Showing 33001 words to 36000 words out of 122205 words

Chapter 12 - BUZU BOOK2 COMPLETE 2

18 Jan 2026

579

muddin ya bar Giyaz, zai iya nakasta Nana nakasa ta har abada, ko ma ya kashe ta, kamar yadda ya furta.
Ya ɗauki Giyaz, ya kai shi can nesa ya sadaukarwa wani boka shi, bisa musayar da za su yi, zai ba shi wani abu mai muhimmanci. Wanda ya yi hakan domin nesan ta shi da Nana da zuriyar Lanti.

Duk da abin da ya yi ya dawo ya dame shi, yana matuƙar ƙaunar mahaifinsa, duk da saɓanin da suka samu, amma babu yadda iya, hakan ne kawai zai sanya ya nisanta shi da Nana.
Sauran 'yan uwan Ƙaisar da tuntuni suke jin haushinsa, suka yo caaa a kan Ƙaisar, har suka nemi hallaka shi, saboda abin da ya yi wa mahaifinsu, amma sun san ko sun hallaka shi, idan Giyaz ya kuɓuta suma sai ya kashe su.
Ɗan uwan Giyaz Duna, ya yi ta ƙoƙari gurin ganin ya kuɓutar da Giyaz, amma abu ya gagara.
Nan suka din ga kai wa Nana hari, da yinƙurin hallaka ta.
Maijidda kuwa bayan mutuwar aurenta, tana gama idda, Iliyasu tsohon saurayinta ya sake dawowa ya aure ta. Ko da Baban Nana ya samu labari, sai ya ce tana sane, ta ƙi zama da shi, saboda ta koma ta auri Iliyasu, dama son zama da shi take yi ba.
Nana ta ga garari tun da ƙuruciya, babu cikakkiyar kulawa, kuma tun ba ta fi shekara uku ba take ganin Ƙaisar, da ma sauran 'yan uwansa da suke ta kokarin azabtar da ita.
Maijidda ta so karɓar ko Nana ce, saboda rashin cikakkiyar lafiya, amma Isa ya hana fafur, ita ma can mijinta ko yaya ta motsa tana son ganin 'ya'yanta, sai ya hau bala'i wai za ta gurin tsohon mijinta.
Tun Nana na ƙarama, take nuna alamun rashin lafiya, amma babu wanda ya kula. Ta kan wuni tana bacci tun safe, har dare babu wanda zai damu. Wasu lokutan ta daina magana ma ko tafiya gaba ɗaya. Idan kuma ta warware ta din ga fitinar da ta fi ƙarfin shekarunta nesa ba kusa ba.
Ta kan ga Ƙaisar a zahiri, ko kuma a cikin bacci. Babu wanda ya damu da ta ci Abinci ko ba ta ci ba, mussaman da Baba ya daina sana'ar komai, sai dai Imran ya nema ya bata. Idan ta fita Ƙaisar ya kan zo a suffar mutum, ya ba ta abinci. Allah ya sanya masa matsananciyar ƙaunarta. Ya fara bayyana a jikinta ne, tun wani duka da Mama ta yi mata, bayan faɗa ya haɗa ta da Jamila.
Sai da ta kwana biyu a sanƙame, tun daga nan suka gane halin da take ciki. Da ranta ya ɓaci sai hankalinta ya gushe. Ƙaisar ya sha ɗauke Nana, a neme ta a rasa kwana ɗaya ko biyu ya je ya ajiye ta gurin sa.
Baba ya yi ƙoƙarin nema wa Nana magani, amma abu ya gagara. Labari ya iske Maijidda halin da Nana ne ciki, bayan da su Adda Saude suka zo ganin su Nana. Rabi ta haɗa tuggu a gurin Baba, ya ce kar su sake zuwar masa gida, kuma ba zai bayar da Nana ba. Wahala ta saka Imrana fara sace-sace saboda su ci Abinci, Rabi ta saka Baba ya kore shi daga gidan. Haka Nana ta tashi a cikin wahala, ga wanda bil'adama suke yi mata, ga wadda Ƙaisar yake yi mata da sunan kulawa.

Ji ta yi tamkar an sanya hannu an shaƙe ta, a dole ta saki littafin ta ja da baya tana tari.

Ta ɗaga kai ta kalli Ƙaisar, bai ce mata komai ba, ya ɗauki littafinsa ya juya ya tafi. Yana barin gurin Haula ta zagayo ta dafa Nana. Ta ɗaga kai ta kalle ta ta ce "Ƙawata, kwana biyu. Hadiminki ya ƙi saurarata balle na sanya ran zai karɓi buƙata ta, ki yi wani abu a kai dan Allah"

Nana ta ce "Haula, gaba ɗaya jinsinku ba abin yadda ba ne, ki rabu da ni da wannan maganar ta ku"

"Shikenan, na rabu da ke, amma kin yi ganganci abin da ki ka yi wa dattijo, Allah kaɗai ya san me zai yi miki idan ya gama jinya. Kuma har Ƙaisar ki ka janyowa shi ma ba zai bar shi ba"

"Duk hukuncin da ya yi wa Ƙaisar yayi daidai, ɗa na gari ba zai taɓa yi wa babansa abin da ya yi wa nasa mahaifin ba"

Haula ta ce "Kash! Nana kar ki zama butulu mana. Sai dai ina fatan kin fuskanci jakar gurin Sarkin baka da ya baki, wace jakar ce"

Nana ba ta ba wa Haula amsa ba, Sayyid ya tashe ta.

"Ma vie" yayi maganar yana matsawa jikinta sosai. Jiki a sanyaye ta amsa masa. Ya ce "Lafiya dai?"

"Mmm"

"Ko Ƙaisar ɗin ne?"

"A'a"

"To me yasa ki ka tsorata? Mene ne ya baki tsoro?"

"Bakomai"

"es-tu sûr? (Kin tabatta?)"

Ta ce "Eh. Haryanzu hannunka lafiya ƙalau ko?"

"Eh, amma akwai abin da ya tsorata ki, gaya mini mene ne?"

Ji ta yi tamkar ta gaya masa, dan a wannan karon ba ta manta abin da Giyaz ya gaya mata ba, a kan idan ya warke zai sake waiwayar su.

"Ma viee"

"Sayyid" ta amsa a hankali.

Ya yi maganar yana taɓa wuyanta "Sanyi ki ke ji Rayuwata"

"Eh, amma ba sosai ba"

"In baki ɗumi ne?" Yayi maganar muryarsa ƙasa-ƙasa

Dariya ta yi ta ce "A'a na yafe, ƙona ni za ka yi"

Shi ma dariyar ya yi ya ce "To ni ki bani sanyin ina so" Ya yi maganar da sigar shawaɓa.

"Wai kai ba ka jin bacci ne? Kawai ka farka cikin dare?"

"Soyayya ce ta tashe ni" Sai da jikin Nana ya ɗan yi sanyi, ta ce "Soyayya kuma Sayyid?"

"Eh, je t'aime ma femme"

"To ai ban san me ka ce ba"

Ya yi kissing ɗin goshinta ya ce "Ina sonki matata" wani abu ne ya tsirgawa Nana, tun daga tsakiyar kanta, har tafin ƙafarta.
Shafa hannunsa ta yi, kamar mai tantamar abin da ya ce, ta ce "Sayyid"

"A'a, kar ki yi tantama, ko ki yi kokwanto, shi yasa na baki sunan Rayuwata. Ko a wannan Duniyar, ko ma a wace Duniyar, kawai ina son matata, saboda ita ɗin Rayuwata ce. Babu abin da zai canza hakan."

"Sayyid ina tsoron idan ka tuna waye kai, ka ji ba ka so na, zan cutu da yawa, zamana da kai na shaƙu da kai sosai zuciyata ba za ta iya ɗauka ba" Ta yi maganar cikin rauni da tsoro.

Ya ɗaga kan Nana, ya sanya hannunsa a wuyanta, ta lumshe idanunta hawaye na bin gefen fuskarta.

"Ƙa'idar ba za ta canza ba har abada, babu ruhin da zai samu nutsuwa a gangar jikin ɗayanmu muddin ba ma tare, ki saka haka a ranki. Sayyid yana son Rayuwarsa. Ko babu raina fatalwata za ta ci gaba da sonki" Nana ta yi ajiyar zuciya tare da dariya, ta shafa gashin kansa.

"Allah ya sa haka. Ina son mijina sosai nima" murmushi ya yi yana kissing ɗin ta.

Har garin Allah ya waye, maganganun Sayyid ne ke kai komo a cikin ƙwaƙwalwa, zuciya da kuma gangar jikin Nana. Wani irin shauƙi da farinciki ne yake kama ta, da tuna kalamansa.

"Amarya" ya yi maganar yana kallon ƙwayar idonta.

"Amarya da wannan ɗin?" Ta yi maganar tana nuna cikinta da ya fito sosai.

Yayi murmushi yana shafa cikin ya ce "Duk da haka amarya ce ai, ko kin manta?" Ya yi maganar yana kashe mata ido.
Ta yi murmushi tana ci gaba da ninkin kayan da ta wanke.

"Sayyid, bari na je kasuwa na nemo kayan magungunan ka, na dafa maka, ka ci gaba da sha, kuɗin hannuna sun ɗan taru, zuwa ranar Monday in Allah ya kaimu, duk yadda za a yi, mu tafi Kano Asibiti. Na ji haryanzu zuciyarka ba ta bugawa sosai, na san ƙarfin hali kawai ka ke yi"

"Gaskiya kin fiye saka ido, ya aka yi ki ka gane hakan, mai magani?"

Ta jinjina kai ta ce "Au haka ma za ka ce ko? Hmm ai shikenan, za ka ga mai magani, yau sai na wanke ka da magani na kulle ka a ɗaki"

"Eh saboda cin zali ba, kuma ke ki gudu, alhalin kamata ya yi ki yi mana tare"

Ganin yadda yake rungumota ta ce "Sayyid na gama shiryawa, fita fa zan yi"

Ya ce "Na sani"

"Ka sani kuma ka ke son na ɓata lokaci? Dan Allah Sayyid jiya throughout the night mu na tare, yanzu kuma...

"Shhhh... Ba ki ji jikina ya fara zafi ba"

"Wallahi lafiyarka ƙalau, normal babu zafi a jikinka, wai wannan surutun duk daga ina?"

Haka ya hana Nana fita, har bayan Azahar, kawai ta zuba wa Sarautar Allah ido. Kuma a fuskar sa take ganin tsantsar ƙarfin hali, amma ba shi da lafiya.
Sai bayan la'asar ta marairaice ta ce "Dan Allah ka bar ni na je na haɗo kayan nan Sayyid, ko haryanzu ba ka gama jin Sanyin ba?"
Ya ɗaga mata gira. "To ga mafici, yi ta fifita, har na dawo" Dariya ya yi yana ɗan jan hancinsa. Ya kamo hannunta ya ɗora a wuyansa ya ce "Kin ji da zafi ko?"

"Ba wani zafi. Waccan ranar ma wayo ka yi mini, wai na baka sanyin jikina"

Dariya yake son yi sosai, amma sai ya yi kaɗan ya cije, ya ce "Ai ni Ƙaisar wasu lokutan taimakona yake yi"

A sanyaye ta ce "Shi me yasa ba ka kishi da shi?"

"In ji wa? Kawai abu ɗaya ne da babu yadda muka iya. Alaƙarsu ta ɗa da mahaifi tana tasiri a rayuwarmu ni da ke"
Cikin mamaki Nana ta ce "Ta yaya? Kuma ya aka yi ka san Ƙaisar ɗan Giyaz ne?"
"Yadda ki ke ganin Ƙaisar ku yi magana, haka nake ganin Giyaz, kuma na fuskanci waye shi a tattare da ni. Yanzu ki je ki dawo"
"Kai amma na yi mamaki fa, kuma ba ka taɓa gaya mini ba. Bari na je na dawo, ina da tarin tambayoyin da zan yi maka"

"Tom sai kin dawo"

Ta saka hijjabinta, har za ta fita ya kirawo ta. Ya ce "Ba ki yi mini ba"

Ta yi masa kiss a goshinsa, da bakinsa.

"Allah ya yi miki albarka. Ki kula mini da kanki, kar wani ya kula mini ke, ki kular mini da babyna ki tafi a hankali ki je ki dawo"

Ta kalli cikin ta ce "To Shugaba, in sha Allah"
"To a dawo lafiya, I love you"

Cikin murmushi ta ce "Inyee ɗan gayu, ka yi furansanci, ka yi turanci, ka yi hausa ga kuma yarenku. Zan koyo yaren da baka iya ba, na din ga tashin kanka da kalaman soyayya"

Ya ce "Je ki dawo ki yi mini waƙa"

"Sai dai na je na yi maka tsifa, na yi maka sabon kitso" ya tsuke fuska yana hararata. Ta fita tana waigensa tana murmushi.

Tana fita ya jingina da jikin bango, yana dafe saitin zuciyarsa, yana haki sama-sama. Ya fito tsakar gida da kyar, ya zauna yana sake danne saitin zuciyarsa da yake jin wani irin abu kamar shocking daga zuciyarsa yana zagayawa bayansa har cikin kansa.
Tsayuwar motoci ya ji a waje, sai dai hankalinsa ba ya kan hakan. Ya ji an daki ƙofar gidan da ƙarfi. Ya ɗaga kai ya ga wasu murɗaɗɗun ƙarti sun shigo cikin baƙaƙen kaya.

Duk da mawuyacin halin da yake ciki, haka ya yinƙura ya tashi da ƙyar, ganin an shigo da Habu hannunsa da sarƙa.

Ya din ga bin mutanen da kallo, Habu cikin matsananciyar damuwa ya zube a kan gwiwoyinsa ya ce "Ka yi mini Afuwa Imam, ba laifina ba ne ka yi haƙuri, na gaza baka kariyar da ta dace" Sayyid ya din ga bin sa da kallo, da alama ma ba ya gane me Habu yake nufi.
Ƙartin nan biyu daga cikin su, suka yo kansa, suka riƙe shi.

A rikice ya ce "A'a, ku rabu da ni. Me na yi muku?"

Ƙoƙari suke su tasa shi su tafi da shi cikin salama, amma ya turje. Suka juya yare zuwa faransanci, su na rarrashin sa, ya wuce su tafi.

"Ba zan je ko ina ba? Ina zan tafi na bar matata" Habu ya din ga girgiza masa kai da alamar ya daina faɗar maganar da yake yi.

"Ku rabu da ni, ina zaku kai ni na tafi na bar Nana" maganar da yake yi cikin ɗaga murya, ga ƙoƙarin turjewa da yake yi, ya sanya zuciyarsa yin rauni, ya yi baya zai faɗi. Suka tare shi suka saɓa shi suka yi waje da shi.
Aka saka Habu a cikin wata motar daban, Sayyid kuma aka saka shi a cikin wata baƙar Highlander mai tint glass, aka rufe suka tafi da shi.

Nana tana tsaye ta bayar da kuɗi, za a bata kankana, dan daga ita har Sayyid, kawai ta ji gabanta ya yi wata irin mummunar faɗuwa. Ta yi shiru, ta jiki gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi. Kawai ta juya ta tafi. Mai kayan yana ta yi mata magana, amma ba ta tsaya ba, ta nufi gida har da ɗan gudu saboda azabar sauri.
Tana zuwa ƙofar gidan ta ga ƙofar gidan a ɓalle, da hanzari ta shiga gidan, tana kiran sunan Sayyid. Amma wayam ba ya nan, ta shiga ɗaki baya nan. Ta duba banɗaki nan ma ba ta gan shi ba.

Ta fita waje da sauri, tana kalle-kalle, ta tafi hanyar inda bishiyar kukar nan take, tana tunanin ko jikinsa ne ya motsa, ya tafi can, sai dai can ma baya nan.
Ta sake komawa gidan cikin tashin hankali, da wani yaro da yake zuwar mata aike ta haɗu a ƙofar gidanta ta ce "Ashiru, ko ka ga Sayyid ya fito daga gidan nan? Wannan mutumin na gidana farin nan?"

"Wasu mutane ne suka shiga gidan suka tafi da shi, a mota suka zo"

Sak Nana ta tsaya, tana ƙure Ashiru da ido, tamkar ma ba ta gane yaren da yaron yake yi.

Ayshercool
08081012143

60

Cikin rawar murya Nana ta ce "Wace irin mota kuma Ashiru? Ka tabattar kuma Sayyid ne?"

"Wallahi na tabattar, ina nan ina wasa suka zo, a motoci wannan farin na gidanki suka ɗaukko."
Tamkar mahaukaciya ta bi sahun motar, ita ce har titi ko za ta ga motar da Ashiru ya ce, amma babu wata alama na za ta ga motar da aka daukar mata Sayyid aka saka a ciki.
Gaba ɗaya ta kasa kuka, sai tsuma da jikinta yake yi tamkar mazari. Tuni rana ta faɗi, an fara kiran sallar magariba, ba ta san tafiyar da ta yi da nisa ba, sai da ta tashi dawowa.
Gidan Uwani ta nufa, ta tarar da ita ta yi alwala, za ta yi sallar magariba.
Uwani ta ce "Ke Nana, uban me ya fito da ke da magaribar nan, ga juna biyu kina da shi, duk da na san ba ki da ɗan aike amma koma mene ne, ai kya bari a idar da salla ko?" Nana ba ta yi magana ba, ta nemi guri ta zauna a ƙasa.
"Ke lafiya kuwa?" Uwani ta yi maganar tana tattara hankalinta a kan Nana. Amma Nana ta kasa magana, sai murza zoben hannunta da take yi, tana ajiyar zuciya.
"Ke ki yi mini magana, kar ki tayar mini da hankali mana".
"Sayyid ne ya ɓata"

"Kamar yaya sai ka ce wani zakara?"

"Da gaske nake"

"To ai ban gane ya ɓatan ba ne? Mutumin da yake jinyar ne ya iya tashi ya fita har ya ɓata?"

"Ai kwana biyu jikin da ɗan sauƙi, dan har ya ce mu zo nu gaishe ki" Ta yi maganar ba tare da tana iya tantance me ma take faɗa ba.

"A'a Nana, wataƙila dai wani wajen ya je zai dawo. Tashi ki yi sallar magariba, zuwa anjima a raka ki gidan ko ya dawo"

Nana jin Uwani kawai take yi, ta tashi ta yi sallar magariba, aka yi isha'i. Uwani ta saka Nana a gaba zuwa gidanta, sai dai kamar yadda Nana ta bar gidan wayam babu Sayyid babu dalilinsa.
Nana dai ba ta gaya wa Uwani abin da Ashiru ya gaya mata ba, na ya ga an zo da mota an tafi da shi ba.
Sai wajen goma na dare, hankalin Uwani ya tashi. Ta sanar da samarin gidan halin da ake ciki. Nan suka bazama a cikin Buda yawon neman Sayyid, duk da galibi ma ba su san shi ba, kwatancensa Uwani ta yi musu, suka tafi yawon neman sa, har gurin jami'an tsaro aka kai rahoto.
Sai dai har bayan sha biyun dare, babu wanda ya ji ko ɗuriyarsa.
Uwani ta saka aka rufe gidan, ta ce Nana ta zauna a nan, ko zuwa dare zai dawo.

Nana a ranta ta ce "Wane dare kuma bayan wannan"

Daren ya zame wa Nana dare mafi tsawo a rayuwarta. Damuwa da tunani ya cika mata zuciya. Ba ta tunanin Sayyid zai iya tafiya ya bar ta. Idan kuma da gaske zuwa aka yi aka tafi da shi, to suwaye su ka tafi da shi? Ina suka kai shi, me ya yi musu? Ko dai wani laifin suke aikatawa ba ta sani ba? Amma shi da yake kwance babu lafiya, kullum tana tare da shi a gida, yaushe har yake aikata wani rashin gaskiya da ba ta sani ba.
A haka har aka yi assalatu, a kan kunnenta.

****

Dare malafar rana, kowa ya bika ya shirya maka.

Danƙareriyar mota ce, ƙirar highlander baƙa, take ta kwarara gudu a saman kwalta, tamkar hanyar domin direban kawai aka yi ta.
Gefe da gefen hanyat baki ɗaya babu komai, banda yashin sahara, sai busassun bishiyu jefi jefi. Kasancewar dare ne, wata ya kai kwana goma sha huɗu, ya haska ko ina, ga taurari sun yi wa sararin samaniyar ado.
Titin ta tsakiyar sahara ya ratsa, wadda yashin saharar ya bayar da sassanyan yanayi.

Kallon sa ya yi, daga bisani ya ce "Kilomètre nawa ce ta rage mana ne?"

Direban ya waiwayo ya kalli mai maganar wandaa fuskarsa a rufe take cikin rawani ya ce "Bai fi 95 kilomètre ba"

"Dans  quelques minutes ?? (Nan da wani lokaci?)".

"Bai fi awa ɗaya ya rage mana ba"

"Dole fa mu ƙarasa dai-dai lokacin da aka umarce mu, ni ina tsoron ma kar ya farka. Ka ƙara sauri"

Ya yi maganar yana haska fuskar Sayyid, da yake kwance a jikinsa ya haɗa gumi, cikin wani yanayi kamar bacci kamar suma, sai dai  yadda yake gumi ya nuna a wahale yake baccin, babu in da yake motsi a jikinsa, sai ƙirjinsa da yake ɗagawa yana sauka lokaci zuwa lokaci, numfashinsa yana fita da ƙyar.

Ya kai hannunsa, ya ɗora a kan ƙirjin Sayyid, idan zuciyar sa ta buga sau ɗaya, sai ta jima kafin ta sake bugawa. Sai dai duk bugawar da za ta yi, da ƙarfi take

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login