Showing 42001 words to 45000 words out of 122205 words

Chapter 15 - BUZU BOOK2 COMPLETE 2

18 Jan 2026

570

yanzu ya ku ka yi da shi?"

"Hmm mu na nan muna ta bugawa, wai sai ta bar gidan nan, ni kuma Nana ba za ta bar gidan nan ba, sai dai mu tafi tare"

A ɗan tsorace Adda ta ce "A'a Maijidda, idan da matsala, a kaita gidan Fati tun da tana da yalwar guri, ko gurin Yakumbo,kar ku samu matsala"

Ta girgiza kai ta ce "Ni na ke son kula da Nana da kaina. A cikin su ban san wanda zai ji ƙan wani ba, dukkaninsu su na buƙatata".

Nana ta farka tana ɗan yin miƙa, ta cewa Maijidda fitsari za ta yi, ta raka Nana banɗaki ta je ta yi fitsari, ta saka ta ta yi alwala ta koma ta kwanta.

Har zuwa yamma Adda na gidan, sai daf da magariba ta tafi, Nana kuma ta wartsake sai ciwon jiki da mararta da ke ɗan murɗawa.

"Nana, ranar Litinin in sha Allah za mu je Asibiti, a fara yi miki awo, kuma zan duba gurin masu magungunan islamic ɗin nan, mu je a duba ki" Nana dai ta yi shiru ba ta ce komai ba.

Da sallar Isha'i, Baban su Walida ya dawo, tun da ya hangi Nana a ɗaki, ya turnuƙe fuska ya kalli Mai Jidda ya ce "Me na ce miki a game da yarinyar nan?"

"Baban Walida, ba a yi wa ɗa mugunta, dan Allah ka yi haƙuri ka bar Nana a gidan nan, ka ga 'yan uwanta ma duk ba su santa ba, ba su saba ba. Kuma ba a san me gobe za ta haifar ba. Wataƙila ita ce mai tallafar rayuwar ƙannen nata nan gaba."

"Ni ba nusari ne kamar ubanta ba, ni zan tallafi rayuwar 'ya'yana. Ba na buƙatar ko sisinta a kan yarana. Ta koma gidan mijinta ko gidan ubanta, idan ba haka ba sai dai ki zaɓa, ko ta bar mini gida, ko kuma auren ki."

Kafin ya rufe bakinsa ta tari numfashinsa ta ce "Na zaɓi 'ya ta, zan tafi tare da Nana, ko a daji ne na rayu da ita na kula da ita. Tun da ba dan wahala da bautarka da ta 'ya'yanka kawai Allah ya yi ni ba. Ba ka da kara Iliyasu. Nan har 'ya na riƙe maka na aurar da ita ban yi mata mugunta ba. Har 'ya'yan 'yan uwanka ka kawo mini na riƙe, ban taɓa muzguna musu ba, na riƙe maka, nawa 'ya'yan ne na banza kenan? Ƙiri-ƙiri ɗan da na durƙusa na haifa ya tsane ni, saboda yana ganin na kawo su Duniya amma ban damu da su ba. Su 'ya'yan da na riƙe maka haifar su na yi? Ko kuma dolena ne su, ni 'yar guda ɗaya ka gaza yi mini kara a kanta? To ka sani duka yau duka gobe shi ke sanya baƙin ba'auzine yin tawaye. Zan zube maka yaranka na ɗauki 'ya ta na tafi da ita, na kula da ita. Ka kwaɗa gidan ka cinye da kai da 'ya'yan naka"

Cikin matsanancin mamaki ya ce "Maijidda, ni ki ke gaya wa wannan maganganun?" Cikin ƙunar rai ta ce "Na faɗa ɗin, shekara nawa na rayu da baƙin cikin rashin ganin 'ya'yana, kullum na motsa zargina ka ke da tsohon mijina. Ƙaddarar haihuwar yaran nan biyu ta sanya ban aure ka da fari ba na fara auren sa, amma a kan dalilinku marasa tushe balle makama kun azabtar da ni da nesan ta ni da yarana. Wallahi wannan karon na zaɓi 'ya ta"

Kamar zubar wuta, haka Nana take jiyo cece kucen su. Dana sanin zuwa gidan ya cika mata zuciya. Tabbas ba za ta so mahaifiyarta ta kashe aurenta, da wannan gayyar 'ya'yan saboda ita kaɗai ba, idan ta bari hakan ya faru ba ta yi musu adalci ba baki ɗaya. Zurfin tunanin da ta tafi, bai bari ta gama jin yadda rigimar ta su ta kaya ba. A cikin daren bayan gari ya yi tsit, ta tashi ta haɗa kan kayanta cif.
Ta laluba jakunkunan yaran na makarantar boko, ta samu biro da takarda ta yi rubutu, ta ninke ta ajiye a kan katifar ta.
Da Asuba, Mama ta zo ta tashe ta, ta yi alawala ta yi sallar Asuba. Ganin yaran na ɗaya ɗakin su na salla, Mama ma tana bedroom ɗinta, tana salla, ya sanya ta lallaɓa ta ɗauki jakarta ta fice daga gidan.
Ta din ga zumbuɗa sauri, tamkar za ta tashi sama, ga faggon kaya. Tafiyar ƙafa ta ci sosai da sosai, har sai da gari ya yi haske, masu abin hawa suka fara fitowa, ta tari wani ta ce ya kai ta tasha. Yana kai ta tasha, ta yi sa'a an yi lodi saura gurin mutum biyu, tare da wata mata suka shiga tasha suka nufi babbar tashar Bauchi.
Daga babbar tashar Bauchi, ta hau wata motar, duk da zuciyarta na raya mata kamar matakin da ta ɗauka ya yi tsauri, wata zuciyar kuma na raya mata shi ne mataki mafi cancanta da za ta ɗauka, mussaman idan ta tuna yanayin yadda ta yi mafarkin Sayyid.
Wayarta ta ciro, ta shiga lambar Ummi, ta rubuta mata saƙo, sai da ta tabattar ya tafi, sannan ta kashe wayar, ta cire layinta daga cikin wayar.

Gari ya ɗan fara haske, Baban su Walida ya fice, a matuƙar zuciye, ya yanke shawarar tafiya ya kai ƙarar ta, tun da dama ya san ya saba samun goyon baya, ba ga taɓa kai ƙararsa ba, amma shi ya kai ta ta, ya fi sau shurin masaƙi.
Su Khadija har sun fara ƙiriniya a tsakar gida, a zuciye kasancewar da takaicin ubansu ta kwana ta daka musu tsawa, ta ce su koma ɗaki, kar su tashi Nana. A zaton ta Nana tana cikin ɗaki tana bacci.

Jamila ce zaune a gidan Ummi, tana jajanta abubuwan da suka faru da Nana, ba tare da ta san ma hakan ya faru ba.

"Wallahi Ummi da an sanar da ni zancen matar nan, da suka ce Nana mayya ce, wallahi da sai na saka an rufe ta, sai na ja shari'a da su har gaban Alƙali, sun san girman sharrin maita kuwa?"

"Hmm ke dai a yi sha'ani, ga shi Nana ta bar gidan, amma an ce Haryanzu tana kwance babu lafiya matar, ni na fi tunanin ko Aljanun Nanan ne suka yi mata wani abin, tun da ta ce Nana take gani. Jamila wayar Nana fa ba ta shiga, ni kaina sai na shafe sati biyu ban yi magana da ita ba, saboda garin babu network. Haka nan za mu tafi kawai."

Ummi ta shirya, da Jamila Abba ta so ya kai su, sai ta yi wani tunani ta fasa, dan ba ta san a yanayin da za su je su tarar da su Nana ba.
Sai dai Ummi ta sha mamaki da suka isa garin, suka tarar da gidan Nana a garƙame.
"Ikon Allah, ita kuwa Nana ina tafi haka? Ko sun je Asibiti ne?"

Jamila ta ce "Asibiti yau Asabar?"

"To maybe emergency suka je, kin san matsalar Zuciya yake fama. Mu ƙarasa gidan Uwani".

Suka zagaya gurin Uwani, ta yi murna sosai da sosai da ganinsu, sai dai ta hau Jamila da faɗan ba sa zuwa sai yanzu, da yake Nana ce a garin.
Ummi ta yi ta bata haƙuri, ta ce sun zo duba Nana ne, sun tarar da gidan a rufe.

"Ohh abin tsiya, ba ma kwa bibiyar halin da take ciki, to Nana tun shekranjiya ta bar Buda, mijinta aka nema aka rasa ko sama ko ƙasa sama da sati biyu, ta ce mini gurin Babarta za ta tafi a Bauchi, babu yadda ban yi da ita mu yi zamanmu da ita a nan, amma fafur ta ce in ƙyale ta, tafiya za ta yi".

Jamila ta ce "Danƙari"

Ummi kuwa "Innalillahi wa Innalillahi raji'un" kawai take maimaitawa.

"Amma me yasa Nana ba ta dawo gida ba, sai ta tafi Bauchi, bayan ta san halin Baba"

"Baban wofi, uban me zai tsinana mata, ko ta je gurin nasa"

Suka gama jimamin da za su yi, suka tashi suka tafi.

Jamila ta ce "Anya Ummi mu gaya wa Baba kuwa?"

Ummi ta ce "Tun da shi ya haife mu, ba dole a gaya masa ba. Wallahi duk cikinmu babu wanda ya sha azabar ds Nana take sha a rayuwarta, da kin ga yadda take shan wahala da mutumin nan, sai kin tausaya mata, gaskiya idan guduwa ya yi ya bar ta, bai yi wa kansa adalci ba."

Suka ci gaba da jajanta lamarin.

Da suka shigo gari, Jamila ta tafi gida, Ummi ma ta tafi nata gidan.

Mama na ganin Jamila ta dawo, ta fara yi mata tambayoyi, amma Jamila ta yi burus, ba ta gaya wa Mama komai ba.

****
Tare da Kawun Mai jidda Iliyasu ya dawo, yana ta faman bambamin ta lalace, abin da ta ga dama shi take aikatawa.
Sai kuma Adda Saude da suka taho tare, dama sai da ta yi tunanin a samu matsala saboda zuwan Nana.

Suka tarar da Maijidda idanunta jawur, fuskarta babu annuri.
Suka zazzauna a falonta, kawunta ya dube ta ya ce "Mai Jidda ban san ki da rashin ji ba, me yake faruwa ne?"

Jiki a sanyaye ta miƙa masa takardar da Nana ta bari a kan shimfiɗarta.

"Wannan ɗin na mene ne?"

"Ku duba" ta yi maganar hawaye na zubo wa daga idonta.

Adda Saude ta karɓa, ta buɗe takardar "Assalamu alaikum, na san lokacin da za ki ga takardata, na riga na yi nisa. Mama ina mai baki haƙuri da matakin da na ɗauka ban sanar da ke ba. Ba zan so a dadlilina nikaɗai ki bar ƙannena ba, dan Allah Mama ki yi haƙuri ki zauna da su. Na tafi neman mijina, a bawa baban su Walida haƙuri, amma kwana biyun nan da muka yi tare, ya fi kowane kwanaki yi mini daɗi a rayuwata na gode sosai Nana Asma'u"

Shiru suka yi bayan da Adda Saude ta gama karanta rubutun, sai sautin kukan Maijidda da yake tashi. Cikin kuka ta ce "Shekara nawa ina yi masa kara, na riƙe nasa 'ya'yan? Amma ni sau ɗaya ya gaza yi mini kara, 'ya'yana sun tsane ni, a kan laifin da ba su suka yi ba, bai yadda su zo inda nake ba, nima kuma ba zan je ba. Idan na yi magana a ce na yi haƙuri, yarinyar nan ga tsohon ciki ina za ta tafi? Mijin da ita kanta ba ta san a ina yake ba" ta ƙarasa maganar tana ƙara rushewa da kuka. Kawu cikin sanyin jiki ya ce "To ita Nanan ya aka ta tafi babu sanarwa?"

"Tun da ta zo yake masifar sai ta bar gidan nan, babu irin magiyar da ban yi masa ba, amma ya din ga ɗaga murya yana bala'i, gaskiya bayan Nana zan bi, ko zan ganta, ban san ina za ta je ba, da ta fita da tsohon cikin nan"

"A'a ba za a yi haka ba, ki yi haƙuri Mai Jidda, rashin kyautawa Iliyasu ba ka kyauta ba, shi ɗa na kowa ne. Kuma tabbas mun daɗe mu na tausar ta, a kan ra'ayinka, ba tare da ba ta damar jin ta bakinta ba. Ka san raɗaɗin da yake cikin raba ɗa da uwa kuwa? Ba ka kyauta ba"

Cikin kuka ta ce "Kawu dama ya bani zaɓi, na zaɓi 'ya ta, ya sauwwaƙe mini na fita na nemi yarinyata"

Kawu ya ce "A'a ba za a yi haka ba, duk inda Nana take yanzu ta yi nisa, kuma idan aka ƙyale ki, ke kan ki ba ki san ina za ki nufa ki neme ta ba. Amma tun da ba yarinya ce ƙarama ba, na san duk inda take Allah zai kare ta, ki ci gaba da yi mata addu'a. Na san ina sha Allah, babu abin da zai same ta, amma batun ki ce ki kashe aure, ki bi ta ki zauna da ita ba mafita ba ce ba, haƙuri kin saba yin sa, a wannan karon ma shi ɗin dai zan baki, na san duk wanda aka ce wa ya yi haƙuri an zalunce shi ne, amma dai ki yi haƙuri.
Kai kuma Iliyasu magana ta domin Allah, ba ka yi kara ba, ba ka kyauta ba ko kaɗan. Yaran nan saboda halinka sun daina zuwa inda take tsawon shekaru, amma daga zuwan yarinyar ka hau bala'i har ta ji, ta yanke wannan hukuncin. Ina kai auren ƙanwarka ne ya mutu, mijinta ya ƙi riƙe 'yar ka karɓo ka kawo mata ta riƙe maka? Har zama fa ta yi da ƙanwarka ta riƙe maka kan ta sake wani auren, amma kai ka kasa yi mata kara, a kan yarinya guda ɗaya tal".
Iliyasu ya zata a wannan karon ma, za a goya masa baya, kamar yadda aka saba tsawon shekaru goma sha, sai dai ya ji wannan karon ba a goyi bayansa ba, sai ya yi tsuru-tsuru, dan haƙuri tabbas ya san Mai Jidda na da haƙuri da kawaici. Kawai ya tsani babansu Nana ne, saboda yadda aka fasa aurensa da ita, ta aure shi, shi yasa tsanar ta shafi su Nana.
Haka aka din ga ba ta haƙuri, Kawunta ya yi ta rarrashinta.

Nana tana zaune a cikin mota, daga jikin taga, tana kallon hanya, yadda ake ta kwarara gudu a motar, tamkar direban zai tashi sama. Gudun da motar take yi, bai dame ta ba, fatanta Allah ya sanya matakin da ta ɗauka, ya zama alkhairi a gare ta.
Duk da ta san Nijar ba gida ne ba, ba unguwa ba ba kuma ɗan ƙaramin gari ba, ƙasa ce sukutum, mai ɗauke da garuruwa daban-daban da ƙabilu masu tarin yawa, balle kai tsaye tana zuwa ta doshi inda za ta gan shi. Duk ba abu ne mai sauƙi neman mutumin da ko ainihin sunansa ba ta sani ba a gari kamar wannan, amma tana jin a ranta motsi ya fi laɓewa, kuma rashin jini rashin tsagawa. Wannan shi ne mataki na ƙarshe da za ta iya ɗauka domin nemawa kanta mafita. Ta yarda da cewa Sarƙar, ƙaddara ce ta haɗa ta da Sayyid, ta yi wa rayuwarta dabaibayi, mussaman da ya tafi ya bar ta da ajiyarsa a tare da ita. Sai dai bayan wannan tana cike da zullumin halin da yake ciki, saboda ta san kaso mafi yawa na mafarkin ta ya kan zama gaske, a jikinta take jin duk a inda yake, yana buƙatarta a kusa da shi.
Hankalinta ne ya dawo jikinta, bayan da ta ji ana cewa, an tsallaka boda sun shiga ƙasar Nijar!.

AYSHERCOOL
08081012143
62

Jamila na ɗaki tana jiyo maganar Baba ya dawo, ba ta fito ba, sai da aka jima sannan ta fito tsakar gida.

Ya ce"Jamila kun dawo ashe? Yaya ku ka baro Nanan?"

Jamila ta yamutsa fuska ta ce "Bamu tarar da Nana ba, ta bar Buda ta tafi Bauchi gurin mamanta, kamar yadda Uwani ta gaya mana"

A fusace ya ce "Bauchi gurin Maijidda? Lallai yarinyar nan ta riƙa ba ta ganin mutuncina, gidan ubanta ne a Bauchin da ta tafi? Uban me za ta yi a can?"

Jamila ta ce "A'a Baba, kar ka ga laifinta fa, a lokacin da take buƙatar taimako, ba a duba ta ba. Na san ta bar Buda ne dan kar ta din ga ɗora wa Uwani ɗawainiya"
Cikin kumfar baki ya ce "Wallahi ba zai yiwu ba, sai ta baro Bauchin nan, tun da dai ba gidan ubanta ba ne ba, kuma laifin Uwani ne ai da sai ta sako ta a gaba ta dawo da ita nan Kano, dan me za ta tafi wata Bauchi" Ummi ce ta yi sallama, suka amsa su na kallon ta.

Jamila ta ce "Ummi ya dai? Ya na gan ki kuma?"

"Ke Ummi, ke ce babbar algunguma, na san duk abin da Nana take yi kin sani, tun da da ke take shawara, ke ki ka bata shawarar ta tafi Bauchi ko?"

Ummi ta girgiza kai ta ce "A'a, ba ni ba ce ba.  Dan hatta ɓatan mijinta ni ban sani ba, ba ta gaya mini ba sai yau da muka je Buda".

Cikin rashin fahimta Baba ya ce "Ɓatan mijinta kamar yaya?"

Ummi ta ce "Baba, duk ba wannan ba. Jamila bayan rabuwarmu ina shiga gida, saƙon Nana ya faɗo wayata, hankalina a tashe yake fa"

"Ban gane ba, saƙon mene ne, ke Ummi ki yi mini bayani gwari-gwari sai wani kwalo-kwalo ki ke yi mini"

"Baba, yau da muka je Buda, Uwani ta sanar mana, mijin Nana an neme shi an rasa kusan sati biyu. Har gurin 'yan sanda suka kai cigiya ba a san inda ya tafi ba.
Bayan mun dawo ina shiga gida, saƙon tex message ɗin ta, ya shigo wayata. Ungo ka karanta message ne kusan kashi uku ga shi nan"
Ya saka hannu ya karɓa, cike da fargabar abin da zai gani.

"Assalamu alaikum, Ummi ya ki ke, ya su Islam. Ki yi haƙuri ban sanar miki ba, ba na son ɗaga miki hankali ne. Sayyid fa ya ɓata, daga na je sayo abu, na dawo na neme shi na rasa, ba na son ci gaba da ɗora miki ɗawainiya, ita ma Uwani yau da gobe sai Allah, ba ƙarfi ne da ita ba. Na je Bauchi Mama ta karɓe ni hannu bibbiyu, amma kamar zuwana zai zame mata matsala a gurin mijinta. Na san ko na koma gida, babu lallai Baba ya karɓe ni, na yanke shawarar na tafi Nijar, ko zan ga Sayyid ko danginsa. Kar ku ɗaga hankali gurin nema na, in sha Allah ba zan aikata abin da zai zame mana abin Allah wadai ba. Yanzu haka ina hanyar Niger, kar ku yi wahalar nema na, in sha Allah zan kasance cikin aminci, ku taya ni da addu'a. Nana Asma'u" A fili Baba ya karanta saƙon. Cikin fusata da tashin hankali ya ce "Wace irin mahaukaciyar yarinya ce Nana? Uban wa ye da ita a Nijar ɗin da ta wanke ƙafa  ta tafi can? Banda tsabar hauka da rashin hankali da wauta, a gidan uban wa za ta sauka? Ba nan ta ce mini ba ta san suwaye danginsa a can ɗin ba, to gidan uban wa ta tafi?"

"To Allah dai ya kiyaye ya sa ba ɗaukar magana ta tafi ba" Mama ta yi maganar tana kwaɓe baki, wanda tun da aka fara magana da ba ta saka baki ba.

Bai kula ta ba ya ce wa Ummi "Ke kira mini ita dan ubanta ta dawo gida, ko ƙasa nake ci ta zauna mu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login