Showing 18001 words to 21000 words out of 122205 words
goro ƙwarya dubu biyu ta rafi ta ce a bawa mamman wakilin rafi, gaisuwar iyaye" sai kuma aka saka shewa. Ba yau Nana ta fara ire-iren wannan jiye-jiyen ba, amma ta tsorata da wannan sosai da sosai. Ta rirriƙe Sayyid, ga sanyin da take ji ya fara damunta.
Cas cas cas, ta fara jin sautin kaɗawar wani abu mai kama da abin ado na mata.
Ta kalli tsakar gidan ta hango wata irin zanƙaleliyar mata, mai tsawon gaske ƙafafuwanta duk sarƙoƙi, ta yi shigar Fulani, sai dai ita ma ba a iya ganin sawayenta tamkar a kan iska take tafiya. Ta ɗan ƙara buɗe idonta, ta ga rana ce tarwai a tsakar gidan, ga dandazon mutane ana ta hada-hada. Sai dai shigar mutanen irin na zamanin da ne can baya sosai, kamar dai taron wani abu ake yi.
Wata mata ta hango sanye da kayan saƙi farare tas, ƙugunta sanye da wuri, kanta babu ɗan kwali duk ta yi wa tulin gashinta adon wurin, hannunta riƙe da sandar dargaza, tana kaɗa ta tana juyi.
Wannan bafulatanar ce ta tsaya a bakin ƙofar ɗakin Nana ta ce "Baƙuwarmu, bikin girka ake yi, ko za ki taso ki ga yadda muke gudanar da al'adun bikin girka?" ta yi maganar tana zuro zanƙalelen hannunta cikin ɗakin Nana".
"La'ilahaillalah, Sayyid, Sayyid wayyo Baba" ta tashi a gigice, rirriƙe ta ya yi, ya janyo wayarta, ya haska ta. Fuskar sa cike da mamaki yake kallon ta, yanayin fuskarsa ke bayyanar da alamar tambaya.
"Sayyid wata mata ce, wata mata ce take ziro hannunta, tsoro nake ji, wasu mutane ne a tsakar gidan nan" ya haska ɗakin ta ga babu komai, haka tsakar gidan ma dare nesai hasken farin wata, babu komai. Sai a lokacin ta fahimci mafarki take yi. Ya ji jikinta ya yi sanyi ƙalau, amma bai ga Ƙaisar a gurin ba, bai kuma ga wata alama da take nuna yana gurin ba.
Gaba ɗaya ta nemi ko addu'a ɗaya, ta rasa a cikin kanta. Ta kaɗa ta raya amma babu abin da ya zo da kanta. Tana so ta karɓi wayarta ta kunna karatun Alƙur'ani, amma ko ƙwaƙƙwaran motsi ba ta son yi, saboda tsoron da take ji.
Da ƙyar wani baccin ya ƙara sace ta.
Babu babban abin da ya ba shi mamaki, irin yadda da safe take komawa normal, babu ma alamar akwai wani abu da yake ba ta tsoro cikin daren.
Haka ta ci gaba da sabgoginta. Sai dai gaba ɗaya a kunyace take, ko idonsa ba ta iya kallo, saboda abin da ta aikata ya kama ta cikin dare. Shi ga tausayin kan su, ga kuma dariya ta ba shi.
*****
Baba yana zaune yana shan koko da ƙosai a tsakar gida, sai ga kiran wayar Uwani.
Ya kalli wayar tasa ya ce "Tofa! Wannan jarababbar tsohuwar ko me za ta ce mini, take kira na da safiyar nan oho.
Ya ɗaga kiran ya saka a kunnensa. Sai dai ba ya jin ta sosai saboda rashin network. Ba ta haƙura ba ta din ga kira har sai da ransa ya fara ɓaci.
"Uwani ko a haƙura da wayar ne, kin ga babu network ne"
"A'a ina jin ka yanzu. Amm dama kiran ka na yi, na tambaye ka ina Nana kuwa?"
"Nana, tana gidan mijinta"
"Gidan mijinta wanne?"
"Mijinta dai na aure"
Uwani ta ce "Eh a ina gidan yake?"
"Amm can wajen gidan Ummi ne"
"Rufe mini baki, mutumin banza da na wofi. Ai kwana uku kenan ina neman layinka, amma bana samu saboda garin nan bamu da natiyok ake cewa ko me?"
"Uwani wai me ya faru ne?"
"Ai ba za ka san meyafaru ba, tun da ka bar yarinya tana ragaita ita kaɗai ranta ga miji mai larura,an kore su daga gidan haya, ba su san ma inda za su je ba, kana zaune hankalinka kwance. Ai ko 'yar riƙo ce Nana ka duba lamarinta"
Ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba, ta wanke shi ta tas, ta ƙare masa zagi da cin mutunci, ta ce kuma za ta kira Yaya Atine ma, sai ta ci ubanta.
Ran Baba ya yi mummunan ɓaci, kenan Ummi da Nana haɗa kai suka yi, suka kai ƙararsa gurin Uwani. Ya kira Ummi ita ma ya fara sauke mata kwandon tijara. Ranta ya ɓaci ta ce "Ni fa Baba ban kai ƙarar ka gurin kowa ba, Uwani ce ta kira waya, mu na tsaka da alhinin halin da Nana ne ciki, na gaya mata komai, kuma ni na faɗa ba Nana ba. Shi ne ta ce Nana su koma Ƙauye can gurin ta".
Sai kuma Baba ya yi sak. "Ƙauye kuma? Ta yi me a ƙauye?"
"To Baba zaman nan ɗin ya ƙi, kai kuma ka ƙi taimakawa, babu yadda muka iya Nana tana Buda"
"Ke Ummi ki na ji na, duk yadda za ki yi, ki nemi kuɗin mota, ki je Buda ki taho mini da 'ya ta. Lallai ya sakar mini 'ya ku taho tare, ya je Allah ya ba shi lafiya"
"Baba ya sake ta, 'yan uwansa ma ba a sa inda suke ba, wa za ta bar wa shi a can?" Yana cikin bambami kuɗin wayar suka ƙare.
Dama Mama na tsaye tana jiran ya gama wayar, yana gamawa ta dube shi ta ce "Wato Nana ta kaso aurenta ta dawo ko? To wallahi ta dawo gidan nan ba ta da gurin zama, wai har ka manta irin zaman azabar da muka yi da yarinyar nan a cikin gidan nan? Babu bacci kullum bala'i da tashin hankalin iskokai, ba zai yiwu ba wallahi"
Sai dai kafin Baba ya ba ta amsa, suka ji Suwaiba ta ƙyaƙyace da wata irin dariya mara daɗin ji tana faɗin "Asma'u a ƙauyen Buda, tushiya masomar dawa, kowa ya bar gida gida ya bar shi" ta yi maganar tana ci gaba da ƙyaƙyata dariya kamar ba mace ba.
"Ke Suwaiba meye haka, wannan wace irin dariya ce? Ban hana ki irin wannan dariyar ba kamar ba mace ba?"
Suwaiba ta ce "Ina ruwan ki da dariyata"
Baba kawai ya gyaɗa kai, ya gyara hularsa ya fice ya bar gidan gaba ɗaya.
****
Rashin maganar nan ta Sayyid, ba ƙaramin damun Nana take yi ba, abin ya yi yawa sosai.
A wannan karon ta yi sa'a, ya bar ta ta je gurin Uwani, daga nan kuma ta je ta yo musu sayayya. Ta tafi ta bar shi da wayarta, domin ta ɗebe masa kewa.
*****
Alhaji Zailani ya saka sabon layin da ya sayo a cikin waya, ya kira lambar Nana. Sayyid yana kwance yana jin yadda wayar take ta vibrating, amma ya yi banza. Saboda ko ya ɗaga ba iya magana zai yi ba.
Jin mai kiran ba shi da niyyar daina kiran, ya sanya ya ɗauki wayar zai kashe. Sai dai ya fasa kawai ya ɗaga kiran ya kara a kunnensa.
"A tunanki dan kin yi blocking ɗin lambata, zai sanya na kasa cimma burina a kan ki ne? Yanzu hankalina ya dawo gare ki, na saka an kori mijinki daga gurin aiki. Kuma zan nemo ki duk inda ki ka shiga sai na cika burika a kanki" wani irin jiri Sayyid ya ji ya fara ɗibar sa.
"Ba za ki yi magana ba?" Alhaji Zailani ya yi maganar yana kallon wayarsa. Wani irin haske ya ga wayar tana yi, tana fafar fafar za ta ɗauke. Mamaki ya kama shi, dan wayar ba ta taɓa yin haka ba. Fitilun ɗakin suka ɗauke, duhu ya gauraye ɗakin nasa. Sai ya rikice ya tashi tsaye yana waige-waige.
"Karo na biyu, ka sake shigowa hanyata, duk da gargaɗin da na yi maka, cewar mallakina ce, ina sake yi maka gargaɗi, kafin na tona maka asiri." Alhaji Zailani ya toshe kunnensa, saboda wani irin sauti da yake ji mara daɗi, ga ɗakin yana ta jujjuya masa.
Can ya ji shiru ya daina jin sautin, ya buɗe idanunsa a hankali. Sai dai ya ga Shukura a tsaye a gabansa, jini yana bin ƙafafuwanta, ga wuƙa a hannunta, tsirara ta.
Ya miƙe cike da razani, ya fara ja da baya.
"Daddy ina jaririna? Ka bani jaririna Daddy" Ya ci gaba da ja da baya. Da gudu ta bi shi, da wuƙar tsirararta. Ya fita da gudu yana ihu.
"Alhaji lafiya kuwa? Anya hawan jinin nan bai fara taɓa maka ƙwaƙwalwa ba, ya ya zaka din ga ihu haka?" Hajiya Amina ta yi maganar cikin mamaki tana kallonsa. Ya kalli gurin ya gan shi a kan gado, a ɗakinsa. Yana son yi wa Hajiya Amina tambayoyi, amma abu ya gagara saboda tsabar razani da tashin hankalin da yake ciki.
AREWABOOKS
*****
Uwani ta din ga yawo da Nana a cikin ƙauyen nan, tana nuna ta a dangi, tana gaya musu 'yar gurin Isa ce. Dan galibi ba su santa ba.
Nana gaba ɗaya hankalinta yana kan Sayyid da ta baro a gida, shikaɗai tana gudun kar ta je yana buƙatar wani abin. Ganin gantalin ya yi yawa, ga duk inda suka je sai Uwani ta tsuguna ta surutu kamar babu gobe.
Tun Nana tana jurewa, har ta gaji ta ce "Uwani, na bar mara lafiya a gida, ko za mu je inda zan yi sayayyar, na koma kar na je yana buƙatar wani abin.
Uwani ta ce "Kuma fa haka ne, to mu je na raka ki. Na so ma sai ranar kasuwa za ki je sayayyar, an fi samun rahusa. Ai tun da Allah ya sa ki ka zo garin nan, za ki yi ta ganin 'yan uwa da dangi, za a yi ta zuwa duba mijin naki ma"
Ita dai Nana ta yi shiru, dan duk surutunta, Uwani sai da ta saka ta gaji, ga azabar tafiyar ƙafa da suka sha.
Ta rakata inda ta yo musu 'yan sayayyar kayan abinci, gaba ɗaya tsoron taɓa kuɗin take yi. Gani take yi kamar ƙarewa za su yi.
Uwani ta raka ta har gida, sannan ita ma ta zagaya, ta koma nata gidan.
Nana ta shiga ɗakin da Sallama, tana faɗin "Sayyid, ka ganni sai yanzu ko, ka yi haƙuri Uwani ce ta din ga ja na, ƙafafuwana kamar su karye" Sak dai ta yi shiru ganin wata irin kwanciya da ya yi a kife a kan cikinsa, hannunsa a lanƙwashe, kuma ba kamar mai ruf da ciki ba.
Ga shi a tsakiyar ɗakin, ba inda ta tafi ta bar shi ba.
Ta zube kayan ta nufe shi jikint a sanyaye, gabanta na bugawa saboda fargaba da tsoron ko mutuwa ya yi.
Aikuwa tana juya shi ta ɗan ja da baya a tsorace tana sauke numfashi.
Wayarta ta gani a ƙarƙashin inda ya kifa, idanunsa a kakkafe, babu baƙar ƙwayar idon, sai farar. Ga jikin zafi rauuu tamkar wuta.
Ajiyar zuciya ta yi cike da damuwa, ta matsa kusa da shi ta yi Bismillah ta fara rage masa kayan jikinsa. Ta ɗebo ruwa ta din ga shashshafa masa tana sake nanata Bismillah.
Ta je ta rufe ƙofar gidan, ta dawo ta cire rigar jikinta, ta kwanta a jikinsa, tana rintse idanunta saboda raɗaɗin da take ji a fatarta.
Wani irin nishi yake, tamkar zai yi gurnani, yana miƙa jikinsa yana ƙara sandarewa.
A hankali ta ji tamkar hankalinta yana gushewa, ita ba a farke be, kuma ita ba mai bacci ba. Ta ɗan ɗaga idonta, ta ga Ƙaisar tsaye a jikin ƙofar ɗakin yana kallon su. Ta yi shiru ba ta yi motsi ba, kuma ba ta yi magana ba, fatanta Sayyid ya samu sassauci daga azabar raɗaɗin da yake ji.
"Ko dai ki bi a hankali, ko wannan ɗan tayin na cikinki ya yo waje saboda zafin jikinsa. Ko kuma Giyaz ya yi masa mummunar illa." Nana ta ɗaga kai ta kalli inda Ƙaisar yake, jikinta ya yi mata wani irin nauyi, ba ta ko iya motsa ɗan yatsanta.
"Babu irin kashedin da ban yi miki ba tun da fari, ki ka yi burus da ni, gani ki ke kawai cutar da ke ne kaɗai abin da nake yi.
Amma tun da jimirnki taurin kai, wahala sai ranar da Allah ya yanke miki, tukuna ma." A hankali ta lumshe idanunta har ta daina jin muryar Ƙaisar.
****
Cikin damuwa Maijidda take kallon Saude ta ce "Yaya Saude haryanzu lambar Nanan ba ta shiga ko? Gaba ɗaya na kasa nutsuwa duk ji nake hankalina a tashe".
Saude ta ce "Dan Allah ki daina damun kan ki, in sha Allah tana cikin ƙoshin lafiya, kin san sharrin wayoyin nan, da rashin network, amma zan ci gaba da kiran ta, da na same ta zan sanar miki, kuma zan sake zuwa har gida na haɗa ki da ita."
"To Allah ya sa dai lafiya, kin ga na yi, na yi, na kaɗa na raya, Baban su Walida ya ƙi ba ni wayata, tsawon wannan lokaci haka nake zaune babu waya. Kuma duk wasu dabaru da zan yi na samu dama na je Kano na samu na ga yaran nan, abu ya ci tura sai ka ce ba Muslimi ba, ba ya jin magiya ba ya jin rarrashi".
"A'a kul Maijidda, uban 'ya'yan naki ki ke cewa kamar ba musulmi ba, kar ki sake. Ki rabu da shi da halinsa. Duk da Nana tana cewa za ta zo ita da mijinta, idan ma ba su zo ba, ni zan sake komawa na gano miki ita in Allah ya yarda. Iliyasu kuma ki rabu da shi ku lallaɓa kar ki fusata shi ya yi wani abin da ba a fata"
Maijidda ta yi ajiyar zuciya, ta jinjina kai kawai, amma gaba ɗaya ba ta cikin nutsuwarta.
****
Abu kamar wasa, aka shafe kwanaki biyar, Sayyid yana cikin wannan yanayin, sai dai Nana ta juya shi, ta goge masa jikinsa, ta yi masa ƙanin wanka a ɗaki, ta shafa masa turare ta saka masa kaya.
Ga shi juya shi kawai aiki ne, saboda yadda ya yi mata nauyi, ga jikinta babu ƙwari saboda azabar laulayi. Juriyarta ce kawai ta sanya ba a gane mawuyacin halin da take ciki, dan ba ta taɓa yarda ta kwanta.
Ga shi jikinsa duk ya kumbura, mussaman ƙafafuwansa.
Tana zaune ta yi shiru tana kallonsa, kawai tamkar an yaye mata wani abu daga kanta, sarkin baka ya faɗo mata. Sai da ta ɗan zabura ta tafi tunanin ko yana wani hali yanzu?.
"Ko dai can zan kai ka Sayyid?" Ta yi maganar tana kallonsa.
"To ni da ban ma san a ina yake ba, ta yaya zan kai ka?"
"Kul mene ne sahihancin magungunan da yake bayarwa? Mene ne halacci ko haramcin abin da yake yi, da za ki je neman magani gurinsa?" Wata zuciyar ta gargaɗe ta.
Sai kuma ta yi shiru, tana tuna irin wahalhalun da ta sha, da faɗi tashin gurin masu magani, ita dai tana da yaƙinin har gurin bokaye da 'yan tsubbu an kai ta, domin a nema mata magani. Domin wasu ƙarara ayyukansu da abubuwan da suke faɗa, ne nuni da kaucewa hanyar gaskiya.
"Allah na tuba, Allah ya sanya ba wannan ne dalilan da ya sanya nake ta shan wannan wahalar ba. Allah ka yafe mini, ba da son raina aka din ga kai ni wasu guraren ba.
Allah ka bamu lafiya da ni da mijina, Ubangiji Allah ka yaye masa wannan larurar, ka dawo masa da tunaninsa. Allah ban yanke tsammanni da daga falalarka da ni'imamominka ba"
Ta juyo a hankali ta dubi gurin da yake, ta ga idanunsa sun dawo daidai yana kallon ta. A rikice ta ce "Sayyid"
"Ma vie"
Cikin tsananin murna ta ce "Alhamdillah, ka tashi?" Ya jinjina kai yana lumshe idanunsa da suka yi masa nauyi. Ya ja jikinsa ya tashi zaune da kyar. Sai dai jikin nan duk a kumbure,ga kuma haki da ya farfaɗo da shi. Haka yau ma ta taimaka masa ya yi wanka ya ci Abinci ya fara rama sallolinsa a zaune.
Kallonsa take yi cikin damuwa, yakamata a ce sun koma Asibiti. Amma kafin a nemo mota a saka shi, su yi sammako su koma Asibiti, aiki ne. Mussaman da babu wadattacen kuɗi a hannun ta.
A take ta tuna da maganin da sarkin baka yake haɗawa masu hawan jini, da wanda ɓarin jikinsu ya shanye a sakamakon hawan jini da matsalar zuciya.
Ba ta jira ya idar ba, ta zari hijjabi ta yi waje. Ta din ga tuhumar kanta da yadda aka yi tuntuni ba ta tuna ba, sai yanzu. Tun da su magunguna ne da yake haɗa s da saiwoyi ba wani surkullen ya yi ba.
Ta dawo ta tarar ya dawo bakin ƙofa ya zauna yana kallon hanya.
Tafiya mai nisa ta yi sosai da ta fita, ta samo ɓawon kwakwa da sassaƙen zogale, sai kuma farin zoɓo.
Ta hura wuta ta wanke su, duk ta zuba a tukunya ta zuba ruwa, ta kawo ɗan kanumfari ta zuba a ciki.
Sai da ta kammala sannan ta koma gurinsa, ta ce "Ka yi haƙuri, magunguna na je samo maka, na fita ka na salla"
"To na gode"
"Allah ya baka lafiya shugabana, Allah ya sanya ya wuce kamar ba a yi ba"
"Amin. Ke ma Allah ya baki lada, ya saka mini ke a aljanna. Ya sanya ki maƙwabci Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam a aljanna" waro ido ta yi ta gigice gaba ɗaya hawaye ya fara zirarowa daga idanunta ta ce "Sayyid ba ni da aikin da zai kai ni wannan matsayin. Amma ban san matsayinka a gurin Allah ba. Ban sani ba ko Allah ya karɓi addu'ar da ka yi mini. Amma a ce na maƙwabci Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam. Innalillahi wa Innalillahi raji'un Sayyid na rasa me zan ce. Baiwa ce mai tarin zunubai kuma mai tarin rauni. Amma Allah kai mai yawan rahama ne da falala, Allah ka amsa wannan addu'a da ya yi mini shi ma ka ba shi abin da ya roƙa mini"
Ya yi murmushi ya ce "Amin rayuwata"
"Sayyid, anya an taɓa yi mini addu'a da ta tsuma ni kamar wannan? Subhanallah, subhanallah. Na ji daɗi wallahi"
Shima idanunsa ne ya cika da hawayen, ya ci gaba da bin ta da idanunsa. Kawai sai Nana ta ji ta manta kaso mafi yawa na damuwarta. Da ta tuna Addu'ar da ya yi mata sai murmushi ya kasa barin fuskarta.
Maganinta ya daɗe yana dahuwa, ta sauke ta mayar da ruwan girki. Ta tsiyaya masa a kofi, ta je ta zauna a gaban sa.
"Sayyid ga magani na dafa maka, mu jarraba, bamu sani ba, ko Allah zai sanya a dace" ya kalli kofin ya kawar da kansa gefe, yana ɓata rai.
Ta marairaice ta ce "Dan Allah ka sha, babu ɗaci ko bauri fa"
"Ba na son magungunan nan, babu