Showing 81001 words to 84000 words out of 122205 words

Chapter 28 - BUZU BOOK2 COMPLETE 2

18 Jan 2026

627

ta numfasa ta ce "Ki yi haƙuri, Hasna ce ta saka ni aiki, ta ce idan na gama, na je na huta"

"A'a ba zai yiwu ba, ni ce mini a aka yi kawai za ki yi mata aiki, dan hakan idan kin gama ki saka hannu ku ci gaba da aikinmu, wa za ki bar wa wannan aikin?"

"To ki yi haƙuri, na gaji gaskiya ba na jin daɗi" kawai ta fice, tattaunawa suka shiga yi a tsakanin su, yadda za su kawo ƙarshen Nana a gurin baki ɗaya.
A ƙarshe suka yanke shawarar, su ƙara ƙaimi su ɓata ta a gurin Hasna, ganin yadda ita ma ta sako Nana a gaba da tsangwama.

Bayan sallar isha'i, Nana ta daɗe a zaune tana tasbihi, tunanin gidansu da 'yan uwanta ya addabi zuciyarta, ga shi abin da ta fito neman har yau babu labari. Ta daɗe tana addu'a kafin ta nemi guri ta kwanta.

Washegari ma su na ta aiki tun safe har Yamma, sai ga Hasna ta shigo.

Duk yadda Hasna take da kyau, ita da Al Hussain, wannan da suka shigo ta fita kyau, tamkar balarabiya, jawur da doguwa sai dai siririya ce sosai. Fuskarta ta sha make up, sai zuba ƙamshi take yi.
Ta yafa ɗan siririn mayafin abayarta a kanta. Sai kallonsu take ɗaya bayan ɗaya tana yatsuna fuska su na yare ita da Hasna.
Duk suka gaishe su, Nana kuma ta yi burus.
Hasna ta nuna mata Nana ta ce "Kin ganta nan"

Asal ta yamutsa fuska ta ce "Ya na ganta baƙa ƙirin haka, ina fatan ba na ƙazanta ba ne?" Nana ta yi mamakin jin Hausa raɗau a bakinta.

"Ke ina ruwanki da baƙinta, ba dai Abinci ya yi ba?"

"Eh kin san ba na son ƙazanta ne"

Hasna ta ce "Sauran ma'aikatan namu ma ai akwai baƙaƙe, kuma kema kin san da ba ta da tsafta, ba zan saka ta yi miki girki ba.Ke Nana ba ki ganni da baƙuwa ba ne?" Nana ta ɗaga kai ta kalle su, ta yi shiru tana wasa da wuƙar hannunta, saboda ciwon da maganganun da suke yi ya yi mata, na cin zarafin baƙar fatarta da danganta ta da ƙazanta, duk ba wai duhu ne da ita sosai ba.

Shiru Hasna ta yi ta kamo wata hirar, ganin alamun idan ta matsa Nana za ta yarfa ta ne a gaban baƙuwarta. Ba a taɓa ma'aikacin da ba ya shakkar ta ba sai Nana. Duk abin da ta saka ta na aiki za ta yi, amma ba ta son rainin hankali.

Bayan sun fito Asal ta tsaya ta kalli Hasna ta ce "Hasna"

"Na'am"

"Ina ga yarinyar nan ta yi dai-dai da abin da nake nema"

"Wace yarinyar?"

Asal ta ce "Wannan 'yar Nigeriar, ina buƙatar za ki ba ni ita"

Ayshercool
08081012143

70

Sai da Nene ta tabattar Nana ta ɗan nutsu, sannan suka kwanta.

Washegari Nene ta fita, ta bar Nana a gidan tare da Muhsin. Bayan ta dawo daga gurin sama'arta ta cewa Nana, yakamata ta je ta ɗan sai abubuwan da za ta buƙata saboda tafiyar da za ta yi da nisa, kuma ba su san yaya tsarin aikin can ɗin yake ba.
Nana ta ce "Ni babu abin da nake buƙata, ki bani wani abin na riƙe a hannuna, sauran kuɗin kuma ki riƙe saboda kula da Muhsin na s...

"Biyana za ki yi kenan dan na riƙe miki Muhsin?" Nene ta katse ta.

"Allah ya baki haƙuri, ba haka nake nufi na, na ga dole ɗan abubuwan buƙatunsa duk ke ki ke yi masa Nene, tun da ga kuɗi sun"

"Kuɗinki ba su isa su saka na riƙe miki ɗa ba ko?"

Nana ta ce "Na sani, ai shi ya sanya na ce ki yi haƙuri.

Nene ta ce "Ba zan yi haƙurin ba sai na gama, kin iya kunna ni da na fara faɗa ki hau bani haƙuri, wato in ci kaina to sai na idar"
Nana ta yi mata shiru ta yi faɗanta ta gama.
Washegari Nene ta saka Nana a gaba suka je kasuwa, ta sata ta yi sayayyar kayan sakawa da na ɗan shafe-shafe, ta yi wa Muhsin sayayyar kayan sakawa da pampers. Babu yadda ba ta yi da Nene ba ta ɗauki wani abin ta ce ba za ta ɗauka na.
Nana ta haɗe rai ta ce "Eh dama ba ki ɗauke ni 'yarki ba, shi ya sanya duk abin da zan yi miki ba kya karɓa"

"Ni za ki yi wa wayo, na ji ban ɗauke ki 'yar ba, ni ga ɗana nan" tayi maganar tana shafo Muhsin da ke bayanta. Da ƙyar sai da suka kai ruwan rana Sannan Nene ta karɓi abin da Nana ta saya mata.
Sai dai kan su bar kasuwar har sun shirya. Nana ta ce "Nene kin ce mini ki na da ɗa, amma ban taɓa ganinsa ya zo ba, ba ya zuwa ya gan ki ne?"

Nene ta ce "Kamar ban damu da shi ba ko?"

"A'a kawai dai tambaya na yi "

"Yana can Nigeria"

"To me yake yi a Nigeria ba ya zuwa inda ki ke?"

"Sana'a yake yi, ai ya zo ki na can gurin aiki"
Duk da Nana ba ta gamsu da amsoshin da Nene ta ba ta ba, amma ta basar ta ce "Allah sarki, Allah bai yi zamu haɗu ba".

Haka suka ci gaba da hira suka koma gida, Nana ji take yi tamkar ta ɗauke ɗanta ta tafi da shi.

Gidansu Ashura Nana ta je, ta samu keke ta ɗiɗɗinka kayan da ta sayo, ta sake haɗa jakarta ta ɗauki muhimman abubuwa a kayanta.
Duk da a ɗaki Nene take rufe mata su, ba ta taɓa ganin alamar Nenen tana yi  bincike a cikin kayan ba.

*****
Ko da Jamila suka dawo Kano, fakar ido ta yi ta jefar da wannan tarkacen da aka ba ta aka ce da su za ta kai jini.
Gaba ɗaya da ta tuna abin tsigar jikinta take tashi, ta ji ciwon kanta da zazzaɓi ya ƙaru.
Gefe guda kuma hankalinta yana kan yadda ta ji Hajiya Sa'a tana faɗin za ta sake bayar da ɗan Alhaji Fatuhu. Ta jinjina rashin imaninta mutumin da yake fama da karayar arziki ga ciwo, ya rasa wancan ɗan kuma a sake bayar da wannan kamar ba a yi masa adalci ba. Sai dai gaba ɗaya ba ta san ta ina za ta fara ba, tana jin a ranta kamar yakamata ta tseratar da yaron.
A gida ta tarar da Gaddafi, ta sha jinin jikinta da irin mugun kallon da ya yi mata, amma bai ce mata uffan ba. Suwaiba ma ƙura mata ido ta yi tana bin ta da kallo.
Ta tsuke fuska ta harsri Suwaiba, sai dai Suwaiba ta tuntsure da dariya, kamar za ta shiɗe. Jamila ta yi tsaki ta shige ɗakinsu.
Ba ta tarar da Mama a gida ba, haka ma Baba.

*****

Shiru Alhaji Zailani ya yi yana kallon Doctor Sharif yana sauraren shi, har ya gama karanta masa abin da Shukura ta je ta same shi ta yi masa.
Ya ja numfashi ya ce "Shikenan, aikinka ya yi kyau Sharif, na kuma gode sosai da sosai da ka ke sanar da ni wannan abubuwan, Allah ya saka maka da mafificin alkhairi. Ka je za ka ga saƙo" Sharif ya yinƙura ya tashi ya tafi.

Alhaji Zailani ya numfasa a fili ya ce "Duk da kasancewar ki 'ya mafi soyuwa a cikin zuciyata, an zo gaɓar da ki ka ƙetare layin da bai kamata ki ƙetare ba, kina ƙoƙarin tono abin da zai wargaza zaman lafiya da kwanciyar hankali, dan haka ki yi haƙuri da duk matakin da zan ɗauka a kan ki.

*****
Nana ta jingina da jikin gilashin motar, tana kallon tulin yashin saharar da ya mamaye gurin. Fili fetal hagu da dama duk yashi ne. Cikin yanayi mai kama da bacci take ganin abubuwan da ta din ga gani a bacci cikin saharar.
Ko a yanzun ma su na tafe Sayyid kawai take gani a kan raƙumi yana biye da su a cikin saharar.
Kamar an taɓa ta ta ɗan yi firgigit ta kalli gurin, haryanzu a titin da ya ratsa saharar suke tafiya, zuciyarta ta yi wani irin bugu da sai da ta dafe ƙirjinta.
Sanyi ta fara yana ratsa ta har cikin ƙashinta, ta ɗaga ido tana ɗan waige-waige ta ga ta ina za ta gano Ƙaisar ko wata baƙuwar halittar da ba jinsin mutane ba, sai dai ba ta ga komai ba.
Ta sake jingina da jikin motar tana ta karanto duk addu'ar da ta zo bakinta. A haka har suka shigo cikin gari sosai da sosai.
Nana na son karanta Symbols ɗin da take gani, amma ba komai take iya fahimta ba saboda rubutun French. Babbar hanya mai ɗauke da ƙaton gate ta ciki suka wuce.
Ba ƙaramar gajiya Nana ta yi ba, saboda azabar nisan tafiyar da suka shawo ba, ba su ƙarasa ba sai bayan magariba. Kewar ɗan ta ta addabi zuciyarta, tunaninta yadda za ta din ga sintirin tsakanin Agadez da Maraɗi a wannan uwar tafiyar kamar ta ya da shege.

Wasu irin gidaje ne manya-manya na alfarma da ƙasaita a cikin gurin.
A ƙofar wani gida direban ya tsaya, ya cewa Nana ta fito sun zo. Haka ta saukko ƙafafuwanta duk sun yi tsami saboda azabar gajiya.
Ya buɗe bayan motar ya ɗaukko ƙatuwar jakar Nana, ya rufe motar, ya yi gaba Nana ta bi shi a baya tana karanto addu'oin da suka sauwwaƙa.
Cikin wani matsakaicin gida suka shiga, gidan ya ƙawatu ya yi kyau sosai da sosai.
A falon gidan ya ajiye wa Nana kayanta ya ce "Ki zauna ki jira a nan"

Nana ta ce "Amma wa zan jira a nan ɗin, ban ga alamar akwai mutane a gidan nan ba"

"Za ki gan su, ni a nan aka yi mini umarnin na kawo ki kawai"

Nana ta yi shiru tana nazari, shi kuma ya juya ya fice.
Nana ta din ga rarraba ido, tana son ta yi salla amma babu wanda za ta tambaya. Harabar gidan ta fita saboda ta ga famfo ta yi alwala, ta dawo falon ta yi salla.
Gajiya ta yi ta koma harabar gidan da kayanta, ta zauna tana rarraba ido.
Can ta ji ƙarar mota, aka buɗe ƙofar wani jami'in tsaro ya shigo ya buɗe gate ɗin, aka shigo da wata haɗaɗɗiyar mota aka yi parking ɗin ta.
Aka buɗe ƙofar motar, sai ga Asal ta fito sanye cikin doguwar riga, ta ɗaura mayafin a wuyanta, kanta babu ɗankwali. Har bakin ƙofar shiga suka rakata, ta wuce Nana ta shige ciki kamar ba ta gan ta ba. Nanan ma ta yi zamanta ba ta shiga ba, ta jingina da jikin kayanta taka addu'a saboda a gajiye take matuƙa, ga uwar yunwa tana ji ga tulin damuwa.
Sannu a hankali take tuna yadda ta shigo ƙasar Nijar ba ta san kowa ba, da yadda ta din ga raragefe har zuwa kan zamanta da Nene. Sai ta tsinci kanta da tattara su baki ɗaya tana yi musu addu'a, da fatan dacewa a Duniya da lahira.
Ba ta san iya adadin lokacin da ta ɗauka a gurin ba, ta ji muryar Asal a kanta.
"Wai ke wace irin bagidajiya ce, a Nigeria daga wani ƙauyen ki ke ne?" Nana ta ɗaga kai ta kalle ta.

"Na saka an kawo ki guri, ki shiga ki jira ni kin zauna a waje, na dawo ma kin nemi guri kin zauna ba za ki shigo ba?"

"Ta yaya zan shiga gurin da babu kowa na zauna, ni da ban san ma aikin da ki ka kawo ni na yi miki ba?"

Haushi ya kama Asal, ta ce "To idan kin ga dama ki shigo, idan kuma ba ki ga dama ba, ki yi ta zama a gurin" Ta shige ciki Nana ta bi ta da harara, kamar ba za ta tashi ba, sai kuma ta tashi ta ja kayanta, ta shiga falon ta nemi guri ta zauna a kan kujera. Asal ta saci kallon Nana, da yadda take gudanar da lamarinta cike da ƙarfin hali.

Nana ba ta kula ta ba, ita ma ba ta kula ta ba, Nana ta gaji da zama, ta saukko ƙasa ta miƙe ta kwanta.
Can Asal ta ce mata "Ga kitchen can, akwai abinci"
Daga haka ta tashi ta bar falon.
Nana ta tashi ta shiga kitchen ɗin, ta tarar da Abinci, ta ɗauka ta ci sannan ta ɗan dawo hayyacinta.
A nan falon Nana ta kwana, da Asuba ta yi alwala a harabar gidan, ta koma falon ta yi salla.
Duk wannan abin zuciyarta a cike da zullumin aikin da za ta yi wa Asal.
Da gari ya yi haske, Asal ta fito Nana ta gaishe ta, amma ta yi kamar ba ta ji ba, ta fice ta bar gidan ta bar Nana.
Nana tana nan zaune, aka zo aka ƙwanƙwasa ƙofar falon, ta tashi a ɗan tsorace ta buɗe, wani mutum ya miƙo mata takeaway ya ce "Ga shi nan, aka ce a kawo miki" daga haka ya juya ya tafi.
Nana ba ta sake ganin Asal ba sai dare, ba ta saurari Nana ba still. Ta cika gidan ita da ƙawayenta, suka hau saman bene, suka kunna kaɗe-kaɗe har kusan ɗaya na dare su na abu ɗaya, suka hana Nana bacci.
Sai gefin Asuba suka daina wannan shirirtar, Nana ta din ga mamakin ita Asal zaman kanta take yi ne, ba ta da magabata ko kuwa?
Sai washegari sannan ta saukko ƙasa, a lokacin ƙawayen nata duk sun tafi.
Ta kalli Nana ta ce "Daga yau kar ki ƙara kwanar mini a falo, ga ɗaki can kusa da kitchen, a nan za ki din ga kwana. Na kawo ki ne duk da ba yanzu ne za ki yi aikin naki gaba ɗaya ba, amma za ki din ga yi mini girkin Abinci da ni da ƙawayena, da sauran aikace-aikacen gida.
Abu na farko dalilin da ya sanya na ɗaukko ki, ke ba ƙabilarmu ba ce ba, ba na son saka ido, ba na son surutu
Duk wani abu da za ki ga na yi, ko ina yi babu ruwanki, aikin duk da na saka ki shikaɗai za ki yi mini"
Nana ta yi shiru tana tunani, dama duk wannan abin ba wani branch ɗin za a kai ta aiki ba, wannan zuƙaƙƙiyar za ta yi wa bauta, shi ne har da ci mata mutuncin cewa an yi amfani da kuɗi sai ta yi abin da ake so. Kuma me yasa ba ta zaɓi kowa ba sai ita?.
"Ba kya ji na ne?"

"Na ji"

"Ban gane kin ji ba? Haka zan din ga yi miki magana ki na amsa mini, ke ni fa ba Hasna ba ce ba, dole ki yi mini biyayya ki yi duk abin da nake so".

Nana ji ta yi tamkar ta yi tsaki, ta ce "Amma yanzu fisabilillahi duk faɗin ƙasar nan ki rasa wanda za ki ɗaukko ya yi miki aikatau sai ni. Ni harkar dafa abinci nake yi, amma kin kawo ni nan in din ga yi miki girki da boyi-boyi ba tare da an yi mini bayanin haka ba, ni gaskiya ba a kyauta mini ba"

"Da hakan ki ka dace ai, ko kina ganin kin cancanci wani abin bayan bauta? Idan ba za ki zauna ba ga hanya nan za ki iya tafiya" Ta yi maganar tana miƙewa tsaye.
Har ta yi gaba sai kuma ta tsaya ta ce "Duk wani abu da za ki buƙata akwai shi a kitchen, kina iya dubawa, wanda babu kuma ki sanar mini, shi ma idan ba ki ga dama ba kar ki yi aikin" ta yi gaba ta bar Nana da ta gama ƙulewa.

*****

Gaba ɗaya Shukura ta burkicewa Sagir, ba ɗaga masa hankali ta yi da rigima ba, tattara shi ta yi ta watsar gaja ɗaya take harkokinta, da gaske take ƙoƙarin gano abin da mahaifinta yake ɓoyewa tsawon wannan lokacin da har ya hana Hajiya Amina bincike a kan lafiyarta.
Ga shirin tariyar Yusra Sagir na yi, ga damuwar rashin sakin jiki da shi da Shukura ta yi, ta tattara shi ta watsar.
Ɓangarensa ya saka aka gyarawa Yusra, dama ba amfani yake yi da shi ba, aka ƙara gyara shi, aka haɗa gidan gaba ɗaya aka sake yi masa fenti. Daga gaya mata batun dawo da Yusra zuwa gyaran gidan da kawo kayanta, ba a yi sati guda ba, gida ya ɗau harama.
Duk yadda ya so ya lallaɓa Shukura, ta saukko ta din ga saurararsa ta yi burus da shi.

Nana ta shafe sati guda tana gidan Asal, tana yi mata hidima, ta hantare ta ta kyare ta, dandazon ƙawayen da take tarawa ma, su hana ta sukuni da aiki. Nana ta din ga iya ƙoƙarinta, gurin kai zuciyarta nesa, amma abin ya fara isarta.
Tana tsaka da nazarin yadda za ta ɓullowa lamarin, da safe Asal za ta fita ta kalli Nana ta ce "Ki shirya nan da sati ɗaya zamu bar nan, zamu je asalin inda na ɗauke ki ki yi mini aiki a gurin"

Nana ta ce "Ina kenan? Kuma aikin me?

"Idan mun je za ki gani" Ta ba wa Nana amsar a taƙaice.

*****
Jamila tana kwance tana chatting da Abba, bikinsa saura sati biyu.
Hajiya Sa'a tana ta zaginsa da yi masa bala'i, a kan yadda yarinyar take ta ƙorafin ba ya kula ta, waya ma sai dai ita ta kira shi, babu abin da ya yi masa zafi da ita.
Yanzun ma kamar ya yi wa Jamila kuka.
Ita take ta rarrashinsa tana nuna masa babu komai ya yi aurensa kawai.

"Ƙanwata ko na yi aure hankalina ba zai kwanta ba, kar ki manta da ɓarnar da ta faru tsakanina da ke, ya zan yi da shi"

Ta ce "Na san kai mutumin kirki ne yayana, hakan ne ya sanya ka ke jin damuwa a kan abin da ya faru, amma ka yi haƙuri ka yi aurenka kawai, ina roƙon Ubangiji Allah ya kawo mini wani mijin"

"A'a ki daina faɗa mini haka, zuciyata tana sosuwa, baki da wani miji sai ni in sha Allah" haka suka kasance tana ƙarfafa masa gwiwa, shi kuma yana rarrashinta.
Ta gama wayar ta ajiye, ta ga Suwaiba ta ƙuro mata ido tamkar ba ta taɓa ganinta ba.

"Meye ki ke kallona, lafiya?" Suwaiba ta yi shiru ba ta bata amsa ba, kuma ba ta yi magana ba.

Jamila ta ja tsaki, tana ƙoƙarin kwanciya, Suwaiba ta ce "Jamila"

"Na'am mene ne?"

"Ki ɗauki saƙonki mana"

Cikin rashin fahimta ta ce "Wane saƙon?"

"Na cikin jakarki"

"Cikin jakata kuma? Mene ne a jakar tawa? Wato bincike ki ke yi mini a jakar ko?"

"A'a ni tuni kawai nake yi miki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login