayin, buredi kawai ya ci ya kwanta. Nana jikinta na rawa ta ci tuwon, saboda yadda ranta ya biya, amma ƙarshe amai har ta hancinta sai da ta yi shi.

Kan su kwanta, ta kunna maganin sauro, ta gyara masa shimfiɗa ya kwanta. Ita ma ta hau katifar ta tofa masa Addu'a, sannan ta kwanta a kusa da shi, tana yi masa fifita.

Ta daɗe idonta biyu, kafin bacci ɓarawo ya sace ta. Sai dai kamar a zahiri, kuma kamar a mafarki ta fara jin hayaniya a kanta. Ba ta gama tantance hayaniyar mece ce ba, ta ji wani abu na wucewa ta saman roofin ɗakin. Idan abin ya daki kwanon ɗakin da abin da yake takawa, tamkar kwanon zai buɗe ya faɗo musu a ka.

Ayshercool
08081012143
55

Wata irin yinƙurawa Nana ta yi, cikin azama da tashin hankali ta kifa a kan Sayyid, saboda kar abin da yake takun koma mene ne, ya faɗo masa a ka.

"Ma vie" ya furta da ƙyar can ƙasan maƙoshinsa. Ta ɗago ta fara laluben fuskarsa a cikin duhu.

"Sayyid, ba ka ji wani abu zai faɗo mana ba?"

"A'a"

Ta sake cewa maganar ta dawo "Maganar ta dawo?"

"Eh"

"To sannu" ta furta a hankali cikin tsoro, ta mayar da kanta kan ƙirjinsa a tsorace. Sai dai kamar dole, ta ƙarfin tsiya, wani baccin ya sake awon gaba da ita, tana cijewa da ƙoƙarin hana idonta sake yin bacci, amma abu ya ci tura, baccin ya kuma awon gaba da ita.

Ganinta ta yi a tsaye a tsakiyar ɗakin, itakaɗai babu Sayyid. Ana ta cigaba da hayaniyar da ba ta gane me ake faɗa. Ta din ga waige-waige tana tunanin ina ya shiga haka? Sai dai ba ta gama tunanin ba ta ji muryoyi daban-daban suna faɗin "Lale da manyan baƙin garin Buda. Barka da zuwa." Sai kuma ta ji ana dariya tare da ci gaba da hayaniya.

Idonsa biyu, yana jin yadda ta yi wa hannayensa wata irin muguwar damƙa, ta nutsa faratanta a jikin fatarsa, dan tuni ya karaya jini ne yake fita daga fatar tasa. Ta din ga juya kanta a kan ƙirjinsa tana kuka tana faɗin "A'a, mu ba baƙin ku ba ne ba, ba gurinku muka zo ba, mu ba baƙinku ba ne" jin ta fara ɗaga murya, ya sanya ya murginata gefensa, ya zame hular kanta yana shafa gashinta a hankali, tare da hura mata iskar bakinsa a kunnenta. Daga haka sai ta yi shiru, ta ci gaba da bacci.

****
Barira sai da ta sha jini leda biyu a Asibiti da allurai da magunguna, amma tana komawa gida, abu ya ƙara rikicewa. Domin kuwa babu damar ta sanya haƙarƙarinta a ƙasa ta fara bacci, wannan jibgegiyar magen za ta bayyana, su hau kokowa da ita. Duk sai magen ta yayyage mata fuska da jikinta. Idan ta tashi sai ta ji jikinta na yi mata wani irin zugi da raɗaɗi.
Ta cewa mijinta ita fa ba za ta koma wannan gidan ba. Ya sanar mata an tashi su Nana, daga su sai su Sajida a gidan kamar da, amma ta hau kujerar naƙi ta ce gidan ne ba za ta koma ba. Shi kuma ya ce sai dai ta yi ta zama a gidansu, dan ba shi da kuɗin kama wani gurin.

Shukura ce tare da Hajiya Amina, suke hira. Ta je yi mata sannu da zuwa dawowar da ta yi daga umara. Alhaji Zailani ya yi sallama ya shigo falon.

"Daddy sannu da zuwa"

Ya ƙare mata kallo ya ce "Yauwwa, mara tawakalli da ba ta san ƙaddara ba" Ta yi shiru tare da sunkuyar da kai. Duk irin kashedin da nake yi miki, da rarrashin da na yi miki, ba ki ji ba abin har ya kai ki dizga bawan Allah nan, a gaban mutane kina cewa yana kashe mutane, idan ya yi ƙarar ki kina da shaida a kan haka?"

Ta yi shiru ta sunkuyar da kai. "Tambayarki nake yi" Ta girgiza kai alamar a'a.

"Amma ki ke wannan iƙirarin, maimakon ki mayar da hankali a kan fatan Allah ya raya na gabanki, ya ba ki wani. Ba ki kyauta ba" Hajjya Amina ta yi ta kallon Shukura ko za ta ba shi haƙuri, amma ta yi mursisi.

Ko da ya shiga ɗakinsa, babbar rigarsa ya cire saboda azabar gumin da yake yi. Dan tun da Doctor Sharif ya gaya masa ga yadda suka yi da Shukura hankalinsa ya yi mummunan tashi. Ya kuma sake jaddada wa Sharif, muddin wani abu ya fita to babu hannunsa a ciki. Kuma likitan ya yi masa bayanin process ɗin da ya bi, abu ne mai wahala a gano. Ya yakice gumi ya nemi guri ya zauna.

Hajiya Amina ta ce "Me yasa ba ki ba shi haƙuri ba, kina kallon yadda ya yi fushi?"

"Mummy, duk wannan abubuwan kamata ya yi a tsaya a saurare ni, a kuma fahimce ni. Da hankalina fa ta yaya zan din ga iƙirarin an kashe mini ɗa haka kurum. Mummy ranar da za a yi mini aiki, kina bacci cikin dare, na kasa bacci saboda damuwar da nake ciki, aka buɗe ƙofar ɗakin, aka zo aka kama hannuna aka laluba cannula, aka yi mini wata allura a cikin duhun nan. Tun da aka yi mini allurar nan. Na ji kaina ya fara juyawa, ina neman na fita hayyacina, duk iya ƙoƙarina na kasa, na ji jikina na ƙamewa kamar zan yi jijjiga. Saɓanin da da idan za a yi mini allura cikin dare, za a ƙwanƙwasa ɗakin, sai kin tashi kin ce a shigo tukuna, a kunna ftila a yi mini"
Mummy ta ɗan yi shiru, cike da mamakin me yasa tuntuni ba ta faɗa ba, amma domin kawo ƙarshen maganar, sai kawai ta kawo gigin ciwo ne ya sanya ta ga haka a lokacin. Dan haka ta ce "Duk da haka wannan ma ba hujja ba ce, ke da ki ke fama da ciwo ina za ki tantance wani abu ma. Dan Allah ki bar zancen nan"
Shukura ta yi murmushi ta ce "Shikenan, na bar shi"

Sai kuma ta sake cewa "Mummy, Nana shiru, ni yakamata ki kwatanta mini gidan da suke na kai mata Haidar"

"Gidan Alhaji Garba giwa ne fa, kuma fafur babanku ya hana ni zuwa ban san dalili ba" Dummm! Ƙirjin Shukura ya buga, ta ce "Saboda ne ya hana ki zuwan?"

"Ban san dalili ba, za ki je ne? Sabon gidansa nan Kano"

Shukura ta ce "Wace matar ce a gidan?"

"Halima ce, uwar gidan sa"

Shukura ta girgiza kai ta ce "Ba zani ba, gidansu tsohuwar matar Sagir ce"

Mummy ta waro ido ta ce "Ke haba? Dama 'yar Halima ce matar Sagir ɗin?"

"Eh mana"

"Ikon Allah, da na ce wa Daddy, ya taimaka musu, a samo wa mijin Nana, gurin da zai yi gadi, su samu su zauna, shi ne aka samo gidan"

Shukura ta ce "wai canza masu gadi ku ka yi ne?"

"Ina fa, ina nan cikin gida, daga baya ma Yusuf yake gaya mini. Wai zuwa aka yi da motoci da alama daga ƙasar su ne ma, motocin duk rubutun fransanci aka kwashe su kaf, kuma babu wanda aka yi wa bayanin me yasa"

"Ikon Allah, kuma ba laifi suka yi ba?"

"To ina zan sani, ina nan cikin gida?" Suka ci gaba da tattaunawa da jajanta lamarin. Har wayar Nana suka jarraba kira, su ji ko ita nata mijin yana nan, ba a kama shi ba amma wayarta ba ta shiga sam.

****
Da safe Nana ta tashi, ta fara alwala sannan ta zuba wa Sayyid ruwan da yara suka ɗebo musu jiya, dan gidan babu ruwa. Ya yi alwala a ƙofar ɗakin, sannan suka koma ciki ya yi salla. Sai dai bai ga alamun ta san abin da ta yi cikin daren jiya ba.
Ƙarfe tara da rabi, Uwani ta aiko yara da kunu da 'yar tsala aka kawo wa su Nana.
'yar aiken ta ce "Uwani ta ce idan kin gama karayawa, wai ki je"

Nana ta ce "To, zan zo a ce mata mun gode sosai da sosai, Allah ya biya ta"

Ta koma ta zauna a gaban Sayyid ta ce "Sayyid, ka ga kunu ne da 'yar tsala za ka iya ci, ko na nemo maka wani abin?" Ya girgiza kai.

"To za ka iya cin wannan ɗin?" Ya gyaɗa mata kai.

Kunun tsamiya ne, na daka ba niƙa ba, ya sha kayan ƙamshi, sai dai babu suga ko kaɗan a ciki, ga tsamiyar nan cau har ka.
Ƙuli-ƙulin 'yar tsalan, ya sha barkono, ta zuba masa a kofi ta ba shi. Ya saka hannu ya karɓa.
Tun da ya yi kurɓa ɗaya, ya yi shiru. Nana ta ce "Za ka iya sha kuwa?" Ya jinjina kai ya ci gaba da sha, saboda Nana.
Ya haɗa da 'yar tsalan nan, duk da ba son Abincin yake yi ba.
"Sayyid, idan ba zaka iya cin Abincin nan ba, ka bari na nemo maka wani"

Ya ɗaga kai ya kalle ta, sai dai ba baki, dan haka ya harare ta, ya ci gaba da cin abincin.
Ta yi murmushi ta ce "Ni ka ke harara ko, aishikenan"

Ya gama karyawa, ta saka ɗankwalinta, ta goge masa bakinsa da hannunsa. Ta ce "Bari na je kiran da Uwani take yi mini, daga nan na saka a raka ni, na ɗan yi mana sayayya, dan na san dole za ta daina bamu Abinci yau da gobe sai Allah"
Bai ba ta amsa ba, ya jingina da bango, saboda yadda yake jin daɗin hakan, yana lumshe ido.

"In je?" Ya yi mata shiru, kuma yaƙi yi mata wata alamar, da za ta gane ya amince ko a'a.

Cikin shagwaɓa ta ce "Sayyid" ya kawar da kansa gefe, ya ƙi buɗe ido.

"Duk da maganar nan ɗaukewa take yi, amma dai tun asalinka miskili ne, ina ta magana ka ƙi kula ni, ni ce fa rayuwartaka guda ka ke wa haka?"

Murmushi ya yi, tare da saka hannunsa a cikinta, yana shafawa a hankali.

"Wai ba za ka kalle ni ba?" Ta yi maganar tana juyo da fuskarsa. Ya ƙara rintse idanunsa, wai ba zai kalle ta ba. Nana ta din ga dariya.

Ya ja jikinsa a hankali, ya kwanta a kan cinyarta, ya zuba wa cikinta ido, tamkar zai gano abin da yake cikin.

"Idan na haihu na ga yadda za a yi, da kai da jaririn wa zai bar wa wani cinyar nan" Ta yi maganar tana shafa gashin sa.

*****

Hajiya Sa'a ce take cin abinci, tana kallon Jamila, da take ta cakala kaɗan-kaɗan.

"Jamila ya ne? Ki saki jiki ki ci abinci mana" Jamila ta jinjina kai ba tare da ta ce komai ba.

"Ko dai haryanzu abin da ya faru ɗin ne yake damun ki? Tun wuri ki ajiye wannan abin, ki ci gaba da rayuwar ki cikin kwanciyar hankali. Ɗan ƙaramin abu ne fa, ranar da aka ce ki bayar da jini kuma ya zaki yi? Ki na gani Safiyya ta tafi Dubai ma sarin kaya, kuma duk harka ce ta ƙungiya ta ɗaukakata haka. Har gara ke ma da ba ki da aure, Safiyya da aurenta, amma kalli yadda ta kama ƙasa, mijin ma ita yake yi wa biyayya, ki saki jikinki dan Allah ki daina wannan damuwar.
Ki ƙarasa cin abincin, Talatu ta gyara gidan, idan an zo ana son kaya, kin san gurin da suke, zan je sake duba Fatuhu ne, daga nan na je a gyara mini kaina"

"To Mummy a dawo lafiya"

"Yauwwa Daughter Allah ya sa"

Ta gama abin da take yi ta fita, bayan fitar ta, Jamila ta tashi ta nufi harabar gidan, tana kallon flowers ɗin da aka ƙawata harabar da su. Jibga-jibgan motocin Hajiya Sa'a uku na hawa. Ga na ɗanta Abba biyu. Iya harabar gidan abar burgewa ce, ta yadda duk mai rai zai yi fatan ya samu wannan wadatar. Sai dai kash, hanyar da aka bi gurin tara dukiyar, duk wanda ya ji muddin yana da imani, sai ya gudu da ƙafafuwansa.

Ji ta yi kamar wani abu yana bin wuyanta, ta juya a hankali ta ga Abba ne a tsaye, yana saka abin fulawa a wuya.
Ta yi guntun murmushi ta ce "Yaya Abba"

"Na'am ƙanwar Abba. Ya na ganki nan lafiya dai ko?"

"Lafiya ƙalau, ba ka fita ba?"

"Yau ba zan fita ba, ba na jin daɗi ne gaba ɗaya, dan da zazzaɓi ma na kwana wallahi"

Cikin tausayawa ta ce "Kash, sannu Allah ya ba ka lafiya. Ka je Asibiti mana"

Abba ya ɗan numfasa ya ce "Na sha magani already, dan haka ba sai na je ba, zo mu je mu zauna ki yi mini hira, na san zazzaɓin zai sauka gaba ɗaya" Dariya ta ɗan yi ta ce "Ai ni ban iya hira ba"

"Ba wani nan, amma ki na yi da Mummy ai, gaskiya mu je sai kin yi mini" Tana dariya ya wuce gaba ta bi bayan sa. Sanyin halin Abba ya fara tasiri a zuciyar Jamila.

*****
Alhaji Fatuhu na zaune, Hajiya Suwaiba ta gama gyara jikinsa, fuskarsa ɗauke da damuwa, ya kalli uwar 'ya'yan nasa ya ce "Haryanzu Fadilan ba ta haihu ba?" Ta taɓe baki ta ce "Tana can ba ta haihun ba tukuna."

"Allah ya sauke ta lafiya" ta yi shiru ba ta amsa ba.

"Yakamata a sallame ni na koma gida haka, na gaji da zaman Asibitin nan gaba ɗaya"

A hasale ta ce "To mu koma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login