Showing 108001 words to 111000 words out of 122205 words
cutarwa ne.
Wani ɗan kwando ta gani ƙarami, an nannaɗe shi ba za ta iya ganin mene ne a ciki ba.
Wata zuciyar ta raya mata, ta kwance ta ga mene ne a ciki, wata kuma ta hana ta,sai dai har ta gama grkin dare tana kallon kwandon tana tunanin mene ne a ciki? Waye zai bayar da saƙo babu suna, kuma me yasa sai ita za ta kai? yanayin saƙon dai kamar babu gaskiya a lamarin.
Da fargaba ta haɗa da ɗan kwandon ta nufi sashinsa gabanta yana faɗuwa.
Yau shikaɗai ne a zaune, babu Asal. Duk da ruɗewar da yake yi idan ya ganta, amma ya ji daɗin ganin ta kawo masa Abinci, dan tun safe bai sake cin komai ba.
Sai dai yau ba iya faɗuwar gaban yake ji ba, har da wata ƙara, mara daɗin ji makamanciyar wadda ya din ga ji daren da zai fara ciwo.
Ta ajiye kwanukan ta ce "Barka da yammaci Sayyid, fatan ka na lafiya."
"Alhamdillah" ya furta ba tare da ya shirya hakan ba, yana mamakin daga ina wannan sautin yake. Ita kanta Nana ba ta zata zai amsa mata gaisuwar da ta yi masa ba.
Ganin babu Asal a gurin, ya sanya Nana zuba masa Abinci da shayi. Ta kalle shi duk da yadda yake yi mata wani irin kwarjini da a baya bata taɓa zaton yana da shi ba ta ce "Ko yanzu ma sai na ɗanɗana?"
Ya girgiza kai alamar a'a. Ya sauka daga kan kujerar, yana jin ƙarar nan na ci gaba da addabar kunnuwansa.
Cike da son basar da abin da yake ji, dan gujewaa sake faruwar abin da ya faru a wancan karon, ya yi Bismillah ya fara cin abincin.
Duk da a takure yake da yadda take kallonsa, kuma ba zai taɓa iya cin abinci a gaban wanda bai kamata ya ci ba, amma ya kasa yi mata magana, kuma bai ji hakan da ya yi a matsayin wani laifi ba a matsayin sa na ɗan gidan mulki ba, wanda hakan yana cikin kamewa da suke da ita, musamman ma shi da hakan ya haɗu da ɗabi'unsa.
"Sayyid, ina jin yadda mutanen gidan nan suke yabon ka, sosai da sosai da yabon karamcinka. Duk da a baya ban so zuwa gidan nan aiki ba, amma sai dai na ji babu daɗi da yadda ni ban samu wannan karamcin daga gare ka ba, sai ma ƙyama da ka ke nuna mini, da ƙabilanci ban sani ba ko dan ni ba ƙabilarku ba ce, kuma ba 'yar ƙasarku ba ce ba, shi ya sanya ka ke yi mini haka. Amma ina neman afuwa idan na faɗi wani abu ba daidai ba ko ya ɓata maka rai, bana nufin hakan shugabana"
Gaba ɗaya babu tsoro ko fargabar Asal ta fito ta tarar da ita a ranta, daɗi ma ta ji na ko ba komai yau ta keɓe tare da shi.
A wannan karon ma, jin maganganun nata ya din ga yi da matuƙar muhimmanci. Yaya zai yi mata bayanin ba tsanarta ya yi ba, baya iya tantance abin da ruhinsa da gangar jikinsa ke nufi a kanta ne. Shirun da ta ga ya yi, da yadda yake jujjuya cokalin ya sanya ta yin ajiyar zuciya, ganin alamun saƙonninta na isa kai tsaye inda take so.
Ta nuna masa kwandon da aka bayar aka ce a ba shi, ta tashi ta fita.
Kitchen ta koma tana ƙarasa goge-goge, kawai. Sai dai ta ji alamun mutum a bayanta. Ta waiwaya ta gan shi a tsaye a ƙofar kitchen ɗin, idanunsa jawur, ga Giyaz a gefensa, cikin suffarsa ta tsohon nan mara kyan gani.
Ya fara takowa cikin kitchen ɗin, yana kusanto ta, gabanta yana faɗuwa ta zuba masa ido.
Ya ɗago mata wata takarda ɗauke da hoton ƙwarangwal yana ci da wuta, an rubuta Imam Hammad Jalaludeen a jiki.
"Waye ya bayar da wannan saƙon?"
Kan Nana ya sara mafarkin da ta taɓa yi, ya fara ƙoƙarin zuwar mata kanta.
"Waye na ce waye ya bayar da wannan saƙon?" Ya yi maganar cikin wata irin murya da ba ta taɓa jin sa da ita ba a rayuwar da suka yi!!!
Cikin rawar murya ta ce "Nima ban sani ba, saƙo ne kawai aka ba ni aka ce na baka"
"Waye? Waye ya bayar da saƙon? Ki gaya mini?"
Ta kame jikinta cikin tsoro ta ce "Ban santa ba wata ce?"
Launin idonsa ne ya fara canzawa, baƙar ƙwayar idon ta ɗauke, sai farin kawai.
"Giyaz" Nana ta furta a hankali.
AREWABOOKS.
Jikinsa ne ya fara ƙamewa, fitilun kitchen ɗin suka ɗauke gaba ɗaya, ta ce "A wannan karon me ka ke buƙata kuma?"
Muryar Giyaz ta din ga ji, yana wata irin dariya. "Ai dama na gaya miki, ki jira dawowata".
"Na fi ƙarfinka, a waccan rayuwar da ya yi, da wannan ɗin ma, na fi ƙarfinka har abada".
"Kar 'yar ƙaramar ƙwarin gwiwar da wancan yaron ya baki, ya sanya ki yi tunanin za ki iya yi mini wani abu, mu zuba mu gani".
Nana ji ta yi abu ya faɗo jikinta mai nauyi, suka faɗi ƙasa tare. Wal hasken fitilar kitchen ɗin ya dawo. Imam ta gani a kwance a gefenta.
Da sauri Nana ta nufe shi, jikinta na rawa za ta taɓa shi.
Amma ta ganta itakaɗai a ɗakin karatun Ƙaisar, cikin azama ta tashi tana waige-waige, ta ga Ƙaisar a tsaya a bayanta.
"Yana ina?" Ta faɗa a sanyaye.
"Na san abin da ki ke ji, amma ya yi wuri, kuskure kaɗan za ki aikata ki lalata komai. Kar ki yi mamakin a din ga bibiyarki, saboda zaɓar ki da matar nan ta yi a matsayin mai dafa abincinsa, kuskure kaɗan ki na iya kwana a ciki ki shiga matsala. Kuma Giyaz zai yi ta tunzura ki, har ki yi wani abin da za ki saka kan ki a zargi. Ki din ga bin komai a hankali"
Nana ta yi ajiyar zuciya, itakaɗai ta san abin da take ji, a kan Sayyid. Dan a gare ta gara lokacin da ya ɓata ba ganinsa take yi ba, amma yanzu ga ta ga shi, amma ya yi mata nisa.
*****
Sagir kuwa ya zama tamkar zararre, aka kwana uku babu Shukura babu labarinta, sai a kwana na uku ya sanar da gidansu Shukura halin da ake ciki.
Hajiya Amina ta gigice ta rasa inda za ta tsoma ranta. Hankalinta ya yi mummunan tashi.
Alhaji Zailani ya din ga yi wa Sagir bala'i, a kan me tun ɓatan Shukura bai gaya musu ba sai yanzu.
Aka ƙara sanar da jami'an tsaro, aka kuma baza komar neman Shukura.
****
Ummi ce ta kawowa Baba ziyara, sai dai yanzu Baba duk ya zama abin tausayi, duk inda ya zauna sai da ya ja uban tagumi ya yi shiru, da ya samu dama kuma sai ya hau zancen Nana. Yanzun ma hirar da yake ta yi wa Ummi kenan.
"Ummi kin ga Nana haryanzu shiru ko? Babu ita babu ɗan uwanta, shi ma tun wannan zuwan da ya yi bai sake zuwa gidan nan ba. Gara shi namiji ne ita kuwa ban san halin da take ciki ba. Nan gida kuma ita Suwaiba yanzu ba ta da maraba da mahaukaciya, na ce a kaita Asibiti babarta ta ƙi yarda.
Ita ma Jamila 'yan kwanakin nan, gaba ɗaya ba na gane kanta, dama kuma babarta ta nuna mini in daina shiga sabgarsu 'yarta ce, saboda abin Duniya"
Ummi ta ce "Gaskiya ne Baba, abin duk babu daɗi kam, amma Baba wani abun an bar gini tun ran zane ne, wannan abubuwan tun daga tushe yakamata a ce an yi wani abu na kaucewa farwuarsu, yanzu sai dai a yi ta haƙuri ana gaya wa Allah. Ta dai ɗan ba shi baki sannan ta tashi ta shiga cikin gidan.
Suka gaisa da Mama a tsakar gida, suka hau hira.
"Wai ina Jamila ne?"
Mama ta ce "Tana ɗaki"
"Amma tana ji na zo, ta yi burus?" Ta yi maganar tana leƙa ɗakin.
Ta tarar da Jamila a kwance ta yi rigingine.
"Jamila yau 'yar shariya ce babu magana ma?"
Jamila ta yinƙura ta tashi zaune, suka gaisa sama-sama.
"Wai ba ki da lafiya ne?"
Ta jinjina kai alamar eh.
"Jamila kin fiye yawan rashin lafiya, Allah ya kawo mana siriki mu sha biki. Ta ga dai mutanen gidan nasu duk sai a hankali, ta yi musu sallama ta tafi.
Hajiya Sa'a tamkar za ta haukace, kwana uku amma sai an yi da gaske take cin abinci kaɗan.
Ta rame ta zabge kamar ta shekara tana larura.
Ko gaisuwar aka yi mata ba ta iya amsawa, idanunta suka koɗe suka yi jawur.
Mutane da dama sun ji mutuwar Abba, saboda mutuwar fuju'a ga matashi, tana taɓa zukata, mussaman Abban da yake mutumin kirki ne, ga girmama mutane.
Ranar da Abba ya kwana uku da rasuwa, Safiyya ta samu Hajiya Sa'a a ɗaki, ta ce "Hajiya yanzu mene ne abin yi, wani matakin ki ke ganin za ki ɗauka a kan wannan lamarin?"
Hajiya Sa'a ta sunkuyar da kai hawaye na zuba daga idanunta ta ce "Duk matakin da zan ɗauka, kafin mutuwarsa yakamata na ɗauke shi, dana sani nake mara amfani na janyo yarinyar nan jikina, sannan idan na matsa, tsaf za ta tona mana asiri, dan haka ba zan saurare ta a yanzu ba, ina cikin matsanancin kewa da alhinin rashin tilon ɗana. Sai dai wallahi sai ta tafi inda Abba ya tafi, ko da kuwa nima zan rasa raina na"
Jiki a sanyaye ta ce "Hajiya ki bi a hankali, kar garin neman gira a rasa idanu"
"Ki zuba ido kawai" ta faɗa a taƙaice tana share hawaye.
Kiraye-kirayen sallar asuba ne ya sanya Nana farkawa, ta ganta a ɗakinta a kwance, ba ta iya tuna abun da ya faru ba tun daga biyo ta da Sayyid ya yi.
Ta kalli ƙwan fitilar ɗakin a kunne, ta yinƙura za ta tashi, kawai ta takardar nan, da ya nuna mata yake tambayarta waye ya aiko da ita.
A tsorace ta ja gefe, tana kallon takardar. Jikinta na rawa bakinta ɗauke da addu'a, ta ɗauki takardar ta sake ƙare mata kallo. Ta ninke ta ta saka a cikin kayanta, ta shiga banɗaki.
*****
Nana na tsaka da aiki a kitchen, ta ji motsi a kitchen ɗin.
Ta waiwaya ta kalli inda take jin motsin, ta ga Asal.
Cike da takaicin babu yadda ta iya, ta ce mata "Barka da safiya"
"Barka, amm na ce akwai abin da ya faru ne? Imam ya ce lallai a tsananta tsaro a gurin girkin nan, ki gaya mini idan da wani abu da ya faru?"
Nana ta girgiza kai ta ce "A'a babu wani abu da ya faru fa"
Asal ta ce "Kar na kama ki da aikata rashin gaskiya, hukuncin da zan yi miki sai kin gwammace kiɗa da karatu" Nana ta yi mata shiru, a ranta ta ce "Kya ji da shi"
Asal ta juya ta fita, Nana ta raka ta da harara.
Mahmudu ne durƙushe a kan gwiwoyinsa, a gaban Abdou matawalle.
Ya numfasa ya dube shi ya ce "Imam Hammad ya samu lafiya, ya dawo Nijar"
Mahmudu ya ɗago kai a zabure, yana kallon Matawalle.
"Ka sani, koma me ka ke yi masa da ka ke mallake shi, mu na sane mun zaba maka ido,mun yi maka talala ne mu ga gudun ruwanka. Tun da ya sako ƙafarsa a ƙasar nan, tun ma yana can, yake zancenka yana cewa kana ina?. To ka tsaya da kyau ka saurare ni, zamu sake ka amma hakan ba ya nufin ka yi 'yanci ne, ko kuma mun daina zarginka, mu na nan mu na saka maka ido a ƙarƙashin takunkumi za mu sake ka.
Sannan kar ka kuskura ka gaya wa Imam batun sace shi da ka yi da rayuwar da ya yi a Nigeria. Dan babu yadda ba a yi ya tuna wani abu ba, amma abu ya gagara. Dan haka ba a buƙatar ya san ya yi wata rayuwa a Nigeria, balle maganar nan ta fita, idan kuwa ka bari a ka ji maganar nan a waje, hukuncin da zai biyo baya ba zai yi maka daɗi ba.
Wannan saƙo ne daga Sultan, ba a buƙatar ya san ya yi wata rayuwar daban, dole ka ja bakinka ka tsuke. Dan ka san hukuncin kisa shi ya dace da kai, an ɗaga maka ƙafa ne, saboda son da Imam yake yi maka, ba a buƙatar abin da zai taɓa masa zuciya"
Mahmudu ya saci kallon Matawalle, yana jin zafin yadda mutumin nan yake ɗora masa sace Imam.
Haka nan ya risuna ya yi wa Matwalle godiya.
*****
Asal ce zaune a gaban Sultan, yake yi mata magana cikin nutsuwa da dattaku.
"Yarinyar kirki, na san za ki yi mamakin sake kiran ki da na yi, duk da jiya kun zo gidan nan, to ina da baƙi ne ban samu mun yi magana ba a jiya, shi ya sanya na ce ki zo yau ina son ganinki"
Asal ta jinjina kai, tana saurarensa cikin nutsuwa.
"Na san kin ɗauki dogon lokaci mijinki baya kusa da ke, wasu faɗi tashin duk da ke aka yi kin san komai. To ga shi Ubangiji Allah ya yi masa dawowa cikin aminci. Sai dai duk da haka haryanzu bai gama samun lafiya ba. Dan Allah dan Annabi ina roƙon ki, ki zama mai haƙuri da juriya da kuma rufa masa asiri. Kin san yadda yake da magauta ta kowacce kusurwa, dan Allah ina sake roƙon ki, ki zama rufin asiri ga Imam, duk abin da ki ka gani wanda ba ki yadda da shi ba, ki zo ki sanar mini ban yarda ki gaya wa kowa ba. Dan Allah ki yi haƙuri da shi ya samu nutsuwa da kwanciyar hankali daga gare ki"
Ta jinjina kai ta ce "In sha Allah Abie, ba zaka same ni da wata matsala ba, zan zama mai rufa wa mijina asiri"
"Na gode sosai da sosai, Ubangiji Allah ya yi muku albarka, ya baku zuriya ta gari masu jin ƙai"
"Amin Abbie, muna godiya sosai da sosai"
Sosai Imam Hammad yake son ya ci gaba da gudanar da al'amuransa da ayyukansa da yake yi, kamar a baya, amma abu ya gagara gaba ɗaya ji yake komai ya fita daga ransa. Jin jikinsa yake yi kamar a ɗaɗɗaure duniyar sam ba ta yi masa daɗi, ga shi takamaima bai san abin da yake damunsa ba.
Sultan ne ya aika da mota aka ɗauke shi, bai san ina za a kai shi ba, bai kuma tambaya ba. Gidan da ake sauke baƙin Sultan nan aka kai shi. Sai ya fara mamakin ko wata ganawar zai yi da baƙin, amma Sultan bai gaya masa ba?.
Sai dai babu zato babu tsammani ya ga Mahmudu.
Cikin matsanancin farin ciki suka nufi juna, Imam ya ce "Mahmudu" Ya rungume shi cikin farin ciki. Sai dai wata irin karaya ta shiga zuciyar Mahmoud.
Imam ya ce "Tun da na dawo nake cigiyarka, na ce ko ba ka san na dawo ba, a Faransa ma sai da na roƙi a kawo mini kai, mu zauna tare na yi jinyar, amma ba a bani dama ba" sai dai jin sheshsheƙar kukan Mahmoud ya ɗaga masa hankali, ya ɗago shi cikin damuwa ya ce "Mahmoud, ko na yi maka wani abu ne?"
Ya girgiza kai yana share hawayensa ya ce "Ai ba ka yi mini laifi, ko me za ka yi mini a duniya kuwa. Murna ce da kewa ta sanya ni kuka"
Jiki a sanyaye ya ce "Dan Allah ka bari, zuciyata ta karaya nima" Sai dai maimakon ya yi shirun, tamkar tunzura shi ya yi, ya sake fashewa da kuka.
Hawaye ne ya cika idanun Imam, ya ce "Dan Allah ka gaya mini idan wani abin ne ya faru, duk ka sanya jikina ya yi sanyi, kamar ban taɓa ganin kana kuka ba"
Ya share hawayensa ya yi ajiyar zuciya ya ce "Na ce maka murna ce kawai nake da ganinka ya shugabana, ina fatan ka dawo cikin ƙoshin lafiya"
Ya yi tsaki ya ce "Za ka fara ko? Waye shugaban naka?"
"Kai mana Allah ya baka nasara"
Kawai ya yi wata dariya ya ce '"Ka ci gaba, zan rama ne"
Mahmudu ya yi dariyar shi ma ya ce "Ba zan iya fasalta adadin yadda na yi kewar ka ba, da farincikin da nake ciki, a sanadin dawowarka ba"
Imam ya ce "Na fika murna da ganinka"
Duk da yau suka haɗu tun dawowarsa, amma ji yake kamar ya gaya wa Mahmudu abubuwan da yake ji, amma sai ya fasa ya ga kamar ya yi wuri.
Shi kuma Mahmudu zuciyarsa cike take da karaya, da kuma tunanin tayaya zai gaya wa Imam Hammad cewa ya yi aure a Nigeria, alhalin ga kashedin da aka yi masa. Ita Nana da suka baro a Nigeria mene ne matsayinta. Ya tuna irin ɗawainiyar da ta din ga yi da shi, da rayuwar da suka yi, amma alamu ya nuna sam Hammad bai san an yi hakan na, dan da ya tuna zai yi masa maganar. A ransa ya yanke dole ya shirya da kansa ya tafi Nigeria neman Nana, kuma ko me za a yi masa idan ya gano ta, dole ya kawo ta ya gabatar da abin da ya faru, ko da hakan yana nufin a yanke masa hukuncin kisa ne, gara ya yi da ya mutu da hakkin Nana a kansa.
Ya din ga mamaki da tambayar kansa, yaya aka yi a wannan karon, Imam ya dawo hayyacinsa ya sake mantawa da rayuwarsa da Nana, bakinsa fal tambayoyi amma babu halin furta su, saboda kashedin da aka riga aka yi masa.
Tare da Mahmoud suka zauna suka sha hira sai dai abincin da aka shirya musu, Imam ya ƙi ci.
"Imam, wai ya na ga ba ka cin abincin ne?"
"Abincin da ya fito daga hannu ɗaya ne tal yake yi mini ɗanɗano a bakina yanzu, idan ba shi ba duk wanda na ci salam nake ji"
Cikin mamaki ya ce "Abincin wani hannu kenan?"
Ya ɗan yi shiru ya ce "Asal ce ta kawo wata mai yin girki daga Nigeria, idan ba ita ta dafa ba, ba na gane kan Abincin"
Ƙwarewa Mahmud ya yi, Hammad ya miƙa masa ruwa yana yi masa sannu, ya yi shiru ya ce "Daga Nigeria kuma?"
"Eh"
"Lallai Imam ka na da rigima, amma duk Nijar sai da aka tsallaka Nigeria aka samo ta?"
Ya ɗan ɗage kafaɗa ya ce "Ka san rigimar Asal, wai a gurin cin abincin Maraɗi ta gano ta, ta kawo ta nan. Zan saka ta yi girki ka zo ka ci"
Mahmoud ya jinjina kai, daga bisani ya kawar da zancen, yana ci gaba da lissafa yadda za