Showing 6001 words to 9000 words out of 122205 words
da hankali, bai ce mini zaka mutu ba, kalamansa sun bani ƙwarin gwiwar da yakamata na samu" ta yi maganar ƙwalla na cika mata idanu.
Ya girgiza mata kai ya ce "Kar ki bari su zubo".
"To ba kai ne ba, komai na yi sai ka ji haushi na?"
Murmushin sa mai matuƙar ƙayatarwa ya yi, ya ce "Ba haushinki nake ji ba, tsaro nake ba ki, saboda tawa ce nikaɗai. sourire (smile) ki yi murmushi mana" ta noƙe kafaɗarta tana tura baki,ta juya masa baya.
Ya matsa bayan nata, ya sumbaci saman bayan ta, ya zagayo da hannunsa ta cikinta, ya kwantar da kansa a kan kafaɗarta. Gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi. Damuwa ce ya ziyarce zuciyarsa, jin yadda Nana ta saki jiki sosai da rungumar da ya yi mata, ko ba a gaya masa ba ya san abin da yake ranta, tuna cewar babu abin da zai iya tsinana mata, ya sanya a hankali ya raba jikinsa da nata, wani irin tausayinta na ratsa ilahirin jikinsa.
Ta maze cikin yaƙe ta ce "Sayyid, ya na ji ka yi shiru ne?"
Ya girgiza kai ya ce "Babu komai"
"A'a akwai wani abu. Dama likita ya ce mu zauna na tambaye ka, ko akwai wani abu da yake damun ka, haryanzu fa jininka bai sauka ba Sayyid"
Ya ɗan sake yin guntun murmushi ya ce "Damuwa ai akwai ta, ba na son ɗaga miki hankali ne kawai.
Haryanzu ina tunanin inda su Habu suka tafi, suka bar ki da ɗawainiya, Kodayake ko suna nan ma, kula da ni ba dolen su ba ne. Sai wahala ki ke sha, wallahi idan ina tuna hakan, sai na ji tamkar numfashina zai ɗauke a cikin damuwa nake sosai da sosai. Ba na son saka ki a damuwa ne kawai".
Nana ta tattara hankalinta ta matsa kusa da shi, ta riƙo hannunsa, ta kalli idanunsa da suka yi jawur. "Idan su Habu ba hakkinsu ba ne kula da ki. Ni yanzu ya zama haƙƙina, na san ba a banza Allah ya haɗa mu ba. Mu ci gaba da addu'a Allah ya kawo mana komai da sauƙi. Amma ina fatan dan Allah ka daina damuwa, idan ciwon nan ya matsanta maka a jikina nake ji, ka daina ba na so" ta ƙarasa maganar cikin shagwaɓa.
Kafaɗarta ya ciza cikin wasa, yana rungume ta. Tamkar ba a cikin damuwa suke ba, suka ci gaba da raha, duk da yadda hayaniyar mata ta cika gidan, tamkar a na taro, saboda dawowar Barira, an cika gidan ana mayar da yadda aka yi.
Ana fara kiran sallar magariba, ta kai masa ruwan ɗumi banɗaki ya yi alwala.
"Za ka je masallaci ne?"
"A'a a nan zan yi"
"To yi sallar. Nima sai na yi muje mu ɗuro gas, ko rabi ne sai kuma na sayo gawayi, Ummi ta bani kurfoti, na din ga haɗawa da shi" Ya jinjina mata kai ya tayar da salla.
Yana kallon ta ta idar, ta buɗe jakarta ta ɗebo sauran kuɗin da suka dawo da su, ta nufi wardrobe ta haɗa su da waɗancan kuɗin. Kawai ta ga kayan wardrobe ɗin a hargitse.
Mamaki ya kama ta, ta san Sayyid ba ya taɓa mata wardrobe, kuma ita ba a haka ta bar wardrobe ɗin ba.
Ta janyo jakar gidan Sarkin baka, ta duba ta ga kuɗin nijar a ciki. Ta laluba ta ɗauki ledar, da kuɗin Nigeria ke ciki ta rasa. Ta watso kayan wardrobe ɗin gaba ɗaya, tana ƙara haskawa da fitilar wayarta.
Yana tsaye yana kallon ta. Muryarta na rawa ta ce "Sayyid"
Ya kalle ta. "Kuɗinmu, kuɗin da ka bani na saka a cikin wardrobe na...naa..ajiye a nan ban gani ba, ko ka ɗauka?"
Ya yi shiru yana kallon ta, a zuciye ta nufi hanyar fita daga ɗakin, ya riƙe ta. Jikinta yana tsuma take ƙoƙarin fizgewa amma ya riƙe ta yana girgiza kai ya ce "Kar ki yi magana, ki yi shiru ko waye mu bar wa Allah. Tun da na shigo, na ga alamar an buɗe ɗakin. Kuma laifinmu ne, da ba mu saka mukulli ba, muka rufe ɗakin kawai."
"Sayyid ba a yi mana adalci ba. Kuɗin Abincinmu da maganinka, sun kwashe gaba ɗaya wace irin masifa ce wannan? Daga wannan sai wannan ya ake so na yi ne?" Ya riƙe ta gam yana shafa bayan ta, a hankali ya ce "Ki yi haƙuri, ki daina ɗaga murya, akwai Allah"
Kuka take yi iya ƙarfinta, tana sheshsheƙa, ya rungume ta gam a jikinsa, shi kansa ya ji zafi da raɗaɗin satar da aka yi musu. Ba iya kuɗi ba, har da wasu daga kayan amfaninsu na ɗakin an ɗauka, ya san kuma hakan sabon ƙalubale ne, saboda ba su da wata hanyar samun kuɗi a yanzu.
Ji ya yi jikin Nana ya saki, kuma jikin yana ɗaukar sanyi. Karkarwa ta fara yi, tamkar ana jona mata shocking.
Cikin matsananciyar damuwa, ya zauna da ita a jikinsa, ya ɗauki wayarta da ta saki a gurin, yana haska fuskarta. Ya ga hawaye na fita ta gefen idonta. Hannayenta da ƙafafuwanta su na lanƙwashewa, goshinta kuma yana tsatstsafo da gumi.
Jin ta ta yi, jingine da wani abu da ba ta san ko mene ne ba. Ta shafa abin ta ji ƙurzunu-ƙuruzunu, tamkar dutse. Gurin baƙi ƙirin duhu ya gauraye gurin, ko tafin hannunta ba ta iya gani. A hankali haske ya fara shigowa gurin, har gurin ya yi haske ba ki ɗaya. Ta ɗaga kanta ta ga ba ta iya gano ƙarshen ɗakin.
Jin tari ta yi a bayan ta, ta waiwaya da sauri, ta ga Ƙaisar a zaune lulluɓe da wani abu mai haske sosai.
"Ƙaisar. Ba ka da lafiya?" Ta yi maganar tana nufar inda yake.
Ya yi shiru bai yi magana ba. Ta sake cewa "Dama kuma ku na rashin lafiya, kamar ka canza gaba ɗaya" ya yi murmushi ya ce "Mu na rashin lafiya mana, guba na ci" Ta waro ido ta ce "Guba kuma? Me yasa?"
"Tsohon nan na jikin mijinki, ya bani."
"Kuma ka sha? Wai meye alaƙar ka da shi? Kuma dan Allah me yasa yake bibiyar mijina?"
"Ba wannan ba, me yasa ki ka kira ni?" Cikin mamaki ta kalle shi ta ce "Kamar yaya? Ni ban kira ka ba ai"
"Fushi da ɓacin rai, duk wanda ki ka yi tamkar kin kira ni ne. Kuma ni yanzu ba ni da wani tasiri sosai, saboda jinya nake yi. Babu wanda ya san ina nan. Giyaz ya saka ni a gaba, ya mamaye Library ɗi na, yanzu rashin ganina zai sanya ya ci gaba da cutar da ku. Ba zan iya wani abu ba sosai yanzu, sai dai zan iya tasiri a kan bil'adama.
Duk ba wannan ba, duba can."
Ta ɗaga kai ta kalli inda ya nuna mata, Library ɗin Ƙaisar ta gani. Ta ga gangar jikin Sayyid a kwance. Tsohon nan ya ɗaɗɗaure shi da wata irin igiyar ƙarfe. Ƙasan gadon da yake kai kuma, wata irin wuta ce take ci a ƙasa. Nana ta zabura a rikice, ta ce "Wannan ai Sayyid ne"
"Ƙwarai shi ne, ba wani ba. Kuma Giyaz shi ya sanya masa matsalar da ku ke ciki na auratayya. Sai dai abu ɗaya zan iya gaya miki. Matsalar zuciya da hawan jini da yake fama, wannan ciwo ne yake damun sa. Amma Giyaz na assasa wani abin. Kuma... Amma dai shikenan"
Nana ta buɗe baki za ta yi magana, ya ce "Kar ki tambaye ni komai, kin san sharaɗin. Kalli" ya yi maganar yana sake nuna mata gurin.
Alhaji Fatuhu ta gani, ta yi ƙuri da ido ta ce "Kamar na san wannan"
"Ba kama ba ce ba kin san shi, ciwo ne da zafin sihirin da aka yi masa ya mayar da shi haka. Sai kuma albishir da nake yi miki, da ƙanwar ki ta zama cikakkiyar 'yar ƙungiyar asiri. Ɗayar kuma wannan bararojin da ta taɓa baki magani, ta aura mata ɗanta, wanda yake baƙin aljani ne. Kuma ta tarkato kan iyalanta duk su na jikinta. Kuma kowanne akwai abin da yake mora a jikinta. Ke in taƙaice miki ma, a kowane lokaci za ta iya rasa hankalinta ko ma rayuwarta gaba ɗaya. Shikenan bissalam"
"Ƙaisar" sai kuma ta yi ido huɗu da Sayyid.
"Kin tashi?" Ta yinƙura ta tashi zaune, tana kallon ɗakin.
Sayyid ya ce "Ƙaisar ɗin ba shi da lafiya ne?" Ya yi maganar yana tsare ta ido.
"Wane Ƙaisar ɗin?"
"Tambayata ki ke yi?" Shiru ta yi, ita ba ta iya tuna koma ma a cikin abin da ya faru ba. Idonta ne ya sauka a kan kayan da suke gaban wardrobe a ƙasa, sai kuma abin da ya faru ya faɗo mata. Afujajan ta tashi ta sake nufar wardrobe ɗin, tana zazzage kayan tana kuka.
"Kuɗin nan fa babu su, an kwashe ki daina wannan dube-duben" ya zauna ta yi shiru ta sanya kayan a gaba tana kallo.
Ya yi mata shiru ya ƙi kula ta, ya kwanta a kan katifa, yadda take a hasalen nan, idan ya matsa faɗa za su yi. Cikin ƙanƙanin lokaci nannauyan bacci ya yi awon gaba da shi.
Barira na kwance a ɗakinta, ta yi ɗaiɗai tana bacci, ta ji kamar ana karta mata farce a ƙafafuwanta. Har ta maze ta ci gaba da bacci, amma ta ji an cigaba. A fusace ta ce "Gali meye haka, za ka din ga karta mini faratanka, ina cikin bacci ne?" Shiru bai amsa ba. Ta laluba ta ji yo ƙeyarsa a can ƙarshen gado, yana bacci. Ta koma ta kwanta, amma ta ji an cigaba, ta tashi zaune tana zabga ashariya.
Ta kunna fitila, ta ga babu kowa. Ta yi tsaki ta sauka daga kan gadon, ta fito tsakar gida domin ta yi fitsari. Bayan ta fito daga banɗakin, kanta ko ɗan kwali babu, kawai ta yi karo da Nana a tsakiyar tsakar gidan tana yi mata wani irin mugun kallo.
Ta haska Nana ta ce "Nana lafiya kuwa?"
Sai dai Nana ba ta yi magana ba, ta sake haska ta, za ta yi magana. Ta ga ta rikiɗe ta zama wata irin ƙatuwar mage, baƙa ƙirin, girman ta ya yi na tunkiya ƙosashiya da ita, ta yo kanta tana buɗe haƙora.
Da gudu Barira ta shiga ɗakinta, tana ihu tana kiran sunan Gali.
"Ke mahaukaciya, mene ne haka za ki din ga ihu kina kiran sunana a tsohon daren nan?"
Ba ta ce masa uffan ba, ta duƙunƙune, tana mayar da numfashi. Ta tsorata sosai da sosai, da ƙyar ta samu ta yi bacci. Sai dai a cikin baccin ma, mafarkin magen nan kawai ta din ga yi tana bin ta, tana karta mata farata tana cizon ta.
Sayyid kuwa yana jiyo kururuwar Barira, hakan bai dame shi ba, sai ganin Nana da ya yi a zaune, ta haɗa kai da gwiwa.
Ya yinƙura ya tashi zaune, bai ce mata komai ba, ya kwantar da ita a kan katifar, ya rufe su da bargo ya rungume ta yana shafa bayanta. Yana jin ta tana kuka, har ta yi ta gaji bacci ya ɗauke ta.
Dauriya kawai yake yi, amma ji yake tamkar ya taya ta kukan.
Washegari, Barira ta tashi da matsanancin zazzaɓi da ciwon kai, ta din ga yi wa mijin kuka, tana cewa ya mayar da ita gidansu, mayu sun kama ta a nan gidan, ba za ta yadda a kashe ta a banza ba. Babu yadda ya iya ya tattara ta ya kai ta gidansu.
Kwanki biyu da sace kuɗin nan, Nana ta rasa abin da yake yi mata daɗi. Dubu talatin ce ta ragu a hannunta, shi ma cikin irin kuɗin da ta zuba a jakarta ne suka fita da su. Kuɗin Nijar ɗin kuma ba ta san ma ina za ta a canza su ba. Bayan haka tayi tunanin idan Habu ya dawo fa, me za ta ce masa? Ta din ga tunanin yadda za ta yi da dubu talatin ɗin nan, ba tare da ta rushe gaba ɗaya ba. Ga shi magungunan da yake sha kawai, na wata ɗaya dubu goma sha biyu take sayen su.
Sai dai kamar yadda yake nanata mata, ta yi haƙuri, ya sanya ta fauwwala wa Allah lamarin.
Kwana biyar da kwashe kuɗin nan, Sayyid ya hana Nana gaya wa kowa. Sai dai cikin dare ba ta iya bacci, saboda lissafi da tunani. Ta kira Ummi ta tambaye ta batun barkono, ta ce ana ta saya, ta sayar da ya kai rabin buhun. Kayan Abinci da Mama ta haɗo mata da su, take ta cancana musu.
Da daddare ba ta iya bacci, saboda damuwa da tunani, sai dai abin yana damun sa fiye da yadda yake damun ta. Su ka wayi gari, ya tashi jikinsa babu daɗi, yana ta numfarfashi.
Abin Duniya ya ƙara damunta, ya kuma ƙi cin komai. Muryar Barira ta jiyo a tsakar gida, da ta dawo, tana maganganu tana ba wa su Sajida labari.
"Mayu sun kama ni a gidan nan, kuma da ƙarfina na dawo, wallahi sai sun ci uban su, kurwata ta fi ƙarfin mutum".
Sajida ta ce "Ban gane mayu ba, suwaye mayun kuma?"
Barira ta ce "Oho, ki zuba ido ki gani, Allah zai tona musu asiri"
"Ni fa ba na son kurman baƙi, a masu shigowa ne mayun, ko kuma zaunannun gidan"
"Na ce ki zuba ido ki ga ikon Allah"
Bai fi mintuna biyar ba, wani irin hayaƙi, mai azabar yaji, ya turnuƙe gidan.
Nana da take lafiya ƙalau ma, ta fara tari.
Shi m tarin yake yi, numfashinsa kamar zai ɗauke, ta ɗaukko mafici ta din ga yi masa fifita. Ta gaji ta tashi, da nufin ta je ta ga me ake ƙonawa yake wannan uban hayaƙin haka. Amma ya riƙe hannunta ya hana ta. Haka suka wuni a galabaice. Sajida ma sai bala'i take yi, tana cewa Barira za ta kashe ta da hayaƙi.
"Wai Sajida ko ke ce mayyar nan ne?"
"Ke kama bakin ki, wallahi ki ka ce mini mayya, sai mun yi shari'a da ke"
Barira ta ce "Sai ki saurara mini, tun da dai ba ke ba ce" Haka suka wuni, Barira tana gana musu azaba, da wannan azababben abin da take zubawa a cikin murhu.
Washegari ma, azabar hayaƙin nan ce ta tashi su Nana, numfashin Sayyid tamkar zai ɗauke saboda azaba.
Nana dai ta ci gaba da daurewa, amma yamma na yi, Barira ta sake cika kurfoti da gawayi, ta tayar da wuta ta afka hayaƙin nan.
A fusace Nana ta fita, ta tarar da ita tana ta girgiza kurfotin, tana zuba wani abu a ciki.
Nana ta ce "Barira, dan zatin Allah ki daina zuba wannan abin. Ina da mara lafiya a ɗaki. Yana da matsalar numfashi, jiya kwana muka yi babu bacci. Kuma da sassafe kin banka wani, kuma yanzu ma ga shi kina sake kunnawa"
Ta kalli Nana ta ce "Ai duk wanda ya hana uwar shi bacci, wallahi shi ma ba zai yi ba"
Nana ta ce "Kamar yaya kenan?"
"Kamar yadda ki ka ji"
"Ni dai koma mene ne, ki yi haƙuri idan ba ki yadda ba, zo mu je ɗakin ki ga halin da yake ciki"
"Babu ruwana da halin da yake ciki, kurwata ce ta fi ƙarfin duk wani maye wallahi"
Nana ta ce "Barira mu ne mayun da ki ke faɗa dama? To Barira ko za mu ci mutum ma ci taki, jiki duk dauɗa?"
"Ko ma duk uban mene ne, tun da aka kama ni aka lasa, an ji zaƙin kurwa ta, wallahi sai mutum ya ci ubansa, miyagun banza kawai"
"Mu ne mayun Barira?"
"Eh ku ne, ko na ce ke"
Nana ta ƙarasa daf da Barira ta damƙi tsintsiyar hannun Barira ta ce "Ki ka ce ni mayya ce?" Barira ta yinƙura za ta fizge hannunta, ta yi bala'i. Kawai ta ji jikinta ya yi wani irin nauyi, kuma jikin ya yi mata wani irin sanyi, ta kasa motsa komai. Kawai ta silale ta faɗi ƙasa.
Ayshercool
08081012143
54
Ihu Sajida ta saka, tare da sauran matan da suke zaune, tamkar ana bajekolin kasuwar ƙauye, suka dare ganin daga riƙe hannun Barira da Nana ta yi, ta faɗi ƙasa. Faɗuwar da ba su da tabbacin, tana raye ko mutuwa ta yi.
Wasu suka yi waje da gudu su na ihu, tamkar garken tumakin da ba su san inda suka dosa ba.
Nana kuwa idanunta a rufe, ta nufi ɗakin su tana tangaɗi, Sayyid kuwa da ƙyar ya lallaɓa ya tashi yana ƙoƙarin fitowa, amma mai afkuwa ta riga ta afku. Nana na shiga ɗakin ta faɗa jikinsa, ya taro ta. Gaba ɗaya jikinta ya saki kuma ya yi sanyi ƙalau, shaidar Ƙaisar ya buge ta.
Ya ɗauki wayarta, ya tura wa Ummi saƙo.
Tuni aka kira mijin Barira, jikinsa na rawa ya shigo gidan, tare da rakiyar wasu mazan.
Ya durƙusa a kan Barira ya taɓa ta, ya ɗago ta, sai dai ya ga tana numfashi, sai dai idanunta a kakkafe, ya girgiza ta yana kiran sunanta "Barira. Barira ki buɗe idonki. Ki na ji na?" Barira ba ta motsa ba, kuma ba ta yi magana ba. Sai dai numfashinta yana fita normal.
Mijinta ya ce "Dan a samo adaidaita sahu mu tafi Asibiti"
Ɗaya daga matan da abin ya faru a gaban su ta ce "Wane Asibiti, ai ko an je Asibiti babu abin da za a gani, Nanan za a janyo daga ɗakin, a yi wa dukan tsiya a sanya ta tsallaka ta, shi ne za ta tashi, kama mata kurwa ta yi"
Ɗaya daga mazan ya ce "A'a ba za a dake ta ba, a kai ta dai gurin hukuma, a san abin yi."
Mijin Barira ya ce "Wane irin kar a dake ta, kana kallon halin da matata take ciki"
Ya miƙe ya nufi ƙofar ɗakin su Nana, cikin ɗaga murya ya ce "Kina ina, ki fito ki tsallake mini mata, ki sakar mata kurwa" Sai dai ya ji shiru, babu wanda ya yi magana. "Ki fito ko na shigo wallahi"
Wani ya ce "Kar a yi haka Gali, ka ga matar aure ce, bai kamata a bi abin da mata suka faɗa ba, kamata ya yi a zurfafa bincike tukuna, kar a ɗauki doka a hannu, a zo daga baya a ji kunya"
Gali ya ce "Malam ni dai ba zan ji kunya ba da yardar Allah, kalli halin da yarinyar nan fa take ciki. Idan ta mutu fa? Wallahi ba zan yarda ba"
A fusace maƙwabcin na su ya ce "To a je Asibiti mana a duba, sai haƙilo ka ke yi, matarka matarka. Kamar ba nan ka ke jibgarta, ake ƙwatar ta da ƙyar ba, sai da aka haɗa