Showing 3001 words to 6000 words out of 122205 words
za mu yi zumunci ba? Nana kina lafiya? Na ji an ce wani baroroji aka aura miki ko?"
Nana ta haɗe rai ta tashi ta ce "Ummi zan tafi, zuba mini Abincin idan kin gama"
Ummi ta ce "Bari na wanke babban flask, kuma idan Islam ta zo ki ba ta kwano na, dan ba zan bar miki ba"
Nana ta ce "Gaskiya sai kin bar mini, ki zo ɗakina, ki ɗauki duk abin da ya yi miki. Kuma a ƙaramin kwano za ki zuba mini. Sayyid na yi masa girki, ni zan ci wannan"
Ummi ta ce "Hajiya Nana, an sake haɗiyar wake kenan, to Allah ya inganta"
"Dawa na haɗiya ba wake ba"
Tsulum Saleh ya sake cewa "A nan unguwar gidanki yake kenan? Na ji Ummi ta ce Islam na zuwa gidan naki. Da aka ce mijin naki gadi yake yi"
A ƙufule Ummi ta ce "Dan zatin Allah Saleh ka fita, ba da kai muke magana ba, babu ruwan ka da mu. Wai har ka manta har ubanmu ka saka a rufe saboda kuɗinka, dan rashin kunya kuma, ka zo zaka addabe mu?"
Sum-sum Saleh ya fice daga gidan. Ummi ta zubawa Nana tuwon shinkafa da miyar yauƙi, har da man shanu, Nana sai haɗiye yawu take yi cikin farin ciki, kamar ta durƙusa ta ci a gurin.
Ummi ta shiga ɗaki, ta ɗaukko wa Nana dambun kifi ta ce "Ungo, jiya na yi shi aka kai mini shago, na ɗebar miki"
Nana ta karɓa tana murmushi ganin sa fal a roba, ta ce "Allah ya yi miki abin da ki ke yi mini na alkhairi na gode sosai" suka yi sallama Nana ta fita.
Tana cikin bin wani lungu, ta ji Muryar Saleh na kiran ta. Ta ƙara saurin da take yi, amma ya cimma ta. "Nana dan Allah ki saurare ni".
Rikicewa ta yi, gani take a kowane lokaci za ta iya ganin Sayyid, ba ta san da wani yaren za ta yi masa bayani ba ya fahimta.
"Nana ki tsaya ki ji mana"
"Wallahi zan yi maka ihun kwarto, wace irin jaraba ce wannan ina ruwan ka da ni ne?" Ganin tana ɗaga murya, kuma Akuyarsa ta yi kuka a unguwar, ya sanya sum-sum ya koma da baya.
Tana zumbuɗa sauri, ta je gida, ta san yana can yana jiran ta. Kawai ta ci karo da shi a wani lungu, yana zaune a kan wata sokawe, ya jingina da jikin bango, shikaɗai ƙwal a layin. Sai da ta razana, ta waiwaya bayan ta, cike da tsoron ko Saleh ya biyo ta.
"Sayyid me ka ke yi a nan kuma, ba ka shiga shiga gida ba?"
"Ba zan iya shiga nikaɗai ba" Ta miƙa masa hannu ta ce "Taso mu tafi" ya miƙa mata hannunsa. Sai dai tun da ya saka hannunsa a nata, sai da ya kalli fuskar ta.
Da suka je gidan, danƙam da mata, ana ta hayaniya. Ya rufe fuskarsa Nana ta yi sallama. Gaba ɗaya suka yi tsit, suka zubo wa su Nana ido, musamman ganin hannunta riƙe da na Sayyid.
Kawai ta ja hannunsa, suka nufi ɗakin su.
"Nana kun dawo" Sajida ta yi maganar, tana kokowa da zaninta tana fitowa daga ɗakinta, saboda kar su wuce ba ta gan su ba.
"Eh sannun ku" daga haka ya tura ƙofar ya fara shigewa. Suna shiga ɗakin matan suka saka shewa, ɗaya ta ce "In dai Namiji ne, yarinya za ta gama wannan iyayin ne"
Nana su na shiga ɗaki Sayyid ya tsare ta da ido ya ce "Nana ba ki da gaskiya"
Gabanta ya faɗi cikin tsoro ta ce "Me na yi?"
"Gumi ki ke yi a iya goshin ki, da karan hancin ki. Kuma tafin hannunki ya ya sanyi, zuciyar ki na bugawa da ƙarfi kuma da sauri. Kin yi wani abu da ki ke ɓoye mini ko?" Haɗe rai ta yi ta fara ƙoƙarin ƙwace hannunta daga nasa.
Sai kuma ya sassauta muryarsa ya ce "Ki daina fushi, ba zan iya barin, duk wani abu na ƙi ya tunkaro rayuwata da ke ba, ki daina fushi"
"To sai ka din ga zargina da rashin gaskiya" ta faɗa a hasale.
Ya girgiza kai ya ce "Ba zargin ki nake yi ba. Na tabattar da wani abu ya faru ne, da ba za ki so na sani ba, idan na sani zamu samu saɓani. Kin manta mu ba kamar sauran mutane ba ne. Kuma ina iya jin abin da yake ranki, kin manta ne?" Ya yi maganar yana murmushi da shafo fuskarta. Dole ta saki murmushi.
Nana dai ta din ga yi wa Allah godiya, da ba ganta da Saleh ba.
Nana tana yi wa Allah godiya, ganin yadda jikinsa ya yi kyau. Duk da yana haki bai daina ba, amma yanzu yana cin abinci. Sayyid na matuƙar son zuwa masallaci salla, amma dole yake haƙura. Saboda da gayya matan gidan suke wata shigar, duk da ba tsayawa kallon su yake yi ba. Ga shi ba ya son kallo, amma yana fitowa sai su yi shiru su zura masa ido.
Ita kanta Nana lamarin gidan ya ishe ta, ba ta ƙaunar zaman gidan nan ko kaɗan.
Maman Nana ta aiko mata da barkonon nan, har da awon kayan Abinci, tamkar ta san a halin da take ciki.
Ummi da kanta, ta je ta ɗauki barkonon, domin kuwa Nana daina zuwa gidan Ummi ta gaba ɗaya saboda Saleh.
Abu kamar wasa har zuwa wannan lokacin, Sayyid ya kasa gane kansa, abin ya fara damunsa sosai da sosai. Ga shi ya kasa cewa Nana komai a kan hakan. Ita ma kuma ba ta ce masa ba, sabgoginta kawai take yi.
Tun Yamma Nana, ke ƙoƙarin shirya duk abin da za su buƙata, saboda washegari za su tafi Asibiti, kuma sammako take so su yi, saboda su ga likita da wuri.
Sai dai duk dauriya kawai take yi, wani irin zazzafan zazzaɓi ne a jikinta, ta kasa cin abinci. Babu abin da take son ci, sama ds kazar da Habu ya kawo farkon auren su. Ga shi ba ta son yin duk wani abu da zai ɗaga wa Sayyid Hankali. Ta fuskanci ko saɓani suka samu, ƙaramar magana sai ta sanya ya fara haki, ya fara nema ya faɗi.
Tana ƙofar ɗakinta, tana soya miya, su Barira su na hira, tana yi wa wata maƙwabciyar su kitso. Suke zancen wata mata a bayan layin, wai sai mijinta ya neme ta ya rasa, sai a yi kwanaki ba a ganta ba, sai bayan wani lokaci a tsinto ta a wani gurin, ko a ganta a ɗaki.
Barira ta kada baki ta ce "Amma ta mayar da mijin nan tasono, ƙarya take yi gantalinta kawai take tafiya. Meye matan auren ba sa yi yanzu?"
Sajida ta ce "A'a Barira, ki daina cewa ƙarya ne"
"Ke wallahi, ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba, a gidan uban wa Aljani zai ɗauke mutum ya kai shi wani gurin? Ke ni fa da ake cewa ana ganin aljanu, ko su tsorata mutum ban taɓa yadda ba, iskanci ne kawai da ƙaryar banza ce, ba wani aljan duk 'yan iska ne kawai.
Nana ta ji wani abu mai zafi ya soki zuciyarta, duk da ba da ita suke ba, kawai ta ƙura wa Barira ido, ko ƙiftawa ba ta yi.
Tun Barira ba ta ankara ba, har ta lura, take ta ji tamkar an kwarara mata ruwan sanyi a jikinta, sai kuma ta ɗan tsorata ta ce "Nana lafiya kuwa?"
Ayshercool
08081012143
53
"Barira, kin taɓa haihuwa?"
Nana ta tambaye ta. "A'a me ki ka gani?"
"Amma dai ki na ganin mata su na ɗaukar ciki su haihu. Kuma kin yarda da abin da suke faɗa cewar haihuwa akwai wahala, duk da ba a bakin mutum ɗaya ko biyu ki ka ji ba. Kin yarda wannan ciwon na haihuwa akwai shi, duk da ba ki taɓa yi ba?"
Barira ta ce "Eh mana, ai wannan kowa ya san haihuwa akwai wahala"
"Kin yadda akwai ciwon haihuwa, amma ba ki yadda akwai na aljanu ba, saboda Allah bai jarabce ki ba, har ki ke ƙarar da cewa matar mutane yawon iskanci take tafiya? Duk wanda zai shaide ta, barin mijinta ne, tun da yake zaune da matarsa a haka, ke mene ne naki da za ki ce mutuniyar banza ce? Idan aka rutsa ki shaidar ina take tafiya iskancin za ki faɗa? Idan aka faɗi abu, ko baki yarda ba gara ki yi shiru ki ce Allah ya kyauta, musamman larura. Idan ba haka ba maganganu irin naki za su iya zama cutarwa a gare su". Jin Nana yau ta saka musu baki a magana ya sanya suka din ga goyon bayan abin da Nana ta faɗa gaskiya ne.
Da fari jikin Barira ya yi sanyi, daga baya ganin kowa ya hayayyaƙo mata, ya sanya ta hau bala'i, har abin ya koma faɗa.
Ita kuwa Nana tun da ta gama zazzagar abin da yake ranta, ta kammala girkinta, ta kwashe kayanta, ta koma ɗaki ta bar su da mayar da zance. Dama ga zafin laulayi, ga takaicin mutanen da ake tarawa a gidan babu dalili, ga kuma zafin ƙazafin da Barira ta yi wa matar, da ita kanta Nana ba ta sani ba, amma maganar da ta yi ta ji sanyi a ranta.
Yana daga kwance a kan katifa ya ce "Rayuwata" Ta ɗaga kai ta kalle shi ya ce "viens(zo) yana yi mata alama da hannunsa.
Ta ƙarasa gabansa ta zauna. "Dan Allah ki daina shiga maganar mutanen nan, ki daina kula su. Ni na daɗe ban ji mutanen da ba na ƙauna kamar su ba. Ba na son su zo su yi miki abin da ba zamu ji daɗi ba"
Ta jinjina kai ta ce "Haka ne, ka yi haƙuri nima ban so na shiga ba, haka kurum na ji maganar ta su kamar da ni suke yi. Sayyid ni da kai mun san azaba da raɗaɗin larurar nan. Ire-iren waɗannan maganannun da yadda wasu suke ganin kamar ciwon nan ƙarya ne, ya sanya da yawa masu larurar da dama a cikin wata damuwar ciwon ya yi musu illa, tun da ba a yarda da ciwon ba balle a ɗaukar musu mataki."
"To ai ba su ce da ke suke ba"
Murya a sanyaye ta ce "Sayyid, duk lokacin da aka yi maganar irin wannan larurar, ina jin tamkar da ni ake. Nima wasu lokutan na kan shiga ɗimuwa, na bar gida a gano ni a wani gurin, duk da ni ban taɓa kwanaki ba a ganni ba. Ta kai ta kawo har a zahiri ina ganin abubuwan nan. Sayyid kai ma fa wasu lokutan ina yi a gabanka ka na gani, to yaya za a ce mutum yana sane ya din ga mayar da kansa mahaukaci? Wanda kuwa duk aka samu da yin ƙaryar irin wannan ciwon, yana buƙatar kai shi gurin likitocin ƙwaƙwalwa, Sayyid ciwon nan babu daɗi, akwai wahala" ta yi maganar hawaye na zirarowa daga cikin idanunta.
Ya tashi zaune ya kai hannunsa jikinta zai rungumota, zafin zazzaɓin jikinta ya ziyarce shi. Ya kalle ta a tsorace ya ce "Ba ki da lafiya?" Ya furta maganar haɗe da haki, saboda yadda ya ji zafin a bazata.
Da sauri ta ɗora hannunta a ƙirjinsa ta ce "Sayyid dan Allah ka din ga ɗaukar al'amurana da sauƙi. Ga shi har girki na yi, ina komai nawa lafiya. Ka san lallaɓawa muke yi, ba ka da cikakkiyar lafiya. Ka daina saurin tsorata ko fusata. Ya saka hannun sa yana ƙara danne hannunta a saitin zuciyarsa. Yana iya ƙoƙarin sa a kan ya din ga saita al'amuransa. Amma ya rasa dalili duk abin da ya shafi Nana, kai tsaye yake jin sa a tsakiyar zuciyarsa. Ba ya iya yi masa shinge ko ya dakatar da shi. Yana so Nana ta haihu da shi, amma wahalar da ya ga tana sha, sai da ya ji dama cikin ya zube ko zata huta.
*****
Tun da Jamila ta koma gida, jikinta a sanyaye yake, gani take yi, duk wanda ya ganta ya san abin da ya faru da ita. Mama kuwa baki ya ƙi rufuwa, saboda Jamila ta zo da abin Duniya. Kuma kamar yadda ta gaya mata, sarin kaya ta raka Hajiya, babu wani bincike ta yarda da hakan ta amince.
Ta zo ba ta iya bacci sam, da ta kwanta bacc6, sai ta ga tamkar za ta buɗe ido, ta sake ganinta, a wannan gurin da suka je da Hajiya Sa'a.
"Jamila" Suwaiba ta kira sunanta, ta waiwaya ta kalle ta.
"Wai ya na ga ki na abu kamar mara gaskiya ne?"
Gaban Jamila ya faɗi ta ce "Me na yi na rashin gaskiyar, me ki ka gani?"
"To ai gani na yi kin kasa sukuni, ki na ta wani mutsu-mutsu gaki nan dai"
"Dan Allah Suwaiba ki ji da abin da yake damun ki, ni babu abin da ya same ni, lafiya ƙalau nake "
Suwaiba ta ce "To ai shikenan"
****
Nana duk sammakon da suka yi, su ne na goma sha ɗaya, a gurin ganin likita.
Wajen sha ɗaya na safe aka zo kan su, Nana suka shiga, sai dai wannan karon wani likitan daban suka samu. Suka gaisa Nana ta yi wa likitan bayanin komai. Tare da ba shi takardun gwaje-gwajen da aka yi masa, da kuma katin da aka rubuta masa magunguna.
Ya karɓa ya duba a tsanake, ya duba Bp ɗin Sayyid, ya duba ƙirjinsa da stethoscope.
Nana ta ce "Doctor yaya jikin nasa? Me ka gani?"
Bai kalli Nana ba ya ce "Me yasa ba ku dawo follow up ba"
Ta ce "Ai ba a bamu lokacin dawowa ba. Dama ni ce naga yakamata mu dawo ɗin. mu na ta ƙoƙarin kuɗin allurar su haɗu ne, ko ba su haɗu ba, zamu yi ƙoƙari ko a anan Asibitin gwamnatin ne, sai mu yi booking a fara yi masa"
Likitan ya ce "Ki na ji na 'ya ta?"
Ta ce "Eh"
"Ai mijinki ne ko?"
Sayyid ya jinjina kai. "To a duniya babu wani abu da Allah ba zai iya ba, babu shi. Batun allura ki bar wannan a hannun Allah. Kuma dan babu kuɗin allaura ba za a daina ganinsa ba. Zamu ci gaba da gwada shi, mu na ba shi magungunan da suka dace. Idan Allah ya yassare kwa zo a yi daga baya. Kuma jikinsa Alhamdillah da sauƙi sosai da sosai. Jinin dai haryanzu bai sauka yadda ake so ba. Amma zai sauka da yardar Allah. Kawai ki din ga kiyaye damuwarsa da ɓacin ransa. Idan kuma akwai wani abu da yake damunsa, ki zauna da shi ku tattauna ki ga ta ina za ku shawo kan matsalar?. Amma babu wani abu in sha Allah" Duk da ba lafiya likitan ya ba su ba, amma kalamansa akwai dattaku da ƙwarewa a kan aiki a cikin sa. Dan haka sosai Nana ta samu relief.
Ya rubuta musu lambarsa ya ce "Duk lokacin da za ku zo, ku kira ni, na baku ranar da nake aiki, ya zo ya din ga ganina." Nana ta din ga yi masa godiya da addu'a shi da iyayensa.
Sayyid ya ja wata takarda, ya yi rubutu ya miƙa wa likitan. Likitan ya karɓa ya duba. Ya yi murmushi ya ce "Madam, ashe kema babu lafiya ya ce na duba masa ke"
Nana ta yi murmushi ta ce "Rashin lafiyata, ai ba komai ba ce a kan tasa, ni na fi damuwa da shi ɗin dai"
"A'a tun da ya nemi alfarma, ai dole a yi masa"
Ya duba Nana, ya yi wa Sayyid bayanin laulayi ne kawai yake damunta, ya rubuta mata abin da zai rubuta mata na magani. Ya kuma ba ta gwaje-gwaje. Sayyid ya ƙi tafiya, sai da suka yi gwaje-gwajen.
Suka koma, ya tabattar musu da babu wata matsala, satin cikinta uku da kwanaki, ya rubuta mata magungunan da za ta yi amfani da su.
Suna tafe a adaidaita sahu, Sayyid ya kasa riƙe murmushinsa, ya kai bakin sa kunnen Nana ya ce "Saura kwana nawa ki haihu?"
Ta kwashe da dariya, ta ce "Ina na sani, ko cika wata ɗaya bai yi ba ma, mu dai ci gaba da addu'a Allah ya bar mana, ya bamu ɗa na gari"
Ya amsa da "Amin."
A bakin titi, Nana ta yi sayayyar salak, saboda shi take sha'awar ci. Suka shiga layin gidan na su.
Su na zuwa gidan, Nana da sauri ta shiga banɗaki, saboda fitsarin da ya cika mata mara. Sayyid tsayawa ya yi, yai shiru yana ƙare wa ɗakin kallo.
Nana ta fito bai ce mata komai ba, ta ɗauki cylinder gas, ta ce "Sayyid gas ya kusa ƙarewa, idan zaka iya fita in anjima sai mu je titi tare mu ɗuro"
Ya ce "To"
"Bari na sake ɗumama miyar"
Ta fito tsakar gidan kenan, Sajida ta ce "Nana, Allah ya taimake ki, da tuni da ke za a tafi bayar da shaida"
Cikin rashin fahimta Nana ta ce "Shaidar me?"
"Jiya hirar da ku ka yi, har ki ke yi wa Barira faɗa, a kan matar nan. Daga jiyan nan zuwa yau magana har ta kai kunnen matar. Ta din ga kuka mijin ya ce ba zai yarda ba da 'yan uwanta. Da yyayyenta ne za su zo su zane Barira. Mijin matar ya hana aka kai ta police station. Tun bayan fitar ku tana can, duk sai da muka je bayar da shaida. Wataƙila dai kafin magariba a sako ta, ta dawo gida."
Nana ta numfasa ta ce "Gara da Allah ya sa ba na nan, dan babu inda zan je, shi yasa a rayuwa yake da muhimmanci mutum ya iya bakinsa. Wannan tara matan da ku ke yi, ku na surutai marasa amfani duk ba hanya ce mai ɓullewa ba"
Sajida ta ce "Wallahi haka ne, shi yasa ki ke burge mu ma"
"Allah ya kyauta"
Har Nana ta yi haɗin salak ɗin ta, ta fara ci, ya lura ba ta fahimci abin da yake faruwa ba, shi ma kuma bai gaya mata ba, ya ci abincin. Ta gama ci ta kalle shi ta ce "Sayyid, ka yi mini addu'a, Allah ya sanya kar na yi aman salad ɗin nan, na rufe sauran anjima zan sake ci"
"Kin cika yaji, sai kin yi ciwon ciki ko?"
Ta ɗan waro ido ta ce "Dama ka gani?"
"Eh ina kallon ki"
Ta ɗan yi murmushi ta ce "Idan babu yajin, ba zai yi daɗi sosai ba. Amma yanzu ya ka ke ji a jikin ka?"
"Ba sauƙi"
"Subhanallah, ba sauƙi kuma?"
Ya ce "Eh, kin je ki na hira da likita a gabana"
"Amma ko ba komai, ya kwantar mini