Showing 117001 words to 120000 words out of 122205 words

Chapter 40 - BUZU BOOK2 COMPLETE 2

18 Jan 2026

633

kayan ta buɗe jakar sarkin baka ta watsa takardar da zoben ta rufe ta ajiye a cikin kayanta.
Bayan sallar magariba aka sanar mata baƙin Imam sun iso, su na can sashin karɓar baƙin sa wanda ɗaki ne a can wajen lambun gidan.
A kwanduna ta shirya kulolin Abincin, ɗaya daga ma'aikatan gidan, ta taya ta kai wa.
Su na zazzaune a ɗakin, gaban su shaƙe da kayan marmari da uban soyayyen nama.
Duk wannan Imam Imam ɗin ne, gaba ɗaya zaune a gurin.
Ayabar hannun Sayyid ta kalla, da ya kai bakinsa ya gutsura fuskarsa ɗauke da murmushi. A take ta ga jini yana bin bakinsa, ayabar ta koma baƙa ƙirin, wasu abubuwa masu tsini tamkar ƙayoyi suka tsiro a jikinta.

Ayshercool
08081012143
77

Rikicewa ta yi, amma ta fara ƙoƙarin daidaita nutsuwarta dan ta san idan ta yi wani gangancin a gurin, babu lallai ta sha ta daɗin rai duba da girman mutanen da suke gurin a zaune.
Ganin ta tsaya ta zuba masa ido, ya sanya ya sauke hannunsa a hankali yana kallon ta shi ma.
Ta ƙarasa shigowa a hankali ta ajiye musu kwanukan abincin.

Zuba mata ido suka yi, gaba ɗaya suka yi shiru daga hirar da suke yi.
Ta ce "Shugabana, ga abincin ko zan jira ku duba idan da abin da bai yi ba?"
Ya girgiza kai ya ce "Za ki iya tafiya"
Sai dai ta kasa tashi, ta ci gaba da rarraba ido.
Ya sake cewa "Za ki iya tafiya"
"Dan Allah ka taimaka mini da ayabar hannunka, yunwa nake ji"

Imam Omar ya ce "Imam Hammad, wai wace ce wannan ɗin? Ta san waye kai kuwa abin hannunka za ka ba ta?"
Ya kalli ayabar ya kalle ta, bai kai ga yin magana ba, ta saka hannayenta biyu ta miƙa masa.
Tamkar soko haka ya miƙa mata ayabar, ba tare da musun komai ba.
Ya ce "Ga wata nan ki ɗauki yadda za ta ishe ki"
Ta girgiza kai ta ce "Wannan kawai ta ishe ni, na gode sosai da sosai"
Duk su ka bi Nana da ido, wasu cike da takaici, wasu kuma mamakin tsaurin idonta, duk da ba abin mamaki ba ne sosai, tun da ba ta san irin girmansu da matsayinsu ba, kasancewarta bare ba ƙabilarsu ba, kuma ba 'yar ƙasarsu ba.

A hankali ta saci kallon hannayensu, sai ta gan su sanye da zobunan nan irin na hannun Sayyid da ya ɗauka ya bata.
A take ta koma gefe ta cinye ayabar, sannan ta yinƙura ta tashi.
Imam Asad ya fara masifar wace mahaukaciyar haka, da za ta zo ta yi musu wannan rashin hankalin, su zuba ido su na kallonta.
Hammad ya ce "Ina mai baku haƙuri, baƙuwa ce a cikin lamarin gidan mulki, ku yi mata afuwa"
Nana tuni ta fice daga ɗakin, aikuwa fitarta ke da wuya, jiri ya fara ɗibanta, bango ta dafa tana bi a hankali, sai dai kan ta kai inda take so ta yanke jiki ta faɗi.
Faɗan Ƙaisar ne ya sanya ta buɗe ido, a matuƙar galabaice.
"Waye ya ce da ki ka karɓa ki ci? Kin san abin da aka yi a jikin ayabar? Ban da na riga na buɗe miki ido ki na ganin abubuwa, da ba zan sake bari ki ga komai a kansa. Sai kin kashe kan ki a banza a kan mutumin nan, gaba ɗaya kin ƙarar da ƙarfinsa a kan ki, wanda ko tabbacin idan ya tuna ki zai miki irin wannan son ba ki da shi"
Nana dai kasa magana ta yi, saboda yadda jikinta yake a mace, duniyar take juya mata.
Ɗaga bakinta ya yi ya zuba mata wani abu mai kama da turiri, ta yi wani yinƙuri ta hau amai ta hanci da bakinta.
Ba ƙaramin galabaita ta yi ba, jin yadda ƙayoyin da suka tsiro a jikin ayabar su na sukar ƙirjinta gurin yinƙurin aman da ta yi.

Cikin fusata mutumin yake magana, "Wane irin wawanci ne haka da shirme da rashin hankali, ta yaya zamu shirya abu ka je ka bari ya ɓaci?"

Cikin damuwa matashin ya ce "Wallahi Tafawa ba laifina ba ne ba, dan har ya fara ci wata yarinya ce ta hana shi ci, wai ya ba ta yunwa take ji"

"Wace yarinyar ce a kaf faɗin Agadez za ta je tsakiyar ku, har Imam zai ci abu ta ce ya bata? Ɗaya daga cikin mugwayen ɗabi'unsa kenan da ya sanya yake zubar da kimar ku a idon mutane maƙasƙanta, har su samu zarafin raina ku. Ban da raini da wulaƙanci har baiwa ta ga abu a hannun Imam na ƙasar Agadez ta ce za ta ci."
Ya buɗe baki zai yi magana ya ce "Ka ga tashi ka bani guri ni kafin na mangare ka" Haka ya ja bakinsa ya tashi ya fice jikinsa a sanyaye.

*****

Alhaji Zailani ne a zaune a falon Hajiya Sa'a, ya je yi mata ta'aziyyar mutuwar Abba.
Ya numfasa ya ce "Wai dama Abban ba shi da lafiya ne?"
Ta girgiza kai ta wassafa masa dukkanin abin da ya faru.
Cikin kaɗuwa yake jin bayanin nata. Ya ce "Ban da ke Hajiya Sa'a, ina ke ina gayyato yarinya da rana tsaka ki janyo ta jikinki, ga shi ta zame miki masifa, haba Sa'a. Ke kin san ba kowa a ke fallasawa sirrin ƙungiya ba, Allah ya kyauta, ya yi mata gaisuwa ya tafi.

*****

Hammad tun bayan tafiyar sauran 'yan uwansa yake tunani daban-daban a ransa.
Tuni aka saita masa wayarsa, ya ci gaba da amfaninsa da ita.
Wayewar gari yana ta jiran Abinci amma shiru, ya gaji da jira saboda yana jin yunwa, ya tafi ya tashi Asal da take ta bacci.
"Imam lafiya kuwa?"

"Ba a kawo mini Abinci ba, ina jin yunwa zan fita"

Kamar ta yi tsaki, saboda ta ji daɗin baccin, haushi ya kama ta, tare da tunanin uban abin da ya hana Nana tashi ta yi masa girki ko ta makara haka.
Ga shi duk hadiman sashen ta kore su, dan haka ta tashi da kanta, ta fita.
A zaune ta tarar da Nana ta jingina da bango, idanunta duk sun faɗa kamar ta kwana tana amai da gudawa.
"Wani wulaƙancin ne ya sanya ba ki tashi kin yi wa Imam girki ba, har ki ka saka na biyo ki nan?"

Nana ta numfasa ta ce "Ba ni da lafiya ne"

"Ba ki da lafiya kuma Imam ba zai ci abinci ba? Kin san ba kowane Abinci yake ci ba"

Wani malulun takaici ya ƙule Nana, wato lafiyarta ba abin da yake gabanta ba ne, kawai fatanta ta yi wa mijinta girki tun da ga baiwa.

"Magana nake yi miki kin yi mini shiru"

"To me zan ce miki, ba ni da lafiya, ai ban taɓa ƙin yin girki ba. Ko wani abu da ki ka saka ni ba, amma yau ba ni da lafiya babu abin da zan iya yi. Idan ke ba za ki yi mini uzuri ba, ki gaya masa kukunsa babu lafiya na san, shi zai iya yi mini uzuri"

A hasale Asal ta buɗe baki za ta yi magana, Nana ta yi mata wani irin kallo, da a dole ta haɗiye maganganun da ta yi niyyar caɓa wa Nana.
Ta haƙura ta juya ta fita, tana tunanin me ta ji ne ko ta gani, ta kasa yi wa Nana rashin mutunci.
Tana komawa ya kalle ta ya ce "Ina Abincin?"

"Wai ba ta da lafiya"

"Me ya same ta?" Ta girgiza kai jiki a mace ta ce "Nima ban sani ba"

Ya so sake wata tambayar, amma sanin halin Asal ya sanya shi ta shi, zai fita.

Ta ce "To ina za ka je ba ka karya ba?"

"Zan samu abin da zan ci, zan je na ga Mahmoud ne" Daga haka bai kuma cewa komai ba ya fita.

Bakin Imam Hammad fal maganganu kamar yadda bakin Mahmudu yake fal maganganu, amma kowanne ya kasa furta wa kowa.
Hammad ne ya numfasa ya ce "Mahmud ina son na koma kan ayyukana, amma Sultan ya ce mini na dakata, akwai abubuwan da nake son yi da yawa."

Mahmoudu ya ce "To ka yi haƙuri, wataƙila akwai dalilin da ya sanya ya ce ka dakata tukuna"
Ya numfasa ya ce "Haka ne, wai yaushe za ka shigo gida ne?"

Ya girgiza kai ya ce "Ba na son shiga gidan nan naku"

"Saboda me?"

"Kai ma ka sani ai"

Imam ya ce "Ban san komai ba. Jiya Imams sun kawo mini ziyara. Ranar Lahadi za mu yi zagayen raƙuma da shan shayi, ka zo mu je tare"

"Imam, ka na manta waye ni, da ƙoƙarin kai ni matsayin da Allah bai kai ni ba, ni dai dan Allah ka yi haƙuri"

"Mahmoudu, idan ba kai ba wa ka ke so na janyo jikina? Ka san komai fa? Shikenan haka ni zan zauna?" Yayi maganar muryarsa ɗauke da rauni.

"Haba jarumin shugabana, ka na fa da wanda ku ka shaƙu, ku ke da kusanci tsakaninku sosai da sosai"

"Waye?" Ya yi maganar yana kallonsa.

"Zan haɗa ku kwanan nan, aure zan ƙara yi maka kwanan nan, ka na son 'yar Nigeria?"

Ƙanƙance idanunsa ya yi yana kallon Mahmoudu. Ya ce "Ga ka nan ga Asal ai"
"Ahh yi haƙuri, kar ka gaya mata sai ta saka a fille mini kai"

Hammad ya yi murmushi yana gyara zamansa.

Sai da Nana ta shafe kwana uku ba ta aikin komai, haka kurum Imam ya ji abin ya tsaye masa ya dame shi, ko ya yi ƙoƙarin mantawa sai ya kasa. Kwanakin nan uku kame-kame kawai yake yi gurin cin abinci, duk abin da zai ci sai ya ga kamar abin zai cutar da shi. Ga uwa uba rashin ɗanɗanon abinci da ba ya ji gaba ɗaya.

Yau da Nana ta lallaɓa ta fito, ta ji ana ta zancen hawan zagayen da za a yi a kan raƙuma.
Har ya yi shirinsa zai fita, ya tarar da Abinci a falo.
Cikin zaƙuwa ya ƙarasa ya buɗe, tabbas ƙamshin girkinta ne. Wani murmushi ya suɓuce masa cike da farin ciki.
Sai dai sam ba su haɗu ba.

Har yau jikinta babu ƙwari sosai, bayan fitarsa ta shiga ta gyara abin da za ta gyara, kawai ta nemi guri ta zauna, tana hutawa wani irin bacci ne ya ɗauke ta a gurin.
Ba ta jima da fara baccin ba, sai ga ta a Libraryn Ƙaisar.
Waiwaye ta fara yi taga ta ina za ta gan shi, sai dai ba ta gan shin ba, sai wata guguwa da ta taso, ta watso mata littafin nan da ta ce ba za ta karanta ba. Ta kalli littafin a gabanta amma ba ta motsa ba, ba kuma ta ɗauka ba. Kawai littafin ya buɗe kansa da kansa, sai mudubin nan ya haska inda ya buɗe ɗin.
Sayyid ta gani a tsaye a cikin sahara ana ta harbo masa kibiya ta ko ina, Sultan ta ta gani yana ƙoƙarin tare masa, shi ana samun sa da kibiyar. Har ya fara gazawa aka fara samun Sayyid.
Ya na tsaka da tarewar aka janyo shi aka nufi wata wuta da shi, da cin ta yake gwanin ban tsoro. Ba ta iya ganin fuskar wanda yake jan na shi, saboda ya rufe fuskarsa da rawani.
Gaba ɗaya Nana ta gigice ta rintse idanunta tana addu'a kar Allah ya ba wa mutumin nasara, can jin shiru sai ta buɗe idonta a hankali.
Sai ta daina ganin wancan lamarin, sai wata taguwa da ake ta ɗurawa wasu abubuwa.
Sayyid na zuwa ya kama taguwar ya hau, yana hawa ta din ga walagigi da shi, ta nufi kan wani rami da shi. Zumbur Nana ta tashi, tare da miƙewa tsaye a falon. Zuciyarta sai bugawa take yi da sauri.
Waje ta yi da wani irin hanzari, ta nufi inda ake shirya raƙuman da za a yi hawan da su.
Raƙuman duk jajaye ne, an yi musu wani irin ado, ga su ƙosassu.
Gaba ɗaya ta ji ba ta yarda da lamarin ba, ta juya ta sake kwasar hanya ta koma sashen su.
Tana zuwa ta ci karo da shi ya fito, sanye da makamanciyar shigar da ya shigo ɗakinta bayan auren su.
Takobinsa na soke a gefen ƙugunsa, babbar rigar jikinsa ta sha aiki.
Kallon Nana ya yi, fuskarta ta nuna rama sosai da sosai.
Nana so take ta yi masa magana amma yana tare da Asal da ta sha kwalliya ita ma, sai hura hanci take yi.
Gaba ɗaya yanayinta ya nuna masa a rikice take, kuma magana ce a bakinta.

Har za su gifta inda Nana take ya ce "Sayyid excuse me"

Asal ta waiwayo ta kalli Nana jin ta ce masa Sayyid maimakon Imam.

Ya kalli Asal ya kalli Nana, sai kuma ya yi taku biyu ya matsa daf da Nana, ya sunkuyo daidai tsawonta.
Gaba ɗaya sauran barorin da suke gurin ma zubo musu ido suka yi.

"Dan Allah kar ka hau Taguwar nan" Ta yi maganar cikin tsoro muryarta har tana rawa.
Ya ɗaga idonsa ya saka a nata, wanda hakan ya rikita ta, tamkar ba ta taɓa saninsa ba.

Bai ce mata komai ba, ya miƙe ya yi gaba. Asal ta bi shi cikin fushi tana tambayarsa "Wai me ta ce maka?"

Ya numfasa ya ce "Da tana son ki ji, ba za ta zaɓi ta gaya mini ba".

"Imam ban gane ba, mene ne abin da ba za ta faɗa kowa ya ji ba?"

"Ai kin san duk wanda yake ƙarƙashina, ina ba shi lokacina na saurare shi. Kar ki manta mutumin da yake da Asal doka ba ta ba shi dama a kan wata wadda ba ƙabilarsa ba, mussaman baƙar fata, kin fi kowa sani na, ki daina saka wani abu a ranki dan Allah"

Ya yi maganar daidai lokacin da suka ƙarasa gurin. Daga nesa Nana take hango an ba shi shayi a kofi, ya karɓa ya shanye, an sake zuba masa ya karɓa ya sha.
Aka cika gurin da kaɗe-kaɗe, juyi suka din ga yi tare da sauran 'yan uwansa Imam, su na wasa da takubbansu, gwanin burgewa. Duk da tashin hankalin da Nana take ciki, sai da abin ya ƙayatar da ita.
Aka jero raƙuman nan, suka din ga kama su su na hawa.
Nana gabanta ya tsananta faɗuwa, cike da ƙwarewa ya kama raƙumin nan ya haye.
Idonsa suka sauka a cikin na Nana, fuskarta ɗauke da damuwa, ya lumshe idanunsa ya saita akalar raƙumin nasa, ya wuce gaba sauran suka bi bayansa.

Mutane suka rufa musu baya, suka kama hanyar barin gidan.
Jiki a sanyaye Nana ta koma.
A tsaye ta jingina a gurin girki, tana tunanin abin da ka iya biyo bayan hawan Raƙumar nan da ya yi.
But Asal ta faɗo cikin huci, Nana ko motsawa ba ta yi ba sai bin ta da kallo kawai da ta yi.
Har gabanta Asal ta zo tana huci "Uban me ki ka gaya wa Imam, kuma saboda me za ki din ga kiransa da Sayyid? Ban yi miki gargaɗi a kan sa ba?"

Nana ta kalle ta, ta ga kar ta yi wani abun da zai sanya ta kore ta a yanzu, dan haka ta sassauta murya ta ce "Haba ya shugabata, Sayyid da Imam duk abu ɗaya ne ai, yana nufin shugaba, mu a Nigeria Sayyid muke cewa, kema idan ki na so sai na kira ki Sayyada. Kuma me Sayyid zai yi da baƙar mace 'yar Nigeria, ai ramin kura sai 'ya'yanta. Kawai ne nemi afuwarsa ne a kan rashin samun gudanar da aikina da na yi, a kwanaki da suka gabata, saboda shi ne ƙa'idar gidan sarauta.
Ki yi haƙuri iya matsayina da aikina nake tsayawa."

Asal ta numfasa tana huci, duk da hankalinta ya ɗan kwanta.

"Shikenan na ji, daga yanzu za ki bar ɗakin da ki ke, za ki koma ɗakin hadimai da ke tsakanin sashen Imam da nawa.
Sannan akwai gurin girki a gurin girki a gurin, yadda za a din ga sauƙaƙa miki, sai dai babu ke babu fitowa a duk lokacin da yake nan, muddin ba abinci ki ka kawo masa ba, kuma ba gyaran sashen za ki yi ba. An dawo da ke sashen nan ne, domin ƙara tabattar da tsaron abincin da Imam zai ci"

Nana ta jinjina kai ta ce "In sha Allah, na gode sosai da sosai"

"Ki hanzarta, ki kwaso kayanki ki mayar can, a yau ba sai gobe ba, ku yi magana da Balaraba ta kai ki"

Nana ta risuna ta yi wa Asal godiya, haka aka yi, a ranar ta kwashe kayanta ta mayar can ɓangaren, barorin gidan na ta ƙara mamakin, yadda a ke ɗaga likkafar Nana baƙuwar haure sama da su.
Nana kuwa murna ta din ga yi, ganin tana ƙara samun kusanci da Imam, ta san addu'a da take yi ce Allah yake taimakonta, kuma tana fatan Allah zai yanke mata wannan wahalar nan kusa.
Fita ta yi da nufin ta kwaso kayan wancan ɗakin girkin ta dawo da su nan, ta ga mutane na kaiwa da komowa a sashen.
Wani ta gani a cikin mutanen fuskarsa rufe da rawani, amma ta ga kamar ta san shi ta taɓa ganinsa, kamar ta bi bayan mutumin, sai ta ji ana faɗin Imam ne ya faɗo daga kan Taguwarsa.!

AREWABOOKS

Nana ta rasa wa za ta nufa ta samu cikakken bayanin abin da ya faru. Ta san za a rina, tun da ta ga abin nan kuma ta din ga ji a jikinta, ta san wani abun sai ya faru.

A can ɗaki kuma, sannu Asal ta din ga jera masa, ya jinjina mata kai kawai.
Ya lumshe idanunsa yana tuna yadda Nana ta roƙe shi kar ya hau Taguwar.

"Wace ce ke?" Ya furta a hankali.

Asal ta ce "Magana ka ke yi ne?" Ya girgiza mata kai alamar a'a.
Tun da ya hau kan Taguwar nan yake jiri, duk yadda ya ƙwarara jikinsa, da ƙoƙarin sarrafata ya kasa, dan daina gani ya yi gaba ɗaya sai jin sa ya yi ya zamo ƙasa.
Ya yi ajiyar zuciya yana sauke numfashi.

"Imam na saka ta dawo ɗakin Hadaimai kamar yadda ka buƙata, ko za ka ci wani abun a kawo maka?"

Ya girgiza mata kai alamar a'a.

"Ina ne yake yi maka ciwo to?"
Ya yinƙura ya tashi ya ce "Babu ko ina salla zan yi"

Yana tangaɗi haka ya shiga ya yi salla, ya sake kwanciya.
Nana na ta kai komo falon babu kowa, tana son ta san halin da yake ciki amma babu wanda za ta tambaya.

Wata tawaga ta ga sun shigo sashen, kallo ɗaya ta yi masa ta gane Sultan, tana son fita tana jin tsoron kar ta yi laifi, haka ta tsaya tana hangen abin da yake faruwa.
Asal ta fito cikin hijjabi suka gaisa, ta yi wa Sultan jagora zuwa cikin ɗakin.

Da hanzari ya nufe shi yana faɗin "Hammad, tashi maza a tafi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login