Showing 24001 words to 27000 words out of 122205 words

Chapter 9 - BUZU BOOK2 COMPLETE 2

18 Jan 2026

634

gangarowa daga cikin idanunsa. Ta ajiye kofin kunun ta rasa abin yi. Kawai rungume shi, ta fashe da matsanancin kuka, sai da ta yi iya yin ta.
Sannan ta cika shi, ta share masa hawayensa.
Ta fara ƙoƙarin ba shi kunun, sai dai tana ba shi, ya haɗiye wani kuma ya zubo.
Ta na yi tana goge masa wanda yake zubowa, ta gama ba shi, ta kama hannunsa su ka je waje, ta taimaka masa ya yi alwala. Ya dawo ya rama sallolin da ta gaya masa ana bin sa. Sai dai ba magana ga hannu a maƙale, da ta kalle shi sai ta ji hawaye ya cika mata ido.
Ganin yana gyangyaɗi a zaune, ya sanya ta saka masa pillow ya kwanta, ta saka hijjabi ta fita.

Tafiya mai nisa ta yi, ta je ta samu wani chemist, bayan sun gaisa ta ce "Dan Allah malam, idan babu damuwa, Bp nake son mu je ka gwadawa mijina a gida"

Ya kalle ta ya ce "A ina ne?"

"Cikin Budu ne, nan unguwar maharba"

"Taɓ gaskiya da nisa gurin nan ba kaɗan ba, ba zan iya zuwa ba sai dai ki je ku zo tare a yi masa"

"Wallahi da zai yiwu, da ba zan zo na roƙe ka ba, yana kwance babu lafiya ka taimaka mini dan Allah"

Ya ce "Gaskiya kin san cajin zuwa gida ma ka yi wa mutum abu daban yake, sai dai idan za ki ba ni dubu biyu"

Nana ta ce "Eh na yarda mu je zan baka in sha Allah" Ya rufe chemist ɗin ya bi Nana.

Su na zuwa gidan, Nana ta shiga ta tarar da shi a zaune ya tashi, ta ce "Sayyid kar ka ga na fita ban gaya maka ba. Na je na samo wani ma'aikaci ne, ya zo ya duba jininka a gani, idan jinin ne ya hau ya sanya hannunka ya shanye, mu tafi Asibiti. Idan kuma ba shi ba ne, sai mu san abin yi." Bai ce komai ba, ta yi wa mai chemist magana, ya shigo ya gwada jininsa.
Ya gwada ya kalli Nana ya ce "Jininsa bai wani hau sosai ba, 140/90 ne" Ajiyar zuciya Nana ta yi. Ta ce "A ganinka wannan hawan zai iya sanya masa shanyewar hannu?.
Ya girgiza kai ya ce "Gaskiya ba na tunanin haka, amma ban tabattar ba tun da ni ba likita ba ne ba. Amma a shekarunaa bana tunanin jinin 140 zai shanye masa wata gaɓa a jikinsa, amma dai ku je Asibiti a ƙara bincikawa"
Nana ta ba shi kuɗin sa, ta yi tai masa godiya. Ta koma ɗaki ta zauna ta yi shiru, tana tunanin ko Uwani za ta tambaya, idan akwai wani mai magani, ta raka su, sai dai ta fasa saboda akwai sauran ɓurɓushin jahilci a tattare su, ba ta son surutu kuma tana tsoron a kai su gurin da ba shikenan ba.

****

Alhaji Fatuhu kuwa kamar yadda ya matsa, sai da aka sallame shi ya koma gida. Gidan nasa ma wani abokin kasuwancinsa ne ya saya, ya bar shi a ciki ya zauna ya bar masa aro.

Sagir yana kwance a kan gadonsa, yana kaɗa ƙafa ya ƙura wa screen ɗin wayarsa ido. Yusra ce zaune sanye da doguwar rigar material, kanta ko ɗan kwali babu, dogon gashin kanta ya sha gyara. Tana ta zuba masa surutu.
Har mamaki yake yi, yadda Yusra ta zama mai ɗan karen surutun tsiya, wanda da ba haka take ba.

"Ya ka yi shiru ne?" Ya wani lumshe ido ya ce "Ina jin ki ai".

"So talk, ka yi magana mana" ta yi maganar tana cika bakinta da guggurun hannunta.

"Ina ga zan shigo Abuja mu haɗu very soon in sha Allah" wata irin zabura ta yi ta ce "Are You serious, dan Allah da gaske?"

"Da gaske nake, zan zo na ganki, amma ki na ganin babu matsala a zuwan nawa? Kar a yi miki faɗa fa, ba zan ji daɗi hakan ba"

Yusra ta ce "Babu wata matsala, ba za a yi mini faɗa ba, ai ba na tare da su Mami, ina gidan Anty Sumayya. Dan Allah ka zo"

Sagir ya yi murmushi ya ce "Kin yi missing ɗina ne?"

Ta gyaɗa masa kai tana murmushi.

"Shikenan, i miss you too, ban taɓa tunanin ma za ki neme ni ba, na za ta ki na jin haushina haryanzu, amma in sha Allah zan shigo, zan sanar miki lokacin da zan shigo na zo na ganki" ya yi maganar yana kashe mata ido.

Shukura ce ta turo ƙofar ɗakin ta shigo, a burkice ya kif wayar yana kallon ta. Ƙarara yanayinsa ya nuna alamun rashin gaskiya, amma ta share shi, ta haye kan gadon ta ja bargo ta lulluɓe jikinta.
Ya matsa kusa da ita yana ɗan shafa ta ya ce "Sweetheart, ya na gan ki kamar a fusace ne? Lafiya dai ko?"

"Lafiya ƙalau" ta amsa a taƙaice. Ɗan shiru ya yi yana tunanin ko dai ji wayar da yake yi ne? Amma a yadda ya santa da azababben kishi, da zargi da ta ji sai ta yi masa magana. Sai dai ya bar abin a haka bai matsa mata da tambayoyi ba gudun kar su yi faɗa.

Tana ankare da take-taken Sagir, na rashin gaskiya. Sai dai ita yanzu ba wannan ne a gabanta ba, bin diddigin mutuwar ɗanta take son yi. Dan haryanzu zuciyarta ta kasa amincewa da natural mutuwa ya yi. Domin haryanzu tana mafarke-mafarke marasa  daɗi da mahaifinta da kuma Doctor Sharif.

****
Aka shiga sati na biyu, Sayyid yana cikin wannan yanayi na rashin lafiya, kuma hannunsa bai saki ba, yana nan a maƙale.
Ga hauka da yake yi tuburan wasu lokutan, wasu lokutan idan ya burkice sai ya shaƙe ta, ko ya hankaɗe ta ƙasa, sai dai ta yi ƙoƙarin kare cikinta. Ko kuma Ya ya ta watsi da duk abin da ya ci karo da shi, a ɗaki ko a tsakar gida. Wasu lokutan ma katangar ɗakin yake duka da kansa. Ya ƙi cin abinci ya ƙi shan magani, ba salla, komai sai dai ta yi masa cikin rarrashi da ban haƙuri. Tun tana jin tsoron ya yi mata wani abin, har ta daina ji, ta zuba wa sarautar Allah ido.
Sannu a hankali ta rage yawan amai, sai dai zazzaɓi da rashin son cin abinci da take yi, hakan ya sanya ta tabattar da cikin jikinta bai fita ba haryanzu. Sai dai ba ma ta cikin nutsuwar da za ta nemi inda Asibiti yake ta je, ta tabattar da halin da suke ciki ita da jaririn saboda tashin hankalin da take ciki.
Yanayin yadda uwani ta lura kamar Nana na ɓoye wani abu, ya sanya ta daina zuwa gidan,ta rage aika yara ma. Sai dai lokaci lokaci, ta kan aika mata da Abinci.
Haka sauran 'yan uwansu na garin ma, su kan aiko mata da sha tara ta arziki saboda su na tausayin Nana, sun san mijinta a kwance yake babu lafiya.
Yawon roro a gona kuwa yanzu Nana ta ƙware, ranar kasuwa ta je ta sayar da abin ta.
Kasancewar ranar Asbar kasuwar garin take ci, sai ta tashi ta yi fanke da sassafe, jikan Uwani Haladu, ya kai mata kasuwa. Ko ta dafa masa zoɓo ta ƙuƙƙula ya tafi da shi.
Idan ta gama komai kuma, ta bi yara gona roro.

Dare ya tsala, amma Nana tana zaune tunkurkur, wuni Sayyid ya yi yana wani irin nishi, ga wannan azababben zafin jiki da yake fama da dhi.
Tana zaune tana tunani, tana jin yadda mararta take motsi, cikin jikinta yake motsawa.
Ba ta da sauran wanda za ta kai kukanta bayan Ubangiji. Ta fara tunanin ƙoƙarin tara musu kuɗin mota, su tafi Nijar, neman danginsa, sai dai idan sun je Nijar ɗin ina za su nufa? Babu tsammani ta ji Sayyid ɗin ya laluba cinyarta, ya kwantar da kansa.
Ta shafa gashinsa ta ce "Sayyid" bai amsa ba, sai dai ya riƙe hannunta. Hakan ya tabattar mata da ya dawo hayyacinsa ne. Haka ta tashi a cikin daren ta tsiyayo ruwan zafi, ta ba shi shayi ta yi masa wanka suka kwanta, ta lulluɓe su da bargo.
Sheshsheƙar kukansa ta ji, duk da yadda ta san ya daɗe yana dauriya, da son ɓoye gazawarsa, sai dai ta ga hakan a idanunsa.

"Sayyid idan ka na kuka, ni kuma ya zan yi kenan? Dan Allah ka daina" ta yi maganar muryarta na rawa. Ta din ga shafa bayansa a hankali, har ya yi shiru, bacci ya ɗauke shi.
Sai dai tun daga wannan, haka aka sake shafe kwanaki biyu, bai sha ko ruwa ba. Dama rashin maganarsa ya daina damunta.
Ga shi yau abin ya tashi sosai, haukan yake yi da gaske. Ta rufe shi a gidan, ta je ta samo gasara a gidan Uwani, ta dawo ta dama masa kunu. Ta nufi ɗakin cike da fargaba tare da fatan ya samu ya sha ko kaɗan ne.
Sai dai ta ji wata irin guguwa ta taso mai ƙarfi.

Jin yadda guguwar ta taso da ƙarfinta, take fatali da duk abin da ta ci karo da shi a tsakar gida, ya sanya ta tashi da azama, ta fara ƙoƙarin rufe ƙofar katakon da take ɗakin. Sai dai tana danna ƙofar guguwar ma na danno ƙofar.

A take ta fara karanto "A'uzubillah, Allahumma inni as'aluka khairiha wa a'uzubika min sharriha. Allahumma inni as'aluka khairiha wa khairi ma fihi, wa khairi ma ursulat bihi, wa a'uzubika min sharriha wa sharri ma fiha, wa sharri ma urisilat biha" take ta ji nauyin da ƙofar ta yi ya ragu, ta samu ta rufe ta, ta juya da sauri ta nufin gurin da yake.

Da fari yana zaune a guri ɗaya ne, amma yanzu Jifa yake da kayan ɗakin da hannu ɗaya, da sauri ta fara  bi tana tattarewa, cike da damuwa.
Cikin siriryar muryarta ta ce "Sayyid za ka ji wa kan ka ciwo, ka saurara ka saurari muryar matarka, ni ce a gare ka, ni ce fa, Husnan ka ce fa" Ta ƙarasa maganar a raunane, duk yadda take ƙoƙarin tare shi ta kasa, domin ta gama firgita da lamarinsa. Tun safe take fama da shi, ya ƙi cin komai, kuma ta kasa sarrafa shi duk rarrashin da ta yi a banza.
Cikin matsananciyar damuwa, hawaye na bin kuncinta ta ce "Ubangiji ka dubi mijin Nana, ka cire masa zafi da raɗaɗin da yake ji, ka saita masa tunani da ƙwaƙwalwarsa, ya yi rayuwa mai cike da nutsuwa da farin ciki irin na sauran mutane" sai kuma ya tsaya cak, ya juyo yana kallonta.
Ta ƙarasa gurinsa, ba tare da fargaba ba ta  riƙo hannunsa cikin nata jikinsa zafi sosai. Ta kalli cikin idanunsa sai taga yana birkice mata yana rikiɗewa kamar ba Sayyid ɗin ta ba, idanunsa har wani hayaƙi yake fitarwa, gaba ɗaya kaminsa sun sauya.
Ta lallaɓa ta zaunar da shi, Ta yunƙura zata tashi, domin ta ɗaukko kununsa ta sake jarraba ba shi, ta ji ya cafko ta yana wani irin sambatu bakinsa na kumfa da dalalar da yawu, da alama magana yake son ya yi mata. Rashin ƙarfin jiki ya sanya ta faɗa jikinsa. Ya ƙanƙame ta sosai, saboda zafin da yake ji, ita kuma jikinta sanyi ƙalau. Ita ma jikinta ya ɗauki rawa, ta lafe a jikinsa ta kwantar da kanta a ƙirjinsa tsawon mintuna, jin ya ɗan nutsu jikinsa ya rage zafin ya sanya ta zare jikinta a hankali.

Ta ɗaukko kofin kunun da cokali, sai wani ɗan ƙaramin tsumma, ta zauna a gabansa ta ɗebo kunun a cokali ta kai bakinsa, sai dai ya tsaya yana bin ta da ido, kamar ya ga baƙuwar halitta, ta buɗe nata bakin, ya kalleta shi ma ya buɗe nasa.
Ta fara zuba kunun a bakinta ta haɗiye, sannan ta zuba masa a bakinsa shi ma. Ya haɗiye sai dai wani na biyo gefen bakinsa, bai haɗiye duka ba. Tana bashi tana goge masa wanda yake  zubowa. Sai da ta tabattar ya ƙoshi, sannan ta goge masa bakinsa. Ta ɗauki kofin ta nufi ƙofa ta buɗe a hankali ta ga an daina iskar, ta fita da kofin ta ajiye, ta tattara abin da guguwar ta watsa sannan ta dawo ɗakin.

Jiki a sanyaye, ta zauna a gabansa tana ƙare wa kyakyawar fuskarsa kallo. Da ƙyar yake jan numfashi yana saukewa.  Ta sanya hannayenta biyu, ta gyara masa gashinsa, da ya rufe masa gefen idonsa, ta saka idonta a cikin nasa, cikin rauni da karaya, idanunta na zubar da hawaye ta motsa bakinta, ta fara magana

"Sayyid, dan Allah ka yi magana ko na ji daɗi, wannan karon ka daɗe ba ka ce mini komai ba. Da na sanya ran ka fara samun  lafiya, amma kullum lamarin nan gaba yake yi. Ka gaya mini wane ne kai? Daga ina ka ke? Ina zan samu danginka da 'yan uwanka, wataƙila kai naka dangin ba za su guje mu ba, za su karɓe mu, tare da sarƙar da ta haɗa ƙaddarorinmu wuri guda, duk da ban kasance ɗaya daga cikinku ba, ni fatana a nema maka magani ka samu lafiya, ba na son ganin ka cikin wannan mummunan yanayin, idan na ci gaba da ganain ka a haka, zuciyata za ta iya bugawa. Dan Allah ka yi magana" Ta yi maganar wasu hawayen na zirarowa daga cikin idanunta.

Ayshercool
08081012143

58
Ya haɗiye wani irin yawu, da yake yi masa zafi a ƙirjinsa, yayi ƙoƙarin ɗago hannunsa na dama, sai ya tuna ya riga ya shanye, ba ya iya komai da shi. Ya buɗe baki da nufin ya kira sunanta, saboda tasiri da kuma ciwon da kukanta yake yi masa a zuciyarsa, amma ya gaza bakin ya karkace yawu ya fara zubowa daga bakin nasa, maimakon kiran sunanta da ya yi yinƙurin yi.
Tana kuka, ta sanya tsumman da tayi amfani da shi wurin ba shi abinci, ta goge masa bakinsa. Ba shi da zaɓin da ya wuce, ba wa hawayen da yake maƙale a cikin idanunsa damar zubowa, ko shi ma ya samu sassauci abin da yake ji.
A hankali ya hura mata iskar bakinsa a fuskarta, a take ta silale ta faɗi a jikinsa.
Ya sanya hannunsa mai lafiya, ya rungume ta, ya ci gaba da kuka. Jikinta gaba ɗaya ya saki.

Ƙaisar ta gani a gurin haɗe-haɗen magungunan sa, yana ta haɗa wani abu a cikin kwalba. Zuciyarta ce take ta azalzalarta, da ƙoƙarin ingizata, sai dai ba ta yi magana ba.

Babu tsammanni, ta ji ya fara magana "Zaɓi ɗaya ya rage miki, a halin yanzu, ko dai ki yadda da abin da na zo miki da shi, ki rungumi ƙaddararki, ko ki na kallo Buzun nan zai mutu, domin ba zai taɓa tuna waye shi ba har abada, muddin Giyaz yana tare da shi. Dan ba na tunanin akwai wanda zai iya raba shi da shi. Idan har bai iya tuna waye shi ba, shikenan kin ga ba ki da wata makoma. Abu ɗaya zai sanya a wannan karon na bar miki abin da yake cikinki, duk da ba ni da tabbacin zai zama mai cikakkiyar lafiya ko akasin haka, Giyaz da muƙarrabansa sun riga sun fara taɓa shi a cikin ki. Kin san meyasa ban ƙarasa lalata wannan cikin ba?" Bai jira ta ba shi amsa ba ya ce "Saboda zan so na ga yadda za ki yi, a lokacin da ɗan zai amsa sunan shege, kuma ba za ki iya hanawa ba, domin ba ki da hujjar kare kanki. Idan Buzun nan ya rayu bai san waye shi ba, ga kuma nakasa. Idan kuma ya mutu suwaye dangin baban ɗan ki? Daga ina yake? Suwaye ahalinsa? Kin san ku a jinsinku na bil'adam da uba ake ado ba riga ba. Babu wanda zai damu da wacece ta haifi mutum, amma za a damu da waye ubansa meye nasabarsa? Tun da ki ka zo garin nan, zuriyarmu suke alwashin yadda fansar su za ta kasance a kan ki. Kafin zuwa wannan ƙadamin babu abin da ban gaya miki ba, na gargaɗi. Dan haka dabara ta rage ga mai shiga rijiya"

Cikin kuka Nana ta hau girgiza kai ta ce "Ba zan yi bori ba Ƙaisar, ba zan yi shirka da Allah ba. Babu tsanani ko wahalar da za ta sanya na rabu da imanina. Amma na rasa gaba na rasa baya, ba dan ina neman taimakon ka ba, ko ka kawo mini ɗauki ba. Na san Ubangiji Allah shi zai taimake ni.
Amma dan zatin Allah idan ka na da hannu a ciwon Sayyid, ka yi mini rai ka rabu da shi, shi ne kaɗai duniyata. Ina matuƙar tausayin sa, ban damu da jinya da nake yi ba, wahalar da yake sha ta isa haka. Idan kuma laifikan zuriyarmu ne suke shafar sa, dan Allah ku yi haƙuri ki ƙyale shi haka"

Cikin sautin muryarsa mai ban tsoro, da ya kan yi amfani da ita, idan ya so razana ta, ko yi mata magana mai muhimmanci  ya ce "Na sha gaya miki na maimaita miki, daga lokacin da ki ka fara bani umarni, kin yadda kin amince da buƙata ta ne. Ba ni da hannu a ciwon mijinki, kuma bai ya cikin zuriyar ku, sai dai ƙaddara mai ƙarfin gaske, ta haɗa ku tarayya guri guda. Amma muddin ki na son ya warke daga wannan rashin lafiya, ba ma iya haka ba, ya tuna waye shi, sai kin karɓi ƙaddararki.".

Nana ta sake marairaicewa ta ce "Ba zan iya shirka ba, ba zan iya zama 'yar bori ba. Zan jure jarrabawata komai zafinta amma ba zan yadda rasa imanina ba"

Ƙaisar ya ce "A cikin biyu dole abu ɗaya ya faru, tunda kakaninki su suka ƙyanƙyashi wannan matsalar. Na yi iya ƙoƙarina gurin dakatar da ita a wancan lokacin, amma ta sake tasowa a wannan karon. Dole a cikinku ɗaya zai warke ya rayu ɗaya ya mutu a haka, dan babu alamar Giyaz zai sassauta wannan mummunan ƙudirin nasa a kan zuriyar ku. Gefe ga aikin da ya karɓa yake yi a akan mijinki, ko dai ki ci gaba da rayuwa da shi, laifukan ku na shafar sa, ko kuma ki yarda ki karɓe ni a matsayin hadiminki ki yi abin da nake so, ni kuma na san yadda zan yi da Giyaz, na baki maganin da mijinki zai warke"

"Ta yaya? Me yasa sai ni? Me yasa ni zan biya zunubin da lokacin da aka aikata shi ba na nan, zunubin da zamanin da aka aikata shi, ya yi nisa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login