Showing 63001 words to 66000 words out of 122205 words

Chapter 22 - BUZU BOOK2 COMPLETE 2

18 Jan 2026

628

kai ta ce "Babu komai"

"Uban me ki ka yi masa?"

"Wallahi ban yi masa komai ba"

Nene ta shaƙe ta, ta ce "Ki gaya mini me ki ka yi masa?"

Cikin kuka ta ce "Wallahi ba abin da na yi masa"

"To me yasa ki ka shigo?"

"Wallahi son shi kawai nake yi"

"Ɗan ki ne da za ki ce son shi ki ke yi, wani abin za ki yi masa kenan" cikin kuka ta ce "A'a Nene"

Nene ta ce "Wallahi na sake ganinki a gidan nan, sai na yi miki shegen duka, babu ke babu jaririn nan"

Nana ta saka hannu ta ture Nene, ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri ki daina dukanta, ai ta ce babu abin da ta yi masa"

Nene ta ce "Ba dan kin farka ba fa? idan ta yi masa wani abin, ni ina banɗaki ke ki na bacci fa?"

Nana ta ce "In sha Allah babu abin da za ta yi masa. Zo mu je na raka ki gida"

Nene ta ce "Nana ki rabu da ita ta tafi gidan"

Nana ta ce "Nene zan raka ta, ni duk inda na ga mai irin larurar nan, tausayi yake bani"

Nene ta ce "Can ta matse muku ke da ita, ku je can ku ƙarata, ni dai na sake ganinta a gidan nan, ta taɓa yaron nan, sai na yi mata shegen duka da itace"
Nana ta kama hannun Ashura da ke ta rarraba ido, suka fita daga gidan.

*****
Hajiya Sa'a ta tattara hankalinta a kan Abba da yake zaune a gabanta a bedroom ɗin ta.

"Magana nake yi maka, ka ɗago ka kalle ni, mene ne a tsakaninka da yarinyar nan Jamila?"

Ya ce "Ba komai"

"To ka buɗe kunnenka da kyau ka saurare ni, na sanya katanga a tsakaninka da ita, babu kai babu ita, kar ka kuskura na ji wata magana a tsakaninka da ita, kuma matar aure na samo maka ita, zan baka lambarta ka kira ta ku gaisa. Ka je ku gana, kuma nan kurkusa za a yi komai a gama. Ka fita daga harkar Jamila, ka fita daga harkar ta na gaya maka na kuma nanata maka, idan ba haka ba daga kai har ita ba za ku ji daɗin abin da zai biyo baya"

Ya jinjina kai jiki a sanyaye ya ce "To in sha Allah zan kiyaye"

"Tashi ka bani guri" ya yinƙura ya tashi jiki a sanyaye, ya fice daga ɗakin,  zuciyarsa na wani irin zafi. Bai taɓa zaton za ta nuna adawarta da maganar haka ba, ganin yadda take da Jamila.

Ko da ya tafi ɗakinsa, kiran Jamila ya shigo wayarsa, jiki a sanyaye ya ɗaga wayar ya ce "Hello Jamila"

"Jamila kuma, yau ba ƙanwartaka?"

"Afuwan a yi mini afuwa"

Cikin damuwa Jamila ta ce "Yaya lafiya kuwa?"

"Lafiya ƙalau, ina fatan kin je gida lafiya, ba ki bari na dawo na mayar da ke ba"

"Ina sauri ne, kuma ba na son wahalar da kai gaba ɗaya. Ko dai Mummy ta yi maka magana a kan ka daina kula ni ne?"

Da sauri ya ce "A'a ai kin san ba za ta hana ba ko kaɗan"

Jamila ta ce "To shikenan, amma dan Allah in anjima ka zo na ganka"

Ya yi murmushi ya ce "Ni ki ke son gani?"

"Eh mana, ko na haƙura?"

"Ina ni na isa, ina yin sallar isha'i za ki ganni a bar ƙaunar Abba"

"To abin ƙaunar ƙanwarsa, sai ka zo" ya sauke wayar yana murmushi, sai dai yana sauke wayar ya ɗan yi shiru cikin damuwa, bayan tuna abin da Mummyn ta gaya masa na kashedi.

****
Muhsin ɗin Nana tamkar ana hura shi, saboda girma ya cika ya yi fam. Ga shi fafur Nana ta ƙi bari a yi masa aski, ta cewa Nene babansa ma ba ya aski, dan haka a bar masa sumarsa.

Nene ta fara jinginar da shi, a tsakanin fululluka tana koya masa zama.

Nene ta ce "Nana bari na hanzarta na fita, ki kula da yaron nan dan Allah, ban da shiririta, ko ki ƙyale shi yana kuka ki yi masa banza"

Nana ta ce "To Nene ki goya abinki ki tafi da shi mana, tun da kullum ba na yi muku abin arziki"

"Kya dai ji da shi, ni dai na gaya miki, kuma wallahi mahaukaciyar can ta shigo, ki ka ɗauki yaron nan ki ka bata, sai na ɓata muku rai daga ke har ita"

Nana ta ce "Ni dai ba wannan ba, Nene so nake na fara bin ki gurin sana'ar nan, zaman gidan nan yana damuna, ba akin fari babu na baƙi"

Nene ta ce "Nima na yi wannan tunanin Nana, amma bai kamata a ce kina matar aure mu din ga fita bakin titi babu iznin mijinki ba, kin san halin maza wasu ba kirki ne da su ba, mussaman ke ga ƙuruciya ma. Sam ba mutuncinki ba ne ba, dama jira nake yi Muhsin ya ƙara ƙwari, na nema miki ko gurin ɗinki ne ko makamancin haka, ki din ga zuwa sannan mu ga ta ina za mu fara laluben mijinki, amma tun da Muhsin ya yi ƙwari, mu fara lalubawa zaman haka ba zai yiwu ba, motsi ya fi laɓewa ai"

Ta jinjina kai ta ce "To shikenan Nene, duk yadda ki ce Shikenan, na gode sosai da sosai Ubangiji Allah ya saka miki da mafificin alkhairi"

Nene ta ce "Amin yarinyar kirki"

Fitar Nene babu jimawa sosai, sai ga Ashura ta faɗo gidan.
Nana ta ba ta ce mata ta shigo ɗakin, amma ta ƙi.

Nana ta tashi ta fita ta shimfiɗa mata tabarma, sannan ta ɗaukko Muhsin, ta zo ta zauna ta ba wa Ashura shi.
Ta karɓe shi tana buɗe baki cikin murna, ta kalli Nana ta ce "Ina son yaron nan"

Nana ta ce "Da gaske?"

Ta jinjina wa Nana kai, ya jima a hannun Ashura, sannan ta ba wa Nana shi, Nana ta mayar da shi ɗaki ta kwantar. Sai dai tana dawowa ta tarar da Ashura a tsaye tana kuka, gefenta ga ƙwarangwal ɗin nan.
Nana ta ce "Me ka ke buƙata ne?"

"Ki na ganina kenan?"

"Eh ina ganin ka, sannan wannan mahaifar da ka ke lasa mene ne ma'anar hakan? Tun da ƙazanta ce"

Ya ce "Lokacin da aka haife ta ne, da za su dawo daga Asibiti, aka manta mahaifar, shi kuma mai motar ya yar a bola, ni kuma na tsinta na biyo ta."

Cikin damuwa Nana ta ce "Amma baka kyauta ba, tun da babu wanda ya yi maka wani laifi ka ke yi mata abin da ka ke yi mata".

Ya ce "Ai mu ba sai an yi mana abu ba, idan mu na son mutum. Kin ga ke ma da ki ke addu'a wasu lokutan, ba dan tasirin Addu'a da ki ke yi, da kuma tsoron uban duƙusa da ake yi ba, da bataliyar da za su shiga jikinki da yawa. Saboda da guda ɗaya ya yi hanya, wasu ma suke samun kafar shiga jikin mutum. Kuma Allah ya taimake ki, Sarkin baka ya rage tasirin uban duƙusa a tare da ke, da duk inda muke sai kin din ga ganinmu, kuma muraran za ki din ga ganin cututtuka da sihiri a zahiri, sai kin kusa haukacewa idan ba ki bayar da magani ba. Kawai dai shi yana lallaɓa ki ne"

Nana ta ce "Yaya aka yi ka san Ƙaisar, kuma ka san Sarkin baka?"

Ya ce "Jaddul Jinn babu wanda bai san shi a nahiyar nan ba, dan haka sanin jikansa uban duƙusa ba abin mamaki ba ne. Sarkin baka kuma shi ne ya mayar da ni ƙwarangwal, mun taɓa artabu da shi da na shiga jikin sata mesa, ya ƙona ni. Kuma na ga kin haɗa jini da shi, ba yadda na iya da ke ne kawai, da sai na ɗauki fansar abin da aka yi mini a kan ki"
Nana ta yi shiru jikinta ya yi sanyi, su na gama maganar Ashura ta juya ta fita ya bi ta a baya.
Nana ta din ga jinjina azabar naci da riƙo irin na halittun nan.

****

BAYAN WANI LOKACI.

Girman ɗan mutum babu wuya, in ji masu iya magana, Muhsin ya cika watanni bakwai, Nana na zaune tare da Nene.
Nene ta kai ta gurin koyon girke-girke, yanzu kuma tana zuwa koyon ɗinki. Nana har mamakin yadda Nene take yi mata take. Sai dai ta fara karaya da yanke tsammannin haɗuwa da Sayyid.
Nene ce ta shigo gidan, bayanta goye da Muhsin, yana ta mamular cukui.
Nene ta sauke shi ta zaunar da shi ta ce "Wannan ɗan naki, idan bai nuna mini halinsa ba, ai ba za a ce ɗan buzaye ne ba, mun taho hanya ya ga raƙuma, wai sai dai mu tsaya ya kalli raƙumi, sai zillo yake a bayana yana ihu, sai da na tsaya na ɓata lokaci yana kallon raƙuma yana miƙa musu hannu. Ya cire hular kansa ya yar, kowa ya ga kansa da wannan kitson sai an tambayi mace ce ko namiji. Ke ma da taurin kan tsiya, kin ƙi bari a yi masa aski, kuma kina yi masa kitso kamar wani mace."

Nana ta yi murmushi ta ce "Ni babu ruwana, ba shiga faɗanku zan yi ba, balle na ji kunya ku gwale ni"

Shi kuwa cukun hannunsa kawai yake mamulawa a bakinsa, Nene ta juya za ta fita tsakar gida ya rarrafa ya bi ta yana kukan ta ɗauke shi.

Nana ta sake yin murmushi ta ce "Na haifa wa Nene ɗa"

Tana jiyo rigimarsa da Nene, ya hana ta aiki, idan ta hana shi wannan ya koma wancan.
Nana ta din ga dariya daga ɗaki, aka jima kuma Nene ta zuba masa shayi sai kuma ya nutsu, guri ɗaya, yana sha yana wasa da gashinsa.
Ashura tana son zuwa gidan Nene gurin Nana, amma tana tsoron Nene, ga Muhsin da ya ganta yake sanya ihu, tsoronta yake ji.

Ɓangare guda kuma, zuciyar Nana na saƙa mata ya kamata ta gusa ta bar gidan Nene, saboda ta ja lokaci a gidan. Amma tana tuna tijarar Nene, da rashin sanin ina za ta dosa. Ba ta san wani irin mutum ne Sayyid ba, mutumin da za a yi alfahari da haɗa nasaba da shi ne ko akasin haka, duk da tana kyautata masa zato. Shi yasa take ɓoye wasu abubuwan, dan kare mutuncin sa da rashin sanin a yaya za ta haɗu da shi.

Washegari da safe Nana ta tashi, ta jiyo hirar Muhsin a tsakar gida.
Ta tashi ta fita kar ya yi wata ɓarnar, sai ta gan shi a lungun kitchen ɗin Nene, ya juyo bayansa, kamar dai wani abun ya samu yana wasa da shi.
"Kai babyn Sayyid, me ka yi a gurin nan, taho ka sha" bai waiwayo ba ya ci gaba da abin da yake yi. Nana ta nufe inda yake. Wata irin narkekiyar mesa ta gani a cikin lungun, shi kuma yana ta duƙunƙuna kanta da hannu bibbiyu yana hira.
Ji ta yi tamkar an ɗaure ta tamau, ta kasa gaba ta kasa baya, kuma ta kasa magana.
Mesar ta miƙe sai ga Ƙaisar ya bayyana a gurin. Muhsin ya ɗaga kai yana dariya yana kallon Ƙaisar.
Ƙaisar ya ciro wani abu a kwalba, ya buɗe bakin Muhsin ya zuba masa, Nana ta rikice amma ta kasa motsa kowace gaɓa ta jikinta.
Muhsin ya kama rigar Ƙaisar yana wasa da ita, yana yi yana kallon Ƙaisar ɗin.
Ƙaisar ya saka hannu ya shafa kitson kan sa, ya miƙe tsaye ya ɓace. Sai da ya ɓace Nana ta iya motsawa, amma duk da haka ta kasa zuwa inda Muhsin yake, sai shi ne ya rarrafo ya nufo inda take.
Ta saka hannu da ƙyar tana dudduba jikinsa, ko wani abin ya yi masa amma jikinsa lafiya ƙalau. Ta shiga fargaba da tsoron me ya ba shi ya sha?.
Ta ja jikinta ta koma jikin bango, ta fara shayar da shi, tana roƙon Ubangiji Allah ya kare mata yaronta daga sharrin su Ƙaisar da kowane irin nau'i na shaiɗani.

Nene na fitowa, ya cika Nana ya tafi gurinta, sai da ya gama wasansa, ya sake komawa gurin Nana.
Tana shayar da shi, tana ganin fuskar Sayyid a tattare da shi, dan hatta idan ya ɓata rai, tamkar mahaifinsa.
Sai dai tunani da tsoron abin da ka iya samun sa, ya gaza barin zuciyarta, tun daga ganin da ta yi wa Ƙaisar da shi.
Ta so gaya wa Nene, amma ta ja bakinta ta yi shiru ba ta gaya mata ba.
Sai dai tun gabatowar magariba, take jin sanyi.
Ta shige ɗakin ta ƙudundune, ta bar su Nene.
Tana tsaye a sahara, sai dai a wannan karon babu ƙurar Saharar, ta hangi Sayyid a zaune yana shan shayi, shikaɗai.
Ta taka sannu a hankali ta ƙarasa inda yake, ya ɗago ya kalle ta yana murmushi.
Ta zauna a kusa da shi, ta ce "Ka warke ne?"

"Da sauƙi, na yi nesa da inda nake jin ciwon, kuma na yi nisa da gurin waɗanda za su kashe ni"

Cikin damuwa ta ce "Ni fa?"

Ya ajiye kofin hannunsa, ya rungumota jikinsa yana kallon fuskarta, idanunsa cike da hawaye ya ce "Yadda ruhinki da gangar jikinki, suka gaza samun nutsuwa, tun bayan rabuwarmu haka nima nawa suka gaza samun nutsuwa. Ina kewarku gangar jikina ta kasa samun nutsuwa, ina buƙatar ki a kusa da ni"
Ita Nana gaza riƙe nata hawayen ta yi, tuni ta ba su dama suke zuba.

Ya girgiza mata kai tare da cewa "Kar ki manta, muddin kina raye kuma ina raye a doron duniya, gangar jikinmu ba za ta samu nutsuwa ba, sai mun haɗu. Ina kewar ki ma vie."
Ya yi maganar yana ƙanƙame ta a jikinsa. Ta buɗe idonta tana ji yadda hawaye ya jiƙa mata fuska.
Ta tashi zaune da ƙyar, ta yi shiru ta tafi tunani. "Nana ba a bori da sanyin jiki, ci gaba da zaman ki a gidan nan, tamkar ki na matsawa dattijuwar nan ne da take ɗawainiya da ke, kuma ba za ki taɓa haɗuwa da Sayyid ki na zaune guri ɗaya ba, yakamata ki motsa".

Ta tashi ta yi alwala, ta yi sallar magariba da isha'i, ta idar ta shiga ɗakin Nene ta ɗaukko Muhsin, ta dawo da shi ɗakinta saboda ko zai farka cikin dare.

Nana ji ta yi tamkar ta fice daga gidan a cikin daren nan, amma ta kasa saboda ba ta san ina za ta nufa ba, a wannan uban daren.

Ta haƙura da niyyar da Asubar fari, ta tashi ta fice, amma bacci mai nauyin gaske ya yi awon gaba da ita, sai da aka kusa idar da salla, Nene ta tashe ta yi sallar Asuba.

Tana idar da sallar kuma, Muhsin ya tashi ya saka rigima, Nene ta ɗauke shi suka tafi ɗakinta.

Tun da wuri yaran Nene suka zo, suka ɗauki kayan Abinci, amma Nene ta ƙi fita ranar ta wuni a gida, yaranta ne suka je suka sayar da Abincin.

Abu kamar wasa a jere kwanaki huɗu Nana tana yinƙurin guduwa, amma Nene ta kasa ta tsare tamkar ta san abin da Nana take shiryawa.

*****
Jamila ta nuna wa Hajiya Sa'a tamkar ba ta san ita ta taka wa ɗan ta Abba burki a kanta ba, Hajiya Sa'a sai shirin bikin Abba take yi, yayin da gefe guda kuma Jamila ta yi blocking ɗin sa, ta daina ɗaga wayarsa gaba ɗaya.

Dama idan Hajiya Sa'a na nan, ba ya iya yi mata magana, da zarar ta fita kuma sai Jamila ta kulle ƙofar sashen. Ya rasa abin da yake yi masa daɗi, har layi ya canza ya kira Jamila, amma tana ɗagawa ta ji muryarsa ta kashe.

Ga shi tun da Hajiya Sa'a ta fuskanci abin da yake tsakanin su, ta daina yawan fita ta bar Jamila a gidan, idan ma fita za ta yi sai dai su fita tare. Sai dai yau Jamila ba ta jin daɗi, dan haka Hajiya Sa'a ta fita ita kaɗai, saboda ta sakankance Abba yana can kasuwa.

Awa guda da tafiyarta, Jamila na kan doguwar kujera tana bacci, ta ji tsayuwar mutum a kan ta. Ta buɗe idonta a hankali ta ga Abba a tsugune a gabanta yana kallonta.

Tashi ta yi zaune tana tsuke fuska tare da gyara zaman rigarta za ta tashi.

Cikin zafin nama da tsoron rashin sabo, ya riƙe hannunta ya ce "Dan Allah Jamila ki tsaya ki saurare ni" ya yi maganar cikin marairaicewa kamar zai yi kuka.

"In saurare ka ka ce mini me Yaya Abba? Dan Allah ka rabu da ni." Ta yi maganar itama idanunta fal hawaye, saboda ba ta taɓa sanin ta kamu da matsananciyar soyayyar Abba ba, sai yanzu da Hajiya Sa'a take ƙoƙarin farraƙa su.

"Jamila dan Allah ki fahimce ni, kin san a son raina ba zan auri wata ke ga ki na bar ki ba, wallahi Jamila ina son ki, ban taɓa son wata 'ya ba sai ke"

Ta kalle shi hawaye na zuba daga idonta ta ce "Ko ma mene ne, ai yanzu aure za ka yi, ka rabu da ni dan Allah"

Girgiza kai ya yi cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali, ganin yadda take zubar da hawaye, zai yi magana ta fizge hannunta ta shiga ɗaya falon, bai yi ƙasa a gwiwa ba, ya sake bin ta yana ƙoƙarin rarrashinta.

Sai dai kash, garin ya rarrashi Jamila, sai shaiɗan ya buga musu ganga su ka taka rawa, duk da Jamila ta fuskanci cin zarafi da keta haddi a ƙungiyarsu ta asiri, a wannan karon ma tsoro da rashin sabo suka yi tasiri a a gare ta, duk da a nasa ɓangaren ma haka ne.

Daga shi har ita suka saka kuka mai cike da nadama da dana sanin abin da suka aikata.

Maganganun Nana suka din ga dawo mata daki-daki, na nasihar da ta din ga yi mata a baya. Duk da babu wanda ya san halin da Nana ne ciki, a tsawon wannan lokacin kusan shekara guda, amma gara Nana da ita, Ko ba komai Nana aure ta yi, ita kuwa fa da fari bokaye da aljanu sun kwanta da ita, a wannan karon kuma ruɗin soyayya da sharrin shaiɗan.

"Jamila, dan Allah ki yi haƙuri, ki kuma rufa mini asiri, ke ma kin sa hakan ba halina ba ne ba, amma duk yadda zan yi, zan aure ki, ni na fara aikata ɓarnar nan, kuma zan gyara ta in sha Allah"

Jamila ta kalle shi ta kawar da kai, tana jinjina lallai Abba bai san komai ba, tun da bai iya gane ba budurwa ba ce ba, duk da bayan abin da Hajiya Sa'a ta kai ta aka yi mata, bazama ta yi neman magungunan gyara.

Ya lallaɓata ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login