Showing 102001 words to 105000 words out of 122205 words

Chapter 35 - BUZU BOOK2 COMPLETE 2

18 Jan 2026

630

dawowata ba za ta yi mata daɗi ba, tun da na tashi daga jinya nake tunanin yadda zan ƙuntata mata na ƙuntata maka.
Ya ɗagowa Ƙaisar wata kwalba, da wani farin haske yana yawo a cikin ruwan da ke cikin kwalbar.
"Ka ga wannan, tunaninsa ne a ciki na duk wani abu da ya shafe ta na rufe shi ba zai taɓa tuna ta ba har abada. Sai dai ta dauwwama gararamba babu makoma. Na ga ka yi wa ɗanta riga-kafi, dan ka hana ni cutar da shi, sai dai ka riga ka makar...
Ƙaisar ya ce "Kai ne ka makara, dan cutarwar da ka yi masa a ciki ma bai yi tasiri ba. Kar ka manta Bil'adama ce. Kar ka manta aiki aka baka ka shafe wancan tunanin nasa, ba ka taɓa tunanin zai tuna waye shi ba, sai ga shi yanzu ya tuna waye shi, dan haka wannan ma baka da tabbacin zai manta rayuwarsu har abada"
Giyaz ya ce "Za ka gani, ka zuba ido zaka ce na gaya maka, duk wata hanya da zan bi na tsohe farincikin yarinyar nan na ƙuntata mata sai na yi"

"Kana tunanin akwai sauran wahalar da ta rage wadda ba ta sha ba a baya? Haryanzu ba ka san suwaye biladama ba, waɗanda ka ke ta'amalli da su miyagun cikinsu ne, hatsabibancinsu kawai ka ke gani. Amma wannan karon ne za mu yi fito na fito na gasken gaske tsakanin ni da kai a kan yarinyar nan. Kar ka manta ka fi ni shekaru da daɗewa a duniya, hasali ma kai ka haife ni, amma ni marubuci ne, kuma manazarci sannan masanin magunguna kar ka ƙetare iyaka, zan iya baka mamaki."

Giyaz ya sake kecewa da dariya ya ce "Gaskiya ne marubuci, kuma masanin magani, ka buɗe wannan kwalbar idan ka isa ya tuna waye shi saboda ka taimaki uwar gijiyar ka, ka faranta mata.

Ƙaisar ya ce "Kai ka yi imani da cewa ka rufe tunaninsa a kwalba, amma kai zan cewa ka zuba ido ka ga ikon Allah"

Giyaz ya ce "Shikenan ina zuba ido" daga haka ya ɓace ɓat daga libraryn.

Har bayan azahar Imam yana tare da Asal, sai dai da aka kawo abincin rana, ba Nana ce ta kawo ba, Asal ta yi ta bala'i a kan kar wanda ta sake gani a sashen, idan ba a nemi izini ba ko kuma idan Nana ce ta kawo ba.

Ta kira Imam da nufin ya ci abincin rana, sai dai ya yi loma biyu ya  kalli Asal ya yi shiru, ya tsiyayo shayi daga cikin haɗaɗiyar butar shayin, ya kai bakinsa, ya ɗan sha kaɗan ya ajiye, ya ɗauki robar madara ya buɗe yana sha.

"Amour" ta furta a shagwaɓe ya ɗaga idanunsa ya kalle ta.

"Ba ka ci abincin ba fa"

Ya girgiza kai ya ce "Ba irin na jiya ba ne"

"To wai meye a cikin na jiyan ne da ya sanya shi daban?"

Ya girgiza kai ya ce "Nima ban sani ba, kawai dai wannan ɗin ban ji ɗanɗanonsa ba, kin san haryanzu jikin nawa sai a hankali, ba na cin abinci sai da na dawo ɗin nan"

"Kuku fa na samo maka mussaman daga Nigeria, ta iya girki ita ta yi maka na jiyan ma, sai dai muguwar kidahuma ce, kuma ba ta da kirki amma ina da tabbacin ba za ta cutar da mu ba, a can gidan cin abinci na Maraɗi na ɗaukko ta mussaman saboda kai" Ya jinjina mata kai tare da yi mata alamar jinjina.
Sai dai a baɗini cikin ƙwaƙwalwarsa, Nigeria da ta ambata sai da tsigar jikinsa ta tashi, gabansa kuma ya faɗi. Duk dabarun da Asal yakamata ta yi ta saka ya ci abincin nan ya ƙo ci, ya sha madarar raƙumi ya ce ta ishe shi ba sai ya ci abincin ba.
Asal ta ɗanɗana Abincin, sai dai ba ta ji wani rashin ɗanɗano ba, abincin ya yi daɗi amma shi ya ce babu ɗanɗano.

Da daddare Asal ta tafi ta yi wanka, ta je ta samu Nana, idan ba ta yi girkin daren ba, za ta gwada mata mene ne matsayinta a gidan.
Sai dai ɓangaren Nana, tun da ta ji su Ramata duk sun ruɗe, wai an yi girki Imam ya ƙi ci, Asal sai bala'i take yi, kuma ta ce kar su sake dafa wani abu a kai masa muddin ba Nana ba ce ba.

Yana zaune yana kallon labarai, shikaɗai a falon ya ji yanayinsa ya fara canzawa. Ya yi shiru yana tunanin me yake shirin faruwa da shi ne haka.

Ta turo ƙofar ɗakin ta shigo da sallama, tana shigowa idanunsa suka haɗe lokaci guda. A zahiri ya ga shocking ɗin da jikin Nana ya yi, dan sai da farantin hannunta ya yi rawa. Sai dai shi ma na sa jikin ya yi, amma da sauri ta sunkuyar da kanta. Gabanta ya yi mummunan faɗuwa bayan ganin Giyaz da ta yi a tsaye a gefen Sayyid yana kallon ta yana dariya.

Ya ƙura mata ido yana son gane wani abu da shi kansa bai san mene ne ba.
"Ita ce 'yar Nigeria da Asal ta samo?" Ya tambayi kansa a zuciyarsa.
Zaucewa ya kusa yi, bayan da Nana ta ƙaraso daf da shi ta ajiye farantin, ya ji ƙamshin turaren sa na tashi a jikinta.
Ko da Nana ta ɗago ta saci kallonsa, ta gan shi a nutse yana kallon talabijin ɗin sa yana kaɗa ƙafafuwansa, kamar ma bai san ɗan Adam ya wanzu a gurin ba.

Tuni hawaye ya cika mata ido, ganin mutumin da ta yi rayuwa mai cike da so da ƙauna tare da shi, abokin wasanta abokin hirarta, ya zame mata wani na daban a yanzu. Ba ta kai ƙofa ba Asal ta ƙwala mata kira.
Ta yi maza ta goge hawayenta ta juyo.

Wani abu ya caki zuciyar Nana, ganin Asal da wata 'yar riga a da guntun wando, babu kunya ko makamancin ganin idon Nana ta ce "Zo zan gabatar wa da amour ke"

Ta zauna a kusa da shi tamkar za ta shige cikinsa,  ta ce "Imam, ga wadda nake gaya maka, kukun da na samo maka 'yar Nigeria"

Sayyid ya yi wa Asal wani kallo yana ɗan lumshe ido, Nana tamkar ta zunduma ihu, sassaucin da ta samu ɗaya shi ne ganin ƙirjin Asal  babu wani abin kirki na jan hankali, duk da yadda ta taƙarƙare tana banƙarewa. Guntun tsaki ya kusa ƙwacewa Nana.

A hankali cikin magana daki-daki ya ce "Babu masu girki a Niger, har sai an tsallaka Nigeria?"

"Eh mana, duk dan saboda na burgeka ne" ta yi maganar cikin shagwaɓa tana shafa sajensa.

"Idan ba ki burgenin ba fa?"

"Haba Imam, me yasa haka dan Allah?"

"Na ji, amma idan ta girka a samu mai kawowa ba na son ta din ga shigo mini nan"

Nana ta kalle shi, zuciyarta ta tsananta bugawa.

"Gaskiya Imam ba na son barorin nan su din ga shigowa sashenka, mugwayen munafukai ne duk nan yadda da su ba,  ba kuma zai yiwu maza su din ga shigo mini"

Ya buɗe baki zai yi magana, Nana ta tsare shi da ido.
Asal ta kalle ta ta ce "Je ki kawai sai da safe, rigima yake ji" Nana gani take kamar da gayya Asal take wannan abubuwan.
Ba ta san lokacin da ta furta "Shegiya" ba a hankali.

Bayan fitar ta, Asal ta ce "Imam me yasa baka son ta din ga shigowa ne?"

Ya lumshe idanunsa ya buɗe ya ce "Tsoro take bani, idan na ganta gabana faɗuwa yake yi."

A zaton Asal, Nanan muni ta yi masa, shi yasa baya ƙaunar ganinta, dan haka wani irin farinciki ya kama ta, ta ci gaba da lallaɓa shi a kan ya yi haƙuri Nana ta din ga shigowa sashen tana kawo masa abincin.
Shiru ya yi mata ganin ba ta fahimci mai yake nufi ba, dan da suka yi ido huɗu da Nanan gani ya yi tamkar ta na yi masa kallon tuhuma, shi da bai taɓa ganinta ba, da zai iya zai so ya samu dama ya tambaye ta, ya ji ko laifi ya yi mata. Ko kuma ma ba mutum ba ce ba, da yake jin jikinsa ya canza a duk lokacin da ya ganta.
Sai dai ya ci Abincin da ta kawo, da daddaren.

Nana kuwa rabi da kwata kwanan tsaye ta yi, tayi kukan har ta gaji. Ita yanzu kawai ta zuba wa sarautar Allah ido.
Furucin Sayyid ya rusa duk wani ƙwarin gwiwa da take da shi.

Da safe kuwa da ta yi girkin,  da wuri ta kai cikin ikon Allah, ba kowa a falon.
Kusan awa ɗaya da rabi da kai Abincin aka aiko kiran Nana, ta san za a rina, saboda abin da ta aikata, ta san dole a neme ta.

Kanta tsaye ta shiga falon Imam, ta tarar da fuskarsa jawur hatta idonsa ma ya yi ja.
Asal cikin bala'i ta hau Nana da faɗa.
"Kashe mini miji za ki yi? Na ɗaukko ki ina tunanin za ki yi abin arziki, amma ki yi yinƙurin kashe shi, ban gaya miki sharaɗin wani abu ya samu mijina a dalilin abincinki ba?"



AREWABOOKS

Nana ta zuba wa Asal ido, sannan ta kalle shi ta mayar da idonta ga Asal ta ce "To ai ni ba ki gaya mini me na yi ba"

"A kan me za ki cika yaji a cikin abinci ki cika tafarnuwa? Bayan ba ya son abinci mai yaji da yawa"

"Ki daina yi mini faɗa, tun da ba ki gaya mini baya cin abinci mai yaji ba, kuskure ne bai kamata ki yi mini faɗa ba dan yau ɗaya na yi kuskure ba, amma bari na ɗanɗana Abincin na ji, sai na ga me zan gyara a gaba"
Ta nufe shi gadan-gadan ta kalli fuskarsa, yadda ta koma sak lokacin suna tare, tana ba shi abinci mai yaji, ba zai yi magana ba sai dai ta gani a fuskarsa.
Ta durƙusa ta ɗauki cokalin da ya ci abinci da shi, ta ɗiba ta kai bakinta, ta ɗago suka yi ido huɗu da shi, ya sunkuyar da kansa da sauri.

Ta risunar da kai ta ce "Tuba nake Shugaba, na yi kuskure in sha Allah zan kiyaye hakan ba zan sake ba. Ba a gaya mini ba ka cin yaji da yawa ba ne, amma zan kiyaye"
Ya sake ɗaga ido suka yi ido huɗu. Ya rintse idanunsa yana tunanin wace ce wannan? Meye haɗinsa da ita jikinsa yake rikicewa a duk lokacin da ya ganta? Sai dai duk da wannan tambayoyin da yake da su, kalmar shugaba da ta kira shi da ita, ta din ga yawo a cikin kansa.

Nana ta miƙe tsaye ta kalli Asal da tsaya tamkar ta fashe, ta ce "Dan Allah ku yi haƙuri zan sake kiyayewa, ba zan sake maimaita kuskuren da na yi ba".

Kawai Asal ta janyo Nana, cikin mamaki take kallon Asal. "Nana ina ki ka samu wannan turaren?"

Cikin rashin fahimta Nana ta ce "Wane turaren?"

"Wanda yake tashi a jikinki, Imam ba ka ji ba?"
Shi dai ya yi shiru bai ce komai ba.
Nana ta ɗage hijjabin jikinta, doguwar rigar da aka ba ta ta bayyana a jikinta da tamkar sai da aka aunata aka ba ta ta ce "Rigar da aka ba ni ce take ƙamshin, nima a haka aka bani ita"

Ta tsaya tana yi wa Nana kallon tuhuma da rashin gamsuwa da abin da ta faɗa, sannan babban abin da ya ƙara ɗaure mata kai, yadda Nanan yau take ɗauke da ƙwarin gwiwa yau.

"Cherie, ki sallame ta kawai ya wuce"

Asal ta saki Nana tana bin ta da kallo.

Ta ce "Na tafi da Abincin na dafo wani ne?"

Asal za ta yi magana ya ce "A'a"

Nana ta ɗauki farantin Abincin nata ta yi waje tana murmushin nasara, dan ta fuskanci ta fara dagula wa Asal lissafi.

*****

"Ba wai-wai nake ki ji ba, gaskiya ne Hammad ya dawo Agadez kuma cikin hayyacinsa ba hauka ba, ya aka yi haka ta faru, kuma har Sultan yana iƙirarin ya yi jinya ne a faransa, yanzu ya warke zai ci gaba da gudanar da ayyukan sa, yaya aka yi aka haihu a ragaya?"

"Waye ya ce ya warke ɗin ne? Babu waraka a tattare da Imam Hammad"

"Amma kai ka ce zai haukace ya bar ƙasar nan baki ɗaya, amma ya dawo cikin ƙoshin lafiya, an ce ma wai jinya ya yi a faransa"

"Imam Hammad bai warke ba, kuma ba jinya ya yi a faransa ba, ya bar ƙasar nan ya yi nisa ya je ya yi rayuwar ƙasƙanci ba tare da tuna waye shi ba ma. Sai dai an samu mushkila inda ya tafi ɗin, wanda a can nake tunanin an ɓata mana fiye da rabin aikin ma, akwai dai yadda aka yi aka gano inda yake, amma tabbas ya yi nisa da gida ba tare da sanin waye shi ba. Amma warkewa kam bai warke ba, an samu matsala ne wani ya shiga cikin aikin ya ɓata wani abu , amma wannan ce gaɓar da ta fi cancanta mu sake hargitsa shi, za a ƙara ƙaimi a kan aikin, komai zai tafi yadda yakamata, a ƙaryata Sultan ya kunyata a idon duniya, a lokacin da ɗan nasa abin ƙaunarsa zai yi hauka tuburan duniya ta sani"

"To shikenan, ina nan ina zuba ido, ina kuma jiran ji daga gare ka, da kuma abin da zai faru."

*****
Nana ta girka Abincin rana, ta shirya shi a kan tray, ta je ta ajiye a falon Imam.
Ta ja ta tsaya ta ƙi tafiya.
Ta daɗe a tsaye, kafin su fito tare da Asal. Ganinsu taren ba ƙaramin dukan Nana ya yi ba, amma ta danne ta koma gefe ta sunkuyar da kai.

Ja ya yi ya tsaya, saboda yana kusanto Nana, yana jin tamkar zuciyarsa za ta tsaga ƙirjinsa ta fito, ya din ga jin tamkar zai fita hayyacinsa.

Asal ta kalle shi ta ce "Yaya dai?" Ya ɗaga kai ya kalli inda Nana take, kawai ya juya ya koma ɗaki.

Ta ƙaraso gaban Nana ta ce "Ke ya aka yi ne? Ba cewa na yi miki, ki din ga ajiye abincin ki tafi ba?"

Nana ta haɗiye wani abu mai ɗaci ta ce "Ki yi haƙuri, dama wata alfarma zan nema na a gurinki"

"Ta me?"

"Kin ce dole na kula da abin da mijinki zai din ga ci na yi taka tsantsan, to kuma gurin girkin yana can waje, duk da idan ina girki tsayawa nake yi a gurin girkin, amma ina jin tsoron kar wani ya shiga ya yi wani abu na ba dai-dai ba a yi zaton ko nice, shi ne na ce ko za a yi wa ɗakin girki mukulli a bani?"

Asal ta ɗan yi shiru, sannan ta ce "Kuma kin yi magana mai kyau, zan san abin yi in sha Allah, za ki iya tafiya" Bayan Nana ta fita, ta koma da bayata shiga ɗakin, ta tarar da shi a kan gado ya takure jikinsa ya yi shiru, jin motsinta ya sanya ya waiwayo.
"Imam, meyafaru ne wai?"

"Na ce miki yarinyar nan ta daina shigowa, bana jin daɗin jikina idan na ganta, ina kyautata zaton ma ba mutum ba ce ba"

Asal ta tuntsure da dariya ta ce "Mutum ce fa, dan dai kawai ba ka son hayaniya ne, kuma ba hankali ta cika ba. Amma ai Abincinta yana yi maka daɗi, shi ka ke ci fa, kuma idan ba ita ta yi ba baka ci"

Ya numfasa ya ce "Ni dai kar ki ɗaukko abin da zai zame mana matsala"
Ta karairaye murya ta ce "Imam ba zan taɓa kawo abin da zai cutar da mu ba, ka kwantar da hankalinka za ka daina ji, ka san ita ba ƙabilarmu ba ce, ba kuma 'yar ƙasarmu ba ce ba, shi yasa ka ke jin haka, amma ka kwantar da hankalinka"

Ya jinjina mata kai kawai bai ce komai ba, ya san ba za ta taɓa fuskantar halin da yake shiga ba.

*****
Yusra da Sagir su na zaune a falonsa, yana ta kallon agogon hannunsa, Shukura yake ta jira ta fito yana so ya haɗa su, ya yi musu nasiha, amma kusan awa guda da yi mata magana, amma shiru ba ta fito ba.
Ransa ya ɓaci da irin wannan wulaƙanci da take ta yi, ya rarrashe ta, ya ba ta haƙuri amma ta ƙi sauraren sa, sai wulaƙanci take yi masa yadda ranta ya ga dama. Ga shi yana tausayinta saboda tsohon ciki da yake jikinta, ga hawan jini, amma ko a jikinta tsakaninta da shi gaisuwa ce kawai, bayan wannan idan zai shekara yana magana, ba za ta kula shi ba, sai dai ya gaji ya tashi.
Yanzun ma har ya fusata zai je ya same ta, sai ga shi ta fito, fuskar nan babu annuri da alama ma fita za ta yi.
Ta zo ta nemi guri ta zauna, ta yi shiru ba ta ce komai ba.
Yusra ma ta kalle ta ta basar, ba ta kula ta ba.

"Mu na nan mu na ta jiran ki tun ɗazu, amma baki fito ba"

Fuska a ɗan tsuke ta ce "Shiryawa na tsaya yi ne"

"Ina za ki je ne?"

Ta kwaɓe fuska ta ce "Awo" Ta ba shi amsa a taƙaice.

Ya numfasa dan ba ya son biye mata, dan ya ga a kusa take, ko alamar ganin Yusra ba ta yi ba.

"Amm dama ba wani dalili ya sanya na tara ku a nan gaba ɗaya ba, ina son in gabatar muku da juna, sannan kuma na yi muku nasiha a kan haɗin kai da zaman lafiya.
Shukura kamar yadda ki ka sani tun da farko, kafin na aure ki, na auri Yusra sai dai ƙaddara ta gifta mun rabu. Ke ma kuma Yusra na sanar da ke bayan rabuwarmu na auri Shukura.
Dan haka ina mai roƙonku a kan zaman lafiya da haƙuri da juna, domin na samu nutsuwa na yi muku adalci.
Yusra ga Shukura, Shukura ga 'yar uwakki Yusra"
Da ƙyar Yusra ta ce "Sannu"

Haushi ya kama Shukura, wai sanni sai ka ce wadda take ciwo, da ya san zai dawo da Yusra dan me zai sake ta ya aure ta.

Sagir ya ce "Shukura tana yi miki magana fa"

Shukura ta ce "Hankalina na yana kan tafiyata Asibiti ne, ba na jin daɗin jikina. Amarya ina yi miki barka da zuwa, Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya" Ta ƙarasa maganar tare da miƙewa da ƙyar.

"Shukura ki tsaya mana mu gama sai ki tafi"

Cikin fushi ta ce "Na ce maka fa bani da lafiya, kwana na yi ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login