Showing 30001 words to 33000 words out of 122205 words

Chapter 11 - BUZU BOOK2 COMPLETE 2

18 Jan 2026

569

hanata.
Da kansa littafin ya buɗe, a daidai shafin da tsaya da karantawa wancan karon.
Jiki na tsuma ta ci gaba da karantawa.

Jama'ar da suke gurin girkar, wasu suka watse a dalilin gakin sarkin Aska ya bayyana a gurin, kar ya gansu ya hukunta su. Bayan musayar yawu a tsakanin Duna da uban duƙusa, Sarkin Baka ya yi girgiza ya ɓace.
Uban duƙusa ya saka aka ɗauki kakan Lanti, a ka kai shi gida. Ita ma Lantin tana zuwa gida ta faɗi ƙasa.
Ba ta sake farfaɗowa ba sai washegari. Sai dai bayan farfaɗowarta, ta tarar da kakanta cikin mawuyacin hali, wanda hakan ba ƙaramin ɗaga mata hankali ya yi ba.
Cikin damuwa mijinta ya ce "Lanti sai da na gaya miki ina jin tsoron wannan abun, ki ka ce babu komai, ina tsoron kar rikici ya ɓarke a garin nan"

"Babu rikicin da zai ɓarke, ka kwantar da hankalinka, ni dai kawai fatana na kawo ƙarshen Sarkin Aska."

Kakan Lanti da ya yi tari, sai aman jini, dama ga jikin tsufa, ya zamana ko tashi baya iya yi saboda buguwar da ya yi. Kwanaki huɗu da faruwar lamarin, Lanti tana yi masa hayaƙi da ganyen ɓaure. Ya riƙo hannunta ya ce "Ya ke jikata, ki sani na yi miki Girka da babban Aminina, kuma ya ɗaukar mini alƙawarin ba ki duk wata kariya, da zama mai hidima a gare ki, kuma ya yi alƙawarin bawa zuriyarmu kariya daga cutarwar miyagun Aljanun cikin su. Dan haka a duk lokacin da ki ke buƙatar ganawa da shi, ki sanya kayan saƙin ki, ki ɗaura gurunki. Sai dai kar ki kira shi a guri mai ƙazanta, ba ya son zama a guri mai ƙazanta, kuma ba ya zama a guri mai najasa. Sannan 'yar ki Duna ne ya shafe ta, kuma ga wannan abu da ya faru, abu ne mawuyaci ta warke, sai dai idan uban duƙusa ne ya samo mata magani. Ni na san ba zan rayu ba, Duna ya riga ya yi mini illa, dan haka ki kula da mutanen Buda. Yana gama faɗin haka wuyansa ya karye. Lanti ta fashe da kuka, ya buɗe baki yana son ya yi mata magana amma ya kasa, har ya daina motsi ya mutu.
Nana ta yi kuka ba kaɗan ba, da mutuwar Kakanta.

Ƙaisar ne a tsaye a kan wani dogon tsauni, gabansa kuma Giyaz ne, da yake kamannin da shi sak, tamkar ya yi kaki ya ajiye.

"A kan me za ka je ka aikata wannan shirmen da ka yi? Ko har ka manta da cewar fansarmu za mu ɗauka a kan abin da mutanen nan suka yi mana?"

"A'a Giyaz, mutanen nan ba su ne ainihin waɗanda suka fara rigimar nan ba, kuma ɓarnar da aka yi musu ta yi yawa. Babu amfani rashin zaman lafiya da tashin hankali. Kuma ka duba irin cutarwar da abokinka Duna ya haɗa kai da sarkin Aska yake yi wa mutanen garin nan. Yakamata a zauna lafiya, haɗa kai da bil'adama ana cutar da jinsinsu ba zai haifar da ɗa mai ido ba."

"Rufe mini baki Ƙaisar" Ƙaisar ya kalli mahaifinsa jin ya kira shi da sunansa na yanka, saɓanin sunan da yake masa kara da shi, na uban duƙusa wanda da shi ake kiransa saboda kara ga mahaifinsa. Dan duk cikin bataliyar 'ya'yan da ya haifa, ya fi ƙaunar sa. Ya ɗora da cewa "Kar ka manta abin da suka yi wa Mahaifina Jaddul Jinn wanda yake kaka ga duk wani Aljani da yake nahiyar nan, da yadda ake girmama shi, sai mene ne dan a azabtar da su. Dan mene zaka hau kan bil'adama a matsayin bawa, duk da kasancewar ka ƙasaitaccen matashin aljani da ake ji da shi a jinsinmu" ya yi maganar cikin ɗaga murya, muryarsa na amsa kuwwa a ilahirin dajin.

"Zaman lafiya da kwanciyar hankali, mu rayu mu da su babu cuta babu cutarwa. Lalata musu amfanin gona, sanya musu rashin lafiya da makamantansu duk ba zai sanya ku huce ba, tun da waɗanda suka yi laifin na sun mutu basa nan"

"Uban duƙusa yanzu ka fifita bil'adama a kan ni mahaifinka?"

"Ko ɗaya, sai dai ka san muna mutunta yarjejeniya. Mun yi yarjejeniya da abokina, zan ci gaba da bawa zuriyarsa kariya, zan kula 'yar sa zan din ga kawo mata magunguna tana bayarwa. Kuma ya yarje mini ci gaba da yi wa zuriyarsa hidima, da bayar da magani ta hanyar waɗanda aka haifa da tauraron 'yar sa Lanti"

"Ƙarya ka ke yi Ƙaisar. Ɗana ba zai zama bawa ga gajiyayyun halittu kamar bil'adama ba, ka sani yadda suke yi mana kallon halittu maƙaryata, haka su ma ba su da cika alƙawari. Ka tuna kai makaranci ne, manazarci kuma marubuci. Ka karanta litattafai da ni kaina ban san adadinsu ba. A ɗakin karatun ka akwai litattafan da aka rubuta dubbanin shekaru kafin zuwanka Duniya. Ka yi yawace-yawace a Duniya domin neman abubuwan rubutawa, kuma ina da tabbacin ka karanta tarin kashedin da magabantanmu suka yi mana a kan bil'adama. Dan haka ba zan bari iliminka da soyayyar da nake yi maka, su ƙare a kan yi wa biladama hidima ba, ba ma su su yi maka ba. Sai dai ka zaɓa, zama da mu ko kuma hidima ga bil'adama!"

Ayshercool
08081012143
59

Ƙaisar ya ce "Haƙiƙa kai Babana ne, ka so ni mai sonka ma ya so ni. Kuma na san ni ne ruhi mafi soyuwa a gare ku. Ka tallafawa burikana da bani damarmaki a matsayina na ɗanka. Sai dai ka tuna, na kawo girman da zan iya yankewa rayuwata hukunci. Kamar yadda ka faɗa; na karanta kashedin da aka yi mana a litattafan magabata, na yi yawon neman labarai a duniya, amma babu inda na ga an ci riba da tashin hankali da yaƙar juna. Kuma Aljani bai taɓa nasara a kan bil'adama ba, komai tasirin cutarwar da ya yi masa.
Na yi abota da bil'adama, na karanci wasu abubuwa masu muhimmanci dangane da zamantakewar su. Kuma ina son na yi amfani da ilimina na sanin magunguna, na sanar da wasusn su, domin samun waraka daga wasu cututtukan da mu ne muke haddasa musu su.
Dan haka ina mai baka haƙuri, na riga na yi alƙawari ba zan iya warwarewa ba. Sannan ba a banza zan yi wa zuriyar sarkin baka wannan aiki ba. Kamar yadda na gaya maka, sun sadaukar mini da duk wani mai irin tauraron Lanti, domin gudanar da burina na son yaɗuwar ilimin bayar da magani"

Cike da ƙunar rai Giyaz ya numfasa ya ce "Shikenan, ka yi abin da ka ke so, amma ka je, na sallama ka daga cikin zuriyaramu, kar ka sake danganta kanka da mu" daga haka Giyaz ya ɓace.

Lanti ta damu da mutuwar kakanta, sai dai ba a rufa sati ba, 'yar ta ma mai larurar shan Inna ta mutu. Ta shiga tashin hankali sosai da sosai, tamkar za ta zauce.

Hankalin Sarkin Aska kuwa ya yi mummunan tashi, bayan da Duna ya sanar da shi cewar, da Uban duƙusa aka yi wa Lanti girka. Kuma cutar da Uban duƙusa ka iya kawo fitina da tashin hankali a tsakanin su kan su Aljanun. Duk da zafin bil'adama da Giyaz yake ji a kan abin da suka yi wa mahaifinsa, amma ba zai lamunci kowane Aljani ya taɓa masa ɗa ba.
Sarkin Aska ya ji baƙin ciki ba kaɗan ba,  da abin da Duna ya gaya masa, bayan tabattar da cewa ya samu abokiyar hamayya a garin.

Ƙaisar ya fara bawa Lanti magunguna, ta fara aikin bayar da magani a garin. Babu nasiha da rarrashin da ahalin Ƙaisar ba su yi masa ba, a kan ya janye daga harkar taimakon biladama, amma fafur ya ƙi ya ce ba zai daina ba. Akwai kyakykywar fahimta a tsakanin Lanti da kuma Ƙaisar.
Lanti ta kuma samun juna biyu, ta haihu sai dai ɗan da ta haifa, ba ta haife shi da irin taurarinta ba.
Aka shiga zazzafan takun saƙa, a tsakanin Lanti da Sarkin Aska, dan mutane suna tururuwar karɓar magani a gurinta. Domin ita ba ta tsauwwala wa mutane, kuma ba ta neman su kawo wani abu da ya fi ƙarfinsu. Duk da Giyaz ya sallama Ƙaisar, amma hakan bai bayar da damar, 'yan uwansa su iya cutar da shi ba.
A lokacin sai zuriyar Jaddul Jinn wasu suka goyi bayan zaman lafiya, kamar yadda Ƙaisar ya yi, wasu kuma suka zauna a kan bakar su na lallai sai an ci gaba da cutar da bil'adama da duk wanda ya fito daga wannan tushe na Buda.
Sarkin Aska ya ci gaba da jan Aljanu, yana sadaukar musu da jini, yana amfani da su ta hanyar tsafi, da kuma alwashin taimaka musu a duk lokacin da suke buƙatar hakan.
Cike da baƙin ciki, Giyaz ya zura wa Ƙaisar ido, babu yadda ya iya da shi.
Ganin abin da Sarkin Aska yake ci gaba da yi, duk a ƙoƙarin sa na mamaye garin a ci gaba da tsoron sa, ya sanya Lanti ta ƙara zage damtse a kan harkar bayar da magani da laƙantar hanyoyin da za ta kawo ƙarshen Sarkin Aska.

A haka ta haifi yara biyar maza, duk babu mai irin tauraronta, gaba ɗaya abin ya damu Ƙaisar, ganin babu wanda zai iya gadar ayyukan Lanti.
Sai dai a jininsin mutane ma, 'yan uwan Sarkin Aska ba sa ƙaunar abin da yake aikatawa na zaluntar mutane.
Wata jakar fatar damusa, Ƙaisar ya sanya Lanti ta fara haɗawa, wadda da ita take burin kawo ƙarshen Sarkin Aska, saboda babu irin mugun hari da yinƙurin da Sarkin Aska ba ya yi, dan ya kashe ta.
Sai da ta shekara biyar, tana aikin jakar nan, tare da jiƙata da magunguna daban-daban. Ban da zanen hatimai kala-kala da yake cikin jakar.
Ta haɗa kai da ɗan uwan Sarkin Aska, baya nan ya je ya ajiye masa jakar a ƙasan abin kwanciyar sa. Kuma ƙaisar ya ɓatar da sahun sa, ta yadda babu wanda ya gane a cikin aljanun da suke yi masa hidima. Tun da ya kwana a kan jakar, Aljanun da suke yi masa aiki, suka watse suka bar shi, ya kamu da matsananciyar rashin lafiya da sai da ta yi ajalinsa. Yana mutuwa kuma aljanun suka fantsama kan 'ya'yansa da jikokinsa, sai dai aka rasa wanda zai gaje shi gurin ci gaba da aikin zaluntar al'ummar da yake yi. Sosai mutanen gari suka yi murna da mutuwar sa. Babban ɗan sa da suke bokancin tare ma, cewa ya yi ba zai iya ba.
Ƙin samun wanda zai gaje shi, ya sanya aljanun fara sanya wa iyalansa cututtuka. Wasu kuturta wasu suka makance, har da waɗanda suka haukace. Aka din ga ɗauki ba daɗi da Lanti, a kan sai ta warkar da su. Ƙaisar ya gargaɗe ta a kan babu ruwanta ta rabu da su.
Lanti ta shafe shekaru Ashirin da bakwai, tana aiki tare da Ƙaisar tana harkokinta na bori da bayar da magani, haka zalika ita ma ta yi wa mutane da dama girka, masu sha'awar harkar bori. Akwai bikin 'yan bori da ake gudanarwa da nuna bajinta duk shekara, wanda a nan ake yi wa masu so girka, ake bikin bajekolin abubuwan ban mamaki, na gidaje daban-daban.
Maharba su yi na su, wanzamai, 'yan bori da dai sauran su.
Domin bayan mutuwar Sarkin Aska an ɗan samu zaman lafiya, tun da dama shi yake assasa duk wata fitina da rashin zaman lafiya. Sai dai aljanu ba su fasa cutar da su da razana su ba, duk da Lanti tana iya kokarinta. Sai dai ita ma bayan wannan shekarun ta koma ga Allah.
Sai dai kan ta mutu, a cikin jikokinta an samu guda ɗaya da take da irin tauraronta.
Dan haka bayan mutuwar Lanti, aka ci gaba da ba ta kashi tsakanin mutanen garin, da Aljanun da sarkin Aska ya yi aiki da su, har ma da waɗanda ba 'yan asalin garin ba ne.
Sai dai babu yadda Ƙaisar zai yi, a lokacin jikar Lanti ba ta kai lokacin da za ta iya bayar da magani ba. Kuma har a lokacin ba a fasa yi masa magiyar ya rabu da bil'adama ba. Gaba ɗaya ya nesan ta kansa da Ahalinsu.

Bayan jikar Lanti ta fara tasawa, Ƙaisar ya fara bijiro mata, domin yin gadon kakarta, sai ta kasa ɗauka sai ma taɓin hankali da ta samu, duk da ta ɗan taɓa bayar da maganin amma ba sosai ba. A hakan ita ma ta yi aure ta hayayyafa.
A cikin 'ya'yanta aka samu wadda ta gaje ta, duk da ba irin tauraronta ɗaya da Lanti ba. A lokacin Musulunci ya shigo cikin mutane, duk da bai yi ƙarfi a garin Buda ba.
Asma'u ta bayar da magani ita ma, ta yi aiki tare da Ƙaisar, sai dai ba ta da ƙarfin zuciya da juriya irin ta Lanti. Gaba ɗaya ita ma ba wani daɗin aiki ya ji da ita ba. Ko yaya ya buɗe mata ido ta ga abu, sai ta kwanta ta hau jinya. Daga baya ma ta watsar ta tattara komatsan borin ta ajiya, ta ce ta tuba ta daina.
Ganin ba a samun masu irin tauraron Lanti, ya sanya Ƙaisar fara sarewa, da haƙura da batun bayar da magani ta hanyar bil'adama. Sai dai yana iya yin sa gurin bawa zuriyar su Lanti kariya, daga cutarwar zuriyarsu.
Duk abin da yake faruwa, Giyaz yana ankare da Ƙaisar, kuma yana murnar yadda ɗan sa ba zai ci gaba da zama bawa ga bil'adama ba.

Aka din ga samun ci gaba a garin Buda, wasu suka din ga barin garin su na tafiya fatauci, wasu kuma tashin hankalin Aljanun da ya addabi garin ne ya sanya suka bar garin, ciki har da wasu daga cikin zuriyar Lanti.
A can Bauchi aka haifi Maijidda, har ta girma, an saka mata rana saura watanni uku aurenta, su ka zo Buda, a nan suka haɗu da Isa, ya ƙallafa rai a kanta.
Yayar kakarta ta ce sai an warware wancan baikon da aka yi da na can garin Bauchi, an yi da Isa, saboda ƙara danƙon zumunci, kuma hakan zai sanya su din ga kawo musu ziyara a kai a kai, da ƙara samun zaman lafiya a tsakanin zuriyar maharba da ta wanzamai.
Aka mayar wa da wancan na Bauchi kuɗinsa, ita kuma ta auri Isa.
Gidansa na Kano, inda yake harkokin kasuwancinsa, nan ya tafi da ita. Ya ajiye ta a gidansa da suke tare da matarsa babar Gaddafi.
Ya ɗora wa Maijidda son duniya, kamar a kanta ya taɓa aure. Ba uwargidansa ba, hatta 'yan uwansa sai da suka fara jin haushin Maijidda saboda ba ya ɓoye son da yake yi mata, ga ta yarinya ƙarama amma su na ganin kamar ta mallake shi, dan shekarunta goma sha shida a lokacin.
Kasancewar daga zuriyar Sarkin Aska Maijidda take, ta auri ɗan zuriyar Sarkin Baka, sai Aljanun da suka yi wa sarkin Aska hidima, suka shiga cikin lamarin auren, su ka fara haddasa musu matsala. Haka kurum sai ta ji ta tsani Isa, ba ta ƙaunar ganinsa ga yawan rashin lafiya. Kishiya da facaloli suka sako ta a gaba, ga jarabar dangin miji.
Ana haka ya samu matsala da uwargidansa, da ta haifa masa Gaddafi da Ummi, ya sake ta. Nan ma aka ce Maijidda ce sila.
Ya auri Rabi, suka zama ita da Maijidda. Yayarsa Atine ta ƙara haɗe kai da Rabi, su na cizguna mata.
Maijidda ke riƙon su Gaddafi, tana iya kokarinta amma kullum cewa ake yi tana azabtar da su. Kasancewar Gaddafi ya fi Ummi wayo, ya tsani Maijidda cewa yake saboda ita aka saki babar su, kamar yadda Yaya Atine take faɗa. Ita kuma Ummi tana matuƙar ƙaunar Maijidda.
Nan ma Rabi ta saka Maijidda a gaba, da kishi da ƙage kala-kala.
Bayan haihuwar Imran sai da ya shekara uku da rabi, ta haifi Nana. A lokacin Isa ji yake kamar ba a taɓa yi masa haihuwa ba sai a kan Nana. Ya saka mata suna Asma'u, sunan kakarsa da ta riƙe shi take bala'in son sa. Hatta hakika biyu ya yi wa Nana, Ummi ma da ya saka mata sunan mahaifiyarsa bai yi mata abin da yake yi wa Nana ba.
Isa kofur ne na 'yan sanda, abokan aikinsa suka yi masa ƙage, aka kore shi daga aiki har da prison. Ya koma harkar fawa, ya fara samun rufin asiri, harka ta buɗe masa yana samun rufin asiri sosai , sai dai kasancewar sa mutum ne da ba shi da sirri, duk samun sa sai ya bayar da labari, abokansa suka jefe shi sana'ar ta fita daga ransa ya daina zuwa ko ina, sai zaman gida.
Tun da Allah ya sanya aka haifi Nana Ƙaisar ya ganta ya rikice, tamkar Lanti ta yi kaki ta ajiye saboda kamanin su. Ga irin tauraronta ɗaya da Lanti. Gaba ɗaya Ƙaisar ya tattara hankalinsa a kan Nana Asma'u yana ganin, ya samu uwar gijiya a zuriyar Lanti. Giyaz na fuskantar abin da ke shirin faruwa, ya fara ƙoƙarin raba Ƙaisar da Nana. Dan kullum yana tattare da ita. Wasu lokutan ya zungure ta tayi ta kuka. Manyan bokaye da ƙungiyon Asiri na zawarcin son yin aiki da Ƙaisar, saboda tarin baiwa da kuma ilimi da binciken ƙwaƙwaf da yake yi. Wanda za su aiki da shi ne, ya din ga taimaka musu, su kuma su din ga yi masa hidima, amma fafur ya ƙi. Saboda ba ya son duk wata alaƙa da jini.
Ƙaisar ya yi tafiya zuwa wata ƙasa, ganawa da wani tsohon Aljani, a kan wani rubutu da yake yi, ya dawo ya tarar an saki Babar Nana, ita kuma Nana ta daina magana, ta daina tafiya ga Baba ya ƙwace ta, ya hana Maijidda ita. Ya fuskanci aikin mahaifinsa ne Giyaz. Ya je ya same shi yake tambayar sa me yasa ya yi wa Nana haka.
Giyaz ya ce "Ka sani ba zan taɓa sake yadda, ka zama bawan bil'adama ba, da ka sake zama bawan bil'adama gara na kashe ta ko na kashe ka, kowa ma ya huta."
Ƙaisar ya san Giyaz ba ya magana biyu, idan ya faɗi magana sai ya aikata.
Dan haka Ƙaisar ya fara ƙoƙarin kare Nana, ya yi amfani da jakar da ya saka Lanti ta haɗa, ta yi amfani da ita gurin kashe Sarkin Aska. Ya ƙara yi mata aiki, da saiwoyi da wasu hatimai, ya yi wa Giyaz tarko da ita.
Cikin matsananciyar sa'a, Giyaz ya faɗa tarkon Ƙaisar, saboda ya san

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login