Showing 60001 words to 63000 words out of 122205 words
Abinci.
Nana tana kwance tana bacci da azahar, saboda yadda Muhsin ba ya barin su bacci da daddare, saboda ba ya ɗaga wa Nana ƙafa da tsotso, ga kuka sai dai Nene ta taya ta riƙonsa.
Yana gabanta yana bacci, ita ma ya ɗauke ta, ta ɗaga kai ta ga ya shigo ta ƙofar ɗakin. Tana kwance ba ta motsa ba ta ga ya ƙaraso ya zuba musu ido, daga ita har Muhsin, ya sanya hannunsa ya shafa gashin jaririn, ya durƙusa ya sumbaci gishin yaron. Sannan ya kalli Nana idanunsa cike da hawaye.
"Sayyid, yaushe za ka zo ka ganmu? Mu na buƙatar ka a kusa da mu, dan Allah kar ka tafi ka bar mu"
Ya kama hannayenta ya riƙe a cikin nasa, sai dai bai yi magana ba. Sai da aka jima sosai yana murza yatsun ta a hankali sannan ya ce "Ma vie"
"Na'am"
"Gangar jikina ta kasa samun nutsuwa, rayukanmu su na kewar juna, ki kula mini da rayuwata da ke jikin ki, da jikin ɗa na, ina ƙaunarku Nana"
Riƙe Sayyid ta yi, tana kuka tana "Dan Allah Sayyid kar ka tafi ka bar mu, mu na buƙatar ka a rayuwarmu, dan Allah Sayyid, dan Allah"
Nene ta yi shiru tana kallon yadda Nana ta riƙe ta tana kuka.
Da yake sheshsheƙar Nanan ta jiyo, ta taho ɗakin tana zuwa ta tarar da Nana tana nema ta danne jaririn. Bayan ta ɗauke shi ne, Nana ta riƙe mata riga.
Nene ta zuba wa Sarautar Allah ido, Nana ta buɗe idanunta a hankali ta ga yadda ta riƙe Nene gam. A hankali ta cika ta tana sunkuyar da kai. Sai dai ta ɗaga kanta tana kallon ɗakin, tana jin ƙamshin turaren Sayyid a hancinta.
Nene ba ta ce mata komai ba, ta goya Muhsin ta fice da shi daga ɗakin.
Nana ta lallaɓa, ta tafi gurin da kayanta suke, ta bubbuɗe jakar kayan shafe-shafensa, da take ta adanawa tana kallon su tana jin daɗi. Sai dai a wannan karon hawaye take yi, tare da jin zuciyarta tamkar za ta buga. Ta zazzage kayan ta din ga bin su da kallo, ta ɗago Azurfarsa da ya ba ta, ta ce ya yi mata yawa, ya ce ta ɗaure da zare ta yi sarƙa da shi.
A hankali ta furta "Da mutuwa ka yi na san Allah ne ya karɓe ka babu yadda na iya, da aurenmu ne ya ƙare shi ma na san wannan ƙaddara ce, ba a kaina a ka fara ba. Amma ban san a wani hali ma ka ke ba, duk a inda ka ke ina fatan Ubangiji Allah ya sanya ka na cikin aminci da kwanciyar hankali Sayyid.
****
Yana zaune a kujerar da ke cikin ɗakin, da abu a cikin kofin yana sha a hankali.
Murmushi ya gaza barin fuskar Sultan, ya zauna a kusa da shi yana murmushi ya ce "Alhamdillah, sauƙi yana samuwa Imam, ya jikin naka?"
Ya kalli Sultan ya mayar da hankali ya ci gaba da shan shayin da ke cikin kofin hannunsa ba tare da ya furta komai ba.
Cikin damuwa Sultan ya ce "Har yanzu ba ka gane ni ba Imam?"
Har yanzun dai bai yi magana ba, bai kuma fasa shan shayinsa ba.
Sultan ya riƙo hannunsa guda ɗaya cikin nasa, ya ce "Imam ka kalli Abbanka mana, ka yi magana ko hankalina zai kwanta"
Ya waiwaya ya kalli dattijon.
Cikin murna Sultan ya ce "Ka na jin abin da nake faɗa?" Ya yi shiru yana ci gaba da kallonsa, bai yi magana ba.
"Ka yi mini magana ka ce wani abu mana"
A hankali ya zame hannunsa daga na dattijon, ya tashi daga kan kujerar ya koma gadonsa na marasa lafiya ya kwanta.
Sultan ya yi shiru yana kallonsa, sai dai ya rasa abin da yake yi masa daɗi. Kar a ce ƙwaƙwalwar ɗan sa ta taɓu. A yadda alaƙarsa da ɗan sa take, ba ƙaramin abu ne zai sanya ya yi masa haka ba.
Kwanciyarsa ke da wuya, ya fara jijjiga, a rikice Sultan ya nufe shi. Sai dai ya fara kururuwa yana faɗin "Wuta zafi"
Matawalle ne ya shigo ɗakin da sauri, suka rufu a kansa, Sultan ya din ga tofa masa Addu'a. Har ya daina jijjigar.
Abdou ya kalli Sultan ya ce "Abubuwa fa kamar ƙara rikicewa suke yi, mene ne abin yi yanzu. Ina tsoron a bi diddigi a gano halin da yake ciki fa"
"A fita da shi waje kawai, wataƙila a dace a can, ni na kasa gane kan abubuwan da ake yi masa a nan"
"A wannan yanayin, da ihun da yake yi"
"Abduou" Sultan ya kira sunansa cikin ɗaga murya.
Abduou ya risunar da kai ya ce "Za a shirya duk abin da yakamata, za a yi abin da ka ce".
Jamila ce take ta juyi a kan katifarta, tana jiran reply ɗin Abba, saboda chatting suke yi. Sai dai shiru bai yi reply ba har ta gaji ta yi bacci.
Da safe sai gurin sha ɗaya ta tashi daga bacci, da yake tana fashin salla.
Ta duba wayar, ta tarar da tarin messages ɗin sa da kiran waya, ta share ta je ta yi wanka ta shirya.
Daga tsakar gida ta ce "Mama ni na wuce"
"Ba za ki tsaya ki karya kumallo ba?"
"Zan ci a can, sai na dawo"
Suwaiba na tsakar gida, tana goge kaushi, ta ce "Jamila"
"Yes" Jamila ta amsa.
"Nana fa na gaishe ki, ba ki ga jaririnta ba"
Jamila ta ce "Ai dama ke da Nanan, kan ku ba ƙalau ba, shi yasa ke kaɗai take kawowa ziyara a mafarki." Sai kuma ta ɗan yi shiru cikin damuwa ta ce "Allah sarki Nana, ko ta na wani halin yanzu oho" ta ɗan ja numfashi ta sauke ta fita, tana ci gaba da tunanin Nana.
A falon Hajiya Sa'a ta tarar da Abba yana zaune yana Video game. Tana shigowa ya yi murmushi ya tashi zaune ya ce "Sannu da zuwa"
Ta murguɗa masa baki ta nufi bedroom ɗin Hajiya Sa'a.
"To ai ba ta nan" ya yi maganar yana miƙewa ya bi bayanta.
"Me na yi miki ne ki ke hararata? Na tura miki saƙo duk ba reply"
Ta kalle shi ta ce "Ba jiya na yi ta jiranka da daddare ba, ka ƙi kula ni"
"Eyya, bacci ne ya kwashe ni, ki yi haƙuri"
"Ba wani nan, da budurwarka ka ke chatting ka share ni"
Ya waro ido ya ce "Wallahi ba ni da wata budurwa bayan ke, kema kin san ba na iya kula 'yan mata kema da ƙyar ai na gaya miki ina son ki" sai kuma ta tuntsure da dariya ya taya ta shi ma.
Za ta yi magana kawai Hajiya Sa'a ta shigo falon, ta gan su a zaune a kan dining suna hira har da dariya, alhalin a gabanta basar da juna suke yi.
Ɗan saroro Hajiya Sa'a ta yi tana kallon su, Jamila cike da bariki ta ce "Mummy sannu da zuwa" "Yauwwa" ta amsa a taƙaice. Abba ma kam kasa magana ya yi gaba ɗaya.
Ya yi wa Jamila sallama ya fita, sai dai Hajiya Sa'a ta yi kicin-kicin ta ƙi sakar wa Jamila fuska gaba ɗaya.
Jamila kuwa ta din ga ƙissimawa a ranta, muddin abin da take zargi ya zama gaskiya game da Hajiya Sa'a za ta ba ta mamaki ba kaɗan ba.
*****
Kwanci tashi asarar mai rai, Nana ta kwana arba'in cif da haihuwa.
Sai da Nene ta kwana goma sha biyar, ba ta fita gurin sana'arta, saboda jegon Nana sai dai yaranta su je, sai bayan kwana sati biyun sannan ta fara fita, shi ma da wuri take dawowa.
Ranar da Nana ta kwana arba'in, ta saka Nana ta shirya suka je gidan su Hajara.
Sun yi murna sosai da sosai da ganin Nana, duk da ta rame, amma yanayin ta akwai nutsuwa a tattare da ita.
Auwwalu ya ɗauki Muhsin ya ce "Ohh Allah ka bamu mu ma ɗan kyakykywan jariri, ka ga ɗa kamar na larabawa"
Hajara ta amsa da "Amin dai"
Nene ta ce "Ka ga fitsararru, babu ko kunyar idona?"
Auwwalu ya ce "To ai addu'a muka yi. Ban da rashin kara ma, a ƙa'ida fa ɗan nan, sunana na ya kamata a saka masa"
Nene ta ce "Saboda kai ɗin waye?"
Nana ta yi murmushi ta ce "Yaya Auwwal, ai sunanka ne da shi, laƙanin ne kawai ba ɗaya ba"
Ya yi murmushi ya ce "Kuma fa haka ne" sosai suka karrama su Nana. Da suka tashi tafiya ma, sai da suka kuma bawa Jaririn kyautar kuɗi da kaya, a so samu Nana ba ta so suka karɓa ba, amma Nene ta amshe.
Da suka dawo kuma ta zagaya da Nana gidajen maƙwabta, suka gaggaisa.
Tun da suka doshi wani gida, Nana ta din ga jin gabanta na faɗuwa, kamar ta cewa Nene ba za ta shiga ba, amma ta kasa. Ta din ga addu'a tare da fatan Allah ya rufa mata asiri ya sanya ba wani abin ne zai faru da ita ba, ko Ƙaisar ne zai dawo ya hana ta sukuni a ƙasar da ba ta da kowa ba.
Ko da su ka shiga cikin gidan, sai Nana ta fara jin sanyi, yana ratsa ta a hankali.
Aka shimfiɗa su tabarma, da ƙyar Nana suka gaisa da mutanen gidan, ta nemi guri ta zauna. Sai ta daina gane abin da Nene suke faɗa ma. Ta din ga jiyo muryar su Nene can nesa da ita, hakan ya tabattar mata da gidan akwai wani abu.
Wani irin sauti ta din ga ji, a cikin kunnunwanta, kamar gurnani kamar nishi.
Ta daina ganin su Nene gaba ɗaya, sai wata mata da ta fito ta tunkaro ta. Ga matar babba da ita amma jikinta ɗauke da zaren mahaifa daga cibiyarta dogon zaren har kan wani baƙin ƙwarangwal da yake bin ta, hannun ƙwarangwal ɗin kuma mahaifa ce yake lasa da jini da komai a jiki.
Jikin Nana ya hau tsuma, ta din ga kallon matar da ƙwarangwal ɗin, tana son yin addu'a ta kasa.
"Nana" ta ji muryar Nene ta kira sunanta.
Sai ta buɗe ido ta kalli Nene.
"Tashi mu tafi yamma ta yi"
Nana ba ta motsa ba, ta ga matar da ta gani yanzu tare da ƙwarangwal ta nufo ta.
Matar gidan ta ce "Kar ki kuskura ki taɓa ta, yi haƙuri dan Allah ba ta da cikakkiyar lafiya ne" ta yi maganar tana kallon Nana.
Sai dai matar ba ta tsaya ba, ta yi kan Nana gadan-gadan. Wani irin azababben ƙarf ya zo wa da Nana, ta ji zuciyarta na tafasa jira take matar kawai ta ƙaraso gare ta, ta illata ta.
Amma Nene ta danƙi hannun Nana, ta hana matar ƙarasawa gurin Nana ta ce "Ke Ashura, meye haka ne? Ba ki ga baƙuwa ba ce?"
Matar cikin wata irin harɗaɗiyar magana da zubar da yawu ta ce "Magana zan yi mata, ta saka wannan ƙwarangwal ɗin ya daina bina" gaba ɗaya suka kalli Nana. Ɗaya matar ta ce "Wani ƙwarangwal ɗin, rabonta da magana ma fa ta fi sati biyu"
Kawai matar ta saka kuka, lallai sai ta je gurin Nana, ta cewa ƙwarangwal ya daina bin ta.
Nene ta ja hannun Nana suka yi waje. Sai dai ta ji jikin Nana tamkar gawa saboda sanyin da ya yi.
Su na zuwa gidan Nana ta nemi guri ta zauna, ba ta cewa Nene uffan ba.
Can bayan magariba, sai ga matar da su ka je gidanta ta zo, Nene ta ce "Gaji lafiya kuwa?"
"Dan Allah Nene ki taimaka mini, ko 'yar nan taki za ta zo mu je gurin Ashura, sai ihu take tana burgima tun da ku ka tafi"
"Ta zo ta yi mata me?"
Gaji ta ce "A'a ban sani ba ko akwai wani taimako...
"Taimakon me?" Nene ta katse ta.
"Kin san dai Ashura ba hankali ne da ita ba, wataƙila almatsutsan haukanta ne kawai ya tashi take wannan abubuwan, ki tafi babu inda Nana za ta zo"
Gaji ta fita jiki a sanyaye, dan idan ta matsa sai Nene ta balbale ta da masifa.
Nene ta ajiyewa Nana nonon raƙumi, da abincin dare, amma ta ƙi ci saboda sanyin da take ji.
Nana ta haɗa kanta gwiwa, tana jin yadda jikinta yake tsuma ta ce "Sayyid sanyi nake ji"
"Ke Nana" Nana ta ɗago ido ta kalli Nene. "Ba za ki ci abincin ba ne?"
"Na ƙoshi, amma dan Allah Nene mara lafiyar can ta can gidan, ta faɗi wani abu a kaina ne?"
Nene ta ce "Za ki ba ta magani ne?" Sai Nana ta yi turus tana kallon Nene, gabanta yana tsananta faɗuwa.
"Ba ta ce komai a kan ki ba, amma idan kin amince za ki yi magana da aljanin nata, ko ki bata magani kamar yadda ake so ki yi, sai mu je"
Gaban Nana ya faɗi, ta bi Nene da kallo cike da mamakin, yaya aka yi Nene ta san wannan maganar, alhalin ko da wasa ba ta taɓa gaya mata ba.
"Nana mamaki ki ke yi? Ai ba a banza na yarda na karɓe ki muke zaune a cikin gidan nan ba da ni da ke.
Tun zuwanku na ga abubuwan da na gani a tattare da ke.
Na ga inuwar rauhanin aljani a tattare da ke, kuma da alama ko dai kin gamu da baƙin aljani a hanya, ko kuma kin yi rayuwa da shi, saboda akwai warinsa a tattare da ke, saboda yana ta'amalli da jini, har ma warin nasa yana ƙoƙarin danne, ƙamshin rauhanin da yake tattare da ke. Sannan akwai alamu na alaƙa mai ƙarfi a tsakanin wannan rauhani da Aljanin da yake tattare da ke. Jiri ne ya fara ɗibar Nana, cikin wani yanayi mai kama da fitar hayyaci ta ce "Nene, wace ce ke? Ya aka yi ki ka san abin da ban gaya miki ba? Ki gaya mini ke wace ce?"
"Nana, masu iya magana suka ce mugu shi ya san makwantar mugu. Ni na yi harkar bori da bayar da magani, ni baƙin aljani ma na gada daga gurin mahaifina. Ya azabtar da ni ya hana ni aure, na ƙi bayar da magani ya shanye mini ƙafafuwa, na daina al'ada na fara hauka tuburan. Sai da na bayar da magani, bayan wasu shekaru, na daina al'ada na fara hauka tuburan. Sai da na bayar da magani, bayan wasu shekaru, na gaji na ce zan ajiye, saboda kullum cikin larura nake, ga shi ya sanya na saka a yi ta zubar masa da jini. Ya sake burkita ni, ya hana ni aure, na koma ciwon hauka yau na kuturce gobe na daina gani, anjima na kasa tafiya. Ya buɗe mini ido nake ganinsu muraran a siffofi na ban tsoro, nake jin maganganun su a cikin kunnuwana. Ya ɗauke ni ya kai ni can wata uwa duniya ya yasar da ni, na yi ta gararamba sannan ya gaji ya dawo da ni. Ko ya saka na yi ta zubar da jini babu ƙaƙƙautawa.
Duk inda muka je neman magani, sai a ce sai dai na haƙura na ci gaba da bayar da magani.
Da ƙyar wani mai magani ya raba ni da shi, ta hanyar yin amfani da wani aljanin. Ya kafa sharuɗɗa sai da aka yi masa yanka, da sauran abubuwa dai na sharuɗɗa sannan Allah ya raba ni da shi. Bayan mun rabun ma, da ƙyar na samu na yi aure, shi ma dai kusan kullum cikin rigima da miji, na zo babu haihuwa, sai rigima sai dai ya dage ya ƙi rabuwa da ni. Sai daga baya Allah ya bani haihuwar ɗa namiji, daga nan ban sake haihuwa ba. Yarona yana can ƙasarku Nigeria. Mijina kuma Allah ya yi masa rasuwa, ni kuma na ci gaba da sabgogina ban sake wani auren ba, duk da wasu lokutan haryanzu abubuwan na taɓa ni."
Nana tana Libraryn Ƙaisar, daga can nesa take jiyo maganar Nene.
Kai tsaye gurin mudubin nan ta nufa, cike da fatan ta sake ganin ko fuskar Sayyid ne, amma ta tarar da mudubin wayam, sai ma baƙi ƙirin da ya yi.
Ta daɗe a tsaye ta zura wa mudubin idanun amma babu alamar wani abu zai bayyana a mudubin ta gani.
Ta hango littafin da ta fara karantawa a yashe a ƙasa, inda ta yasar da shi, hakan ya tabattar mata da Ƙaisar ba ya cikin ɗakin karatun nasa na wani lokaci.
Ta sanya hannu ta ɗauki littafin, ta nutsu ta ci gaba da karantawa.
"Idan ka bari tsoro ya ɗarsu a cikin zuciyarka, to tabbas ba za ka iya cimma abin da ka ke hari ba. Tun da kawar da mahaifinka bai yi maka wahala ba, wannan ma ba zai gagare ka ba, ka kashe su ɗaya bayan ɗaya, ka yi mulki cike da izza ka tara sojoji da runduna da za ta razana duniya".
Ire-iren waɗannan kalamai na ziga da kambamawa, ya sanya matashin saurayin jin kansa na daɗa kumbura, tare da ji a ransa zai aikata komai domin cimma burinsa.
Ana tsaka da jimamin mutuwar shugaba a garin, ya ci gaba da tattara sojojin sa na ƙarƙashin ƙasa, da shirya hanyoyin da zai bi gurin kawar da dukkanin wanda ka iya kawo masa tangarɗa.
Ganin babu abin da ake yi a farkon littafin, ban da tsagwaron zalunci, zubar da jini da rashin tausayi ko imani, tsananin ƙiyayya da kisan kai a tsakanin 'yan uwa, duk don kowa yana kwaɗayin ɗarewa gadon mulki.
Ga bautarwa ta fitar hankali ga na ƙasa ba tare da afuwa ko sassauci ba, sai Nana ta ji gaba ɗaya littafin ya ishe ta, ba ya yi mata daɗin karantawa, har ma gara na tarihin Buda a kan wannan.
A hankali ta buɗe idonta, da ya yi mata nauyi, ta ga gari ya yi haske, ta shafa gefenta ta ji babu Muhsin, kawai ta yi zaton ko Nene ce ta goya shi, dan idan Nene na nan, tsakaninta da Muhsin shayarwa ne kawai, ita take yi masa komai kamar ita ta haife shi. Tana ɗaga kai ta ga wannan mahaukaciyar, riƙe da Muhsin a hannunta, gefenta ga wannan ƙwarangwal ɗin baƙi ƙirin da shi kamar an gasa shi da wuta.
Ihu Nana ta saka a cike da matuƙar razana, ba wai dan ta ga ƙwarangwal ɗin ba, sai ganin ɗan ta a hannun mahaukaciya ga aljani a bayanta yana ta lasar jinin jikin mahaifar da ke ɗauke da zaren cibi.
Ayshercool
08081012143
66
Nece ce ta fito hankali a tashe, ta shiga ɗakin da Nana take ciki, ta tarar da Ashura a tsaye rungume da jaririn Nana.
A matuƙar fusace ta ƙarasa ta karɓe Muhsin, ta ajiye shi a kan katifa, ta ce "Uban me ya shigo da ke ki ka ɗauke shi?"
Cikin tsoro ta girgiza