Showing 84001 words to 87000 words out of 122205 words

Chapter 29 - BUZU BOOK2 COMPLETE 2

18 Jan 2026

574

da saƙonki na cikin jakar"

Jamila ta tashi zaune ta ce "Wai wani saƙon? Miƙo mini jakar dai na gani"

Suwaiba ta ce "A'a ba zan taɓa miki jaka ba"

Jamila ta janyo jakar ta fara buɗewa ta ga abin da Suwaibabta dame ta a kai. Cin karo ta yi da wannan 'yar tsanar da ta riga ta jefar. Saura ƙiris ta kurma ihu, ta rikice gaba ɗaya jikinta ya hau rawa, a tunaninta tun da ta yar shikenan ta rabu da ita.
Suwaiba kuwa ta tuntsure da wata irin mahaukaciyar dariya, ta din ga yi tana ƙyaƙyatawa tana kallon Jamila. Gaba ɗaya Jamila ta kiɗime ta rasa abin da yake yi mata daɗi, gaba ɗaya jikinta ya hau rawa tamkar ta kurma ihu, sannu a hankali kanta ya fara juyawa ta fara gani dishi-dishi, dole ta rufe jakar ta nemi guri ta kwanta.

*****

Alhaji Zailani ya kwana biyu bai je gidan Alhaji Fatuhu ba sai yau. Sai dai ya sha mamakin ganinsa a harabar gidan da sanda yana dogarawa yana tattakawa a hankali, yana tsaye a kan ƙafafuwansa yana kallon yadda Muhsin yake ta gudu a harabar gidan.
Sai da ya aro jarumta sannan ya iya danne abin da ya ji ya taso masa na tashin hankali da mummunan baƙin ciki.
Da ƙyar ya iya washe baki ya ce "Ikon Allah, Abokina kai ne haka nake gani?"

Alhaji Fatuhu ya yi murmushi ya ce "Ka ga ikon Allah ko? Sannu da zuwa Bismillah" ya yi maganar yana nuna masa ɗaya daga kujerun da ke ajiye a gurin.
Alhaji Zailani ya zauna suka ƙara gaisawa

"Bani labari, ya aka yi sauƙi ya samu haka, wani Asibitin ka je ne?"

Alhaji Fatuhu ya ce "A'a na ga an yi na Asibitin ne babu wani ci gaba, Fadila ta zauna ta din ga yi mini bayani, na amince muka fara gwada na islamic, cikin ikon Allah sannu a hankali wannan ɗaurewa da nake ji a jikina ya yi mini sauƙi, wannan gigicewar da nake na ji kamar zan yi hauka shi ma Alhamdillah ina daɗewa ban ji ba, wannan warin ma da nake ji ya ragux

"Amma Fatuhu ya za a yi ka biye wa mace da shirmen ta, ga na Asibiti ana yi kawai ta saka ka fara wani na shirme, sai ka je ka yi abin da za ka kauce wa hanya tukuna?"

"A'a nima na jaddada mata, ta kuma tabattar mini da babu kauce hanya a ciki, kuma nima shaida ne, shi ya sanya ma nake amfani da magungunan kuma ana samun ci gaba"

Alhaji Zailani ya miƙe ya ce "Haka ne, to bari na je dama ina da gurin da zan je na biyo, sauri nake yi"

"Ba zaka tsaya ku gaisa da mutanen gidan ba?"

"Sauri nake yi zan sake dawowa"ya yi maganar yana yin gaba cikin ƙunar rai, ji yake yi tamkar ya kashe Alhaji Fatuhu ya huta, dan shi bai taɓa zaton zai kawo yanzu bai mutu ba.

*****

Al Hussain ne a tsaye ya tsare Hasna da ido, yana yi mata faɗa cikin matsanancin ɓacin rai.
"A kan me za ki yi haka? Dan me za ku yi mata dole, ai ba ɗaukar ta aiki muka yi saboda buƙatar mutum guda ba. Abin da yake cikin yarjejeniya shi ne ta yi wa gidan Abincinmu aiki, idan ma canza gurin aikin ne, wani reshen zamu mayar da ita, amma dan me za ku haɗa kai ku yi mata haka wannan wulaƙanci ne da cin zarafi, kuma ga shi bama 'yar ƙasarmu ba"

"Ni fa Al Hussain na kasa gane maka, ko son yarinyar nan ka ke yi ne? To bari na tuna maka kai Buzu ne, buzun ma farin buzu ka san abin da nake nufi ai, kuma matar aure ce ko bazawara dan ta ce mana tana da ɗa ma"
"Ni ba wannan na tambaye ki ba, dan me Asal za ta yi amfani da ƙarfi da kuɗi ta tursasa mata yin abin da ba ta so, ai ba haka ake rayuwa ba"

"Ai na san za a yi haka, babu bayanin da ban yi mata ba taƙi yadda, ga shi ni yanzu ka zo ka saka ni a gaba da jaraba, sai ka je ka dawo da ita ni ba zan iya ba"

"Ke dai da ki ka yi hakan ki je ki dawo da ita, idan ba haka ba daga ke har ita na rubuta masa abin da ku ka aikata, daida yake da ku"

Ta kwaɓe baki ta ce "Wa ya san ma inda yake, mutumin da ake tunanin ya ɓata babu wanda ya san ma yana raye ko yana mace?"

"Hakan ya baku damar cin karenku babu babbaka daga ke har Asal ko? Yayi muku kyau" Hasna ta fice tana jin haushin masifar da Al Hussain yake ta yi mata, duk yadda ta yi ƙoƙarin hana Asal ɗaukar Nana.

*****

Ana gobe su Nana za su bar wannan gidan, Asal ta sanar da Nana ta shirya washegari za su bar nan.
Ita dai Nana ta sanya wa sarautar Allah ido, rayuwarta ta zama tamkar tamaula daga nan zuwa can, ba ma ta da 'yancin tambayar ko sanin inda za a kaita sai dai inda ta tsinci kanta kawai.
Ta sha aiki ta gama, ta ɗan zauna a falo tana hutawa, sai ga ɗaya daga gayyar ƙawayen Asal ta saukko ta kalli Nana ta ce "Dan Allah ina son shayi"
Nana ta ce "Akwai a kayan Abincin da na girka"
"Shayin kanumfari kawai nake so bana son Shan na girfa"

"Ga gurin dafawar can, idan ki ka je akwai komai, ki dafa ki sha idan kin matsu"

"Ke, kin san wace ce ni ki ke gaya mini haka?"

"Ban san wace ce ke ba, kuma ba na buƙatar sani"

Asal ta saukko tana tambayar lafiya.

Ta gaya mata abin da ya faru, ta kalli Nana ta ce "Wai ke me yasa ba ki da mutunci, ban gaya miki dole ki girmama baƙina ba, mene ne a cikin dafa shayi mintinan nawa ne kin yi kin gama?"

Ta kalli Asal ta ce "Ki yi haƙuri, wallahi ko cokali ba zan iya sake ɗauka ba, yau na bautu a gidan nan ke kin sani, kuma ban taɓa yi miki ƙorafi ba, amma yanzu dai na gaji gaskiya"

Suka juya yare suka yi magana, ba ta san me suka ce ba, ta ga sun koma kan bene.

Washegari da wuri suka ɗau hanya, sai dai ga mammakin Nana, har da rakiyar jami'an tsaro, kuma a wannan karon shigar Shadda Asal ta yi, an yi wa shaddar aiki tun daga sama har ƙasa.
Mota ɗaya suka hau, ta ce Nana ta hau gaba, ita kuma ta hau baya.
Sai da aka kuma wata tafiyar mai nisa, sannan ta ga sun tunkari wani  irin ginin ƙasa tamkar ginin ganuwar Kano.
Ginin ya ƙayatar da Nana sosai da sosai.
Jami'an tsaro ne suke gadin ƙatuwar ƙofar gurin, da wasu Buzaye farare tas sanye da rawani.
Nana kamar ta ce a tsaya, ta duba buzayen nan ɗaya bayan ɗaya ko za ta ga Sayyid ɗin ta cikinsu. Sai da motar su ta tsaya, suka sauke glass ɗin motar.
Da Hausa suka gaisa, suka yi mata sannu da zuwa, ɗaya daga cikin su ya kalli Nana ya ce "Wannan fa?"

"Baƙuwata ce" ta ba shi amsa, ya jinjina kai motar ta shige.
Su na shiga Nana ta ga ai gari ne guda a cikin ganuwar nan.
Sun ɗan yi tafiya kafin su shiga wani ƙaton gida.
Nana ta tsaya tana ganin yadda aka yi wa ginin ƙasa wani irin ado mai ƙayatarwa.
Tun da suka doshi shiga gidan, ake gaida Asal cikin girmamawa, ita kuma ta yi fuska sai taku take cike da ƙasaita, kamar ba ita ce suke rashin hankali da ƙawayenta a wancan gidan ba.
Wannan gidan saɓanin wancan da mutane a ciki, kuma da alama duk a ƙarƙashin Asal suke.
"Wace ce ita?" Nana ta tambayi kanta. Sai da suka ƙarasa wani falo, sannan ta yi wa wata dattijuwar magana da yaren su.
Matar ta kalli Nana ta ce "Bahaushiya ce ke ko? Zo mu je na kai ki masauki"
Babu musu Nana ta bi ta, matar ta kai ta wani daki ta ce nan ne ɗakinta.
Sai da Nana ta kwana biyu a gidan, ba ta sake ganin Asal ba, ba kuma ta aikin fari ba ta na baƙi kawai tana zaune, sai dai za a kawo mata Abincin safe, rana da dare sau uku a rana. Sai dai babban abin da ya dame ta, tun da ta shigo gidan, network ɗin wayar ya sauka gaba daya, ko ta kira Nene ba ta shiga sam.

A kwana na huɗu, da daddare dattijuwar matar nan ta zo ta kira Nana. Babu musu Nana ta tashi ta bi bayanta.
Sun yi 'yar tafiya su na ratsa faluka masu kyau da ado, sannan suka bi wata ƙofa. Sanyin A.C ya daki Nana, ga wani irin haɗaɗɗan ƙamshi. Asal ta hahakimce a kan kujera kaɗa ƙafa.
Ta kalli dattijuwar ta ce ta jira a waje. Daga ƙasa wata matar ce a zauna a kan carfet, ta gurfana kamar tana jiran Asal ɗin ta gafarta mata.

Nana ta yi turus tana tunanin a ina za ta zauna, sama ko ƙasa.
Matar ta kalli Nana cikin zare ido ta ce "Ke ki rage tsawon ki, kin tsaya mata a ka"
Nana ta ja guri ta zauna a kan carfet ɗin ita ma.
Asal kamar ba za ta yi magana ba, sai da ta gama iyayinta ta sauke ƙafarta ƙasa ta dubi Nana ta ce "Amm na saka an kirawo mini ke, saboda ki san abin da na kawo ki gidan nan ki yi. Ke dai da ganin gidan nan kin san ba gurin da za a yi wasa ne ko shirirta ba, babban gida ne na mulki.
Saboda dalilin girki da kuma wani dalili na ƙashin kaina, ya sanya na kawo ki gidan nan. Ba a ɗaukko bare wanda yake ba jinin gidan nan ba, ko ƙabilarmu ba ya yi mana aiki, amma na ga wasu abubuwa a tattare da ke da ya sanya na kawo ki cikin gidan nan.
Kamar yadda na gaya miki, ina ƙara jaddada miki, zaman ki a gidan nan dole ki yi taka tsantsan, babu ruwanki da shishshigi, saka ido, gulma ko kuma shiga abin da babu ruwanki.
Sannan kar ki kuskura wani ya ce zai haɗa kai da ke a yi wani abu, rayuwarki za ta iya salwanta ba tare da kowa ma ya sani ba, dan haka sai ki san irin zaman da za ki yi."

Nana ta yi shiru ta gama sauraren ta, sai dai har a lokacin ba ta ji dalilin da ya sanya Asal kawo ta gidan ba, dafa abinci kowa ma zai iya mai yasa sai ita.

Wannan matar da ta tarar a zaune, ta tafi da ita, ta kai ta gurin da ake girke-girken abinci, da gaya mata yadda jadawalin girke-girken gidan yake. Ta ɗaukko kayan ds Asal ta bayar a ba ta, na kayan shafe-shafe da mayukan wanka zuwa kayan sakawa.
Da Nana ta koma ɗakinta, ta kalli kayan ta fara tunanin Allah ya sa ba kwance Asal ba ne, dan gara ta saka kwancen Ashura da ta saka na Asal, da ba ta da mutunci.
A washegari Nana ta fara aiki a wannan madafa, sai dai madafar daban-daban ce. Akwai wadda ake girkin da ma'aikatan gidan ne suke ci, akwai wadda na baƙin da suke zuwa ne, sai kuma masu girka wa Asal abinci daban, dan haka Nana na cikin masu yi wa Asal girki.
Sosai matar nan ta ƙara jan kunnen Nana, a kan ta kula da kanta, dan muddin aka samu matsala ba za ta sha ba.
Nana a ranta ta ce "Ji wata jaraba, da wannan wahalar mutum ya girka abin da zai ci mana da kansa."

Kwana huɗu da fara aikinta, ranar Alhamis da daddare, tana shirin kwanciya, aka ƙwanƙwasa ƙofar ɗakinta.
Ta tashi ta buɗe, ta ga shugabar girke-girke ta gidan, kamar yadda aka gabatar mata da ita a baya.

"Ki sako hijjabinki, ki biyo ni"

Nana ta saka hijjabinta ta fito tana tunanin ko lafiya.

Harabar gidan matar ta yi, Nana ta bi bayanta, ta nuna mata mota. Nana ta kalli dare ya yi kuma an zo da mota an ce a tafi da ita.
Cike da mamaki Nana ta shiga motar, sai ta ga mutum uku, da su ma duk tare suke aikin girkin a gidan a cikin motar.

Ta shiga ta zauna, ita ma shugabar ta su ta shiga. Nana ta gaza haƙuri ta ce "Dan Allah ina za mu je ne?"

"Za ki gani"

"Eh amma na ga dare ne fa"

"Idan mun je za ki ji dalilin fitar" Nana ta yi shiru tana tunani, ita ba ma wannan ba, hankalinta ya koma kan rashin samun damar kiran waya da ba ta iya yi, kuma ba a kiranta ya shigo. Dan sai da ta tambayi ɗaya daga cikin masu aikin, ko matsalar daga wayarta ne, ta ce mata kar ta kuskura ta bari ma a san tana da waya, dan sai an ƙwace ta.

Tana ta zancen zuci, har suka isa inda aka tsaya suka sauka, aka shiga da su.

Asal ce a tsaye, tare da dattijuwar matar da ta saka ta raka Nana masauki. Suna tsaye a cikin ɗakin Nanan.

Asal ta ce "Zazzage mini kayanta, ki ɗaga mini komai ɗaya bayan ɗaya"

Ayshercool
71


Ɗaya bayan ɗaya, aka din ga zazzage kayan Nana. Aka zazzage su tsaf aka Azzage jakar da ta zuba kayan turarukanta da mayukan shafawa, duk ba ta ga wani abu ba, sai jakar gurin sarkin baka.
Ta nuna jakar ta ce "Mene wannan?"

Ta ɗago jakar ta ce "Jaka ce"

"Buɗe ta ki zazzage na gani" Ta fara kokowar buɗe jaka, amma babu gurin da zata buɗe ta. Kawai ta ce "Shikenan" ta fice ta bar ɗakin.

Can gurin kuma Nana tara su aka yi, su shida. "Na san za ku yi mamakin dalilin da ya sanya aka kawo ku nan, to zaɓo ku aka yi saboda an yarda da amanarku, ana daf da yin taro da Sultan da kuma dukkanin Imams na gidan nan. Dan haka ku aka zaɓo za ku yi girki na musamman. Amma ku sani kamar yadda wasu sani wasu ba su sani ba, muddin aka samu wata matsala ko ƙware wani ya yi, a sanadin abincin da ku ka dafa, to ku tabattar da rayuwarku za ku biya. Dole ku yi taka tsantsan ku kula." Matar ta yi maganar daki-daki.

"In sha Allah" suka amsa mata.

Ta ce su bi bayanta, suka je wani ƙaton guri, ɗauke da nau'oin kayan masarufi kala-kala. Ta yi musu bayanin da su ne za su yi amfani su yi girkin, sannan ya zama dole su sanya wa bakinsu sakata su yi aiki cikin amana, kuma kada wanda ya san su aka zaɓa da za su yi wannan girki. Nan ma suka amsa, ita dai Nana sai kallo da ido, dan abubuwan sun daina ba ta mamaki, wannan maganar ce ta sanya aka taso ta a daren nan, sai ka ce wanda za su girkawa wasu waliyyai abinci.

Ko da aka mayar da su Nana gida, ta sha mamakin ganin kayanta a hargitse a cikin ɗaki. Da mamaki ta ƙarasa kan kayan nata, ta ɗaɗɗaga.
Cikin takaici Nana ta tashi ta fita, sai dai kowa ya tafi makwancinsa ya kwanta. Kawai ta ji taku a bayanta. Ta waiwaya ta ga Asal na fitowa.

"Har kun dawo kenan?"

"Eh, sai dai na shiga ɗakina na tarar da an caje mini kayana an zubar da su a ƙasa, ban sani ba ko kina da masaniya a kan haka?"

Asal ta ce "Me yasa ki ka zarge ni?"

"Saboda na ga ba a gudanar da komai a gidan nan sai da izninki"

Asal ta yi murmushi ta ce "Haka ne, kina da kaifin ƙwaƙwalwa kamar yadda na yi tsammani, ni na saka aka caje kayanki saboda na san da wa nake zaune"

"Me yasa ba ki tambaye ni abin da ki ke buƙatar sani ba, za a caje mini kaya"

"Saboda a ƙarƙashina ki ke, a gidana ki ke zaune dole na sani idan da wani abu da ki ke tattare da shi na cutarwa"

Nana ta ce "Kin yi kuskure, dan ina zaune a ƙarƙshinki, ina da personal life ɗina, da 'yancin adana abin da yake sirrina, bai halatta ki bincikar mini kaya a bayan idona ba. Yaushe na san ki, da zan ƙulla wani abu da zan cutar da ke? Kina gudun hakan ki jawo ni ki ka kawo ni?"

"Yi ƙasa da muryarki, kar ki kuskura ki ɗaga mini murya, kin san matsayina? Za ki iya janyo wa kan ki gagarumar matsala muddin ki ka ci gaba da yi mini magana ba ladabi"

"Babu ruwana da matsayinki, da koma me za ki yi mini, kar ki sake shigar mini ɗaki ki taɓa mini kaya, idan kuma ki ka ci gaba za ki iya binciko abin da zai hana ki sukuni, idan kin ji ba ki yarda da ni ba, ki sallame ni na koma inda na fito, ba zai yiwu na zauna da ke kina zargina kuma kina cin dunduniyata ba."

Asal ta bi Nana da kallon mamaki, amma ta danne mamakinta ta haɗiye fushinta, ta ce "Gaskiya ne, kin yarda da kan ki har haka kenan? Shikenan amma idan na ga akasin abin da ya fito daga bakinki, za ki sha mamakin abin da zai faru"

Nana ta yi mata banza, ta koma ɗakin nata, ta gyara kayanta tsaf.
Ta kulle ɗakin ta koma ta ɗaga katifar ɗakin, ta ɗaukko wata jaka, a cikin jakar ta zuba duk tarkacen kayan Sayyid. Ajiyar zuciya ta ts yi, da tayi wannan dabarar ta ɓoye su. Haka kurum take jin kayan na buƙatar sirri.
Ta nemi guri ta kwanta tana sauke numfashi a hankali, tana tunanin yadda rayuwa ke ta jujjuyata.

*****

Shukura na zaune a ɗakinta tamkar zuciyarta za ta yi bindiga ta fito, Sagir ya buɗe ƙofa ya shigo ɗakin. Kallo ɗaya ta yi masa ta sunkuyar da kai. Tuni t yi shirin kwanciya baccinta, sai ƙamshin turare take zubawa.
Ya sha manyan kayansa, hannunsa riƙe da baƙaƙen ledoji. Ya zo ya zauna a kusa da ita, tamkar ta kifa masa mari haka take ji.

"Wai har kin yi shirin kwanciya? Na zata zaku gaisa tukuna sai ki kwanta" Mugun kallon da ta yi masa ya sanya shi haɗiye maganar da ya yi niyyar yi.
"Ga wannan naki ne" Ya yi maganar yana ajiye mata ledojin hannunsa.
Ba ta kalli kayan ba, kuma ba ta motsa ba.

Ya matsa kusa da ita,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login