Showing 105001 words to 108000 words out of 122205 words

Chapter 36 - BUZU BOOK2 COMPLETE 2

18 Jan 2026

621

na jin daɗin jikina"
Sai kuma ya tuna takaicin abin da take yi masa ya sanya bai je ya ganta da daddare ba, ya wuce gurin Yusra.

Shukura kuwa tuni ta nufi ƙofa, ya bi bayanta yana "Ki tsaya na sauke ki a Asibitin"

Ta girgiza kai ta ce "A'a ka koma gurin amaryarka, kar ka bar ta itakaɗai"

Jiki a sanyaye ya kira sunanta, ta ɗaga ido ta kalle shi. Idanunta sun yi jawur sun cika da hawaye.

Hannu ya sanya yana share mata hawayen da ya fara gangarowa kan kuncinta, ya ce "Dan Allah Shukura ki daina, ban dawo da Yusra dan na ɓata miki rai, ko na cutar da ke ba, wallahi kukan nan da ki ke yi da rashin walwalar ki yana damuna ba kaɗan ba, dan Allah ki daina"

Ta ce "Tom, bari na tafi kar na makara"

Ya ce "Bari na canzo kaya na zo na kai ki"

Ta ce "Kar ka damu, zan iya driving ai, yanzu zan dawo in sha Allah"

"To me za ki sayo mini idan kin tashi dawowa?"
Murmushin yaƙe ta yi ta ce "Me ka ke so?"

"Abin daɗi, sai kuma uwa uba ki ƙara yi mini murmushin nan dan Allah"

Murmushin ta sake yi tana taɓa jakarta.

Ya dafa cikinta ya ce "A dawo lafiya Allah ya tsare, ki kular mini da kan ku sosai. Dan Allah ki daina fushin nan da ni Shukura, kin ga yau zan dawo gurinki, kuma ina son zuwa inda ki ke amma yadda ki ke yi mini ne ba na jin daɗi, har fargabar zuwa inda ki ke nake yi. Dan Allah idan na zo kar ki haɗe mini rai dan Allah sweetheart"

"Tom"

"Tom ɗin nan kuwa ta kai zuci?"

Shukura ta ce "Ta kai mana"

"Yauwwa babyna, ina jiranki, ki dawo da wuri dan Allah"

"To in sha Allah"

Ya buɗe mata motar, yana jin daɗin yadda ta sakar masa fuska, tsayawa ya yi janta da hira, yana tsaye a bakin ƙofar motar, ita kuma tana ciki a zaune. Abin mata da miji sai ga Shukura tana dariya, da haka suka yi sallama ta fita.
Yusra kuwa sai da haushi ya kama ta, yadda ya yi ficewarsa ya je ya shantake a gurin Shukura, kamar ma ya manta da wanzuwarta a gurin.

*****

Duk yadda Asal take ɗokin Imam, gaba ɗaya gani take kamar ba a cikin nutsuwarsa yake ba, kamar wani abu yana damunsa, babu yadda ba ta yi ba a kan ya gaya mata mene ne yake damunsa ba, amma ya ce mata shi babu abin da yake damunsa.

A hankali ta yi juyi a kan gadon, ta zuba masa ido yadda yake ta uban gumi, tare da yin haki, har sai da ta ɗan tsorata. Sai dai ta ga ya yi juyi ya ci gaba da baccinsa.

Kwana biyu Nana ta daina yadda su haɗu, kamar yadda ya buƙata, sai dai yau da ta shiga ta tarar yana nan. Babu tsammani ya ga Nana, hakan ya sanya ya ɗan zabura, har sai da ta gani.
"Sayyid ina kwana" Shiru ya yi yana tunani, sai kuma ya maze bai motsa ba.
"Ban san laifin da na yi da ya sanya, ka nemi na daina zuwa inda ka ke ba, amma idan laifi na yi maka, ina neman afuwarka Sayyid"
Sannu a hankali kalmomin da ta yi amfani da su, suka din ga shigarsa ɗaya bayan ɗaya, yana jin kalaman na da wata fassara da yakamata ya sani, amma ya kasa gano fassarar, duk da yana jin yaren na hausa, kuma da shi ta yi maganar. Ƙamshin turaren sa da Asal take faɗa, yanzu ma shi yake ji yana tashi a jikinta.
Ta miƙe ta yi waje cikin sanyin jiki, kawai ya tashi ya yinƙura, ya bi bayanta. Sai dai ya tsaya a bakin ƙofa yana tunanin to idan ya bi bayanta ina zai je, ko kuma me zai ce mata?. Kawai ya koma da baya ya nemi guri ya zauna.

*****
Satin bikin Abba ya kama, Hajiya Sa'a duk ta yi busy, Jamila kuma ta rage zuwa gidan gaba ɗaya.

Hajiya Sa'a tana ta jiran Abba za ta aike shi, amma shiru har sha ɗaya na safe bai fito ba, haushi ya kama ta dan muraran yake adawa da auren nan da zai yi.
Bala'i take ta yi, tare da alwashin ɗaukar mummunan mataki a kan Jamila. Dan a cewarta ita take ziga shi.

Ta shiga ɗakinsa tana bala'i, kawai ta gan shi a kwance yana bacci.

"Abba wannan wane irin bacci ne har haka? Kai da muke da hidima a gaba, dan ka nuna mini ban isa ba, shi ne za ka nemi guri ka yi ta baccin asara" Sai dai ya yi shiru bai tashi ba.
Ta ƙarasa ta ɗala masa duka a ƙafafuwansa, amma shiru bai tashi ba.
A iya saninta, Abba ba shi da nauyin bacci, amma yau dai abin ya yi yawa. Ta jirkita shi, ga mamakinta kawai ta gan jini a hancinsa, da bakinsa ga fatarsa ta yamutse jikinsa ya yi fari ƙwal. Sai dai yanayin jikin nasa ya nuna akwai nutsuwa a tattare da shi.

Wani irin magigicin ihu Hajiya Sa'a ta yi, ta hau kururuwa tana jijjiga gawar Abba, tana kiran sunansa da wata irin murya ta tashin hankali, girgiza shi take yi tana ihu da kururuwa a kan gawar, amma Abba rai ya riga ya yi halinsa.
Hajiya Sa'a ta tashi da gudu ta nufi cikin gidan, tana ihu tana kururuwa tana "Wayyo Allah na shiga uku, dan Allah ku zo ku taya ni duba ɗana me ya samu Abba, dan Allah ku taimake ni kar Abba ya mutu ya bar ni na shiga uku na lalace"
Tuni mutanen da ke gidan, suka fito aka je aka dudduba aka tabattar da mutuwar Abba.
Ɗaya daga cikin ƙawayenta ta ce "Kuma ba guba ya sha ba, ko wani abu ko ba shi da lafiya?" Hajiya Sa'a babu baki sai kuka kawai da take yi.

Safiyya ta ja ta tayi waje da ita, ba su tsaya a ko ina ba sai bedroom ɗin ta.

"Hajiya me ki ka fahimta game da gawar Abba?"

Cikin kuka da tashin hankali ta ce "Ni ban fahimci komai ba"

"Duk wanda muka bayar a ƙungiya, yana zubar da jini ne ta hancinsa da bakinsa, kuma fatarsu haka take komawa, wani ya bayar da Abba a ƙungiyar Asiri, ko tamu ko wata ƙungiyar".

Wani irin ihu Hajiya Sa'a ta zunduma, Safiyya ta toshe mata baki tana faɗin "Hajiya ki rufa mana asiri kar ki tona mana asiri a gano mu"

Wayar Safiyya da ke aljihunta ce ta fara ringing, ta ciro ta sai ta ga Jamila ce take kiran wayar.
Ta kalli Hajiya Sa'a da ke zunduma ihu sannan ta ɗaga.

"Na san zuwa yanzu Hajiya tana cikin mawuyacin hali. Ba za ta iya ɗaga waya ba, amma ina taya mu jaje da ni da ita, Abba ya zama sadaukarwarmu na shekara da ni da ita. Ina fatan zuwa yanzu ta ji abin da ake ji, a duk lokacin da ta bayar da jinin wani ga ƙungiya, ina fatan Allah ya gafarta wa Abba sadaukarwar da ya yi, ya ceci masoyiyyarsa da kuma tseratar da ɗan ƙanin mahaifiyarsa, kuma Abba bai mutu ba, sai da ya san abin da muke aikatawa. Sannan ina taya mu murna, ina ɗauke da cikin Abba a jikina. Ba zan gushe ba ina yi wa Abba a addu'a, da yi masa fatan rahama. Abba mutumin kirki ne, kuma rayayye da ya fita daga cikin matacciya Allah ya sa ya huta"

75

Jamila ta katse wayarta, wani irin kuka ya ƙwace mata, ta din ga wani irin kuka mai gunji.

Mama ce ta faɗo ɗakin cikin damuwa ta kalli Jamila, ta ce "Jamila lafiya kuwa, nake jin kukanki tun daga tsakar gida?"

Jamila ta yi shiru tana ci gaba da gunjin kuka.

Cikin damuwa Mama ta ce "Jamila, ni fa na kasa gane miki a 'yan kwanakin nan, wai mene ne yake damunki ne? Gaba ɗaya ba ki da sukuni, ga koke-koke ko Hajiyar ce ta kore ki ne?"

Ta girgiza mata kai alamar a'a.

"To mene ne?"

"Dan Allah ki ƙyale ni na ji da abin da ya dame ni, Wayyo Allahna"

Duk yadda Mama ta kaɗa ta raya, ta yi rarrashin amma fafur Jamila ta ƙi magana, taƙi gaya mata halin da take ciki, haka ta gaji ta bar ta a ɗakin.
Tana fita Jamila ta ƙara rushewa da kuka, wani irin zafi take ji a ƙirjinta, soyayyar Abba ta din ga ji sabuwa fil a cikin ranta, ba ta taɓa tunanin al'amura za su kasance kamar yadda suka kasance a yanzu ba. Ji take tamkar ta kashe kanta ta huta, ko ita ma tattara ta shiga uwa duniya kamar yadda yayarta Nana ta yi.

*****

"Imam Asad, haba ba kar manta sunan naka, kai jarumi ne, ina mai tabbatar maka da cewa Hammad ba zai zama Sultan a Agadez ba, duk wannan abubuwan da Sultan yake yi da rawar ƙafar da yake yi, mun san abin da yake nufi, dan mun san inda baki ya karkata ta nan yawu yake zuba. Amma Hammad akwai abubuwan da ya rasa, da ƙa'idojin da bai cika ba, dan haka burin Sultan na Hammad ya maye gurbinsa ba zai taɓa yiwuwa ba har abada"

Imam Asad ya gyara zamansa, fuskarsa ɗauke da damuwa ya ce "Anya kuwa? Duk abin da Sultan yake so, dole shi muƙarrabansa za su yi su mara masa baya, ina jin tsoron ya furta Hammad ya maye gurbinsa, muddin ya furta ko yana raye ko ba ya raye, sai an zartar da shi, sai dai idan Hammad ne ya bar Duniya"

Mutumin ya ce "Kar ka yi la'akari da haka, ko me zai ɗauke mu zamu aikata, ko mene ne, babu wanda zai gaji Sultan sai Imam Asadullahi Jalal, dan haka ka ci gaba da ƙoƙari, burinmu dole ne ya cika"

Imam Asad ya jinjina kai cike da gamsuwa.

*****

Cikin damuwa Sagir yake kallon agogon hannunsa, yana sake kiran lambar Shukura, ƙarfe biyar da rabi na yamma amma shiru ba ta dawo ba.

Duk da Yusra sai da suka yi rigima da shi, a kan yadda ya tafi ya bar ta ɗazu, sai dai ta damu ganin fuskarsa babu walwala yana ta kallon waya.

"Baby wai wa ka ke ta kira haka ne?"

"Shukura nake kira, ta ce mini 9zata daɗe ba, tun safe da ta fita haryanzu ba ta dawo ba"

Yusra ta basar ba ta kuma cewa komai ba, sai dai abin ita ma sai ta ji hankalinta ya tashi, ganin har ya fita masallaci sallar magariba Shukura ba ta dawo ba.
Yana dawowa ya dubi Yusar ya ce "Ba ta dawo ba ko?"

"Eh ba ta dawo ba, ko ta biya wani gurin ne?"

Jiki a sanyaye ya ce "Ba na tunanin hakan, ko za ta biya wani gurin, duk faɗan da muka yi tana gaya mini, ba ma ta da yawan yawo, ba ta fiye son fita ba, idan ba gidansu za ta je ba. Bari na je gidansu, na kuma je Asibitin na ji"

"To Allah ya sa tana lafiya, to ko haihuwa ta yi a Asibitin suka riƙe ta, na ga cikin nata ma sha Allah ya tsufa sosai"

Ya girgiza kai ya ce "Da haihuwa za ta yi, da tuni an kira ni an sanar mini, bari na je na gani"

Yusra ta ce "To Allah ya sa tana nan lafiya dai"

Ya amsa da Amin, ya fita.

Gaba ɗaya sai Yusra ta ji hankalinta ya tashi.

Gidansu ya fara zuwa, ya shiga suka gaisa da Hajiya Amina, sai dai bai ga alamar Shukura ta je gidan ba, ya wayance da nufin zai tafi da Haidar, amma Haidar ɗin ya ƙi bin sa.
Hankali a tashe ya tafi Asibitin doctor Sabo, aka ce masa tun safe ta je awo, sha ɗaya da rabi kuma ta bar Asibitin, kamar yadda har a cc camera ya nuna.

Nan hankalin Sagir ya dunguzuma, ya ƙara ruɗewa ya burkice, duk inda yake tunanin Shukura za ta je, ya je bai same ta ba. Wayoyinta da su na shiga, amma suka daina.
Ya tafi gurin 'yan sanda ya kai report ɗin ɓatan Shukura, bai koma gida ba sai sha biyun dare.

Yusra na ganinsa ta tashi tana tambayarsa "Yaya an ganta?"

Jiki a sanyaye ya girgiza mata, take gabanta ya faɗi ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Allah ya sa ba saboda ka dawo da ni ne ta tafi ba, Ubangiji Allah ya sa ta dawo, ni zan iya tafiya ma na bar muku gidan, idan zamana ne ba ta so ta bar gidan"

"Shukura ba za ta bar gidan nan saboda na dawo da ke ba. Dan kan ta fita mun yi magana ta fahimta da ita, mun daɗe mu na magana, ba saboda ke ne ta bar gidan nan ba"

Gaba ɗaya Sagir ya kasa rintsawa, sai damuwa da tashin hankali, haka ita ma Yusra, ƙarshe ma kuka ta saka tana cewa saboda ita ne Shukura ta fita ba ta dawo ba.

*****

Yau da Nana ta bushi iska, harabar gidan ta fita tana zagayawa, sai dai zuciyarta a cunkushe take, gaba ɗaya tunaninta yana kan Muhsin, kewar ɗanta take yi sosai da sosai, ga wannan azzalumar matar ta hana ta tafiya, sai dai ita kanta hankalinta ya rabu kashi-kashi ne, ga tunanin Muhsin ga kuma Sayyid da take ganin samu a lokaci guda take ganin rashi.

Sai a yau ta ƙara tabattar da girma da ƙasaitar gidan, ba ta taɓa ganin raƙumi da ake faɗa ba, sai yau a cikin gidan.
Ban da dawakai, da wasu dabbobin ma da ba ta san sunansu ba, ba kuma ta taɓa ganinsu ba.
Asal ta hango hannunta a cikin na Sayyid, an fito da wata danƙareriyar mota, sun shiga an ja sun fice. Nana ta tsaya ta yi shiru cikin damuwa.

Cikin matuƙar farin ciki dattijuwar matar fara ƙal, ta miƙe ta rungume Imam Hammad.
Cikin girmamawa ya durƙusa zai gaishe ta, amma ta hana shi ta ce "Ai ni yakamata na kwashi gaisuwa shugabana. Ina ta yi wa Sultan ciwon bakin ban gan ka ba, ya ce a bari ka huta kar wanda ya je gida aka dame ka, har sai ka fito dan kan ka"

Ya yi murmushi ya ce "Na same ku lafiya?"

Ta ce "Alhamdillah, sannu Imam Hammad, an sha jinya Ubangiji Allah ya sanya kaffara"

Asal ta ce "Wai ni ba za ki yi mini sanun ba, kin maze kamar ba ki ganni ba"

Matar ta ce "Wa yake ta taki, ga mara lafiya"

Gimbiya Bilkisu ta yi musu kyakykywar tarba, aka karrama su da Abinci kala-kala, amma ya ƙi ci. Hirar ma idan ta yi sai dai ya yi murmushi kawai, bai fiye tofawa ba.

Bayan sun gama da sashen Gimbiya, suka nufi sashen Sultan.

Imam Hammad na shiga falon Sultan, Sultan ya miƙe cikin farin ciki fuskarsa ɗauke da murmushi.

Abdou ma murmushin ya saki, cikin girmamawa suka gaisa.

Imam Nuradden, da Imam Asad duk su na tare da Sultan.
Cikin girmamawa suka gaida Hammad, fuskarsa ɗauke da murmushi ya amsa musu.

Sun taɓa hira kafin Sultan ya ce "Imam Hammad, zo muje ka raka ni tattaki mana, na miƙe ƙafafuwana"

Imam Asad ya ce "Sultan, mu ma mu yi maka rakiyar ne?"

"A'a ku da kullum muna tare ga baƙona da muka yi shekaru ba ma tare"

Yayi maganar yana riƙe hannun Hammad, suka fita ta wata ƙofa. Imam ya din ga kallon gidan tamkar baƙonsa, kamar ba a ciki yake rayuwa ba a baya.

"Hammad"

"Na'am Abi"

"Kamar wani abu yana damunka, ka gaya mini mene ne"

Imam ya yi murmushi ya ce "Babu abin da yake damuna, idan ma akwai ban san mene ne ba"

Sultan ya ƙara tattara hankalinsa a kan Hammad ya ce "Ka tabattar? ba ka fa da wanda zaka gaya wa dauwarka idan ba ni ba, ka daina wannan zurfin cikin Imam ba na so ka gaya mini"
"Babu abin da yake damun Hammad ɗinka fa"

Sultan ya yi murmushi yana dafa kafaɗar Hammad.
"Ka san haryanzu miskilin ɗan yaron nan, mai guje-guje a harabar nan nake gani, ya yi guje-gujensa ya faɗi ya ji ciwo, ya zo ya yi ta yi wa Abinsa kuka, ya ce sai na ce ciwon ya daina yi masa zafi, kuma na daki rama masa na daki ƙasar na rama masa"
Hammad ya yi dariya sai da haƙoransa suka bayyana ya ce "Duk da wannan gemun na fuskata haryanzu wannan ɗan yaron naka ka ke gani?"

"Eh mana, gani nake kamar jiya Sarah ta haifa mini kai. Allah ya jaddada rahama ga Umminka"

Ya amsa da Amin cikin sanyin jiki.

Sultan ya sake numfasawa ya ce "Hammad, haryanzu babu wani abu da ka iya tunawa bayan fara rashin lafiyarka?"

"Ban tuna komai ba"

Ya ɗago hannun Hammad ya ce "Bamu san fa inda zobenka yake ba haryanzu, abin ya dame ni, ina tsoron a farga da babu zoben nan, ina tsoron abin da ka iya biyo baya, idan aka gano babu zoben nan"

Ya kalli yatsun nasa ya ce "Abiena, duk abin da Allah ya ƙaddara zai faru dole zai faru ka daina damuwa. Ni yanzu ina mamakin Mamudu bai san ina Agadez ba ne?"

Sultan ya ɗan ji dumm, sai kuma ya ce "Ni na hana a sanar da dawowarka, sonake ka samu lafiya sosai, amma dole za a sanar masa da dawowarka"

Imam ya ce "Ni zan je na same shi, ya ganni a bazata"

Sultan ya ce "A'a zan saka a sanar masa, zai zo har gida ya same ka"

Ya ji daɗin kasancewa da mahaifinsa, sai dare sannan suka tafi gida tare da Asal. Duk wunin da suka yi bai ci komai ba, har suka koma gida.

Nana ta kammala aikinta na yau, ta yi wanka tana zaune a ɗakinta, tana karatun Alkur'ani. Kawai ta din ga jin kamar akwai wani abu da ba daidai ba.
Ta ajiye Alqur'anin ta tashi ta tafi ɗakin girkin Abincin Imam.
Wata mata ta gani ta kawo kai za ta fita daga kitchen ɗin, alahalin babu wanda yake shiga sai ita sai Balaraba ko Asal.

Nana ta ce "Baiwar Allah lafiya kuwa?"

"Saƙo ne aka bayar, ke ce mai girkin Imam, dan haka ke za ki kai masa"

Cikin rashin fahimta Nana ta ce "Wace ce ke? Kuma waye waye ya bayar da saƙon, kuma saƙon mene ne?"

"Ba ni da lokacin amsa tambayoyinki, babu ruwanki da kuma saƙon na mene ne, ga shi can na ajiye miki a cikin kitchen ɗin, kaiwa ne kawai naki"

Nana da mamaki ta bi matar ta kallo dan ba ta taɓa ganinta a gidan ba.
Ta shiga kitchen ɗin da sauri, ta fara kalle-kalle tana tsoron kar ta je wani abin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login