Showing 96001 words to 99000 words out of 122205 words

Chapter 33 - BUZU BOOK2 COMPLETE 2

18 Jan 2026

632

buɗe ta. Kawai ta ce "Shikenan" ta fice ta bar ɗakin.

Can gurin kuma Nana tara su aka yi, su shida. "Na san za ku yi mamakin dalilin da ya sanya aka kawo ku nan, to zaɓo ku aka yi saboda an yarda da amanarku, ana daf da yin taro da Sultan da kuma dukkanin Imams na gidan nan. Dan haka ku aka zaɓo za ku yi girki na musamman. Amma ku sani kamar yadda wasu sani wasu ba su sani ba, muddin aka samu wata matsala ko ƙware wani ya yi, a sanadin abincin da ku ka dafa, to ku tabattar da rayuwarku za ku biya. Dole ku yi taka tsantsan ku kula." Matar ta yi maganar daki-daki.

"In sha Allah" suka amsa mata.

Ta ce su bi bayanta, suka je wani ƙaton guri, ɗauke da nau'oin kayan masarufi kala-kala. Ta yi musu bayanin da su ne za su yi amfani su yi girkin, sannan ya zama dole su sanya wa bakinsu sakata su yi aiki cikin amana, kuma kada wanda ya san su aka zaɓa da za su yi wannan girki. Nan ma suka amsa, ita dai Nana sai kallo da ido, dan abubuwan sun daina ba ta mamaki, wannan maganar ce ta sanya aka taso ta a daren nan, sai ka ce wanda za su girkawa wasu waliyyai abinci.

Ko da aka mayar da su Nana gida, ta sha mamakin ganin kayanta a hargitse a cikin ɗaki. Da mamaki ta ƙarasa kan kayan nata, ta ɗaɗɗaga.
Cikin takaici Nana ta tashi ta fita, sai dai kowa ya tafi makwancinsa ya kwanta. Kawai ta ji taku a bayanta. Ta waiwaya ta ga Asal na fitowa.

"Har kun dawo kenan?"

"Eh, sai dai na shiga ɗakina na tarar da an caje mini kayana an zubar da su a ƙasa, ban sani ba ko kina da masaniya a kan haka?"

Asal ta ce "Me yasa ki ka zarge ni?"

"Saboda na ga ba a gudanar da komai a gidan nan sai da izninki"

Asal ta yi murmushi ta ce "Haka ne, kina da kaifin ƙwaƙwalwa kamar yadda na yi tsammani, ni na saka aka caje kayanki saboda na san da wa nake zaune"

"Me yasa ba ki tambaye ni abin da ki ke buƙatar sani ba, za a caje mini kaya"

"Saboda a ƙarƙashina ki ke, a gidana ki ke zaune dole na sani idan da wani abu da ki ke tattare da shi na cutarwa"

Nana ta ce "Kin yi kuskure, dan ina zaune a ƙarƙshinki, ina da personal life ɗina, da 'yancin adana abin da yake sirrina, bai halatta ki bincikar mini kaya a bayan idona ba. Yaushe na san ki, da zan ƙulla wani abu da zan cutar da ke? Kina gudun hakan ki jawo ni ki ka kawo ni?"

"Yi ƙasa da muryarki, kar ki kuskura ki ɗaga mini murya, kin san matsayina? Za ki iya janyo wa kan ki gagarumar matsala muddin ki ka ci gaba da yi mini magana ba ladabi"

"Babu ruwana da matsayinki, da koma me za ki yi mini, kar ki sake shigar mini ɗaki ki taɓa mini kaya, idan kuma ki ka ci gaba za ki iya binciko abin da zai hana ki sukuni, idan kin ji ba ki yarda da ni ba, ki sallame ni na koma inda na fito, ba zai yiwu na zauna da ke kina zargina kuma kina cin dunduniyata ba."

Asal ta bi Nana da kallon mamaki, amma ta danne mamakinta ta haɗiye fushinta, ta ce "Gaskiya ne, kin yarda da kan ki har haka kenan? Shikenan amma idan na ga akasin abin da ya fito daga bakinki, za ki sha mamakin abin da zai faru"

Nana ta yi mata banza, ta koma ɗakin nata, ta gyara kayanta tsaf.
Ta kulle ɗakin ta koma ta ɗaga katifar ɗakin, ta ɗaukko wata jaka, a cikin jakar ta zuba duk tarkacen kayan Sayyid. Ajiyar zuciya ta ts yi, da tayi wannan dabarar ta ɓoye su. Haka kurum take jin kayan na buƙatar sirri.
Ta nemi guri ta kwanta tana sauke numfashi a hankali, tana tunanin yadda rayuwa ke ta jujjuyata.

*****

Shukura na zaune a ɗakinta tamkar zuciyarta za ta yi bindiga ta fito, Sagir ya buɗe ƙofa ya shigo ɗakin. Kallo ɗaya ta yi masa ta sunkuyar da kai. Tuni t yi shirin kwanciya baccinta, sai ƙamshin turare take zubawa.
Ya sha manyan kayansa, hannunsa riƙe da baƙaƙen ledoji. Ya zo ya zauna a kusa da ita, tamkar ta kifa masa mari haka take ji.

"Wai har kin yi shirin kwanciya? Na zata zaku gaisa tukuna sai ki kwanta" Mugun kallon da ta yi masa ya sanya shi haɗiye maganar da ya yi niyyar yi.
"Ga wannan naki ne" Ya yi maganar yana ajiye mata ledojin hannunsa.
Ba ta kalli kayan ba, kuma ba ta motsa ba.

Ya matsa kusa da ita, ya riƙo hannunta, ta fizge hannunta ta haye kan gadon ta kwanta.
Bai ji haushin abin da ta yi masa ba ko kaɗan, ya san idan ba ta son sa ba za ta yi kishinsa ba, sai dai ita ma Yusra tana buƙatarsa tun da tun farko bai kamata ya sake ta saboda larurarta ba.
Ya tashi ya kashe mata fitila, har zai fita ya koma gaban gadon, ya durƙusa daidai fuskarta ya ce "Ki yi mini afuwa Shukura, ban yi haka domin na cutar da ke ba, ko na muzguna miki, dan Allah ki kwantar da hankalinki saboda lafiyarki da abin da yake cikinki" Daga haka ya tashi ya fice. Sai da ya fita sannan ta ba wa hawayen da suka maƙale a ƙirjinta damar zirarowa, zuciyarta ta din ga yi mata ƙuna, tamkar ta tashi ta bar gidan.

Duk da ya fita da damuwar halin da Shukura take ciki, amma bayan wani ɗan lokaci tuni ya manta, suka ci suka ƙoshi da shi da Yusra.
Bayan sun gabatar da salla, sun yi addu'oi, suka yi zamansu kawai su na hira.
Sai gurin ɗaya saura sannan suka tashi suka kwanta.
Yadda Sagir yake murna da kasancewa da Yusra, ko aurensu na fari bai yi haka ba, tuni wani nannauyan bacci ya yi awon gaba da su, daga shi har ita.
Shukura kuwa yadda ta ga rana haka ta ga dare, ga wani irin zafi da ya addabe ta duk da na'urar sanyaya ɗaki da ke cikin ɗakin.

Washegari sai ƙarfe sha ɗaya na safe ya shiga ɗakin Shukura.
Idonta kawai ya kalla ya ga alamun rashin bacci a tattare da idanunta, sun yi jawur sun kumbura.

"Oum Haidar" ya kira sunanta, yana zama a kan gadon, tana shan tea.

"Ina kwana" ta faɗa a taƙaice.

Idanunsa ya sauka a kan ledar da ya kawo mata, babu alamar ko taɓa ledar ta yi.

"Shukura me yake damunki ne haka? Na kawo abu ko taɓawa ba ki yi ba, kin yi bacci makuwa"

"Sagir, dan Allah ka tashi ka bani guri, ni bana buƙatarka a kusa da ni, kaɗaici nake so"

"Ni ki ke cewa na fita na baki guri?" Ya yi maganar yana nuna kansa.

Ƙoƙarin mayar da hawayen da ke shirin zubo mata take yi, amma abu ya gagara kawai ya fara zubowa ba tare da ta shirya hakan ba.

Jikinsa ya yi sanyi, ganin yadda take kuka sosai da sosai.

Cikin kwantar da murya, yake ƙoƙarin rarrashinta, amma ta tashi ta shige banɗaki ta bar shi a gurin.

Ya yi shiru ya rasa abin da yake yi masa daɗi, shi babbar damuwarsa ma cikin da take ɗauke da shi, ga matsalarta ta hawan jini.

*****

Tamkar bayi haka su Nana suke aiki, kullum za a ɗaukkosu daga wancan gidan da Asal take, a kawo su nan su wuni su na aiki. Har mamaki take yi wannan mutanen su kuwa har su nawa ne, dan kamar har da almubazzaranci a cikin lamarin.
Sai dai kowa cikin kaffa-kaffa yake aikin tare da fatan kar wani abu ya biyo baya da za a kama su da laifi.

Kwana na uku, wanda ranar suka dafa normal Abinci, sauran kwanakin kayan snacks ne suka din ga yi. Duk cikin su Nana ce 'yar Nigeria, sauran duk 'yan Nijar ne, sai dai galibinsu baƙaƙen buzaye ne.

Sai da suka kammala aikin, aka ba su wasu kaya fararen dogwayen riguna, da rigar girki, aka saka su kai Abincin wani ɗaki.
Katafaren ɗakina da dogon tebur, an gyara shi sai tashin ƙamshi yake yi. Sai dai gabanta ya yi mummunan faɗuwa da jin irin ƙamshin da yake tashi a ɗakin.
Take jikinta ya hau rawa, har ta nemi ta kifar da abin da ta ɗaukko.
Ta ɗaga kanta a hankali ta kalli jerin manyan frames ɗin da ke ɗakin, sai dai mutanen jikin hotunan, dukkaninsu fuskokinsu a rufe yake, ba ta iya gane kowa daga cikin su ba.

"Ke Nana ki kai mana kin ja kin tsaya" Nana ta jinjina kai jiki a sanyaye ta ƙarasa gaban teburin. Ta ajiye kayan, ta ɗaga kai ta kalli yadda ginin ɗakin yake da matuƙar tsayi.
Jiki a sanyaye ta ci gaba da kai komo, su na shirya abincin.
Bayan sun shaƙe teburin da uban kayan Abinci, aka ba su umarnin su tsaya kar wanda ya fita.
Su na tsaye Nana ta kalli agogon ɗakin, ƙarfe goma na dare.
Wani ƙaton mutum ya shigo, ya kalli gurin da yadda aka shirya teburin, ya kalli su Nana ya ce "Waɗanan ne suka yi girkin?"

Balaraba wadda ita ce ta jagoranci su Nana gurin girke-girken ta risuna ta ce "Eh su ne ranka ya daɗe"

"Wace ce wannan? Na ga kamar ba tamu ba ce" Ya yi maganar yana nuna Nana, da gaba ɗaya rabin hankalinta ba ya jikinta.

Balaraba ta ce "Gimbiya Asal ce ta zaɓo ta, ta saka ta a cikin masu girkin"

Ya yi shiru yana kallon Nana, daga bisani ya jinjina kai ya kalli Balaraba ya ce "Ki je, su su tsaya" Ta jinjina kai ta fice.
Wata ƙofa aka buɗe, wani matashi ya shigo fuskarsa ɗauke da murmushi, gaban Nana ya yi mummunar faɗuwa, dogo ne sanye da farar jallabiya ya ɗaura hirami a kansa, ba dan ta yi wa Sayyid kyakykywan sani ba, za ta iya cewa shi ne. Ƙirjinta ya tsananta bugawa, sai dai kafin ta daidaita nutsuwarta, wani ma ya biyo bayansa, shi ma dai kamarsa ɗaya da Sayyid ɗin.
Tunani ta fara yi ko Giyaz da Ƙaisar ne suka fara yi mata gizo suke yi mata wasa da tunani.
Ɗaya bayan ɗaya suka din ga shigowa, sai da ta ƙirga mutum biyar cif, biyu kamar su ɗaya sak, sauran ukun kuma su na kama amma ba sak da Sayyid ba. Duk suka jeru a kan kujerun teburin nan. Sai dai babbar kujera babu kowa a kai, kujerun gefe da gefen kujerar ma babu kowa a kai.

Ɗaya daga cikin su ya ce "Ko waye zai hau wannan kujerar?" Ya yi maganar yana nuna ɗaya daga kujerun da babu kowa a kai.

"Wannan karon dai za mu ji me Sultan zai ce mana a kan maganar"

"Nima dai abin da nake son ji kenan, magana ta gama cika gari ba a san inda yake ba, ana ma tunanin ko ya mutu suke ɓoyewa"

Nana ji ta yi ana busar sarewa a ƙofar bayan su, gaba ɗaya suka ja gefe domin bayar da hanya.

Wani dattijo ne fari sol, mai dogon gemu ya shigo jallabiyarsa baƙa, ya lulluɓe kansa da hiraminsa.
Gaba ɗaya ta ga abokan aikinta sun rikice, duk sun sunkuyar da kansu ƙasa, Nana kuma ta yi masa ƙuri da ido. Sai dai ba shi take kallo ba, ji take tamkar numfashinta ya ɗauke, kamar ba a cikin duniya take ba, duniyoyin da Ƙaisar ya saba kaita ne ya caza mata kai, banda haka wani irin mummunan gizo ne wannan?.
Gaba ɗaya matasan suka miƙe tsaye, cikin matsanancin mamaki suna kallon na bayan dattijon.
Tamkar yana tausayin ƙasar haka yake taka ta, yana ɗan yin rangaji kaɗan, sassanyan ƙamshin turaren sa da ko a mafarki ta ji shi tana tantancewa ya karaɗe ilahirin gurin, fiye da ƙamshin turarukan da ke tashi a gurin.
Ta kusa da ita ce ta ja hannunta da ƙarfi, saboda yadda ta tsare shi da idanunta ko ƙiftawa ba ta yi.
Ya zo zai gifta ta, amma ko gurin da suke bai kalla ba, ɗaya bayan ɗaya suka din ga rungume shi, cike da murnar da wasu har zuci, wasu kuma iya ta fuska ce. Ta ga ya zauna a kan kujerar da ake tababar wa zai zauna a kai kafin ya shigo.
Abdou ya ce "Kun yi mamaki ko? Ba ku yi zaton ganinsa ba?"

Ɗaya daga cikin su ya ce "Gaskiya ne"

Sultan ya yi murmushi ya ce "Kamar dai yadda na gaya muku a baya, Imam Hammad yana Faransa neman lafiya, bayan tsawon wannan lokacin, yau ya kasance tare da mu a liyafarmu ta ƙarshen shekara, dama wannan ne bazatar da na ce zan yi muku"
Nana ta kalli hotunan nan, sai ta yanzu hotunan babu rawani, kowa hoton fuskarsa ce. Ta tsayar da idonta a kan hotonsa da aka rubuta Imam Hammad Jalal Agadez. A take ta tuna da sunan gidan cin abinci da ta yi wa su Al Hussain aiki. H.J Agadez.
Sunan rukunin gidajen da ta fara zama da Asal shi ma sunan da ke jikin symbol ɗin unguwar kenan. H.J Agadez.
Duk surutun da ake yi, da murnar ya dawo, yana ƙame a kan kujera, fuskarsa babu yabo babu fallasa.
Sai daga bisani ya saka hannunsa ɗaya a kan ƙirjinsa ya risunar da kansa ya ce musu "Merci(Na gode)
Duk da a hankali ya furta, amma ko cikin murya dubu Nana ba za ta gaza tantance ta Sayyid ba.

Abduou ya kalli su Nana, ya kalli mutumin ɗazu da yake tambayar wace ce "Guda biyu daga cikin su ta zo ta ɗanɗana Abincin nan"

Mutumin ya ƙare musu kallo, ya nuna Nana ya nuna wata ya ce su je su ci kafin a ci.
Nana ba ta san a yadda take iya ɗaga ƙafafuwanta ba, saboda ba ta jin su a jikinta, zuciyarta kuwa kamar za ta tarwatse saboda bugun da take yi fiye kima. A hankali ta ƙarasa gaban teburin. Ɗayar ta din ga bubbuɗe Abincin, ta fara ɗanɗanawa.

"Ke kina da gaskiya kuwa? Ki ɗanɗana aka ce?" Abduou ya yi mata maganar cikin tsawa.

Rikicewa ta yi gaba ɗaya, ya ɗaga idonsa ya kalli inda jikinta yake rawa, suka yi ido huɗu, ya kawar da kansa yana mamakin yadda take a ruɗe.

Ta ɗebo shinkafa a cokali, amma hannunta karkarwa kawai yake yi.
Sultan ya ce mata "Kina lafiya kuwa?" Ta jinjina masa kai alamar eh.

Sultan ya ce "Na fuskanci a tsorace take ne kawai, a kaita ta je ta huta, wataƙila mun yi mata kwarjini ne"

Aka saka Nana a gaba aka fitar da ita daga gurin.

Fitarsu ke da wuya, jikin Nana ya din ga wata irin kyarma, haƙoranta na haɗuwa da juna, wani irin jiri ya din ga kwasarta.
Balaraba ta nufo su da sauri, ganin Nana na dafa bango.
Ya kalli Balaraba ya ce "Maza ki kaita ta huta, wataƙila ta yi aiki da yawa ne ta gaji, gaba ɗaya ta rikice, a kirawo likita kuma ya duba ta.

*****

A hankali Nana ta yi juyi, ta buɗe idonta ta ganta a ɗakin da take kwana.
Wata irin ajiyar zuciya ta yi, da ta tabbatar da mafarki ta yi ba gaskiya ba ne abin da ya faru.
Hamdala ta yi ta ce "Ni dai na san mafarki ne da ma, dan babu yadda za ayi Sayyid ya ganni ya kasa kula ni, ya nuna kamar bai sanni ba. To wannan idan gaskiya ne ma, ta ina zan fara bayanin ni matarsa ce a yarda da ni? Mutumin da na ji ana batun ya daɗe a faransa yana jinya, anya ma Sayyid ɗina ne? Tun da dai mafarki ne duk da sauƙi.

Sallama aka yi a ɗakin, ta ga Balaraba ta shigo ɗakin. Ta ce "Kin tashi?"

Nana ta yi shiru tana kallonta.

"Ina ga aiki da ki ka sha a kwanakin nan ne, ya sanya ki ka gaji zazzaɓi ya kama ki, Likita ya ce a bari ki huta sosai da sosai. Gimbiya Asal ta ce a baki hutu na kwana uku ki warware kan ki koma bakin aiki."

Nana ta jinjina kai kawai, tana kokawa da ƙwaƙwalwarta, domin ta tabattar gaske ne, ko kuwa dai mafarkin ne? Ta tashi ta yi alwala ta yi salla, sai dai gaba ɗaya jikinta ciwo yake yi mata, ga matsanancin ciwon kai da jiri da take ji, dan haka ta nemi guri ta sake kwanciya.

*****

Jamila ta ɗauki jakarta ɗauke da wannan tarkacen da take kira da tarkacen jaraba, ta fita waje, ta samu ta sayo fetur a 'yar jarka, ta samu guri ta zuba musu fetur ɗin ta kunna musu ashana ta ƙone su.

Ta tashi tana kallon yadda suka din ga ci da wuta, ta bar gurin.
Kai tsaye ta tari abin hawa ta tafi gidan Hajiya Sa'a.
Hajiyar ta yi iya ƙoƙarinta gurin ɓoye jin haushin Jamila da take yi, ta karɓe ta hannu bibbiyu har ta taya ta lissafin kuɗin kasuwancinta da kuma kayan da take da su a ƙasa.
Bayan sun kammala ta ce "Ni kuwa Jamila, yaya batun ƙungiya wa za ki bayar ne?"
Jiki a sanyaye ta ce "Haryanzu ban gama tunani ba ne ba"

"Tsoron dai ki ke ji haryanzun ko?"

"A'a na rage ji"

"To ki yi ki hanzarta ki yi abin da yakamata amma kin tsaya. Ni kalli nawa nan na shirya komai aiwatar wa kawai ya rage mini, sai na je gidan zan yi, na sake bayar da ɗan Fatuhu"

Jamila ta kalli drower da Hajjya Sa'a ta janyo, tana nuna mata 'yar tsanar nan.

Jamila ta ce "To idan ban kai kowa ba, akwai wani abu da zai faru ne?"

Ta ce "Au da kara zube za ki zauna ki ƙi bin umarnin ƙungiya? To idan ba ki kai kowa ba, jininki aljanin zan shanye ki mutu" Cikin Jamila ya yi wata irin ƙara bayan tuna ta ƙona kayan. A tunaninta shikenan ta huta sun rabu.
A ranta ta ce "Wannan wane irin bala'i ne na jefa kaina a ciki, Ubangiji Allah ka kawo mini agaji na rabu da wannan masifar.

*****
Fafur Nana ta ƙi yadda zuciyarta ta amince abin da ya faru gaskiya ne ba mafarki ba, saboda ta riga ta saba da irin wannan cazan kan da Ƙaisar ya kan yi mata wasu lokutan, har ta gaza banbance abin da yake zahiri da kuma mafarki.

Nana suna ɗakin girki su na ta ɗorawa da saukewa, ta kalli shugabar su ta ce "Dan Allah a gidan nan, babu yadda zan yi na samu waya, ina son

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login