Showing 66001 words to 69000 words out of 122205 words

Chapter 23 - BUZU BOOK2 COMPLETE 2

18 Jan 2026

622

gyara jikinta, ta nemi guri ta kwanta, ya rasa abin da yake yi masa daɗi. Ya koma part ɗin sa ya rufe ƙofa, kawai ya fashe da kuka. Bai taɓa tunanin aikata zina a rayuwarsa ba, ba ta taɓa burge shi ba, bai kuma taɓa kawo ta a ransa ba. Sai dai yau ya wayi gari da aikata ta dumu-dumu.

Sai dai wani abin mamaki duk da abin da ya faru a tsakanin su, bai daina jin matsananciyar ƙaunar Jamila ba. Ya rasa dalilin da ya sanya Mummy ba ta son alaƙar su, duk da irin kusancin da yake tsakaninta da Jamilar.

A kwance Hajiya Sa'a ta dawo ta tarar da Jamila. Ta ce "Daughter haryanzu jikin ne? Ko Asibiti za mu je ne?"

Ta girgiza kai ta ce "A'a Mummy na sha magani ai"

"Yakamata ki warke, mun kusa zuwa taron ƙungiya fa na shekara, lokaci ya kusa"

Kawai Jamila ta gyaɗa kai.

"Ga shi kuma haryanzu babu wani labari da ki ka samo, a kan 'yar uwakki, dan haka sai ki shirya sadaukar da jini"

Jamila dai ta yi shiru, tana jin kamar ta kashe tsinnaniyar matar ta huta.

*****

Nana na zaune tana shayar da Muhsin, Nene tana gefe tana lissafa kuɗin da aka kawo mata daga gurin sayar da Abincinta.

Nana ta numfasa ta ce "Nene wai me yasa kwana biyu ba kya fita gurin Abinci ne?"

Nene ta kalle ta ta ce "Na fita ki samu damar guduwa ko?"

Nana ta yi turus tana kallon Nene.

Nene ta yi murmushi ta ce "Yarinyar nan ki na wasa da ni, tuni na gane duk wani take-taken ki ai, jira nake yi na ga iya gudun ruwanki. Ke yanzu idan ki ka fita gidan uban wa za ki je? Ki na da tabbacin za ki iya sake haɗuwa da mutanen da za su kula da ke ne? Ko an gaya miki kowa ne zai iya yin taimako?

Kin tattara kayanki gaba ɗaya, kina ɗauke ɗanki daga ɗakina, jira ki ke yi ki samu dama ki gudu, to ki tafi duk inda za ki tafi, amma ba za ki tafi da jaririn nan kina gararanba a gari ba, tun da duk ƙoƙarin da nake yi a kan ki ba kya gani. Kina zaune a nan na saka ana ta yi mini cigiyar masu gadi da suke zuwa Nigeria, ko akwai wanda ya san mai suna Habu ko Sayyid ki ka ce sunansa ko wa? Anma ba kya gani, to ki fita ki tafi duk inda ki ka ga dama, tun da ba ki da kan gado, kuma ba ki san darajar igiyoyi ukun da ke kan ki ba"

Nana ta sha jinin jikinta, da faɗan da Nene take yi mata. Ta ce "Dan Allah Nene ki yi haƙuri, na ga na ɗora miki ɗawainiya ne ga shi haryanzu ina zaune babu wani labari a kan sa".

"Ni na ce kin ɗaura mini ɗawainiya ne uwar iya? Ki yi duk abin da ki ka ga dama"

Nana ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri ba zan sake ba" Nene ta yi mata shiru, daidai lokacin kuma Muhsin ya gantsarawa Nana cizo, da 'yan haƙoran da suka fara leƙowa.

A fusace ta dake shi a kan pampers ɗin jikinsa, ta cire shi daga jikin Nonon, ta zaunar da shi tana ƙara tsuke fuska tare da hararsa.

Sexy eyes ɗin sa irin na mahaifinsa ya zuba mata, yana kallonta ko ƙiftawa ba ya yi, gaba ɗaya ya rikiɗe fuskarsa ta koma ta Sayyid sak, farar fatarsa ta yi jawur.

Nene ta ce "Yaka yaron kirki, ka ƙyale ta da halin ta, shi ne za ki huce a kansa, ai ni na yi miki ba shi ba"

Ya rarrafa ya koma jikin Nene ya kwanta yana ci gaba da kallon Nana. Sai kuma jikinta ya yi sanyi ta ji zuciyarta ta yi mata nauyi da abin da ta aikata, ba tare da duba ƙanƙantar ɗan yaron nata ba.

Ta shige ɗakinta ta mayar da kayanta da ta haɗe guri ɗaya inda suke. Wayarta ta ɗaukko da babu layi a cikinta, ta duba jakarta ta ɗaukko memorynta ta mayar kan wayar, ta fara duba hotunan Sayyid da ke ciki. Har da hotunan  Haidar ɗan gurin Shukura a cikin wayar, da hotunanta na aure da aka yi mata da wayar.

Gaba ɗaya ta ji tana kewar ƙasa Nigeria, amma hakan bai sanya ta ji za ta iya komawa a yanzu ba.

Tunaninta ya katse bayan da ta ji muryar wata ƙawar Nene a tsakar gida, wadda ita ta yi hanyar kai Nana gurin koyon girke-girke. Amma Nana ta ƙi fitowa.

Hira suke yi da Nene, take ba ta labarin ma'aikata ake nema, wanda suka iya girki sosai a wani restaurant, na wata Hajiya a can cikin birnin Maraɗi.

Nene ta ce "Ba na yi wa Nana irin wannan harkar ne, saboda mutanen banza, ba dan haka ba ai da na ce ta je, tun da ta iya girki sosai"
Matar ta ce "To ai a ɓangaren girki kawai za ta zauna, su na buƙatar kuku amma mai tsafta wadda ta iya girki, kuma tana biya sosai kin san buzayen nan kamar ba su san ciwon kuɗi ba, buzuwa ce mai gurin"

Nene ta ce "Ai kin ga tana da yaro, shayarwa take yi, ai da na ce a kaita, amma idan za su ɗauke ta da yaron shikenan".

"Anya kuwa, gaskiya ba na tunanin haka, ba ma za su yadda ba. Idan ta tafi a ƙalla za ta iya yin wata, ba ta zo gida ba, za a ba ta komai a can. bari na tashi na tafi dama tsayawa na yi mu gaisa sai anjima"

Suka yi sallama matar ta tafi.

Nana ta fito da sauri ta ce "Nene, ina son zuwa gurin abincin buzayen nan"

Nene ta ce "Kin yarda mijin naki buzu ne kenan? Daga an ce gurin buzuwa kin rikice za ki je, bayan da kin ce mini ba ki san ƙabilarsa ba, Allah dai ya shirye ki."

Nana ta yi shiru, tana mamakin yadda aka yi Nene take iya gano ta idan ta yi mata ƙarya.

Nana tun dukan da ta yi wa Muhsin, juyin duniya har la'asar bai ƙara waiwayarta da sunan ta shayar da shi ba.

Sai da ta ji sun cika, sun fara damunta, sannan ta ɗauke shi ta ba shi, amma fafur ya ƙi karɓa, ta kaɗa ta raya ya ƙi sha.

Nene tana kallon su, ta ƙi magana, ta dama masa kunu ta haɗa da nono ta zaunar da shi ta ba shi ya sha, ya ci gaba da wasan sa.

Nana ta ga sun mayar da ita saniyar ware ma. Har garin Allah ya waye, bai saurari Nana ba.

Ta sake ɗaukarsa, saboda yadda nonon ya cika, yake yi mata ciwo, amma fafur yaron nan ya ƙi sha.

"Dan Allah yaron kirki ka yi haƙuri ka sha, ba zan sake dukan ka ba, dan Allah ka sha ba ka isa yaye ba" Nana ta yi maganar cikin damuwa.

Nene ta kwashe da dariya, ta ce "Kin ga ki ƙyale yaron nan, ina ga fa ya yi zuciya ya yaye kansa, sai dai yi haƙuri"

Kamar Nana za ta yi kuka ta ce "Nene wata takwas sai ya yaye kansa? Ya yi wuri ai"

"To ba ke ki ka janyo koma mene ne ba?, tun da kin ce da babansa yake kama komai da komai, wataƙila har halayensa ya ɗaukko, kuma wataƙila wannan abin da ya yi akwai abin da yake nunawa bamu gane ba. Tun da yana shan kununsa, yana rarrafensa, ki rabu da shi kawai. A haɗa sabaya da sauran saiwoyi, ki yi ta sha saboda kar su lalace".

Kamar Nana za ta yi kuka ta ce "Nene wata takwas fa"

"To ai ga ki nan ga shi. Sai ki ba shi ya sha ai"

Da Nana ta ɗauke shi da nufin, ta shayar da shi, sai ya hau zunduma ihu,yana turjewa sai dai ta ƙyale shi.

Nana ta din ga jinjina yadda aka yi, ɗan wata takwas ya san ya yi zuciya da abu.

Sai da aka kwana huɗu, Nana ta ga da gaske ya yaye kansa, iyaka ya zo jikinta ya yi wasan sa ya tafi.

Nene ta ce "Nana ki daina damuwa fa, girmansa tubarkallah da ƙiriniyarsa kamar ta ɗan shekara guda ce, ki rabu da shi kawai, daga yanzu idan za ki yi magana ki din ga yi masa da girmamawa, ki daina yi masa tsawa, manya ba sa son wargi. Kuma ki din ga duba darajar sunan da ki ka sanya masa" ta yi maganar tana yi wa Muhsin rawa.

"To Nene sai na bari ya lalace ba zan ce masa bari ba?"

"A'a ban ce kar ki ce masa bari ba, amma a wannan yanayin shi sarki ne, abin da yake so haka za ki yi haƙuri ki yi masa. Da kin tsaya a zare masa ido kawai da haɗe rai, amma saboda na yi miki faɗa, ki ka haɗa masa da duka, kuma ki ka ƙwace ki ka dungurar da shi, dole ya bar miki abin ki ai".

Nana kalle shi yana ta wasa da kofi, yana bugawa a ƙasa, shi ma ya ɗago ya kalle ta. Sayyid ta tuna lokacin da ya ritsa ta yana yi mata kashedin a kan daina yi masa tsawa ko ɗaga masa murya.

Wani guntun murmushi ya suɓuce mata.

Nene ta ce "Ni kuwa Nana ga shawara"

Ta ce "To Nene"

"Kamar yadda ki ke faɗa motsi ya fi laɓewa, na ce ko dai za a jarraba ki je gurin aikin nan, na harkar dafe-dafen ko Allah zai sanya a dace. Duk da ba na jin a jikina, masu kuɗi a cikin buzaye masu katafaren gurin abinci, za su iya tafiya aikin gadi, amma bamu san ina rana za ta faɗi ba"

Nana ta ɗan yi jimm sannan ta ce "Ban san ya zan yi ba ne, tun da kin ga ga Muhsin. Ko za su din ga bari na je na dawo kullum?".

Nene ta ce "Ki na ji fa ta ce sai ki yi wata ba ki zo gida ba, kuma akwai tazara a tsakaninmu sosai, kuma ba zai yiwu ki tafi da Muhsin ba, ba za su yarda ba. Amma ga shawara idan kin ga kin yarda da ni, ki bar mini Muhsin a nan, ki je ko ai

kin na wata uku ki yi, ko Allah zai sanya a dace, sai ki ci gaba da cigiyarsa a gurin."

Ayshercool

08081012143

67

Nana ta yi turus, tana kallon Nene.

Nene ta ce "Ba zan yi miki dole ba, dan kuwa wannan magana ce da kowacce uwa sai ta jinjina girmanta da nauyinta.
Sai dai ni ba zan takura miki ba kuma ban ce sai kin yadda da ni ba, ko mene ne za mu yi shi ne a gaban hukuma, mu je mu yi yarjejeniya mu saka hannu sannan ki tafi. Ban san dalilin da Allah ya sanya ya haɗa ni da ke ba, duk rashin son mutane na, ki ka shiga raina ba nake tausayinki ke da yaronki. Har ga Allah ina fatan ki haɗu da mijinki ko danginsa, ki samu ki koma gida ki nutsu ki kula da yaronki. Kamar yadda na gaya miki ne, ba zan yi miki dole ba, ki je ki yi shawara idan kin amince shikenan, idan ba ki amince ba babu wani abu, ni dai fatana Ubangiji Allah ya bayyana abin da ki ka fito nema".
Nana ta yi shiru, ƙwaƙwalwarta gaba ɗaya ta ɗauki caji da tunani daban-daban.

****
Jamila kuwa tun da ta je gida, Mama take tambayarta ko lafiya ta ganta wani iri, amma ta ce mata babu komai.
Ta shiga ɗaki ta nemi guri ta kwanta, sallolinta kawai ta yi na magariba da isha'i ta sake kwanciya. Gaba ɗaya abin Duniya ya gama damunta, dana sani da takaici duk ya cunkushe mata zuciya.
Wayarta ce ta fara ringing, ta duba ta ga baƙuwar lamba ce, jikinta ya ba ta Abba ne, ta ɗaga kiran ta saka a kunnenta.
Muryarsa ƙasa-ƙasa ya kira sunanta ya ce "Ya jikin naki?"

"Da sauƙi" ta amsa a hankali hawaye na ci gaba da gangarowa kan kumatunta.

"Dan Allah Jamila ina ƙara ba ki haƙuri, kuma ki dubi girman Allah ki rufa mini Asiri, ke ma kin san hakan ba halina ba ne ba. Wallahi na rasa inda zan sanya zuciyata na rasa abin da yake yi mini daɗi. Yanzu haka zazzaɓi ne a jikina. Dan Allah ki yafe mini Jamila, na san koma mene ne duk laifina ne. Amma in sha Allah kamar yadda na yi miki alƙawari zan aure ki Jamila, wallahi ina son ki, duk abin nan laifin Mummy ne amma ki yi haƙuri ki yafe mini"
Jamila ta ci gaba da kuka, ta kasa ce masa komai, ya ƙara ruɗewa ya ce "Dan Allah ki yi mini magana, dan Allah ki yafe mini idan ba ki yafe mini ba na san har na koma ga Allah, ba zan samu nutsuwa ba" Ya yi maganar yana kuka mai cike da nadama tamkar ƙaramin yaro.
Duk yadda Jamila ta so jin haushinsa sai ta kasa, tabbas ita shaida ce wannan ba halin Abba ba ne, dan da halinsa ne da ba zai din ga wannan kukan ba, zai ga ya ci bulus ne kawai.

"Yaya Abba na yafe maka, mu haɗu mu nemi yafiyar Allah, sannan ka daina kukan nan dan Allah, ka sha magani ka kwanta. Kuma Asiri idan na tona kaina na tonawa ba kai ba, Ubangiji Allah ya yafe mana"

Ya tashi zaune a kan gadonsa, cikin damuwa ya ce "Da gaske kin yafe mini Jamila?"

"Eh Yaya Abba, sai da safe, kaina yana ciwo sosai"

"To na zo na kai ki Asibiti ne?"

Jamila ta ce "A'a, na sha magani ina jin bacci ma, sai da safe" ta katse kiran tana ƙara duƙunƙunewa a cikin bargo.

Wata irin ajiyar zuciya ya din ga yi, ya nemi guri shi ma ya kwanta, zuciyarsa fal tunani daban-daban.

*****

Nana hankalinta ya rabu kashi-kashi, a jikinta ba ta jin Nene za ta cutar da ita, duba da yadda take ɗawainiya da ita da ɗanta, tamkar ita ta haife ta. Sai dai ta yaya za ta iya ta tafi ta bar ɗan ta, da matar da babu dangin iya babu na Baba a tsakanin su.
Sai dai tabbas akwai buƙatar ta gusa, ta yi wani yinƙuri, domin ci gaba da ƙoƙarin haɗuwa da mijin nata, amma ba ta ji ta gamsu da wannan shawarar ba.
Sai dai tun da suka yi maganar nan, da ta kwanta take mafarki ga ta a gurin girke-girken, tana cikin gurin girkin, ta waje sai ga din ga jiyo muryar Sayyid yana magana. Idan ta fita sai ta neme shi ta rasa, sai dai ta ci gaba da jin muryar ta sa, nesa da ita kaɗan, sai dai ba ta san daga wane ɓangaren muryar tasa take ba. Sai ta yi irin wannan mafarkin sai ta farka.
Ta rasa abin da yake yi mata daɗi, kawai sai ta ci gaba da addu'a a kan lamarin, ta juya ta ci gaba da bacci, sai dai babu tsammani sai ga ta a ɗakin karatun Ƙaisar, an yi mata gyara sosai, an ƙara yawan litattafan da suke ciki.
Ya saka mudubinsa a gaba, yana ta zuba masa wani ruwa yana wanke shi.
Bai ce wa Nana komai ba, har ta gaji da tsayuwa, ta ɗan yi gyaran murya. Ya ɗaga kai ya kalle ta. Ta ce "Sannu da aiki"

"Yauwwa" ya amsa yana tashi tsaye.

Ta ce "Kwana biyu ina ka shiga ne?"
Ya ɗaga kai ya kalle ta ya mayar ya sunkuyar yana ɗaukar wani littafi.

"Amm dama ina ta son na ganka, na tambaye ka, sannan na roƙe ka alfarma. Dan da kai da Giyaz da duk wani mai son ɗaukar fansa a kan zuriyarmu, ya ɗauka a kaina, dan Allah ku ƙyale mini yarona. Na ga rannan ka ba shi wani abu da ban san ko mene ne ba, dan Allah kar ku yi masa komai"
Bai ko motsa ba, balle ta sanya ran zai yi mata magana.

"Ƙaisar ka yi magana ma dan Allah"
"Na ce miki ne? Ko har kin manta abin da ki ka faɗa a kaina, saboda abin da na yi wa mahaifina a kan na kare ki?"

Sai kuma Nana ta yi shiru, ta sha jinin jikinta.

Ya wurgo mata littafin nan da ta fara karantawa, ya ce "Ga wannan ki ci gaba da karantawa, wataƙila zai yi miki amfani a gaba" Ta kalli littafin ta kalle shi, ta ce "Me yasa ka amince na karanta wannan littafin, wancan kuma ka hana ni karantawa? Ni ba zan iya ci gaba da karantawa ba, babu komai a ciki sai tashin hankali da zubar da jini na tsagwaron rashin tausayi da adalci, ni bai burge ni ba, ba zan karanta ba"

"Ko? Amma idan an yi magana sai ki nuna kamar babu wata halitta da ta kai ɗan Adam tsarki da tsoron Allah. Allah ya karrama ɗan Adam a kan dukkanin halittunsa. Amma ba duk ɗan Adam ne mai tsarkin zuciya ba. Wannan zubar da jinin da kashe-kashen da yake rubuce a cikin littafin nan, da gaske an yi su, domin cimma buƙatar Duniya, kuma haryanzu ana kan yi ma. Abu ne da ya faru wani ƙarni a baya, kuma abin yake ta bibiyar zuriyar har wannan zamanin. Na ce ki karanta kin ƙi, kin ce ba kya so shikenan ba zan yi miki dole ba, amma bari ki ga wani abu.
Ya ɗauki littafin ya buɗe cikin wani feji, ɓangare ɗaya na bangon littafin zane ne, ɓangare ɗaya kuma bayanin yadda taswirar zanen take ne. Ya haska littafin a jikin mudubin.
A nan take hoton ya bayyana a jikin mudubin, wannan ɗakin da take ganinta a ciki ita da Sayyid shi ne ya bayyana a jikin mudubin, ba iya haka ba har ƙamshin da gurin yake yi ta fara ji a hancinta.
A rikice ta ce "Nan gurin? Dama ina son sanin ina ne, yaya aka yi muke zuwa gurin nan ni da Sayyid, kuma idan abu ya faru a gurin kamar gaske."
Ƙaisar ya rufe littafin ya ce "Ai kuma kin yi wa kan ki, ba zan bayar ba. Ya jefa littafin sama ya ɓace ɓat ita kuma ta tashi daga baccin.

****

Kwana biyu Jamila ba ta je gidan Hajiya Sa'a ba, saboda jikinta da ya matsa, idan Abba ya kira wayarta a kashe, ga shi ba ta zuwa gidansu, shi ba abin ya tambayi Mummy ba.
Yana kwance a ɗakinsa, ya tura mata saƙo. "Hankalina a tashe yake ƙanwata, dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login